Dan Minister 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mrs Nashe Category :  Love

Chapter   3 / 12

6K to 9K   out of 35K words

otal Zan kwana muna da cashiya da bazaniba Amma saboda kun batamin Rai Dole nabar muku gidan Wai yau meyake faruwa da nine ake tabatamin Rai gobe America Zan tafi nahuta da nanjeria gabadaya Dan nasan wannan tsohun zeyi kirana naje Kuma bazaniba Nan da sati biyu ma muna da fatin da zamu agidan gonarka na mazagai

tashi yayi yaje yashirya yai ficewarsa ko sallama bewa iyayan nashiba yai ficewarsa yabarsu zaune afalo

Hajiya Fatima tace kunfi kusa alhamdulillah tinda har mahaifinka be bariba bare Kai kaga tafiyata ai bani da tacewa akan Dan gwal tashi tayi tabar alhaji sani Tai tafiyarta abinda zemata anfani

Alhaji sani kanshine yadau caji Yana ta tinanin yanda ze yiwa nabil aure saboda bayaso yarasashi afili yace nabil kayi hakuri banaso narasaka Dan Zan shiga wani Hali kilama Nima nabika Dan bazan jure rashin ganin,kaba nabil yanzu menene abinyi ita Fatima Ina zuwa wajanta zatahau gayamin bakar mgn tahau yiwa mutane waazi Zan ta rarrashinka nabil har seka yarda da mgnar aurannan

Yau nabil yadawo daga America satinsa biyu Acan shi da abokansa beso dawowaba saboda fatin da zasuyi na murnar ranar haihuwarsa a gidan gona na mazagai zaayi Dan Haka yadawo shi yace anan yake so yayi shagalin murnar ranar haihuwarsa saboda San gidan gonar da yakeyi kwansa biyu da dawowa aka hada shagalin

yau akeyin taran yagaiyaci manyamanyan abokansa du zasuzo bakaramin kudi akakashe awannan taran murnar haihuwar tasaba fadama Bata bakine du wannan abinba akeyi hajiya Fatima da malam usuman kakan nabil du Basu saniba taro yayi taro kowa yazo shikadai kawai ake jira motocinsane suka jero Akan layi sababbi dal alhaji sani ne ya canjamai su motocin masu dankaran kudi daga kasar waje aka kawosu shigarsama tawannan ranar daban take Haka motocinnan suka shigo garin mazagai dagudu suna badawa mutane kura kowa se kaucewa yake lokacin shatuwa da zugar kawayanta sunfito zasu Wasa sukazo zasu shige tagabansu motocin saura kadan su buge shatuwa akwai wani ruwa dake tare ahanya takai motocin sukabi tacikin ruwan gabadaya wannan ruwa yabatawa shatuwa jiki motar har tana gogarta shatuwa seda tafadi kasa ta kurje abin yayi mugun batawa shatuwa Rai motar da nabil yake ciki ita tafi ballatsawa shatuwa ruwa ko su tsaya suka shigesu warsu dagudu

Abin yamugun konawa shatuwa Rai tace Kan uba wayannan suwaye yau senaga ko suwaye musamman wannan motar da tafi kowacce Kyau aciki wlh bazan yardaba Sena Rama yau zasuga mezan musu

Kawayan nata sukace Kai jikan faffah usuman ne wlh karki yarda sekin Rama muje murakaki muma zamu tayaki

Dagudu sukabi motocin har motocin suka shiga gidan gonar ahankali su shatuwa suka faki idan mutane suka shiga gidan gonar Suma Babu Wanda yakula dasu

nabil aka budewa kofa yafito habawa Nan guri yadau shewa anamasa oyoyo su shatuwa Baki suka saki suna kallan ikwan Allah namiji suka gani da wata shiga Wanda Basu santaba harda su sarka yahade Rai sewani Shan kamshi yake

Me shatuwa zatayi inba dariyaba sauran kawayantama dariya suka fara nabil jiyayi kamar anamasa dariya juyawa yayi bega kowaba cigaba yayi da tafiya wajan da aka tanadar Masa Dan zama

Anfara gudanar da shagali du su shatuwa nagani wajan tayoyin motar da nabil yafito ciki shatuwa taje dakanta tanemi kusa ta fanfasa duka hudun bayan tagama Kai tsaye wajan nabil tadosa tabayanshi taje da ruwan kwata dauke ahannunta acikin wani gwangwani tabayanshi Tatsaya

tace Kai Dan daudu rabi aljani rabi namiji rabi Dan daudu juyo kaganni nicenan shatuwa masifa tsokana jikar iya ikwan Allah kowa yaci tuwo Dani Miya yasha

