Author : Nainerh KD Category : Romance
domin kowace rana akoy abinda zasu karanta sanan a kulun sai yayi mata wa'azi sosai sosai , sai yanzu ta san cewar itama mutun ce mai daraja domin an haliceta a jinsin bil'adama , idan yana bata tarihin manzanin mu da irin yanda suka sha gwogwormaya dan yada adinin musulunci sai taji wani irin shaukin adininta taji wata irin soyayar adininta taji haushin shekarun da ta shafe a bola bata zuwa ta saurari karatu koda yaran na tsokanar ta ,
Bangaren Malan Yunus yana matukar jin dadin karatu da Yar Mahaukaciya domin idan yana koya mata karatu tana bada hankalinta gaba daya ga saukin daukan harda domin akoy tambayoyi sosai kan du abinda ya koyar da ita
Yau ta kama alhamis tun da safe Yar Mahaukaciya tayi aikace aikacenta ta gama ta dora girkin su karfe biyu ta sauke komai har jus jus dinsu da suke hadawa ta gama ta saka a frij Hajiya Hawau sai aikin sanu take jera mata , sai da ta gama taje tayi wanka ta fito ta daura zaninta ta zira rigarta na atampa ta fito ta nufi falo wajen hajiya Hawau
Tana shiga ta zauna kasa , saman kapet wanan na daya daga cikin al'adunta sam bazaka ganta saman kujera idan baban mutun na sama ita sai dai tayi zamanta a kasa koda kuwa ka tashi tana matukar jin kunyar hawa wajen da ka tashi
Hajiya Hawau ta dago kanta daga kalon da take tace : taso maza yau na kunce miki kitson nan da na yi miki uwa mai takaba
Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta matsa kusan Hajiya Hawau ta kunce daurin dan kwalin kanta Hajiya Hawau ta kama tsifa
Suna tsaka da tsifar Docter Idriss yayi salama ya shigo cikin falon da Sauri Yar Mahaukaciya ta shiga kiciniyar kwace kanta don ta rufe domin KO hijab babu a jikinta gashi rigarma ba zumbuleliya bace
Hajiya Hawau ta kama baki ta ce " ke zauna min kaji min yarinya to dan wanan dan neman ya shigo shine zakina kokarin ganin kin kwacen kanki? To ba yayanki bane shi din?
Idriss ya zauna ya ajiye jakarsa baka da alama daga office yake , ya dago kansa ya ce " Iyancy mitar mai kike yi ne?
Hajiya Hawau ta turo daurin dan kwalinta gaba ta kankance idanuwa ta nuna masa yatsarta ta ce " Kai wanan yaro ka kiyayeni , ka FITA a idona na rufe aradu zan kai kararka wajen ubanka dan ni din nan da kake gani daidai nake da kai
Idriss ya bushe da dariya har yana rike ciki ya ce " haba Madame haba madame mai yayi zafi kiyi hakuri kin sani sarai ke din ta kudin ce KO?
Ta kuma turo bakinta , Yar Mahaukaciya tayi murmushin diramar Hajiya da jikanta ta dan juyo fuskarta ta ce " Yaya ina yini ya aiki
Idriss da sai yanzu ya lura da ita domin da ya shigo ya ji dai hajiya Hawau na mita aman bai san mitar mai take yi ba , ya amsa salamarta idanuwansa a saman tarin gashin kanta da ake kuncewa
Ya ce " Hajiya wai atach ne yar taki tayi?
Hajiya Hawau ta ce " Allah ya kiyashemu da Karin gashi, ai gashinta ne ba wani atach
Idriss ya zaro ido ya ce " Aman ya naga uwa na nasaru wanan kalar gashin ai ba na hausawa bane kinga fa ja ne ga tsayi aman kina yi masa shampo KO ?
Yar Mahaukaciya ta dago kanta idanuwanta yana mage ta saukesu a fusfar idriss ta ce " YAYANA kuma mainene shampo?
