shaye,shaye abokanka inkuma ba hakaba to tsohuwar Nan da jikarta sun maka wani mugun abin sun kaika an haukatama zuciya akansu shikenan baffah zamu rasa nabil ai Dole naje har gida na ci mutuncin tsohuwa iya
Nabil yace wlh daddy karma kafara inhar kana sona to karka yiwa iya komai Dan ran shatuwa ze baci intaji Kuma zata dada guduna Nima Kuma yanzu inasan iya kome zatai min bazan kulataba Nima kakatace nidai abinda nakeso da Kai ka tayani Nemo shatuwa mukuma je mubawa iya hakuri mubawa baffah hakuri mukuma bazama neman matata adu inda take aduniyarnan
MINISTER wani gumine yake ta keto Masa duda sanyin esin da ke wajan zare Ido kawai minister yake tayi Yana kallan nabil
Me hajiya Fatima zatayi inba dariyaba har da rike ciki tasaki Buda tace Allah ngdma ranar muke jira yau gashi tazo Allah karabamu da abin kunya ko wana irine Naga yanda zaayi wajan zuwa gurin iya ba da hakuri da wajan baffah da alhaji yanzu Dan Allah bakaji kunyaba tin ba a je ko inaba ai ga abinda muke ta fadamaka Ni da baffah gashi kashiga fadansu yanzu zaka dawo kaji kunya gashi dai yaro yadawo yace yanasan matarsa saura iya ita Kuma zamuga yazatayi garama ita tsohuwace akwai shiruftun tsufa Kai kuwafa ai Babu wani tsufa da kayi Allah kadawo da shatuwa lfy muyi kallo muna daga gefe yanzufa tinda kana san danka seka Rakashi neman shatuwa da bawa iya da baffah hakuri du kuma se kamanta abin kunyar da kayi nasan yanda San nabil yarufema Ido ko cewa yayi kabawa shatuwa hakuri Bata zakayi ko to karma ku sakoni Dan bansan komaiba Akan batan shatuwa shine mijinta shi zefi kowa sanin inda matarsa take to mawai yaushe ta Bata ai kullin in yazo se na tambayeshi ya matarsa se yace lfy take har sako nake bashi yakai Mata du wayake kaiwa
Nabil zuwa gaban hajiya Fatima yayi yace mommy Haka mukayi da ke kinface kema kina Sona Dan Allah in kinsan inda matata take ki fadamin ko wani abinda na keyine bataso du ki fadamin wlh Zan Dena
shi dai minister har yanzo kallan nabil yake ko hajiya Fatima yakasa bawa amsa
Hajiya Fatima tace gaskiya abubuwa da dama bataso kakeyinsu Kuma ta fadamin Allah sarki har kuka take abin tausayi ko akansu ta guduma Allah masani Kuma ai badan Allah zaka denaba kaga Kenan in kaganta ta dawo zaka koma ruwa kaci gaba da halinka da bataso Kuma dada guduwa zatayi
Jiki na Bari yace wlh mommy nayiwa Allah alkawari Zan Dena danshi badan itaba tinda du kema kin fadamin Babu Kyau abinda nakeyi kecefa abokiyar shawararta kibani shawarar yazanyi na gyara ammafa wlh ko Ina iya take Sena Nemo gidanta na fada Mata halin da ake ciki dan itama ta Hura muku wuta kufito Mana da ita aini yau masifar iya ikwan Allah zata yimin Rana Kuma yanzu ita zanna gani inajin Dadi azaman shatuwa kafin aganta
MINISTER hannu binbiyu yasa yai tagumi Yana Jin ikwan Allah
Hajiya Fatima in takalli minister taga yanda yake ta raba Ido ga gumi na ta keto Masa dariyace take dada kamata Babu halin yi saboda nabil Kar yaga tana ta dariya yadau du maganganunta azaman Wasa ko yaudara zega Kuma tasan inda shatuwa take Dan Haka ta hade Rai ta nuna batasan komaiba
Tace Ni yanzu nabil azamana na mahaifinyar,ka Kuma me baka shawara Zan baka wasu shawarwari da zasu anfaneka Amma seni da Kai
Nabil yace mommy Ni yanzu nakeso muyu mgnar muje ko dakin,kine
Tace to tashi muje
Nabil yace daddy muna zuwa kaima da mgnar da zamuyi da Kai Kuma gobe kashirya mazagai zamu tare wajan iya da baffah
