Author : Nainerh KD Category : Romance
farida a hanun sa inda yayi mata kashe da Babar murya cewar ba ita ba taba lafiyar yar sa idan ba haka ba shi da ita sai dai su raba hanya
Tun daga Ranar ta fita harkar mu gabaki daya banda mijinta, Ana haka muka wayi gari ba ita ba labarin ta sanan ba yarinya
Banban hankalin sai da Farida ta bayana a gaban mu tayi mana korar kare kan bata san mu ba , abin mamaki shi ma a lokacin take yanke ya nuna bai taba ganin mu ba , muna ji muna gani muka fito ba tare da sanin inda Rafi'at ta nufa ba
Haka muka ci GABA da rayuwa da gadon abana , cikin haka itama mama ta rasu ta barni ni kadai , Allah shine gatana a haka har na zama wani Abu a duniya aman a kulun ina neman Yar uwata ruwa a jalo
Cikin ikon Allah , Allah ya hada mu a ka'aba ,bayan mun zauna ta bani labarin mutumin da ya ceceta Wani Baban malami mai fada a ji a kasar Kano , shi ya kade ta da mota bayan ya dawo daga karatu tsakar dare, cikin ikon Allah tana farkawa cikin hankalin ta ta farka, sai dai tsananin mamakin ganinta a cikin daudar nan da kuma alamar haihuwa da tarin tambayoyin inda muke harda y'arta suka sake saka ta a rudani
Da kyar da adu'a da ban baki da rokon Allah ta samu nutsuwa inda ta fadawa Malan labarin rayuwarta abinda ta sani harda tana konce rungume da Islam Farida ta shigo ta watsa mata wani jini a jikinta sanan ta turo mata wani kasko tirare ya Bade dakin daga nan sai ganin ta da tayi a asibiti
Jin hakan Malan ya gane cewar aikin asiri ne, daman ya shiryawa iyalan sa tafiya haji sai ya saka ta itama da niyar idan ta dawo zasu tafi Lagos ta neme mu ,
Hajiya fadimatu ta sauke ajiyar zuciya ta ce" lale rayuwar ku na cike da abin al'ajabi, aman Alhamdulilah yanzu komai ya zo karshe tunda har sakayar Ubangiji ta fara aikinta
Muryar Hajiya Rafi'at ce ta katse musu hirar tasu inda tana ta zubar da hawaye ta kama hannayen Hajiya fadimatu ta ce " aunty kiyi min rai ki kaini na ga yarinyata dan Allah
Hajiya fadimatu ta dafa hannunta cikin tausayawa ta mikar da ita ta ce " mu tafi, domin nima ina son ganin wani irin farin ciki Yar fadimatu zata yi na yin arba da magaufiyar ta sanan ta san cewar ba laifin mahaifinta bane dan ta tsinci kanta a bola ba
Haka suka dugunzuma suka nufi gidan su AA Mubasshir dan hada Yar Mahaukaciya da Mahaifitarta,,,,,,,muje zuwaπππππππππππππππππππππππππππππππππππππ³πͺBelles Γ©crivaines du Niger
*'YAR π§π»*
*MAHAUKACIYAπΉ*
*_Na SAJIDA_*
64
Readers na kuma yin mantuwa Sunan kishiyar mahaifiyar Yar mahaukaciya *Hajiya Falmata* na gode.
Suna isowa gidan tayi kokarin bude kofar ta fita Hajiya Fadimatu ta riko hannunta ta ce " maman y'a ta Dan Allah ku Dan dakata na Fara shiga nayi mata bayani a tsanake Dan bana son ta kuma suma domin a dalilin ta ga Hajiya hafsat sai da ta suma,
Hajiya Rafi'at tayi murmushi ta koma ta jinginar da kanta, ko ba komai mutumin da ya rungumi gudan jininka ya kaunace shi ai ya isa a girmama shi,
Cikin nutsuwa ta tura falon ta shiga, hango Yar Mahaukaciya tayi tana zaune still kukan take bata daina ba, ga goshinta da jini, Cikin faduwar gaba ta karasa ta dago kanta
Yar Mahaukaciya na yin ido hudu da Hajiya Fadimatu ta fada jikinta ta saki wani kukan,
Hajiya Fadimatu ta shafa bayanta a hankali ta ce" wa ya kuma batawa y'a ta rai? Wa ya saka min yarinya take kuka?