Idriss ya hadiyi wani yau da ya tsaye masa a makogoronsa a ransa ya kara yarda tabas Ramat ba bahaushiya bace to aman wai ita wace yare ce?
Ya ce " hajaju ki bar kan nata mana na kaita saloon a wanke mata idan mun dawo sai ki dadaure mata
Hajiya hawau da daman hanayenta sun gaji sosai ta ce " to dan Albarka Ramatutu tashi ki dauko hijabinki ku tafi a wanke miki da abin wankewa kinji ?
Yar Mahaukaciya ta mike tana dan jan rigarta dan ta rufe mata jikinta aman ina da Sauri Idriss ya kawar da kansa daga dubanta yana fadin a'uzubilah yana kawar da kansa ,
Ta dauko zumbulelen hijabinta ta zira Idriss ya bar jakar Ma'aikatan NASA a nan suka shiga mota
Daidai zasu FITA daga harabar gidan sai ga Sahla da kawarta Alisha sun shigo suna shan kidan su ran Sahla ya gama baci domin wanan ai zubar mata da mutunci ne Idriss yayi niyar yi ya zai dauko wanan bagidajiyar a motarsa kuma gashi kawarta Alisha ta gani ga irin yanda Alishan ke maseefar son Idriss din
Alisha ta waigo ranta a bace ta ce """"""""""
Love u
🏳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
15
hajiya hawau cikin bacin rai ta nuna Sahla da hanu ta ce " ke yarinyar nan kin fiya neman magana , shin yaushe zaki fara mutuntani ne? Ki tuna ni fa na haufi mahaifinki aman kashinki yafini daraja , ta girgiza tana kama hanun Yar Mahaukaciya ta juya ta ce " Idrissu karka ce mata komai ka barta duniya ce , ta kuma juyawa wajen Mubasshir da ita ya kurawa ido bai taba ganinta a irin wanan halin ba tabas KO wacece wanan tanada baban mukami a wajen Hajiya ,
Hajiya ta hade hanayenta biyu tana kalon sa tace" Yarona dan Allah karka hukuntata dan ta batamin ka barta ta hukunta kanta da kanta , ka BArTA ta gane cewar mutun yafi kudin nan nasu daraja , ta ja hanun Yar Mahaukaciya suka nufi kicin
Gaba daya jikin Sahla yayi sanyi aman fa batayi nadamar abinda ta aikata ba
Idriss da tunda ya tare Yar Mahaukaciya ya shiga wani yanayi Wanda eh lale bazai ce bai taba shiga ba aman wanan kam yafi na kulun yana bukatar yin nesa da mutane dan ya dandance abinda ke kokarin damunsa ya mikawa Mubasshir Hanu ya ce " friend sai mun hadu nayi ciki
Mubasshir ma ya mike ya ce " muje tare kasan inada abun yi
Haka suka tafi suka bar Sahla nan zaune duk irin kwaliyar da ta sha da kanshin da take zubawa duka suka tashi a banza domin Wanda tayi dominsa KO kalon banza bata ishe shi ba , ranta ya kuma baci ta kara kudurtawa ranta sai tasan wacece wanan yarinyar mai kama da aljanu sai ta binciki lamarinta
Shigar su Hajiya Hawau kicin Yar Mahaukaciya ta dakata
Hajiya Hawau ta juyo tana kalonta , Yar Mahaukaciya ta duka gwuiwoyinta a kasa cikin shashekar kuka ta ce " Dan Allah kiyi Hakuri Hajiyata ki dena fushi dan an bata min ki sani fushinki na Konan raina kakata bani da kowa sai Allah sai ke kiyi hakuri ki yafe mata
Hajiya hawau ta tsura mata ido ba komai ya birgeta ba sai kalmar kakarta da Yar Mahaukaciya ta furta a hankali ta saka hanayenta biyu ta dagota daga tsugunin da tayi ta ce " ba komai jikata na hakura na daina fushi , ki tayani da adu'a Allah ya karkato min da hankalin dana kaina
