Author : Nainerh KD Category : Romance
ta kasa daga hanunta da alama ya karye fuskarta kuwa har ta canza kala, ta ja jiki ta rike kafar Idriss tama kasa kukan du irin azabar dake tsigarta, idannuwanta ta dago har jini ya dan konta ta zuba masa su ta ce" mai ke faruwa Yaya Idriss ?
Idriss shima ido cikin ido ya ce" Sahla asirinku ne ya tonu,
Sahla ta zaro ido ta ce" wani asirin mu ? Ni da Wa ?
Idriss ya ce" asirinku na shirin ku na halaka rayuwar bayin ALLAH da suka yi muku rana dan ku malake abinda ba naku ba, ke harta asirin da mama ke yiwa dady na ta juya shi yanda ta ga dama ya karye Sahla, yanzu haka ta bine wani à kofar dakin dad Bata tsoron yayi dawowar bazata dan kawai ta tsoratar da Hajiya (hawau) cewar dad ya mutu yana dakinsa idan ta tsalaka ta haukace à cewar bokanku, Allah ya taimaka muna shigowa dakinta muka nufa dad cike da mamakin za'ayiwa mama sherin bin bokaye sai gashi yaga haza domin shaida ta kirarin mutun da kansa KO ta Zina ta shaidu,
Sahla zuwa wannan lokacin ta gama tsurewa, tsoro da fargaba da tashin hankali da kunya suka mugun lulubeta, cikin nauyin harshe ta ce" Wa ya fada muku ?
Abanta cikin wata irin murya mai cike da kunci ya ce" Wanda ya boye mana dan ya kare mu, Wanda ya zuba muku ido dan yaga imanin ku, Wanda à cikin ruwan sanyi ya dago ku à fili *ALLAH* kenan, Wanda baya baci,
Sahla ta waigo ta zubawa fuskar Mubasshir ido a ranta tana tunanin ashe ya ji komai shi yasa yayi tayi mata tambayoyin nan ?
Idriss ya Mike ya nufi kofar dakin mahaifiyarsa ya bude dakin, tana jingine da kofar tana sauraron komai, ta dora hannunta à kai tana tunanin yanda aka yi hakan ta faru ai kuwa Bara ta kirayi boka ta fada masa ta bashi hakuri ya kuma shirya mata wani sihirin ( oh wai Kin manta rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya ?)
Budewar da yayi tana tsaye, ya zuba mata ido itama shi take kalo, ai kuwa ta shiga zaro ido hango mutanen falon, ta fito tana inda inda ta ce" aa fa, aa fa, wannan duka karya ne, ni ban aikata ba, aban Sahla karka yarda à hadani da kai, kai kasan à yanda
Nake kula da hajiya bazan iya cutar da ita ba, kai kafi kowa sanin hakan KO ? Ta juya wajen Idriss ta ce" Docter kaima ai shaida ne matso nan ka furta mahaifiyarka ba abinda tayi kowa ya tashi ya fice gidansa,
Sahla ta ce" mama.
Hajiya Marhaba ta juyo gabanta ne yayi wani irin faduwa, fuskar Sahla ta Haye tayi sindim, jini �a shigar mata ido ga hannunta ta kasa daga shi
Hajiya Marhaba ta ce " ubanwa ya taba lafiyar jikinki ? Fada min ubanwa ya dake ki ?
