dashi ba tace Ni banajin yunwa kasan me mommy tabani naci daga dawowata yau har farfesun kaza tabani naci Ni kadai tace Wai ko anty Amina Kar nabawa taci itama tamata nata se da safe kaje ka kwanta tajuyamai bayaya
Murmushi yayi azuciyarshi yace du wayanki Aisha bazan iya barinkiba yau karfin Hali kawai nake tin da naganki ciwan marata yake neman tashi
dakyar yasamu ya lanlabata sukayi nafila yai musu addu'a sosai ta zaman lfy da samun zuri,a tagari Madara me sanyi yabata Tasha dakyar sannan yajata sukaje suka kwanta daganan labari yacanja kala tsakanin nabil da Shatuwa aikuwa tafada Taji awajansa Dan gabadaya yafita hankalinshi Dan azaba jitayi Babu wani bambanci tsakanin ranar farko da tayau dan ta gurzu ahannnunshi tin tana daurewa se da tafara Mai Kuka da magiya sannan yaji tausayinta yabarta Amma ba Wai Dan yagaji da itaba jiyayima gabadaya tafi ranar farko haduwa
hawayene yake tazubo Masa shima a idansa ga wani farin ciki da natsuwa da yakeji azuciyarshi addu'a kuwa tashata awajansa awannan ranar tayarda nabil na Santa sosai Kuma yacanja yanzu yasan darajar mace Dan yanuna Mata gata sosai Wanda Bata taba kawo Haka daga wajansaba wankama shi yai Mata ajikinshi takwana mutsi kadan tayi seya tambayeta menene kome takeso har gari yawaye ranar ko masallaci bejeba agida sukayi sallar asuba tare suka dada komawa bacci
Basu tashiba se da karar wayar kiran Amina tatashesu tace taturo direba yakawo musu abin Kari yabuga kofar su yaji shuru Kuma masu gadi da yaransa sunce sunanan Babu inda sukaje har da tsokanarsa tace ko lfy Baku tashiba ko du gajiyar tafiyace da Shatuwa tayi jiya
wayar nabil yakwashe Yana dariya lokacin Shatuwa tatashi itama se kallan fuskarshi takeyi suna hada Ido dashi Tai maza tarufe idanta sumbatarta yayi yace amaryata takaina kintashi lfy yagajiyar tafiya Yana dariya me zansamu yanzu
Kukan shagwaba tahau yimasa tafada jikinshi tace bayan Kaine kagajiyar da Ni Ni Babu wani abu da zaka samu awajena fishi nake dakai se nakira anty Amina da mommy nakai kararka ka wahalar musu da Ni iya Kuma Naga yanzu kana neman kwacemin ita ko na fadamata bayanka zatabi
Dariya yafara Yana rarrashinta yace yihakuri aishata farin cikina fitilar rayuwata ai in kinyi fishi Dani zanshiga damuwa tuba nake kidince Ni imarki ta iya rudar da mutun yamanta da komai ke ta dabance nagodewa Allah da ban taba hada jiki da wata maceba se ke Kuma insha Allahu kece tafarko kece takarshe ngde Allah da yabani Mata irinki Allah yaiwa baffah albarka da su mommy bazan manta da ranar murnan haihuwata da naje mazagai muka hadu awannan ranar na rike ranar tana da mahimmanci awajena kingama siye rayuwata kinsamar min da Jin dadi da nutsuwar da bantaba jiba arayuwata rufe idanki matata kiga wani abu
Rufewa tayi mukullin mota me tsada yadanka Mata ahannu tare da wata gidan sarkar daham Dan kareriya
Ido tabude taga abinda yasa Mata ahannu kallanshi tatsaya yi tana mamaki takasa ma mgn
Yace kinfi karfin Haka awajena Aisha nadade da sayamiki wannan kyautar se mgnar Fara aikina a asibitin da daddy yaginamin zanfara aiki in mungama cin amarcinmu zan dinga duba bayin Allah Ina temakwansu shima du acikin kyautar da nai mikine da murnar dawowar matata gareni da Jin dadin farin cikin da Kika bani
Shatuwa rasa bakin mgn tayi rungume nabil tayi tana kukan farin ciki tana tamasa ruwan addu'a da gode Masa
Yace ya Isa Haka matar Nabil Bari naje nabudewa Dan Aiken da anty Amina ta turo yakawo Mana abin Kari munbarshi atsaye tin dazu
Soyaiya me tsafta da birgewa nabil da Shatuwa suke gudanarwa atsakaninsu inda suke burge kowa Kuma ake alfahari da su har yawan shakatawa suka tafi cin amarcinmu akasar waje inda suka kwashe wata Daya Acan sannan suka dawo gida suna dawowa ba dadewa nabil yafara aiki asaban asibitin shi da minister yabude Masa Yana aiki sosai Yana temakwan marasa shi mutane na alfahari da shi talakawa nayabansa sosai