Yar Mahaukaciya cikin fuskar tausayi ta ce " nayi alkawarin saka aban gidan nan a adu'a Allah ya ganar da shi
Hajiya tayi murmushi ta ce " mû je kinga Dan Aljannah naji tashin motarsa bai sha fura ba , karbi ki saka min a frij nasan zai dawo gobe sai na dama masa
Yau tunda safe gogo Fatima kawar Hajiya Hawau ta turo yaro a fada mata jikanta mai wata shida ya rasu , Hajiya Hawau harda kuka ta dauko hijabinta zumbulele ta zumbula ta dauko goronta da carbinta ta yiwa Yar Mahaukaciya salama tana fadin sai dare idan tana son ganinta mai gadi ya kaita , ta kama hanya ta shiga adaidaita sahu tayi tafiyarta
Zaune yake a office yayi shiru yana nazari ya zama wajibi ya koyawa yarinyar nan hankali yana matukar sonta yana so ta san darajar mutane domin shi mutumin mutane ne , tabas zai kai kudin aurenta aman fa zaiyi iya yinsa dan ta gane cewar mutun rahama ne , yayi murmushi da ya tuna irin abinda zai hadata da shi abinda tafi tsana ne wato tsofafi , yayi nisa da tsare tsarensa a cikin zuciyar sa kawai fuskarsa ta hasko masa furar Hajaju ba shiri ya hadiyi yau ya mike ya shiga tatare wayoyinsa dan kuwa yayi missing din furar nan yau har kwana 24 bai sha ba da jiya ya sha aka bata masa rai yayi tafiyarsa ,
Tunda Hajiya Hawau ta tafi Yar Mahaukaciya bata zauna ba sai da ta wanke gaba daya kayansu masu dauda ta kai bayan gidan ta shanya , ta dawo ta dauki tsintsiya ta wanke tsakar gidan ta koma wajen shukar mangoron gidan ta share tas ta kwashe ta dawo ta kuna tiraren wuta mai dadin kanshi sanan ta shiga bayi ta kuma yin wani wankan ta dauko zani na sabuwar atamparta ta daura ta dauko jar Riga ta saka ta daura dan kwalin zanin ga Jan kunshinta da ta kunsa ya fito yayi shar da shi batayi wata kwaliya ba KO mai bata murza ba domin yanayin garin da dan zapi zapi ta fito ta saka silifas dinta ta shige kicin ta shiga kiciniyar hada dan jus a Kofi dan kuwa yau baza tayi girki ita kadai ba , ,, bayan ta hada ta dawo wajen da ta wanke ta shinfida tabarma baba ta zauna ta saka cokali a cikin kofin ta fara shan fruits salat dinta ,
Cikin takun kasaita ya shigo cikin gidan da salamarsa cikiciki yanda ya saba , Yar Mahaukaciya kam bata ji ba hakan yasa bata dago kanta ba aman hancinta ya jiyo mata kanshin Dan Aljannahn Hajiya , kasa kasa ta kali kafarsa ta ga cikin takalmi kafa ciki ne yake tafe gabanta ya fadi domin Hajiyar bata nan yanzu budurwar sa zata zo ta shifka mata rashin mutunci ,
Karasowa yayi yana dan kalonta a ransa ya ce " Ashe kunshi nayiwa wasu matan kyau , shi bai taba ganin kunshin da ya birge shi kamar wanan ba , Yar Mahaukaciya ta dago kanta da tsoro tsoro ta tsura masa ido , ita kawai mamakin gashin kansa take uwa mace
Cikin fada fada ya ce " Meye
Yar Mahaukaciya tayi gagawar sada kanta kasa kunya ta rufeta a ranta ta ce " baki iya kalo ba , Yar Mahaukaciya baki iya kalo ba , aman a fili ta ce " Bata nan Hajiyar
Ya yatsina fuska ya ja kujera nesa da ita ya zauna , a ransa yana fadin melodius , kuma wani bangaren na zuciyarsa ya ce , ina ruwanki da ni 😌
