tasa Mata shatuwa sukuma su suwaiba suke Kiran shatuwa da humaira wani lokacin Suma shatuwa suke cemata Dan iya tace batasan humara suna Kiran ta da shatuwa tinda aka haifi shatuwa duwata kulawarta takoma wajan iya ita taraineta Kuma ita ta yayeta bakaramin gata da sangarta shatuwa iya tayiba Dan tana nuna Mata so da gata ko dawasa Bata Bari adaki shatuwa haka shatuwa take zaune Babu Arabi Babu bako gashi yanzu shekarar shatuwa Sha hudu
Nabil ne awajan shakatawa Sha da abokansa shi Yana gefe cikin wata runfa azaune Kan wata kujera Kayan Shane kala kala agabansa yadora Daya Kan Daya yanajin waka Yana binsu da kallo abokan Kuma inbanda shaye shaye su da yanmatansu Babu abinda sukeyi
watace ita Daya tataso zata shige wani taje gurin nabil yaran yace Mata Iska nawahalar Dame Kayan Kara in dai nabil ne wlh sedai kimutu bazaki taba samun abinda kikesoba awajanshi dankuwa shi yanmata basa gabansa du wani shaye shaye da kikasan anayi Banda nabil danshi duka bayayi kawai shi Dan ya hulene shikadai du wani gurin shakatawa yanasan zuwa Kuma shikadai yakeso yayi rayuwarsa awajan bar shi dai dajin Kade Kade da wakoki da Kuma rashin mutunci in kashiga gonarsa mu har tinani muke nabil bashi da lfy kamar se annemar Masa magani Yana gani zamuyi yanda mukeso da yanmatanmu agabansa amma shi Babu shi ko akansa inmunyimai mgn seyace shi Yana da kankami bayasan kazanta ba ze iya taba kowace maceba ko yahada jiki da ita yafiso yayi rayuwarsa haka Dan Haka karki kuma Masa mgn Akan Wai kina sanshi indai nabil ne zemiki wulakancin da Bazaki taba zataba Ni Dame nabil yafini da kikaki Sona Ina tabinki kina min wulakanci yarinya kizo inda akesanki kibar wancan Mara lfyar da ko Mata nawa aka ajjemai baze iya sarrafasuba sedai yakallesu da Ido
Yarinyar tace mesuna finah indai Akan San nabil ne yanzu nafara Kuma semun kwanta gado Daya da nabil senayi yanda nagadama dashi kanaji kana gani kwalelanka banayi ko ana Dole
Tashige Tai tafiyarta wajan nabil
Saurayin dariya yasa yace Allah yaba da saa ai Bari bashegiya bace da ubanta yanmata
Finah nazuwa gun nabil tabaya tarungumoshi tana sauke numfashi tace Dan Allah nabil karkace komai karkaimin mgn sanka da shaawarka zasu kasheni kabarni naji dumin jikinka Dan Allah kazo muje dakin da nakama ko zafine karagemin kaji
Ranshine yai mugun baci afusace yasa hannu yai wurgi da ita tafadi gefe Daya tashi yayi yarufeta da duka yace ke har kin Isa kihada jiki Dani kazama irinki ninan da kike gani babu matar da zanhada jiki da ita kema yau da Kika tabani kinyi babban kunkure arayuwarki Dan Sena hukuntaki Konasa gusire Miki hannu Ni Nan da kike ganina Mata basa gabana bani da lokacinsu karki Kara zuwa ko tawajan inda nake awaje inkin ganni ninan da keke gani bana Zama guri Daya da Mata natsani Mata bare har su taba jikina banaso yanzu kinja senaje nayi wanka kin batamin jindadin da nakeyi awajannan inacikin farinciki kinkama kin batamin shi yaranshi ya kalla da Ido dagudu suka taho kuje ku hukuntata Senace kusaketa zaku saketa
Abokansane sukai tabashi hakuri suna rokarwa finah harya hakura yatashi yabar wajan Rai abace yatafi gida
WAYE NABIL DA IYAYAN SA
Mahaifin nabil alhaji sani haifenfan garin kanone zamane yakawoshi Abuja mahaifiyar nabil hajiya Fatima haifanfeyar yolace bafulatanace gaba dabaya aikine yakai alhaji sani Yola yaga hajiya Fatima soyaiya tashiga tsakaninsu manya suka shige gaba har sukai aure