Mahaifin Sahla ya ce" ni ne, ni na daki y'ar da nake tir da...... Da sauri Elhaj Muhammad ya ce" kul na haneka da yin mumunan furuci Wa y'arka, SO kake ta shiryu KO ta baude ? Rashin tunani dana sani, kaucewa hanya ya tabata ga iyayen da zasu aibata y'ayansu dan sun kaucewa hanya, To mai zaka yi kenan ? Mala'iku suna gagawar amsar adu'ar iyaye Wa y'ayansu da amin KO wace kala ce dan haka ka kiyaye kar danasani yayi yawa rayuwarka
Hajiya Marhaba ta karewa Elhaj Muhammad kalo cikin kunan rai ta ce" ai dole ka fadi haka, kai ka kilace taka sakaryar y'ar zaka yi mana bariki à nan, toh wly baka Isa ba
Mahaifin Idriss ya juya dan yiwa Idriss magana sai dai abin mamaki bai ganshi à inda yake tsaye ba
Kiriniyar bude dakinsa yake domin idan za'a bude dakinsa sai an sha fama da kofar
Da sauri suka nufe shi aman kafin su Isa har ya bude kofar da gudu hajiya Marhaba ta rike shi aman da yake karfin ba daya ba zai kufce mata Mubasshir ya damko shi, kokowa suka shiga suna kokarin turo shi, garin ta tura shi karya shiga dakin da ta bine abinda zata haukata hajiya hawau da shi, ita kafafuwanta suka shiga, abin ikon ALLAH kawai sai ji suka yi ta kwashe da wata muguwar dariya
À tare suka furta inalilahi Wa'ina ilaihi raj'une, hanayensu à saman kansu
Mubasshir ya saki Idriss Wanda ya juyo jiri na kwasarsa ya zube à nan sumame
Ita kuwa sai dariya take babakawa, haukan dariya hauka mai wuyar warkewa, haka suka yi jigum jigum inda suna waigowa itama Sahla ta suma ( to fa wanzam baka SO à jikinka)
To fans tambayana à nan shin Sahla zata ci gaba da zama à matsayin matar AA ? Haukan hajiya Marhaba ya dace da ita duba da irin abinda ta aikata ? Bawan ALLAH Idriss ya tasa makomar ba masoyiya mahaifiya ta haukace, kanwa ta kauce hanya ? Shin labarin Yar mahaukaciya na kayatar da ku ? Cos ance wai banida masoya 😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*Na*
*Sajida*
79
*Wayo dadi, daukaka abar gudu abar nema, ni kam na rasa bakin magana sai jazakumlah,*
da gudu ya nufe shi yana jijigashi, inda Yar mahaukaciya ta nufi Sahla saï kuka take dan kuwa ita abi kankani ke rikita mata lisafi, tana kuka ta dago kanta ta kale su zata yi magana kenan sai ga abanta ya shigo da gudu yace " ku kama su mu je asibiti
Mahaifin Idriss wato Ilyas ya dago da kansa ya ce" baza'a kaita asibiti ba, sannan ba zan bisu asibiti à yanzu ba, kawai zan rufeta à daki ne naje wajen tawa mahaifiyar,
Elhaj Muhammad ya zuba masa ido ya SO ya takura sa sai dai yayi wani tunanin kawai ya kamawa Mubasshir suka dauki Idriss suka shiga motar da shi,
Elhaj Muhammad ya kali Mubasshir ya ce" kaje ka dauko matar ka domin kaine muharaminta
Mubasshir ya dago Idannuwansa cike da hawaye ya ce" ka yafe min aba, na saki Sahla saki daya
Elhaj Muhammad ya zaro ido ya ce" why Mubasshir zaka yanke danyan hukunci haka saki cikin fushi ?