Yar Mahaukaciya tamkar wata baby ta turo dan bakinta ta ce" Mamana kin ga Yaya ne da matar sa"
Hajiya Fadimatu ta zaro ido tace " wani abu suka Yi miki? Su suka ji miki ciwon nan? Suna ina?
Yar Mahaukaciya ta ce" aa mamana ba fa su suka ji min ba, faduwa nayi, su sun hanani baci na,
Hajiya Fadimatu ta Kama hannunta suka nufi dakin ta, ta dauko kada ta goge mata wajen da jinin ya digu, ta shafa mata Magani wajen da ya kumbura sannan ta zauna ta fuskanceta Cikin nutsuwa ta kirayi Sunan ta, ta ce" Rahma
Yar Mahaukaciya tayi gagawar kalon ta domin ta san tabas abinda zata fada Mai mahinmanci ne Dan kuwa bata taba kiranta da sunanta ba, Cikin mutuwar jiki ta amsa da na. Am,
Hajiya Fadimatu ta ce " *kina son sanin ainahin sunan ki Wanda abanki ya dasa miki?*
Yar Mahaukaciya ta dago kanta a Karo na biyu gabanta ya kuma faduwa ta Kali Hajiya Fadimatu Cikin gargadar murya ta ce" mama kin yarda shi ya haife ni?
Hajiya Fadimatu ta ce" tabas Elhaj Muhhamad Mahaifinki ne, na yarda da hakan,
Yar Mahaukaciya ta kawar da kanta gudun kar Hajiya Fadimatu ta ga hawayen bakin Cikin dake shirin zubo mata,
Hajiya Fadimatu ta dago habarta ta ce" Shin ba hamdallah ta fi dacewa ki Yi na ganin Mahaifinki? Kina fushi da jarabawar ubangijin ki ne? Shin baki duban Wa'inda kika fi? A rayuwar bola da kika Yi Allah ya Kare ki, sanan da kika fito daga bola Allah ya kasance Cikin baki Kariya, kinga rayuwa kin sha wuya, Aman Hajiya Rafi'at ta fi ki Shan wahala du da haka banban burinta ta ganki, balatana Mahaifinki Wanda aka Raba shi da ke a lokacin da Allah ya bashi ke, a lokacin da yake cike da burin ganin kin taso, ya GA girman ki ya ji maganar ki, ya GA dariyar ki, ya ji dumin jikin ki a matsayin ki na y'a kwaya daya da ya malaka a duniya, aka raba shi da matar sa wace suka yi auren soyaya, aka juyar masa da kwakwaluwar sa ya manta kowa sai yau da Allah ya hada shi da ke komai ya karye aman zaki kasa kalon sa y'a ta? Shin wannan ni'imar bata isa kiyi ta murna Kina yiwa Allah godiya ba? Haba *Fadimatul Islam Mai baban suna*
Yar Mahaukaciya dake zubar da hawaye ta tsurawa Hajiya Fadimatu ido Tana sauraron abubuwan da take fada Wanda tamkar da ita take to Aman sunayen da take kira ita ko daya bata Sani ba hakan ya sa ta ce" *wanene Elhaj Muhhamad? Wacece Hajiya Rafi'at? Wacece Fadimatul Islam?*
Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta dago habarta ta ce" *Elhaj Muhammad shine Mahaifinki, Hajiya Rafi'at shine sunnan mahaifiyar ki, Fadimatul Islam shine Sunnan da Mahaifinki ya dasa miki*
AI kuwa Yar Mahaukaciya ta fada jikin Hajiya Fadimatu ta kuma sakin wani kukan, da Kyar ta lalashe ta, tayi shiru ta samu ta fada mata labarin da Hajiya hafsat ta fada mata,
daidai wannan lokacin Yar Mahaukaciya ta yarda da maganar Hajiya Fadimatu sannan ta yarda Elhaj Muhammad mahaifinta ne, to aman ina mahaifiyarta take?