alhaji sani mahaifinshi malam usiman da Yana cikin garin Kano da Zama saboda kasuwancin da yakeyi lokaci daya basansa mahaifi yace Masa yanaso yakoma kyauyan mazagai da Zama saboda gidansu na gado tin iyaye da kakanni gidan yake Kuma sunyiwa iyayansu alkawari bazasu sai da gidanba Dan Haka baban alhaji sani yakoma can dazama yazauna da danginsu awannan babban gidan tindasu sun tsufa sundauko gangara shine mekula da danginsu nacan lokacin su alhaji sani du sun girma Yama Gama makaranta yafara aiki besoba babansa yakoma wannan kauyen na mazagai dandai Babu yanda zeyine tindaga lokacin komai na baban alhaji sani yakoma mazagai Dan Haka akai akai su alhaji sani shi da iyalinsa suna zuwa siyara mazagai gai da kakan su nabil malam usiman
haihuwar Fatima matar alhaji sani bakwai biyu sun mutu saura biyar Kuma duka Mata take haifa ata karshen tasamu da namiji wato nabil shine nabakwai ayaransa danhaka yadauki San duniya yadorawa nabil bayasan lefinsa akasar waje nabil yai karatu Dr ne shi Amma saboda gatan da yake dshi yaki yafara aiki har asibiti nakanshi alhaji sani yace zebude Masa nabil yace bayaso shi bashi da lokacin duba mutane tinda Babu abinda yarasa narayuwa amma duda Haka seda yabude Masa katan asibiti agarin Abuja
yanyun nabil Mata akwai basira akwai hamida akwai Amina da mufida dukansu sunyi sure suna gidan mazajansu uku nakasar waje acan mazajansu suke aiki aminace agarin Abuja anan mijinta yake aiki
iyayan alhaji sani da Yan uwan babansa irin masu kudinnanne kusan dukansu masu kudine alhaji sani shima lokaci daya yabunkasa yazama mekudi Yana kasuwanci Yana aikin gwaunati har akabashi mukamin MINISTER shine yabar Kano yakoma Abuja da Zama Amma Yana da gida akano Kuma du lokacin da yagadama suna zuwa hutu shi da iyalinsa
mahaifin alhaji sani yatsani irin halaiyar Nabil basa shiri Shi da nabil kwatakwata kullin cikin yiwa nabil fada yake da nasiha da alhaji sani shima yanashan fada wajan malam usuman saboda lalata nabil da yayi da gata
hajiya Fatima itama batasan halaiyar Nabil kullin cikin yimasa nasiha take Yan uwanshi matama basasan irin abinda yakeyi saboda gababadaya alhaji sani yatsayawa nabil kome yagadama yayi har masu kula da lfyarshi yazuba Masa jamian tsaro Dan Kar wani Abu yasamu dansa Kano Abuja ansan nabil da irin rashin mutuncin da yakeyi musamman Akan titin mota ko inkataboshi zakaga rashin mutuncinsa ana tsoran nabil sosai musamman masu karamin karfi atsarinshi Kuma yatsani Mata baya shiri da su sekuma gashi mahaifiyarshi hajiya Fatima Bata goyan bayan abinda yakeyi Kuma batasan alhaji sani yake nuna Masa gata seyake gani itama basansa takeba duwani gidan holewa da otal nabil yasansu seya kwana awajan fatinsu Amma kome yake baya shaye shaye abokansa sunyi sunyi yakoya Amma yaki matanma anyi anyi yakoyi harka dasu yaki konawane abokansa sukeso zebasu suyi watsewarsu Amma bandashi yanMata nasanshi kamarme Amma shi basa gabanshi akasar wajema yanmatan turawa sunkawomai Hari Amma bashi da lokacinsu gashi da karfin shaawa Amma bashi da lokacin yanMata bare Kuma maganar aure ko ciwan mararshi yatashi sedai yanemi magani wani lokacin har kwantar dshi ake a asibiti in ciwan yatashi
alhaji sani nada katan gidan gona amazagai nabil nasan gidan gonar sosai intarayo Masa can make tafiya yayini Acan ko yakwana inyaga dama yaje wajan kakanshi malam usiman Wanda suke Kira da faffah wani lokacin Kuma har yaje mazagan yagama hutarwarshi agidan gonar beje wajan kakan nashiba sedai shi malam usuman din inyaji labarin zuwanshi yaje yasameshi acan yaimasa fadan da zemasa yataho gida du lokacin da nabil zeje mazagai baya shigar arziki wanna shigar ta nigogi ita yakeyi mutanan garin suyi takallanshi anacewa jikan malam usuman ne wasu Kuma suyi Allah wadai da shigar da yakeyi Kuma du Wanda yabi hanyarshi inyana cikin mota shi da yaransa buge mutun sukeyi Dan Haka har mutanan gari sunsani anaganin motucinsa zaahau kaucewa ko harabar gidan gonar baabi dosai se intakama dole