Nabil cikin mamaki dajin maganar shatuwa yajuyo ai shatuwa batayi watawataba tajuyemai ruwan kwatarnan akansan da jikinshi

Tace baamin ban ramaba da yau banrama abinda kaminba dako bacci bazan iyayiba saboda takaici gababa in kazo garinran in kaganni kakara watsamin ruwa ka bugeni nafadi su jinmai kuyi Masa Wakar danace zamuyi masa

Nan suka faramasa Waka dandaudu meshigar Mata rabi aljani rabi namiji Dan daudu matamaza meshgar mahaukata kowa yatabomu semun Rama katabo shatuwa jikar iya ikwan Allah

Dan mamaki da takaici wata Kara nabil yasa yaikansu dagudu zedaka kallone yakoma kansu kowa na mamakin meya hadasu Kuma yaakai yaran suka shigo wajan dakyar Nabil yakama shatuwa sukuma yaransa suka Kama kawayan shatuwa kida nabil yasa aka kashe

Nabil yace yau Wana irin hukunci zan muku yau me zan muku nahuce ni kuka batawa ranar haihuwata ke Yar kyauye mezubin mahaukata nikika yiwa haka da ruwan kwata Kika batawa jikina kusake Wakar da naji kunayi min

Shuru kawayan shatuwa sukayi suka kasa mgn saboda yanda nabil ya tsoratasu dukansu jikinsu rawa yake Dan sun tsorata dashi sosai

Shatuwa tace au Wai tsoransa kuke Amma kun bani kunya wannanne zebaku tsoro Toni Bari naimaka dandaudu meshigar Mata rabi aljani rabi namiji nandaudu matamaza kowa yatabamu se munrama
nice shatuwa

Kafin takarasa nabil yadauketa da wani mahaukacin Mari Dan bakin cikin abinda Tai Masa yarasa wana kalar hukunci zemata hannu yasa yashake Mata wuya menai muku meyasa Mata kuke Bina kintaba ganina a Ina Kika sanni sekin fadamin meyasa Mata du inda naje se sunbini se Kuma sun batamin Raina kifadamin Kona sumar da ke meyasa Kika batamin ranar haihuwata kinsan dogwan burin da nadauka Akan wannan ranar kinsan daga Ina nadawo Dan wannan ranar inajin kwatar da aka zubamin nasan wlh Babu meyimin haka se mace Ni bana shiga harkarku Mata Amma ku se kun shiga tawa meyasa kifadamin

Shatuwa takasa mgn Dan azaba se Ido da take zarewa Dan azaba sakinta yayi yakama hannunta na dama yamurde se da hannun yaikara ya tambatar yakarya hannun shatuwa sannan yasaki hannunta

wani mahaukacin Kara shatuwa tasaki Dan azaba tace mugu maye ze kasheni Daman matamaza dandaudu nada karfi haka kasheni zakayi da kakemin wannan tambayar Ni Ina nasani ni kasan mekamin dabaka tsokaneniba da bazan biyoka naramaba ka karyamin hannu wlh Nima Sena karya naka ko Nan gabane ta karasa mgnar tana mai da numfashi Dan azaba

Kuma Dan taurin Kai irin na shatuwa bakinta yaki mutuwa rashin kuya take tamasa shikuma Yana dada tinzira zuciyarshi na dada baci kowa Ido yazuba musu anrasa me Basu hakuri saboda tsoran nabil da bakar zuciyarshi Dan in ransa yabaci abin bakyau baa iya rarrashinsa

Nabil yakalli yaransa yace mekuke jira da wayannan mahaukatan kudakarmin su harse sun jigata kekuma bakinki yaki mutuwa ko to Bari kiga mezansa aimiki yanzu waiyau Ni nabil nine nataba mace haka da hannuna Amma yarinyarnan kin cuceni kingama Dani natsaneki kece mace tafarko da nafara tabawa da hannuna Kuma insha allahu kece takarshe Sena barmiki tarihi yau kamar yanda Kika barmin ya kalli yaransa kubarsu Haka ai sunyi sanyi ku je ku kwasomin buhunhuna acan dakin kukawomin kuga me zanmusu


Ana kawo buhunhunan yace kubude kufara samin wannan marakunyar da na karya ku kullemin ita kusata abutdin mota ku rufeta ita kadai sauranma du ku zirasu abuhu kusasu abut dasu zamu tafi ni nasan inda zamu kaisu