Mubasshir ya kawar da kansa ya ce" banyi saki cikin fushi ba, na gama nazarina kafin Nayi sakin nan domin da à lokacin da nake walafawa Sahla soyayata gareta ta canza tunani Bata bani yaourt din nan ba da lale lale bazan saketa ba, aman à cikin zuciyar Sahla kiyayata tafi soyayata yawa dan haka ka yafe min,
Elhaj Muhammad ya rasa ma mai zai ce masa kawai sai ya kada kai ya koma dakin inda ya tarda Elhaj Inyass ya fitar da du abinda ya san zata iya raunata kanta ya rufeta à dakin sai falasa irin aika aikar da tayi take tana busasa dariya,
Elhaj Muhammad yayi gagawar kawar da kansa dan kuwa sai yaji ba dadi,
Su hajiya Rafi'at da hajiya hafsat suka kama suka dauko Sahla wace kitsonta na atch sai yawo yake tsananin tsayinsa a kanta,
Suna sakata irin motar nan ce jeka da iyalinka, lxus suma suka shiga Mubasshir ya tayar ya kama hanyar asibitin idriss
Suna zuwa da gudu aka karbesu BQ tare da tambayoyin abinda ya faru ba suka dukufa domin ceto ransu,
Zaune suke Yar mahaukaciya ta dora kanta saman cinyar auntynta tana ta sauke ajiyar zuciya, itama Rafi'at din du tayi wani iri da ita sai tunani take na rayuwa,
Hajiya hafsat ta kasa zama sai kai kawo take tana dan leka hanyar dakin da aka shiga da su, kuma sai ta kali AA da yayi wani irin ja na Wahala, kansa à kasa yana kalon yatsun kafarsa,
Elhaj Muhammad ya zuba mata ido yana kalonta, wani irin tausayinta da kaunarta suka kara darsun masa à zuciyarsa, ya kuma kali y'arsa dake konce q cinyar Rafi'at, ya juya ga Mubasshir dake kalon kasa, ya girgiza kai à hankali ya Mike ya kamo hannun hajiya hafsat, har yanzu abin nan bai barta ba na idan hankalinta ya tashi ta kasa zama, yayi murmushi ya jawota jikinsa ya Bata kyakyawar runguma, hakan ya saba yi mata idan har yana son ta shiga cikin nutsuwarta, hakan kuwa aka yi sai ta dora kanta à kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya, tana karawa,
Ta kusan minti biyu à haka ta tuna su Mubasshir fa na wajen da sauri ta kufce daga rikon da yayi mata tana kara jan zumbulelen hijabinta tana kokarin rufe fuskarta,
Mubasshir ya kawar da kansa yana girmama soyayar sirikansa
Docter Halima ce ta fito ta nufo su
da sauri suka Mike har suna hada baki wajen tambayar ya jikin su,
Mubasshir ya kali Yar mahaukaciya da ta ce" ya jikinsa ? Gabansa ya fadi, Muryar docter ta dawo da su inda ta ce" alhamdulilah jikinsu da sauki cikin ikon ALLAH,
An daidaita lunfashinsu, shi an saka masa ruwa aman munyi masa alurar baci wace tana iya daukan awa uku zuwa Hudu yana baci dan ya samu hutu, sai ita an dora hannun, aman tana bukatar kulawa KO ku dauki nurses masu kula da wannan harkar KO ku dauko Wanda zata tsaya tsayin daka dan lafiyarta ta samu cikin sauki da yardar ALLAH
Mubasshir ya ce" docter muna iya shiga mu ganshi KO ?
docter ta ce" eh sosai ma, kuna iya zama ma ai docter ne, ba wata damuwa,
Elhaj Muhammad ya girgiza kai Jin bai damu da rashin Lafiyar sahlan ba, ya ce" docter Ina bukatar à daukarwa kanwar Idriss nurses uku da mai kula da tsaftarta, da mai kula da abincinta, da mai kula da addininta à kan lokaci, du wata kulawa Ina son à Bata kafin ta dan warware
Docter ta ce" Elhaj akoy tsada fa
Elhaj Muhammad ya kaleta ya ce" ba wannan ba, aikinsu shine biyan bukatarmu
Mubasshir suka yi gaba su hudun suka nufi dakin Yar mahaukaciya kafin ya gama ya tarda su,