Inda lokacin tafiya aikin hajji nayi minister yacika alkawarin da yayi nazuwa aikin hajji da yabiya musu iya ikwan Allah ansha kyauyanci da kokekoke a makka ko Ina za a tana katarin nabil da Shatuwa in iya na wata rigimar ko kauyanci dariya su minister suke Mata sunyi aikin hajji lfy sundawo gida lfy
Basu Dade da dawowaba shatuwa tasamu ciki nabil yayi murna sosai da su minister baffah na alfahari da auran nabil da Shatuwa nabil yasa anrusa gidan iyayan shatuwa anyi musu ginin zamani na masu kudi iya nata gidan daban nabil yagina Mata Yana temakwan Yan garinsu mazagai sosai yanda kowa nagarin mamaki yake yanda nabil yake musu barin kudi Yana temakwan su Kuma baya kyamarsu kawayan shatuwa du Suma anmusu Aure yanzu shatuwa tazama abin alfahari amazagai ko Ina hirarta akeyi ita da nabil ana samusu albarka
Shatuwa taci gaba da karatunta naboko Haka take zuwa da ciki ajikinta inda taci sa,a cikin bame laulayi bane
Finah tananan Akan bakarta na ko tahalin Kaka se nabil yazama mallakinta inda tadau aniyar binbiyar lamuranshi ako Ina yake har Allah yabata sa,a taje har asibitin da yake aiki tafaki idan mutane tashige cikin office dinsa lokacin yafita duba marasa lfy dube dube tafara anahaka wayar nabil Tai Kara yamanta betafi da itaba taga sunan da ke dauke afuskar wayar taga ansa farincikina tana gani tagane matar Nabil ce take kiranshi wani mahaukacin kishine yakamata tana dariyar mugunta tadau Kiran kafin shatuwa tayi mgn
finah tace ke Baki da hankaline da zaki kiramin saurayina awannan lokacin ke mahaukaciyar inace muna holewa Zaki takura mana waikema wacece dazaki dameshi munanan agidan da yagina min muna shakatawar mu kinganmu Nan akwancema yanzu muke bacci yadaukeshi yagama hutawa Dani kinganni akwance Akan fadanden kirjinshi Kai gaskiya my nibil ya iya soyaiya ga zumarshi medadi nabil nawane Ni kadai karki Kara kiranshi ko da Wasa kit takashe Kiran tana dariya yarinya du abinki nasan yau se kin barmin nabil Kuma Dole kice yasakeki
Nabil ne yabude kofar yashigo finah taji tsoro jikinta har rawa yake da ta ganshi fakar idansa tayi ta ajje wayar tahau kukan munafurci har da durkusawa kasa tana rokarshi yatemaka ko aurartane yayi dataga yaki kulata jikinshi tafada tarungumeshi kokarin rabata da jikinshi yafara amma ta cukikiyeshi Taki sakinshi tsawa yake daka mata Yana Mata masifa ko akanta shi tsoranshi Kar wani yashigo yagansu ahaka
Suna wannan halin Shatuwa tashigo arude da tsohon cikinta tana Nishi idanta yayi jajaur saboda kuka Allah ne yakawota lfy ko direba Bata jira yakawo taba dakanta ta tuko mota tazo ganin finah rungume jikin nabil shatuwa tadada yarda da abinda finah tagaya Mata awaya ita Kuma Dan makirci se tadada narkewa jikin nabil tana kukan kissa
shatuwa jitayi kanta na juya Mata silalewa tayi kasa ta sume lokaci guda jini yahau zuba ta kasanta ai nabil rudewa yayi besan sanda yai wurgi da finah ba yasaki wata Kara Yana Kiran sunan shatuwa se da nawaje sukaji da gudu mutane suka shigo Dan ganin meke faruwa aciki har da maaikatan asibitin temakwan gaggawa aka hau Bata aka fice da ita dakin haihuwa dagudu nabil nabiye da su du yarude Yama manta wana temako yadace yabata
yaransama shigowa sukayi dagudu suna ganin halin da ake ciki suka san finah tahada wani makircin tsakanin nabil da Shatuwa kamata sukayi suka Tisa keyarta zuwa waje Daya daga cikin yaransa yace muje mu tsareta har se hankalin oga yakwanta nasan zenemeta Dan akwai sa hannunta akan abinda yafaru
Yaran nabil ne suka Kira hajiya Fatima da Amina suka Gaya Masu shatuwa na nakuda Babu Bata lokaci suka taho zuwa asibitin dauke da Kayan da za a bukata na haihuwa Basu Dade da zuwaba shatuwa ta haihu tasamu Yan uku duka Mata nabil na kanta har tahaihu be yarda namiji ko Daya yakarbi haihuwar matarsaba zokuga murna wajan nabil shatuwa ta haifar Masa Yan uku duka Mata har da kukan murna zuwa yayi yarunggume shatuwa Yana kuka ita kuwa Ido ta rufe ko ganinshi batasan yi itama hawayenne ke fitowa daga idanta
Mejego lfy kalu ta sauka Babu wata matsala angyarata ankaita dakin hutu lokacine sukaga su hajiya Fatima nabil zuwa yayi dagudu yarunggume hajiya Fatima Yana dariya da kuka