Andaga shatuwa kenan zaasata abuhu kakansa malam usuman yashigo gurin yaga danyan aikin da jikansa yasa yaransa sunayi cikin tashin hankali yadaka musu tsawa

Yace ku kisankai zakuyi nashiga uku nabil ze jamin mgn zaman garinnan zefi karfina adalilinka rainawa zaku kashe da banzoba mekuke Shirin aikatawa Haka nabil abin naka yakai Haka tinda labari yazomin kashigo garin katara mutane awajannan hankalina yaki kwanciya nace Bari nazo nagani wace tsiyar kake aikatawa Dan nasan halinka Dole sekayi abin fada me wayannan yaran sukai maka har wajan susu ashirin yanzu da ban zoba duka kashesu zakuyi ko Yaya nidai nasan indai akasa mutun abuhu baze shaki iska sosaiba nabil kafadamin mezakai da yarannan ko kafara satar mutane bamu saniba

Nabil yace shikenan hanaruwa gudu kazo komai yakuma baci faffah me yakawoka Nan Wana munafikinne yaje yafada ma meyasa daddy ya sai gidan gona anan yanzu Dan Allah faffah me yakawoka wajannan kokazo kunyatani acikin abokaina wlh faffah Ina raga maka Dan Kai Kaka nane Babu yanda zanyi dakai kasan me sukai min yau kasan wace ranace awajena Kai basanin mahimmanci ranar kayiba bazaka ganeba ko na fadama nifa kasan dokata na tsani Mata banasan Mata meyasa zasu zo su yimin haka Ni Babu abinda zanyi dasu Kano Zan kaisu nayardasu acan Nan yafadawa faffah abinda su shatuwa sukai Masa

Faffah yace nabil meyasa baka da hakuri meyasa kake wulakanta mutane du wannan halayan naka Babu meshi akaf iyalina sekai a Ina kasamo wannan mugun halin kayi kuskuran kula yarinyarnan bakasan itama wacece itaba yanda kake fitinanne itama haka take fitinanniya agarinnan da datayi maka Haka da baka kulataba kazo kafada min ko ka kaiwa iyayanta Kara ko megari Amma yanzu kaga abinda zuciya ta ebeka kayi ka karya musu yarinya kawayanta kasa anmusu mugun duka yanzu da ban zoba Ina zaka dasu kukama masu bin nashi manyan banza se abinda yace muku kuyi kukeyi saboda Kuna karkashinsa ana biyanku kudi acikinku kusan dukanku kun girmeshi Amma anrasa mebashi shawara tagari Dan Kuna tsoransa kace bansan ko yau wace ranace awajankaba nikuwa nasan ko waje ranace yau awajanka ba bikin murnar haihuwarka kakeba yau to nazo tayaka murna nakuma karama biki Daya akan Wanda kakeyi yau Zan karama wani farinciki yanda nasan bazaka taba mantawa da ranarba yanzu da ka karyata me kake nufi kana nufin ka karya banza baka isaba nabil baka karya banzaba kasan karya yarinyarnan me kahadawa kanka ranar auranka ka hadawa kanka wlh yanda ka karyata Kaine mijinta baka karya banzaba yau ka karyataka yau zaka aureta Zan daura maka aure da ita kaga taro biyu kenan Ni nakarama biki Daya Kar Wanda yatafi anan du kubiyomu zuwa gidan megari Dan halartar daurin auran nabil azamanku na abokansa muna gaiyatarku daurin auran nabil sani DAN MINISTER kuzo mutafi

Faffah kanlan mazan da yazo dasu yayi yace Kai kaje ka kiramin umaru baban shatuwa da Kuma iya kakarta suzo gidan megari cikin gaggawa ana nemansu Kai Kuma kaje kataho min da me gyaran karaya zuwa gidan megari

Yan uwan alhaji sani ne wayannan mutanan majiya karfi faffah sasu yayi suka daukarmai nabil cak suka samaishi amota akasa shatuwa itama amota da zugar kawayanta suka ja zuwa gidan megari du abokan nabil da sukazo fatin nashi suka bi bayansu zuwa gidan megari Dan ganewa idansu wannan auran mamakin da zaa daurawa nabil shi

