Hajiya Fatima da nabil daki suka shiga bayan sun zauna
Tace nabil shawarar da zan baka itace ka koma isilamiya cikin biyu ayi Daya ko anemo maka malami Yana koyamaka karatu agida ko kashiga ta malam liman da ke unguwarnan daga magariba ne da Isha akwai Kuma na bayan sallar Isha zuwa karfe goma nadare kazabi Daya kana zuwa karkayi girman Kai ko wata kunya Babu kunya wajan neman ilimi daga Ni har shatuwa bamasan halayanka da kakeyi nafarko maganar Yan aikin gidannan kacire musu dokar in sun ganka suna durkusawa har se kabar wajan kacire wannan dokar in sun ganka Kuna gaisawa cikin mutunci da girmamawa Amma Banda wannan durkusan har kasa Babu Kai Babu Kuma korar wani Dan aiki dake gidannan ko karkashinka Kuma wayanda ka Kora ada ko kabatawa Rai a Yan aiki du kabisu kabasu hakuri Wanda kaga yadace kayiwa alheri kayi Masa se maganar gudu da mota atiti babushi yanzu kudena Kai da yaranka kudena daukan hakkin talakawa Kai da su yanzu se girmamawa da Basu sadaka Kuma wannan kudin da kake rabawa abokanka suna aikata sabon Allah da kudin kadena ka koma rabawa talakawa maganar Jin kide kide du kadena ko karage ka koma Jin karatun Qur'an zuciyarka zatai sanyi zaka rage zafin zuciyar da kake dashi du in kashiga isilamiya zakaji waazi akai Kai abubuwa da dama insha Allahu du Zan na fadama ahankali kadaure kadena kazama me adalli da hakuri ga kowa kaji nabil kakoma mutunta Mata da darajasu kadena cewa ka tsanesu
Yace to mommy du naji Kuma zanyi isilamiyar ta malam liman zan shiga nafi karuwa da wasu abubuwan sosai
Tace yauwa nabil Allah yaimaka albarka
Nabil yaji mgnar hajiya Fatima yafara zuwa isilamiya hajiya Fatima da kanta taje har gidan malam liman Tai Mai bayani Akan nabil zefara zuwa isilamiyarsa ta maza magidanta da matasa Tai Mai bayani halin da nabil yake ciki Kuma Yana yawan temakawa da yawan yin waazi Akan zamantakewar Dan Adam ko malam liman yaji Dadi da Jin bayanin hajiya Fatima Akan nabil
ranar da taje ranar nabil yafara zuwa da magariba
hajiya Fatima taji Dadi sosai yanda taga nabil yafara canja halayansa ko Jin Waka yarage sawa yanzu ko abokansa basosai yake shiga harkarsuba har gida suke zuwa nemansa Amma Haka zasu hakura sukoma jiki bakwari gashi yanzu yarage yiwa abokan nasa bushaSha kamar da ko yajema baya Basu komai baya Kuma dadewa Yan aikin gidansu kuwa sunsamu yancin kansu Babu takura tsakaninsu da nabil Babu durkusawa har kasa ga kyauta da yake ta yawan yimusu kowa yaga canji Akan nabil mutanan garima sun sheda canjawar nabi almajirai in yafita Haka yake raba musu sadaka Dan Allah yadawo Masa da shatuwa lfy wayanda da ko almajirai bayasan ganinsu karatu kuwa alhamdulillah Yana fahimta sosai daga anbiya Masa zerike ga yawan waazi da malam liman yake tayi Kuma Yana shiga kunnan nabil sosai Kuma Yana anfani dashi motocinsu yanzu in sun taho ako Ina memakwan kade,Kaden da akeji da amotocin yanzu kuwa karatun Qur'an akeji natashi in adaki yake ko afalo abin da yake sawa Kenan karatun Qur'an ko gudu da motoci in Yana ciki yanzu andena yanzu kowa yaban nabil yake da samasa albarka ko sarkokin da yake sawa da irin shigar da yakeyi da su fentin kansa yanzu du yadena zarya kuwa amazagai Babu adadi wajan baffah Akan ya temaka ya dawo Masa da shatuwa ga ciwan mararshi yatashi sosai saboda yawan tinanin shatuwa da tinanin garar da yakwasa awajanta hajiya Fatima yanzu tafara tausayin nabil garama yayi sosai yakoma shuru shuru Babu wannan zafin ran da akasansa dashi