Rai abace nabil yashiga mota direbansa yajashi yaransa suka maramai baya dagudu motucin suka fita daga wajan shakatawar dokar nabilce inyana cikin mota baatafiya ahankali dagudu ake tafiya dashi gida yasa aka kaishi tinkan motar tagama tsayawa yabude murfin motar yafito yashige cikin gida kowa yakauce Masa sun durkusa bangaran mahaifiyarsa yashiga lokacin wata Yar aikin hajiya Fatima takwashe kololin da akaci abinci zatakai kicin taga nabil yashigo saboda tsoro gabadaya rudewa tayi tarasa yazatayi Kuma duka hannunta biyu kololinne
wani mahaukacin kallo nabil yawurga Mata yadaka Mata tsawa yakaraso gabanta yadauketa da Mari ya tunkudeta ita da kololin suka Fadi kasa seda kashin kafarta yaamsa wata Kara tasaki
yace kunyi mugun rainaniko Yan aikin gidannan gaba dabaya Sena canjaku Kuma gaki mace shine Zaki tsaya kina kallona har Kiki durkusawa ahanya kina kallona kina wani zaremin idoko Wai meyasa Mata kuke shiga harkata nikuma natsaneku bana sanku bana kaunarku du halinku Daya Baku da kamunkai kema da niyarki kihada jiki Dani da kinyi babban kunkure arayuwarki
Kukan Yar aikinne yasa hajiya Fatima fitowa dasauri Dan tasan kowaye zesa wani kuka agidan tace hm ai Daman nasan sekai Dan mankuli da yaji Kai nabil kaji tsoran Allah katinafa duniya ba matambata,bace karfa kamanta inba mutuwa akwai canjin rayuwa Babu Kyau wulakanta Dan Adam dufa Daya muke awajan Allah tinda shine yayomu kaguji ranar ladama dajin kunyar abinda ka aikatawa mutane karfa rudin duniya yarudeka kamanta da mutuwa da canjin rayuwa nabil wannan abunda kakeyi bahaline mekyauba kadena kaji tsoran Allah waima na tambayeka memata suka yimaka katsanesu haka Anya baka da shafar aljanu nabil kadaure kashiga isilamiya ko malam limanne me Jan sallar masallacin unguwarnan Yana koyamaka karatu ko kanabin wayanda yake koyarwa bayan sallar magariba da Isha kaima kakaru da abubuwa dadama Dan nasan rashin lilimin addinin musulinci ne yake damunka Dama Wanda yai rayu akasar w
turawa ta Ina yasan wani karatun addini bare yai aiki dshi gaba dabaya akidar turawa du kabi ka kwashe Harda Wanda batasuba
Wata dariya nabil yakwashe da ita yace Kai mommy wlh kinsani dariya da Raina amugun bace yake Amma wannan maganarki takarshe da kikayi tasani dariya Wai naje malam liman yakoyar Dani konabi wayanda yake koyarwa haba mommy Dan Allah yakikaji da kike fadar maganar Nan Ni wlh mommy narasa meyasa bakya sona daddy yafi Sona Kuma agaban Yan aiki kike kunyatani ke malama bace daga wajan inkingama kukan munafurcin tinda kingmajin fadan da mommy tagama yimin Kuma zamu hadu kema barin gidan zakiyi mommy kinsan meyasa natsani Mata Ina da dalili meyawa Amma bazaki ganeba mommy natafi dakin daddy acan Zan kwanta nahuta yau wata mahaukaciyace tabatamin Rai shigewa yayi besaurari me hajiya Fatima zata Kara cewaba
Girgiza Kai hajiya Fatima tayi tashige wajan da yar aikin take tabata hakuri
Masoyana barkanmu da sake haduwa asabon novel Dina somin tabine inkun bani kwarin gwiwa da sharhinku nacigaba inkuma Banga ruwan sharhiba natsaya da rubutawa inyamuku Dadi zanga kwarin gwiwar da zaku bani inkuma beyiba zanji shuru nikuma na ajje alkalamina
Bababu Wanda zanturawa ta PC karma abiyoni bana turawa ngd masoyana fatan alheri馃
New writer's
Hakan Take
*Husba'ahfama* 鉂ゐ煈�
*'Yar kwalliya* 馃コ馃拑
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹
馃憼
馃拕馃拝 *DAN MINISTER* 馃拝馃拕
馃馃