suna shiga suka tarar yana konce hanunsa jone da karin ruwa, yana baci aman da ka kale shi sai ka ga ya fada,
hajiya hafsat ta nufi gadon Sahla tayi mata ada'ar samun sauki,
Elhaj Muhammad suka shigo da nurse aka ja gadon Sahla dan à canza mata daki domin jinyar namiji da mace bazai yiwu à daki daya ba
Elhaj Muhammad ya kare yi masa kalo ya ce" da ace inada wata y'ar da na Isa da ita da na aurawa Idriss bisa sharadin idan ta Bata masa ban yafe mata ba
hajiya hafsat itama ta zura masa idon ta ce" ya ALLAH yanda ka yaye mana damuwarmu bisa Imani da muka yi da kai ka yayewa wannan Bawa naka cikin ruwan sanyi sannan ka bashi ikon cinye jarabawar
gaba daya suka amsa da amin, Mubasshir dai na kalonsa kuma sai ya saci kalon Yar mahaukaciya da ta zuba masa idon itama ba tare da wani tunani ba sai tsantsar tausayawa gare shi balatana idan ta tuna Tata rayuwar da ta shude ba'a dade ba
Elhaj Muhammad suka yiwa su hajiya Rafi'at da Mubasshir da Yar mahaukaciya Salama suka nufi gidan su Idriss dan su tarda hajiya Fadimatu dake wajen hajiya hawau suna ta jajantawa da kuma murnar dawowar tunanin Elhaj ilyassssss
bayan tafiyarsu Mubasshir sai ya daina kalon Idriss din gaba daya sai ya dawo da tunaninsa wajen islam da tayi zuru ita da aunty Rafi'at suna ta kalon lumfashin Idriss, wani haushi da mugun kishi ya rufe shi, à ransa ya ce, Tunda ta zura masa ido Bata dauke ba, mai hakan ke nufi ? Tana tsoron ta kawar da kanta ne wani abin ya sami masoyinta ( toh fa eh din Inji ni )
Gani yayi bazai iya jure wannan abin ba, ya Mike yana dan sosa keya ya ce" auntyn mu plz mana bara mu samo muku dan abin matsa baki kafin ya farka
hajiya Rafi'at ta kale shi ta ce" haba freind (domin shekarunsu daya abinka da yan gayu shima idan yana bukatar wata alfarmar ce yake kiranta da aunty) ya zaku barni à nan ni kadai kuma ? Idan ya farka fa ya Zanyi da shi ?
Mubasshir ya ce " ai ba zamu jima ba
hajiya Rafi'at ta ce " toh ka je kai kadai mana
Mubasshir ya zaro ido ya ce" Ina bazai yiwu ba fa hajiya kinga tafiyar mu dan Ina dan yi miki Yar murya aa bye,
Ya ja hannun Yar mahaukaciya wace tayi murmushi diramar auntynta da mijinta na birgeta matuka
Bayan fitar su aikin nata da ta saba ta ci gaba wato kalon sa, Kiran salar da aka yi ne ya saka ta Mike ta cire hijabinta dan taga yana baci kuma zata shiga bayi, ta ajiye à saman kujerar da ta tashi ta nufi bayin
alwallah ta dauro ta fito, tana fitowa ya mayar da Idannuwansa ya rufe ta dauki hijabinta ta dora saman Riga da siket dinta ta jawo dardumar da docter ta Miko ta kabarta sallar la'asar,
Bayan ta gama sallah tayi ta adu'o'inta da ta saba sannan ta daga hannunta sama cikin bayananiyar murya ta fara yiwa ALLAH kirari da shi da fiyayen halinta, ta nemawa iyayenta gafara da Wa'inda suka rigaye mu gidan gaskiya, ta kara nemawa y'ar uwarta kariyar ubangiji da ahalinta baki daya, ta roki gamawa da duniya Lafiya, sannan ta gangaro kan Idriss ta ce" Ya ALLAH alhamdulilah, Allah mun gode maka da wannan rana ALLAH muna rokon ka ka sanya ta zamto alhairi à gare mu, ya ALLAH ga bawon ka nan, kafi kowa sanin dalilinka na ciro kamili daga tsatson Wanda ba kamili ba, ya ALLAH kafi kowa sanin abinda ya dace da wannan Bawa naka domin kai kadai ka san gaibu, ya ALLAH ka sanyaya masa damuwarsa, ka yaye masa kuncin sa, ka bashi ikon kula da mahaifiyarsa da kuma kanwarsa, ka bashi juriyar cinye wannan jarabawar, ka shiryar da kanwarsa, ka baiwa mahaifiyarsa Lafiya, kai kayi komai kai kake da komai ya ALLAH,