New writer's


Hakan Take
*Husba'ahfama*鉂ゐ煈�
*'YAR KWALLIYA*馃コ馃拑

馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹
馃憼

馃拕馃拝 *DAN MINISTER* 馃拝馃拕
馃馃




Written by *Husba'ahfama*


*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*

Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*










5-6













Megari nazaune akofar gida akarkashi wata katuwar bishiya shi da jamaarsa segani sukayi motoci nata jeruwa suna tsayawa akofar gidan shi kallan ikwan Allah suka tsaya yi can Kuma sukaga faffah da yafito awata motar gakuma nabil ga shatuwa du anfito dsu amotar anrukosu zuwa gaban megari ana Haka Sega umaru da iya Suma sun iso wajan

Salati umaru baban shatuwa yafara yace wlh nasani shatuwa ce iya kinganiko abin naki shatuwa yaci gaba har da tsokano gari guda Daman ana cewa muzo ana kiranmu akofar gidan megari nasan shatuwa tayi halin wlh badaniba yau iya sedai koke inzaki iya baruwana wlh


Megari yace iya Isa umaru kajira muji meke faruwa ko mu Nan bamusan meyafaruba ganinsu kawai mukayi

Baffah yace du ku kwantar da hankalinku bawani abin tashin hankali bane sosai alheri ne yakawomu dukanmu Nan yanzu megari Ina neman alfarma dakai da liman da mahaifin shatuwa umaru da Kuma wayannan dattawan garin namu da suke wajannan inaso mudan koma gefe Dan da bayanin da nazo dshi zan muku alheri ne insha Allahu Allah yasa ku goyi bayana Amma Banda iya tadan jiramu tukunna in mungama tantaunawa itama akirata afada Mata aji raayinta

Megari yace to alhamdulillah du kutashi muje wayanda yace yanaso suji mgnar

Haka du suka tashi zuwa wani daki dake soran megari du suka samu waje suka zauna

Baffah ne yafara mgn yai sallama yabude da addu'a yace wani abune yau yafaru tsakanin jikana da shatuwa agidan gonar Dana sani Nan yabasu labarin abinda yafaru tindaga farko har karshe Kuma Ni na hango wani Abu alheri ne inhar kungoyi bayana Dan shima jikan nawa irin shatuwa ne ko ma nace yafi shatuwa da mugun Hali Dan tawani wajan halinsu yazo Daya tawani wajan kuma sun banbanta ta halaye Dan Haka hadin da nakeso ayi zezo dedai kowa acikin susu biyun zasu gyara junansu insha Allahu Dan na hango alheri alamarin Ni malam usuman mahaifi ga alhaji sani Kaka ga nabil Ina neman alfarma agabanku malam umaru mahaifin shatuwa yabawa jikana auran yarshi shatuwa adau rashi yau anan kofar gidan megari saboda abinda yafaru tsakaninsu Dan sukara hankali gaba ga tawagar munan nazo da ita ta Yan daurin aure Ina bawa malam umaru hakuri Akan abinda jikana yaiwa yarshi shatuwa insha Allahu ba ze kumaba Kuma Ni malam usuman namaka alkawari agaban su megari nabil da mu damgin nabil zamu rike shatuwa tsakani da Allah har karshan rayuwarta

Megari yace to fa wannan mgn batamu bace takace umaru Dan Kaine mahaifin shatuwa mu shawara ce tamu aciki Kai muke jira umaru muji raayinka akai

Malam umaru yace to gaskiya Ni wannan hadin auran baze yuwoba ban yarda dashiba Dan kowa yasanni agarinnan bawani kudi gareni ba se rufin asiri Kai Kuma baffah kowa yasanka Kai da ahalinka masu kudine barinma danka sani yafi kowa kudi azuriarka Kuma kowa yasan jikanka nibil da irin halinshi in yashigo garinnan itama Kuma shatuwa kowa yasanta da ita da iya da irin halinsu gankiya Ina gudun abinda zeje yadawo kunfi karfinmu ta ko Ina faffah shima Kuma nabil yafi karfin shatuwa ta ko Ina Dan da ba akasar Nan yai karatuba akasar waje yai karatu shatuwa fa da ko makarantar Allo batayiba bare ta boko wannan hadin baze yuwuba da matsala babba in akayishi kagafa faffah tashin farko haduwarsu me yafaru bare Kuma aka hadasu gida daya suyi zaman aure tare Kuma basan junansu sukeba Kuma nawa shatuwa take Bata wani girmaba Ina da dogwan buri akan shatuwa in Allah yabani iko Ina da burin shatuwa tayi karatu me zurfi sosai Kuma inaso in gyara ta ta Dena wannan halin nata Kuma yanzu ya zaayi da iya da ko tinanin rabuwa da shatuwa batayi ba Dan da kauna me karfi tsakaninta da shatuwa bazama ta taba Yarda da maganar aurannanba Dan bazata yarda arabata da shatuwa ba se dai kukira iya kuji nata ko zata yarda