Written by *Husba'ahfama*
*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*
Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*
Alhamdulillah Alah kulli halin
3-4
Nabil da yashiga dakin mahaifinshi kwanciya yayi yarufe Ido tinani yake akan nacin da Mata sukeyi akansa na suna Sansa afili yace bana sanku kukuma Kuna Sona meyasa kukemin haka bazanyi aureba bani da lokacinku rufe Ido yayi yafara bacci lokaci daya ciwan mararshi yatashi tin Yana daurewa yanaso yayi bacci har abin yagagara juyi kawai yake tayi lokaci daya yahada gumi duda sanyin esin da ke dakin
Ana Haka alhaji sani yashigo dakin Yana ganin halin da Dan nasa yake ciki lokaci daya yarude yakarasa wajanshi labil baka da lfyne meyake damunka
Saboda azabar ciwan da yakeji ko mgn yakasa hannu yasa Yana nunawa baban nashi mararsa
Dasauri alhaji sani yadau waya yakira Dr dake duba iyalinshi ya,fadamasa yai maza yazo dansa ba lfy cikin kankanin lokaci Dr yazo yafara dubashi yaimasa abinda yadace lokaci daya bacci menauyi yakwasheshi
Dr yace yallabai da matsalafa in har Baku dauki matakiba akan nabil Nan gaba kadan ze iya rasa kwayoyin haihuwarsa gabadaya saboda wannan temakwan da ake bashi zedena aiki Dan yanzu magani baya Masa aiki se allura itama nangaba kadan zata Dena aiki ajikinshi saboda Yana da karfin shaawa me zafi agaggauta yimasa aure Dan asamu mafita Kar abin ya illata lfyarshi Dan har aiki abin ze iya sawa aimasa nangaba
Numfashi alhaji sani yaja yace to Dr ngd insha allahu zaaimasa aidolema aimasa Dan kullin burina Naga gudan jinin nabil aduniya
Sallama sukayi da Dr yatafi
alhaji sani dakin matarsa hajiya Fatima yatafi
Yakarasa wajanta yazauna cikin damuwa yafara fada Mata abinda Dr yace akan dansu nabil
Hajiya Fatima tace anzo wajan alhaji aini tintini naso aiwa nabil aure ko zedena wasu abubuwan da yakeyi Amma nasan ban Isa nace wani Abu akan nabil ba kayarda danhaka nai shuru da bakina Kuma da matsala nabil yatsani Mata bayasan Mata tin abin baya da muna yanzu abin nashi yafara bani tsoro gani nake kamar nabil na da aljanu kyama sosai yake nunawa Mata Nima Dan uwarsace babu yanda zeyi Dani muke zaune inuwa Daya dshi Yan uwanshi matama dandai Babu yanda Suma zeyi dasu yake hurda dasu ko hanya bayaso yahada da mace bare Kuma ai maganar aure dazu dazunnan yaiwa Yar mutane duka har targade yaji Mata Dan taganshi yashigo tarude tarasa inda zatabi ya hukuntata Kuma wace macace zata iya Zama da nabil inba Wanda batasan ciwan kantaba irinshi kokuma ta aureshi Dan kudinshi Amma inhar mace me hankalice da tinani wlh bazata auri nabil ba komai kudinku Kai dshi
Alhaji sani yace kefa matsalata dke Kenan indai akan nabil ne alheri baya fita abakinki ai nafiki sanin raayin nabil Kuma da Babu wannan matsalar tashi da tataso da bazan Masa aureba har se ranar da yasoyi Dan kansa bare harnazo wajanki neman shawara Kuma yanzu zanbawa Dana shawara akai Kuma zedauka ko bayasan mace zan bashi shawara ya auri kowace macace inde zatamai maganin matsalarsa tashi yayi yafice cikin fishi
Hajiya Fatima tace Allah yaganar dku Kai da danka alhaji daga Kai harshi kunyi nisa zankira baffah na fadamasa halin da ake ciki nasan Kai bazaka fada masaba
Shatuwace takwashi zugarta sukayi dawa cikin gonakin mutane du gonar da sukaga tamusu Haka zatasa sushiga suyi musu barna sannan subar wajan du sanda tarayo Mata gonakin mutanene wajan wasanta ita da zugar kawayen ta gonar wani me mangwaro da goba suka shiga magwaran yanuna sosai sukai Masa barna sosai Kuma sukaki barin gonar suna tawasa aciki har me gonar yazo ya samesu yaga barnar da sukai Masa ransa yayi mugun baci sosai Kara dogo yadauka yahau dukan du Wanda yasamu Dakar suka,samu suka gudu du yasansu yagane fuskokinsu rainshi abace yatafi wajan megari yakaimai Karar abinda su shatuwa sukai Masa
