Yar Mahaukaciya Complete Hausa Novel

Author :  Nainerh KD Category :  Romance

Chapter   29 / 29

84K to 85.2K   out of 85.2K words

fadi

Ina bata ma jinsa ta tura kofar ta shige tana ta murna sai dai Bata kai ga karasawa ba ta ja ta tsaya tana kalon ikon ALLAH, Aunty Rafi'at ce sai kuka take shekawa an kewaye ta


Turo kofar suka yi suka shigo inda suma suka ja suka tsaya suna kalon ikon ALLAH

Rafi'at ta ce" haba aunty, haba hajiya, kawai dan yaro ya ce " ga abinda yake SO sai à biye masa, haba dan Allah yanzu da girmana à hada ni Aure da yaro karami ? Nafa girme masa fa kuma wly tausayina ne yake ba wani sona ba

hajiya hafsat ta ce " sister wai meye haka ne ? Haba taya za'a zauna ana nuna miki gabas kina kalon yama ? Sunar ce bakya SO ? Idan har baki godewa ALLAH kan ni'imar da yayi miki à yanzu mai zaki yi ? Taya zaki fasara kyautar da Allah yayi miki adu'arki da ya amsa da wata fasarar ? Rafi'at à da inai miki kalon kinyi hankali ashe dai da sauran ki,


hajiya hawau ta ce " aa hajiya ku tashi ku barni da y'ata mu zanta kun ji ?

Hakan kuwa akayi sai da suka tashi suka ga su Mubasshir sunyi cirko cirko da hanu suka yi musu nunin su fice karta gansu

hakan kuwa suka shige inda hajiya hawau ta dage wajen kontarwa da hajiya Rafi'at hankalinta kan auren ta da idriss


ya kasa tsaye ya kasa zaune, du labarin da suke yana dai jinsu ne aman baya fahimtar abinda suke fada,

Hajiya hafsat ce ta fito da faranti da abinci à ciki, ta ajiye ta dauko ta shiga zubawa kuskus ce ta sha muryar jan nama sai kanshin kayan yaji ke tashi, ta mimika musu,, har ta kai kan Idriss ta mika masa ta ce" Idriss ka dawo cikin hayacin ka mana,

Idriss ya juya à hankali ya shiga cacakar abincin

Yar mahaukaciya ta shigo da jus jus ta ajiyewa kowa à gabansa, ta juya ta dauko nata farantin ta zauna Kusa da hajiya Fadimatu tayi bismillah ta debo ta kai bakinta

Wani irin Abu taji ya bigeta à hancinta na kanshin kayan yajin nan da tafarnuwa, kafin ta Ankara tayi wani abin sai kawai taji cikinta ya fara hautsina mata sai ga amai

da gudu ta mike zata nufi Bayi aman Ina dole ta duka à nan tana kwara amai tun karfinta, dan kwalin kanta ya fadi kasa haka mayafinta domin wani irin tukota aman yake

da gudu Mubasshir ya rigayi kowa isawa wajenta ya kamata yana tambayarta Lafiya ? Mai ya sameta ? Wani abin ta hadiye ?


Da kyar ta samu ta gama aman du ta galabaita ya dauketa yayi bayi da ita dan ya wanke mata wajen da ya baci à jikinta, ita kuwa hajiya Fadimatu sai sintiri take tana tambayar ta shigo ne bayin ? inda hajiya hafsat ta shiga gyara wajen

Idriss ya Mike ya fice dan dauko kayan aikinsa domin yana Docter gida har uku hakan ya sa baya tafiya ba malet dinsa mai dauke da yan abubuwan da ya dace domin aikinsa


Daidai zai fita suka yi karo da Hajiya Rafi'at, da sauri ta zaro ido tana yi masa kalon mamaki domin Bata san shigowarsu ba, ido Hudu suka yi inda gabanta ya fadi, tayi saurin sada kanta kasa shi kuwa yaki dakin hanyar balatana ta fice,

Hajiya hawau ta taho tana fadin lafiyarku kuwa yayanan ? Naga kun tsare hanyar ficewa


hajiya Rafi'at ta ce " hajiya shine ai ya tsare hanyar fa

Idriss ya ce" to hajiya ta shige mana ?