da nabil yaga baffah baze bashi amsaba Akan shatuwa Kuma baze dawo da itaba yayanke shawara ko baffah be saniba bare minister yaje ya Nemo gidan iya bakaramin rashin mutunci iya Tai masaba Amma be amsa mataba wajema yanema yazauna Babu korar da batai Masaba Akan yafice Mata daga gida nabil ko akansa yaki kulata Kuma yaki tafiya Dole ta sauko ta saurareshi aikuwa nabil Nagama fada Mata halin da akeciki Tai tsalle ta dire tace batasan zanceba tahau kuka wiwi Akan se annemo Mata shatuwa nabil da yaga haka yai ta tunzurata tana dada Hawa shima har da tayata kuka su baffah sun batar musu da shatuwa
Iya tace Ashe dandaudu me zamanman wando zaka canja kazama mekirki haka har kafara San shatuwa kaima Ashe dai kaima kyakkyawane haka kaboye kyan da Allah yai maka ka koma kamar matamaza nifa da kashigo ban ganekaba se da umaru yai min bayani yace Kaine tukunna na ganeka aiyanzu Kuma Ni da Kai Babu fada munshirya tinda kanasan shatuwata saura Miss Miss Shi,ai wannan uban naka bashi da mutunci baze Dena abinda yakeba Aishi basan shatuwa yakeba Kuma nasan be damuba da batan shatuwa kabarni dshi du zamu hadu Daman da tamu dashi yanzu dai katashi mutafi wajan usuman naji inda yakai Mana ita Kai Dan Miss Miss ka fadamin gaskiya ko dai ubanka Miss Miss yasai da shatuwa bamu saniba takuma fashewa da kuka Ni wlh da magunan yace na kawo Masa wlh Zan kawo Masa ba se yasai da shatuwa ba kumafa agabanka har alkawari naimai in yafara mutunci Zan tara Masa maguna na kawo Masa har gida takuma fashewa da wani kukan
Nabil du dadamuwar da yake ciki se da yafara dariyar maganar iya Yana mamakin karfin Hali irin nata agabansa tana zagemai uba
yanzu damuwa taiwa minister yawa saboda ganin halin da nabil keciki na damuwa gashi minister najin kunyar zuwa wajan baffah yabashi hakuri akan batan shatuwa haka Dole yacire kunya yaje har gida yasamu baffah yabashi hakuri Kuma ya rokeshi Akan Dan Allah in yasan inda shatuwa take ya dawowa da nabil ita
baffah dariya shima yafara Yana kallan minister
Baffah yace Kai sani ko dai mafarki kakeyi ko da yake ai ba kunyace da kaiba in dai Akan nabil ne komai ma zaka iya kaga abinda nake gayama Kenan yanzu gashi yadawo San matarsa Yana ta nemanta yashiga damuwa gashi kaima kadamu kazo kana tayashi neman matarsa Amma da idanka yarufe kadinga rashin mutunci da abin kunya yanzu kaima cewa zakayi ka goyi bayan auran shatuwa da nabil ko Dan baka da kunya kariga du kagama zubar da girmanka na uba a idan shatuwa yanzu ai kadada hankali kakuma dau darasi Akan abinda yafaru Nan gaba San nabil yakuma rufema Ido wlh Fatimace me San nabil bakaiba yanzufa ko shuryuwar nabil baka saniba Ni nasani baka da lokacin tarbiyarsa se ta munamai gata yanzu da ba Fatima mahaifiyarsa da kacuci nabil har karshan rayuwarsa tashi kabani waje se nayi shawara Akan mgnarka
Haka minister yadawo Abuja jiki Babu kwari
Iya ce da nabil sukazo har gida wajan baffah Kan mgnar shatuwa iya nazuwa tafashewa baffah da kuka tana ruwan masifa yafito Mata da shatuwa Dan Miss ne yazo yagaya Mata shatuwa tabata Kuma yasan komai har da hajiya Fatima nabil na gefe Yana Jin Dadi tinda iya tasa Baki fole afito Masa da matarsa