Ya kusan minti ashirin a zaune bai ce mata ufan ba itama ta kama bawan Allahnta tayi shiru , can dai ta mike ta shige cikin falon ta dauko furar ta debo kindirmon mai zaki ta dauko cikui uku masu shegen laushi ta hado da yar madarar ta fito inda ta shinfida tabarmarta ta nemi waje ta zauna ta jera kayan a gabanta tayi zaman makaranta ta dauko kwaryar ta zuba furar da nonon ta maida hankali ta dameta sai da ta damu gaba dayanta ta zuba madarar nan sanan ta saka hanunta a ruwa da sabulun dake gefe ta wanke hanunta ta dauki cikui din nan gaba daya ta cicira shi a ciki ta zuba dan siga ta motsa , nan da nan man ya hayo sama furar ta fara sheki ,
Tunda ta fara dama furar ya kura ido yana kalonta kwarai ya gamsu da tsaftar yanda aka dama furar ganin ta mike yasa ya kawar da kansa , a hankali ta rufe kwaryar furar ta shiga kicin ta dauko karamar kujera ta fito tana taku cike da tsoro ta kawo kujerar gabansa ta ajiye ta juya ta dauko furar da wani ludayi wankake ta dora saman murfin furar ta karasa gabanta na faduwa ta ajiye saman kujerar sanan ta shige falo tana sauke ajiyar zuciya a ranta ta furta tasan ba sha zaiyi ba
Tofah Mubasshir ya zubawa kwaryar furar ido abinka da idan Abu na birge mutun har kanshinta yake ji shawara yake da zuciyarsa shin zai iya sha kuwa?
Ni zan sha 😋😋
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
*This Page Dedicated to Aunty QUEEN MERMUE, Aunty NAFEE ANKER and AUNTY HALILOSS*
16
Ya jima yana kallon kwaryar furar sai ya mika hannu zai dauka sai ya maido hannun nasa , ganin dai ta shige d'akin bata fito ba yasa ya Mika hannu ya bude furar ya saka ludayin cikin nutsuwa ya kara motsata ya debo a cikin ludayin yayi bismillah ya kai bakinsa , bai san sanda ya lumshe idanuwansa ba , ya d'auko k'waryar gaba d'aya Kamar Wanda wani zai warce masa ya maida
Wanene *MUBASshir* ?
D'a d'aya tilo ga Marigayi Elhaj Mubarak Balarabe Mai farin gida , Elhaj Mubarak bai ta6a siyasa ba babban d'an kasuwa ne yana harkar kayan larabawa abayoyi , siga kantu, tiraruka , zamzam inda ya gaji wanan sana'ar wajen mahaifinshi , Matarsa da'ya tilo Hajiya Fad'imatu ya ga sarkin chadi , sun kai shekara goma sha biyu da aure har ta kusa shiga ménopause Allah ya azirtasu da cikin Mubasshir , abin nema ya samu sarkin chadi gaba daya ya nemi alfarmar su koma kasar su har ta haihu irin ganin girman su da Elhaj Mubarak yake yasa bai musa ba suka tatara suka koma , cikin ikon Allah tana rainon cikinta cikin kulawa da d'umbin kauna ga mahaifinta da kuma mijinta harma da al'umar garin , cikinta ya kai wata tara da kwana bakwai ta haihu ta sami da namiji cikin tsananin murna da godiya ga Allah subahanahu wata'ala Elhaj Mubarak yayiwa Yaron huduba da sunan Mubasshir , sosai aka sha shagalin bikin haihuwar Mubashir inda Mahaifin Hajiya Fad'imatu yayi Kiran Elhaj Mubarak ya bashi wata akwati mai dan girma da wani katon kwad'o a jikinta yace masa wanan a bari sai Mubasshir ya girma a bashi sako ne daga kakansa ,
Cikin girmamawa Elhaj mubarak yayi godiya da fatan Alkhairi suka juya Nigeria yaci gaba da harkokinsa na neman kud'i da gine gine na gidaje da sunan D'ansa tilo Mubasshir ,