Hajiya hawau tayi murmushi ta juya tama daina shigan balatana su fake da ita


Rafi'at ta juya itama zata bar wajen da saurinsa ya riko hannunta ya jawota tamkar wata beby ya hadeta da garun dakin

Idannuwanta ta rintse tana mutsukmutsuk da baki, Idriss ya tsurawa bakin nata ido Yana kalonta

Jin yayi shiru ne t'a bude idannuwanta ta sauke su à cikin Idannuwansa, ta kasa janye idonta daga NASA

Idriss ya saki murmushi à hankali ya ce" hei *I Love u*

Aunty Rafi'at ta zaro ido ta kasa dauke idannuwanta daga fuskarsa gabanta na dukan uku uku

Idriss ya kashe mata ido daya ya ce" Yaya dai madame, kalon fa ?????


Da sauri ta sada kanta tabi ta kasa hannun NASA tayi dakin da gudu tana ajiyar zuciya

Yayi murmushi y'a ce " she love me too, yayi gaba abinsa


Yana dawowa dauke da kayan aikinsa ya shiga aune aunensa inda ya bukaci fitsarinta, bayan tayi ta bayar ya kuma daukan jininta �a fice, ita kuwa tayi lamo à cinyar hajiya Fadimatu, inda Mubasshir yake zaune rike da hannunta daya yana dan murzawa, hajiya Rafi'at tana dan shafa gashin kanta ita kuwa hajiya hafsat sai cin abincinta take domin juna biyu ne da ita mai shegen sakata kwadayi du da ba Wanda ta fadawa har shi kansa mai abin,

Hajiya hawau ta kare mata kalo ta ce" wai y'ata watansa nawa ?


Hajiya hafsat ta zaro ido domin ta san da ita hajiya hawau take, ba shiri ta Mike tana fadin " Wa ?, tayi gaba ba tare da ta tsaya an fada mata Wa din ba,

ai kuwa hajiya Fadimatu tayi dariya ta ce" haba kin rigani à fili na rigaki à badini hajiya, Allah ya raraba Lafiya

Yar mahaukaciya ta zaro ido zata Mike Idriss ya shigo da result yana ta murna ya ce" an daura auren


Hajiya Fadimatu ta ce" oh yaren zamani idriss to barka


Idriss ya dan sine kai yana mikewa Mubasshir takardar gwajinsa yana hangen Rafi'at da ta sada kanta kasa tana share hawaye, wannan karen kam kukan dadi take( Wa ya fada miki)

Hajiya hawau ta shigo tana fadin" an daura Aure ba ango, ya akayi baku je masalaci ba ?


Mubasshir da ya buda takardar bayan ya yiwa Idriss barka yayi saurin cewa what ? Yana zaro ido ya kali Idriss yace"docter baka fasara min abinda nake gani ba ?


Idriss ya ce" congratulation, abinda ka gani hakane

Mubasshir yayi saurin kai kansa kasa yayi sujada yana ta murna, yana dagowa ya dagota ya rungume à gaban su hajiya Fadimatu wace itama murnar ta hanata zama, à tare suka yi gaba suka bar masa dakin domin kara rungumeta yake yana lalubar cikinta dake shafe yana fadin"beby boy or girl hi, dadyne, how are u ? Kana cin abinci ? Kana jina ?


Yar mahaukaciya sai sine kai take a ranta tana mamakin rashin kunyar AA












Alhamdulilah , Alhamdulilah, dukan godiya ta tabata ga ALLAH buwayi gagara misali da ya bani ikon ganin Karshen novel dina *Yar Mahaukaciya* Ina fatan du Wanda ya karantashi ya karu da abin karuwar dake ciki sannan Ina neman gafarar du Wanda na batawa sanadiyar wannan novel nawa na biyu bayan *Duk karyar kada na ruwa ne* , Allah ya hada mu à novel dina na gaba mai suna *Daga tafiya daukan soja* Na gode taku y'arku, kanwar ku, yayarku *Sajida* Y'ar mutan Niger,...

29 / 29