*sai da ta gama yiwa kowa adu'a sannan ta fashe da kuka mai tsanani, ta kara daga hannunta sama ta ce" ya ALLAH ka kawo min abokin rayuwana koda da an daura min aure zan koma gareka, ya ALLAH idan wani abin na aikata KO nake aikatawa ka nusar da ni ka yafe min ka bani miji na gari komai talaucinsa, ya ALLAH idan kuwa lokacin Nayi auren ne baiyi ba ALLAH ka kara min hakurin jiran lokacin domin na san da mutuwa da arziki da Aure lokaci ne, ya ALLAH idan..... Ta kuma fashewa da wani kukan ta ci gaba idan kuwa banida raban yin auren ne har na koma gareka ka saka min dangana ka kuma kare ni da sharin Zina ka kara nutsa ni à kogin tsoronka ya ALLAH ka cika min burina amin*
bayan ta gama adu'ar ma sai da ta ci kukanta sannan ta Mike a nutse ta nade salayar ta juyo dan ta ajiyeta
Gabanta ne yayi mumunar faduwa sanadiyar ido Hudu da suka yi , wato Tunda ta fashe da kuka ya zabura ya zauna yana kalon ta kuma yana sauraronta,
wayancewa tayi tana dan murza ido kamar wani abin ya fada mata à ciki ta nufi dan kusa da gadon tana dan inda inda ta ce" """""""""""""
garigajin ganin ji ganjin kara Kaka kara 🙄🙄🙄🙄🙄🙄🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*Na*
*Sajida*
80
Tana murza ido ta ce" au ka farka ? Yaushe ka farka ? Ya jikin ?
Shiru Taji yayi bai ce komai ba hakan yasa ta dago da kanta suka yi ido Hudu, gabanta ne taji ya yanke ya fadi ta shiga kikifta ido
Idriss dake kalonta yana kokontan anya kuwa shekarun da aka ce ta kai kuwa ? Kamar wata Yar budurwa mai shekara 25 haka, ya lumshe Idannuwansa ya ce" shekarunki nawa ?
Hajiya Rafi'at ta dago kanta ta zuba masa ido tana mamakin tambayar sa, yaro karami da shi yana tambayar shekarunta ita tayi imanin ta bashi wata shekara biyu KO uku, ta kawar da kanta ta ce" ban gane shekaruna ba ?
Zaiyi magana kenan Mubasshir ya turo kofar ya shigo da ledodi manya bakake à hannunsa, Yar mahaukaciya na rike da wayoyinsa,
Suna shigowa ya saki murmushi Ya ce" marar lafiyana ya farka ?
Idriss yayi murmushin shima ya ce" ALLAH ya tashe ni broth
Mubasshir ya Mika masa hanu suka gaisa ya zauna yana kokarin bude dan abin motsa bakin,
Idriss kuwa banda kalon hajiya Rafi'at ba abinda yake, gaba daya ta tsargu, tana tsoron karfa aje yaron nan ya saurari adu'arta, ta girgiza kai à ranta ta ce " da kuWa ya cuce ni sosai,
Muryarsa ta katse mata tunani inda ya ce" tashi ki dauko min kofi na sha magani
À tare suka dago, Yar mahaukaciya ta Mike domin dai ta san bazai aiki auntynta ba duda bashi da Lafiya, ga mamakinsu sai ji suka yi ya ce " No ba ke ba, da *Yarinyar* nan nake
À tare suka zaro ido harda Mubasshir, Hajiya Rafi'at ta waiga ta kali Mubasshir ta ce" Freind KO kwakwaluwar yaron nan ta tabu ne ? Cos yana Farkawa ya shiga tambayana shekaruna, ni kuwa anya ba za'a Kira docter ta duba lafiyarsa ba ?
Mubasshir ya ajiye abarbar da ya wanke ya matsa kusan gadon ya ce" broth are u OK ???????
Idriss yayi murmushi ya ce" tabass lafiyana lau broth, i'm Idriss Ilyass, i'm 31 old, ni Docter ne, sannan à wannan lokacin Ina cikin tashin hankalin mamana mai suna Hajiya Marhaba da ta samu tabin hankali da kuma sisterna