Baffah hararar nabil yahauyi yace to kaji Dadi ka fado Mata hankalinka se yakwanta Mara kunya Daman matar taka tana da Rana haka ban saniba ai da cewa kayi baka Santa ko kamanta na tinama to inkai yanzu kana santa itakuma in tace Bata Sanka Naga yanda zakayi Dole ai ka saketa
Kunne nabil yatoshe yace bazan iyaba wlh Babu saki Ni da ita Kuma jikina yabani itama yanzu tana sona Dan Allah ka dawomin da matata baffah wlh ba nabil din da kasani bane da
Baffah yace bani da lokacinka se kutashi mutafi Abuja wajan Fatima tinda yau in Allah Yayarda komai zezo karshe kabar mutane su huta da Kai da kakar taka Wai iya yaushe Kuma nabil yazama jikanki kuma kuka Dena fada
Tace ai yanzu mun shirya Kuma shinake gani azaman shatuwa tinda kun batarmin da shatuwa Kuma shi ne mijinta Ashe Dan Miss Miss na da kirki Haka ban saniba bakaga yanda yake yomin siyaiyaba har kudi yake bani su umaru ma hidima yake Tai musu Ashe yafi ubansa miss miss kirki tasa kuka
Shi nabil yanzu kome iya zatace akansa shi da ubansa baya Jin haushi dariyama take bashi
Baffah da su iya Abuja suka tafi sun Isa lfy minister nagida se ganin baffah da nabil da iya yagani nabil na rime da faggwan kayanta suka shigo
iya Kai tsaye wajan minister taje ta zauna kusa dashi tace to miss miss Allah yadawo Dani Ina shatuwa Ina matar taka Fatima itama Ina Mata kallan me kirki Ashe ka goga Mata mugun halinka ko se wani hararata kake kana zaremin Ido du baze tsorataniba ka fitomin da jikata kawai inma magunan kakeso NASA umaru yatara maka yakawo maka kafito da shatuwa kafin inmaka rashin mutunci
Hajiya Fatima tace yihakuri iya kijira zuwa anjima Zan rakaki inda shatuwa take kici abinci ki huta tukunna kirabu da alhaji Ni da kaina Zan kaiki
yau su Amina zasu dawo gida nanjeria mijinta yagama kwas dinsa har ma kwanaki suka Kara bayan wata shidan da sukayi zokuga murna wajan shatuwa ga kiba tayi ga Kyau takara tadada fari sosai ga turanci tanaji yanzu sosai ga yanzu in anganta bazaace tayi rayuwar kauyeba misalin karfe takwas na dare jirginsu ya iso nanjeria hajiya Fatima ce tatura direba ya dauko Amina da shatuwa Kai tsaye gidan minister aka shige dasu shikuma mijin Amina da yaranta gida suka shige se Amina Taraka shatuwa zata shige gidan nata mijin
Lokacin da suka dawo nabil be dawo daga isilamiyaba iyace da minister da baffah kadai agida shatuwa da taga iya har da kuka iyama kuka tafafa tana mamakin girman shatuwa da kyan da takara iya bakin masifa yamutu se murna ake tayi jikalle tadawo
Tace Allah sarki nabilu Yana Ina yazo yaga shatuwa ta dawo yaro Dan albarka ai ingaya Miki Dan miss miss yajansa yanzu du baya masifar Nan da yakeyi
Takalli Amina kema yannan yar Ina yabanki sallah Zaki kasa alwala Ashe kema kinbi halin Miss Miss har dake asace shatuwa
Kafin Amina Tai mgn Sega nabil yashigo dauke da sallama abakinshi cikin nutsuwa yake tafiya gawani kamshin turaransa da yacika wajan kansa akasa yashigo bema kula da suwaye afalanba shatuwa Ido takura Masa tashi tayi tsaye tana kallanshi Yana dago Kai sukai Ido hudu da juna
New writer's
Hakan Take
*Husba'ahfama*❤👸
*'YAR KWALLIYA*🥳💃
👝👝👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝
👠👠👠
👝👝
👠
💄💅 *DAN MINISTER* 💅💄
🦚🦚
Written by *Husba'ahfama*
*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*
Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*
15-16
Ido suka hau mustsikawa suna dada kallan juna
nabil yace ko dai mafarki nakene ban saniba