Baffah yace karka damu umaru mudai yardarka kawai mukeso da sa albarkarka amatsayinka na uba awajan shatuwa iya kuma Ni da megari munsan yanda zamuyi mu rarrasheta ta yarda da auran Kai dai in tashigo kayi shuru karkasa Baki amaganar

Yace to shikenan Bari naje na kirata tashigo taji meyake faruwa

Umaru fita yayi yakira iya tashigo megari da baffah sukai Mata bayani nanfa Tai tsalle tadire tace batasan zanceba Babu me rabata da shatuwa bare har ai Mata aure da wani Dan gayu Kuma yanda ya karya Mata jika shima nabil se ta karyashi da kanta tace Ni iya fadan yadawo hannuna Ina yake Dan kwal uban yaro Naga shatuwa du tafadamin abinda yafaru da yaran kanku kirani ku fadamin Daman jira nake kufito na kwashe ubansa da Mari nazata dashi aNan ashema babushi yau Babu me rabani da jikanka usuman wlh banki mu doku Ni da Shiba Dan senayi zaman Yan bori Akan kafarsa shima har se na karyashi Zan tashi ai Naga yaran me kirar aljanu da yakoma kala biyu gaba Daya kamar ba Dan hausawaba Kuma kubude kunnanku kuji shatuwa dai bazan taba yarda da wannan auranba bazaaje akashemin jikata abanzaba afa garin masu kudinnan da naji ana fada shi uban yaran yake abawa dansa shatuwa suje su su sayarmin da ita sukara wani kudin Akan kudin da suke dshi

Megari rarrashin iya yayi da dadin Baki Amma fur Taki yarda

Baffah yace haba kekuwa aishatu Kaka wajan shatuwa ia bakisan yanda nake san shatuwa ba tana burgeni yarinya me kirki ga ladabi ga biyaiya na yaba da irintarbiyar da kika bawa shatuwa Dan Haka naso muhada iri da ke Baki iya tawashe Jin anyabi jikarta tin daganan suka hango alamun nasara ki temaka ki yarda da wannan hadin auran Dan Allah Kuma Kinga yau mukeso ashige da ita gidan mijinta dake Abuja Kuma Ni da kene yankai amarya da ango ke zakije kiga inda akakai jikarki da kanki acan zatayi jinya agidan mijinta zakina zuwa kina ganinta akai akai kema kina tayani ganin irin zaman da zasuyi Kuma in kin yarda da auran har kujerar aikin hajji Zan biya Mana Ni da ke muje mu rokarmusu zaman lfy Kinga har uban nabil da mahaifiyarsa du kikai musu kakar abinda da dansu yaiwa shatuwa Kinga se su jamasa kunne ko

dakyar baffah yasha Kan iya ta yarda da auran tate adaura Allah yabada zaman lfy kowa na wajan yayi murna umaru shima hamdalah yayi shatuwa zatabar gabansu yahuta da ba da hakuri da rigimar iya megari yafi kowa murna yahuta da sharia kullin

Megari yace alhamdulillah iya mungode sosai da wannan alfarmar da kikai Mana yanzu muje nasa ayi shinfida kowa ya zauna agudanar da daurin auran itakuma amarya shatuwa ashigo da ita ciki me gyaran karayar Naga ya iso tin dazu yashigo ya dorata kafin agama daura auran muntura Akira mahaifiyar shatuwa itama tasawa yarta albarka Kan atafi da ita

Nan aka shigo da shatuwa me Dori yadorata tana ihu tana komai iyama na ihu har aka Gama Dora karayar hannunta

Akofar gida Kuma Ana gudanar da daurin auran shatuwa da nabil baffah ne waliyin nabil malam umaru shine waliyin shatuwa baffah hannu yasa a aljihun nabil yaciro damin kudi ya irgi dubu dari biyu yamikawa megari yace ga sadakin shatuwa kowa ya sheda megari yasa hannu yakarba yasa albarka yanunawa kowa baffah yamayarwa da nabil sauran kudinsa

nabil yakoma hoto bakinshi yamutu yakasa mgn gani yake mafarki yakeyi

3 / 12