Yace mommy Kinga ikwan Allah ko aishata farincikina ta haifarmin yan uku duka Mata asheni bansaniba Mata zan fara Haifa ayarana nafari na nunawa mata tsana cikin rashin sani Allah natuba kakafeni Allah ngd da kabani kyauta Yara Mata har uku
Amina itama Baki yaki rufuwa hajiya Fatima itama haka shatuwa taga gata kamar zasu Mai data ciki Kiran Yan uwa da abokan arziki nabil yahauyi Yana fada musu haihuwar minister da iya sunfi kowa murnar haihuwar minister gidanshi yasa akadawo da mejego da aka sallameta iya gabadaya tadawo gidan minister da Zama tana rainan Yan uku
Shatuwa Taki yiwa nabil mgn du mgnar duniyar da ze Mata bazata amsa maiba nabil yashiga damuwa sosai tin hajiya Fatima Bata gane meyake faruwaba har tagane sharesu tayi saboda mutane se bayan suna zatai musu mgn
Anyi Taran suna nagani nafada nabil da minister sunyi barin kudi asunan Yan uku ba a mgn
Yara sunci sunan hajiya Fatima da Amina da iya ana Kiran me sunan
Amina
ihisan
Me sunan hajiya Fatima ikiram
me sunan iya iman
akayan barka nabil har da lefe yahadowa shatuwa akwati goma shabiyu yace Daman yayi alkawari se ranar da tahaihu in ze hado Kayan barka ze hado da lefen shatuwa amaryar jego ataran suna har da Yan uwan nabil Mata nakasar waje du dunzo Suma sunyi rawar gani Amina yayar mejego da angwan jego ba a mgn Dan tayi bajinta ta kashe kudu sosai wajan hadu Kayan barka hajiya Fatima ma baa mgn baffah akayan barka har da shanu yahado dasu anyi shagalin suna lfy kowa yakoma gidansa lfy iyace tace Bazata komaba se shatuwa tayi arba,in
Nabil ne yasa shatuwa agaba Yana ta rukwanta Yana ta Bata hakuri Yana ranse Mata shi finah ba budurwarsa bace Amma shatuwa Taki yarda ko saurararshi takiyi
hajiya Fatima ce tashigo tace Daman Nima mgn nakeso nayi daku Wai meyake faruwa tsakaninku
Kuka shatuwa tafara Taki mgn nabil ne ya gayawa hajiya Fatima abinda yasani shatuwa tace wlh ba Haka bane mommy Basu labirin yanda sukayi da finah awaya ranar da zata haihu tayi
Ran nabil yabaci sosai yaranshi yakira yace sunemo Masa finah du inda take sukace ai Daman tin ranar da abin yafaru suna tsare da ita zuwa sukayi suka taho da ita har gaban hajiya Fatima da shatuwa da nabil
nabil da Ido yakalli Daya daga cikin yaransa yaciro bingiga yaseta Kan finah dashi Rai nabil yahade yakoma ainahin yanda yake ada yace kiyiwa matata da mahaifiyata abinda yafaru ranar da kikazo office Dina in bahakaba NASA aharbeki wlh
Nan finah jiki nafari tagaya musu gaskiya tace Dan Allah shatuwa da nabil suyi hakuri ita yanzu tadena sanshi Tama tuba gabadaya gida zata koma gaban iyayanta tayi aure Kar suyi Mata komai su barta tasan yanzu nabil yafi karfinta ko da bare yanzu San zuciyane yaja mata Haka
Hajiya Fatima ce tace da yaran nabil kubarta tatafi tinda tagane gaskiya Kuma tafadi gaskiyar abinda yake faruwa Allah yadada shiryata
Haka finah tafita jiki bakwari tana datasani Takoma garinsu
Hajiya Fatima fita tayi tabar nabil da Shatuwa kunyace takama shatuwa tataho tafada jikin nabil suka rungume juna suna dariya yace gaskiya kin wahalar Dani ko murna da godiya Baki barni nanuna mukiba na haifomin Yan uku da kikayi yanzu tinda kin huce se mgnar komawa gidako tinda kingama wanka iyama gobe tace zata koma
Bayan shekara goma shatuwa tagama karatu inda takaranci fannin lfy tazama cikakkiyar Dr tafara aiki a asibitin nabil tare suke zuwa aiki su dawo tare alokacin yaran shatuwa shida bayan haihuwar Yan uku ta haifi maza biyu Mata biyu
Girma yakama nabil da Shatuwa inda su iya baa mgn antsufa sosai da baffah
Rayuwa nabil da Shatuwa suke da iyalinsu cikin kwanciyar hankali da Jin Dadi
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Anan nakawo karshen Dan minister
Abinda yake dedai Allah yabamu ladansa Wanda mukayi kuskure Allah yayafe Mana Allah yasa muyi anfani da abinda ke cikin sakwan
Se Allah yasake hadamu awani saban novel Dina mesuna🤔😜 inda Rai da lfy Allah yahadamu da alheri
Godiya ta musamman ga masoyana a du inda suke Allah yabar kauna
New writer's
Hakan Take
*Husba'ahfama*❤👸
*'YAR KWALLIYA*🥳💃