Mubashir nada shekara shida suka shirya da mahaifansa suka d'aga saudiya sukayi Sallah daga kasar saudiya Mahaifin Hajiya Fad'imatu tsoho mai ran karfe da mijin Hajiya Fadimatu wato Elhaj Mubarak suka shirya tafiya Chine daga nan su komo Nigeria ,
Ranar da zasu tafi sai da suka raba dare suna hira duk rabin hirar jawabi ne Mahaifin hajiya Fad'imatu ke yi musu ita da mijinta , haka kawai take jin wata irin kaunar mahaifin nata Wace bata taba ji ba , har lokacin tafiyarsu yayi , a filin jirgi ma sai yayi gaba sai ya dawo ya kuma d'ora hanunsa a saman kanta ya ce " Allah yayi miki albarka
Itama tayi murmushi ta ce " amin Abu , haka mijinta ya d'auki yaronsa yayi ta sumbatar goshinsa yana saka masa albarka hardai aka fara Kiran sunaye ya ajiye shi yayi mata bankwana ,
Jirgin ya fara shawagin tashi sun dan daga sai ji kake bam wani irin kara Wanda duk jama'ar wajen suka tsorata wato jirgin da su Elhaj Mubarak ke ciki ne ya kama da wuta inda pilot din yayi yayi ya tsayar da jirgin abin ya faskara , gaba daya mutanen cikin jirgin Allah ya amshi ransu ,
Mutuwar nan ta girgiza Hajiya Fad'imatu ba ita kadai bama ta girgiza mutanen lagos da chad da kuma makah , Allah ya sa sun huta
Bayan rasuwar su sarkin Makka ya rike Hajiya Fad'imatu sai da yaga ta zama normal ya gamsu da ta hakuran sanan ya yarje mata ta koma lagos domin chadin bata da kowa mahaifiyarta ta dade da rasuwa yan uwa ba wani jituwa suke ba haka kuwa mijinta maraya ne GABA da baya ita kuwa bazata iya rayuwa a kasar makah ba tafi son tazo ziyara , kuma tana son ta koma gida KO don ta kula da dukiyar dan Marayanta Mubasshir , Sarkin Makah yasa akayi kiranta ya shaida mata bai hanata tafiya ba aman ta bar Mubasshir ya sauke alkur'ani domin yayi nisa a karatun hakan yasa ta barshi a wajen uwar gidan sarki Abdulrahman ita kuwa ta juya gida
Mubasshir nada shekara tara ya sauke alkur'ani mai girma , a shekara goma ya rubutashi da hanunsa , sanan litatafen musulunci ba wanda baya kokarin ganin ya hadace , kuma ga karatun boko sosai yana samun ci gaba
Mubasshir nada shekara ashirin da hudu har ya kamala karatunsa na boko idan ka Ganshi sak sufar larabawa ce da shi ga yalwar gashi baki sidik ga tsayi gaskiya Mubasshir Allah yayi masa tsararen kyau
Yar gidan sarki abdulrahmane ta mugun kamu da kaunar Mubasshir wato Mubinah Aman ina shi a yanzu yafi son ya koma gida domin Mahaifiyarsa yanzun ta fara gajiyawa kuma ga aboki da yayi Idriss yana mugun kwadaita masa rayuwa a Nigeria duk da Makah karshe Kenan aman garin mahaifiya yafi komai dadi hakan yasa ya tada Bali dole sai da aka shirya kaurowarsa Lagos unguwar dolar sunan unguwar tasa domin gaba daya gidajen unguwar gidajensa ne sai daya daya irin tsafin ginin nan na wasu aman sauran duk nasa ne inda gwomnati ke hayar su .
Dawowarsa Nigeria sosai yaji dadinsa domin yanayin kasar ya birge shi Mahaifiyarsa tayi murna sosai inda ya kama kasuwancinsa yaci gaba da yi , sanan yayi kaka wato Hajiya Hawau domin a rayuwa daga Hajiya Fadimatu sai wanan tsohuwa domin yana jinta sosai a ransa kuma a wajenta ya idasa kwarewa da