Megari sawa yayi akakira iyayan yaran da su kansu su shatuwa har da iya seda tazo cewa tayi se tazo taga me zaayiwa jikarta
Gaba dayansu sunzo sun amsa Kiran megari Nan magari yasa me gona yafadi barnan da su shatuwa sukai Masa
Budar bakin iya tace to yanzu malam me kakeso aimaka wayace karka zagaye gonarka kai Mata kofa yanda Babu Wanda ze iya shiga lefinkane da kayi da yarannan bazasu shigarma gonaba har simaka barna yarannan kwatakwata nawa suke yaran da basugama hankaliba Dan abin kunya kakwaso jiki kakawo kararsu wajan megari yanzu Dan Allah bakaji kunyaba tsofai tsofai dakai
Megona yace ke tsohuwar banza kishiga hankalinki Daman Ina da labarinki inkinwa mutane sunbarki saboda tsufanki Ni inkinmin ba barinki zanyiba kwatakwata shekara nawa Kika bani da zanji tsoran yimiki mgn har naraga maki saboda girmanki ke ko tsoran Allah bakyaji zomuje kiga barnar da jikarki tasa akaimin agona Kuma wlh da nazone akan ajamusu kunne karsu kuma Amma wlh yamzu se anbiyani tinda Babu mutunci gobema kukara barin su suje gonar mutane suyi musu barna
Megari yace Wai ba afada kukeba kuke wannan abinba Karna karajin bakin wani anan iya gaskiya bakya kyautawa haba iya meyasa kike Haka tsufa haukane du abinda kikewa mutane in ankawo Miki Karar shatuwa nasani mutane nazuwa su fadamin ninake Basu hakuri saboda zaman mutuncin da kukayi da iyayanmu nake barinki Amma wlh Daba hakaba da matakin da zan dauka akanki ke da iyalinki da se kinyi mamaki sosai yanzu tinda kingoyi bayan jikarki shikenan zaayiwa mangwaransa da goba kudi ki biyashi ke da iyayan yaran da taja sukaje sukayi barnar Kuma du sanda suka Kuma harku iyayansu se mundau mataki akanku suma Kuma yaran bazamu barsu sutafi hakaba se nasa anmusu bulala yanda Nangaba bazasu kumaba
Kafin megari yagama yanke kudin da su iya zasu biya Sega wasu masu gonar Suma sunkawo karar su shatuwa Haka megari yahada yasa iyayan yaran da na shatuwa suka biya kudadan barnar da sukayiwa masu gonakin megari yasa dogarinsa yaiwa su shatuwa bulala sosai ihu shatuwa take kurmawa haka iya ma take kurma ihu daga anzubawa shatuwa bulala Haka iya zata takarkara tazuba nata ihun du sukabi suka cika wajan da ihu
shidai umaru mahaifin shatuwa takaici yahanashi mgn ga takaicin uban kudin da akasu suka biya gana shatuwa da na iya tinanin irin hukuncin da zeyiwa shatuwa in sun koma gida yakeyi
Nabil be farka daga bacciba se wajan magariba Yana tashi yafito bega kowaba bangaransu yashige yaje yai wanka yafito Yana zaune afalo alhaji sani yashigo shi da hajiya Fatima suka zauna kusa dshi
Alhaji sani yace nabil yajikin naka
Yace da sauki daddy
Nan alhaji sani yafadawa nabil abinda Dr yafada Akan cutarsa yaku Gaya Masa shawar da suka yanke nayi Masa sure
Dariya nabil yayi sosai sannan yahade Rai yafara mgn yace daddy kafasan matsalata da raayina natsanar du wata yarinya mace Ni Babu wani aure da zanyi wlh Dan Zan iya lahanta Yar mutane abanza wlh Dan ko gida daya Bata Isa mu zauna tareba Ni fa daddy bani da raayin aure bazan yiba mezanyi da mace nasan daddy wannan ba raayin kabane raayin mommy ne da wannan tsohon faffah Yama gangara kowa yahuta yaki mutun se shegen taurin Rai yaki mutuwa wlh du sanda tsohonnan yamutu Babu kukan da zanyi Kuma in har aka dauramin aurannan da kowace yarinyace sedai faffah yazauna da ita ko mommy ko Kai daddy Danni bani kuka aurawaba Bari kuga yauma Ni ba agidannan Zan kwanaba a