Shatuwa itama wajan Amina takoma da sauri tace anty Yaya nabil ne wannan Naga Babu shigar da yakeyi ajikinshi ko sarkar Babu
Dariya dukansu suke musu Amina tace nabil ne shatuwa Kinga yacanja ko
Tace eh anty
Rada akunne Amina takewa shatuwa kardai kimanta da du abinda nagaya Miki kifaja ajinki kafin ki saki jiki dashi Amma Naga ke kanki rawa yake niyar ba da kanki kikeyi ke ko Ina se kin nuna wautarki ta ke rikwan kakace
Kafin shatuwa tayi mgn
Nabil yakaraso wajan shatuwa yasa hannu yatabata yaji dagaske itace ba mafarki yakeba hannu yabude almar tazo shatuwa Amina takalla taga Amina na harararta ai shatuwa Bata da mu da gargadin da Amina take mata da Ido na taja ajinta taje da sauri tafada jikinshi suka rungume juna suna dariya
Nabil yace Aisha ina Kika shiga nake ta nemanki meyasa Kika gujeni kinsan wuyar da nasha akanki kinsan halin da nake ciki saboda rashinki Ina kikaje du tsawan wannan lokacin nake ta nemanki waye yasaceki
Shatuwa tace ba anty Amina bace ta daukeni ta gudu Dani america baffah da mommy ne suka sata ta gudu Dani Wai Dan muna fada Ni da kai yanzuma se da taga nayi fishi da ita na dameta da kuka sannan tadawo Dani har cemata nayi yanzu mungirma mundena fada Ni da Kai Amma anty Amina Bata yardaba har da yimin fada tafashe da kuka
Amina hanu tadora aka tazamo daga Kan kujera ta zauna akasa tace shikenan angudu ba a tsiraba goyan Kaka Kenan akwai wauta daga temako se yazama lefi
Nabil ransa yabaci kallan su amina yafara Yana rungume da shatuwa Yana rarrashinta yace yanzu Ashe Daman du rokwan da nake Tai muku kunsan Inda matata take kukaki ku temakeni ku dawo min da ita se da itama ta dameku tukunna kuka dawo da ita anty Amina meyasa kikai Mana Haka kinsan halin da Dan uwanki yashiga akan hakan da kikayi baffah har da Kai mommy kema haka wlh daga yau Kar Wanda yakara dauke min Mata ba da saniba Allah bazan yardaba yishuru aishata gidanmu zamu tafi yanzu rabu dasu daga yau Kar wanda yakuma zuwa yace kizo kuje wani wajan ba da saninaba karki Kuma yarda kibi kowa kinji
Tace to Kuma ai kace katsani Mata baka sansu Kuma Nima kace baka Sona Ni bazan bika gidan kaba bayan baka Sona Kuma bakasan Mata Ni awajan mommy Zan zauna ko anty Amina ko nabi iya mutafi mazagai tare
Muryar nabil narawa yace haba Aisha kuskurene ko Ada da nake fada rashin sanine Amma yanzu nagane gaskiya wlh yanzu nasan darajar Mata Kuma Ina girmamasu ako Ina suke ta dalilinki nasan darajar Mata aduniya nasan Kuma wacece mace kema wlh Ina sanki Aisha Ina kaunarki bazan iya rayuwa in Babu keba kin Zama wani bangare na jikina karki min Haka Dan Allah ki temakeni kiyarda mu tafi gida yanzu karkisa su baffah suyi Mana dariya daddy da iya kusa Baki ku tayani bawa Aisha bawa
Shatuwa tace Babu ruwansu wannan tsakaninmune Suma ai shedane agabansu kasha fada baka San Mata ba sau dayaba ba sau biyuba
Kwacewa tayi daga jikinshi ta haura sama da gudu tana kuka aminace tabi bayanta da sauri nabil shima binsu zeyi
baffah ne ya hanashi binta yace nabil zauna muyi mgn da Kai Kar kadamu zamu tayaka Bata hakuri zata hakura katsaya yanzu muyi mgn dakai kasan shatuwa na da gaskiya ko tinda kowa yasan akidarka takin du wata mace arayuwarka Kuma daga Kai har ita kunsha fada a gabanmu kun tsani junanku Dan Haka muma muka rabaku muka dauke shatuwa ka Dena ganinta Kuma mu munzata temakwanka mukayi tinda bakasan