Hajiya Fadimatu ta kamo hannunta ta ce" zo ki gani,
Yar Mahaukaciya ta Mike Tana biye da ita, daidai sun fito, Su Mubasshir ma sun fito sahla sai kuka take shi kuwa idannuwansa sunyi jajajir yana tafe Tana binsa a baya tana rantsuwar sai ya saki wanan mahaukaciyar yarinyar,
Hajiya Fadimatu ta Kare musu Kalo ta ja Hannun Yar Fadimatu suka sauka inda ladidi Mai aiki ta Sanyo su Hajiya Rafi'at ta cika su da kayan marmari Aman sun kasa taba komai, Sunyi zuru cike da zunlumi Suna ta tinani Hannun Hajiya Rafi'at Cikin na Elhaj Muhhamad sai murzawa yake yana karawa ko sun sami kwarin guiwa,
saukowa suke su hudun domin shi Mubasshir biyo su ya Yi, itama sahla Tana biye da shi Dan ta ci alwashin sai dai ya zabi guda a Cikin su ko kuwa wly kowa ya rasa shi har uwar tasa (to Kaji )
Suna saukowa su duka suka mike Suna hango Yar Mahaukaciya da ta labe a bayan Hajiya Fadimatu,
kasa daurewa Hajiya Rafi'at tayi ta matso a hankali ta ce" *Islam*
Gaban Yar Mahaukaciya ya fadi domin wanan muryar bazata taba mantawa da ita ba,
da sauri ta fito daga buyar ta zaro ido bakinta na rawa ta ce" *Mahaukaciyata ke ce ko Mai Kama da ke ce?*
Hajiya Rafi'at ta lumshe idannuwanta ta buda hannayenta, AI kuwa da gudu Yar Mahaukaciya ta fada jikinta suka kankame juna inda suka saki wani irin kuka na farin ciki,
elhaj Muhammad ya kasa Hana kansa isawa garesu, ai kuwa shima ya isa ya rungume su sai kuka(π€π€£ )
gaba daya falon kukan suke banda sahla dake kalon wani sabon salon rainin hankali, sai Mubasshir dake lumshe ido kukan abin sonsa da mahaifiyar sa na taba masa zuciya,
wasa wasa sun ki daina kukan kuma sun ki sakin junan su, ganin Daman kukan nan shi ta wuni tana Yi, kuma idan ya zuba mata ido sai tayi ta Yi har wata cutar ta Kama ta ya sa ya matso Kadan ya daidaita murya ya ce" *Am Dad ( kuma kaiπ€), am maman Mubasshir, am aunty* kukan ya isa hakanan kar a kamu da rashin lafiya,
Elhaj Muhammad ya Fara tsagaitawa sanan suma suka Yi shiru, aka zazauna, nan Hajiya Rafi'at ta bukaci Yar Mahaukaciya ta fada mata irin rayuwar da suka Yi a bola da kuma yanda aka Yi suka rabu,
Yar Mahaukaciya ta lumshe idannuwanta tamkar a lokacin take rayuwar ta fada musu komai abinda ta Sani har haihuwar Mahaukaciya ita ce sanadiyar rabuwar su,
Hajiya Rafi'at ta zaro ido ta ce" inalilahi Wa'ina ilaihi Raj'une, harda haihuwa nayi a Cikin haukan? To a ina na οΏ½adu da Cikin? Ina abinda na haifan?
Yar Mahaukaciya ta kuma rintse idanuwanta ta ce" abinda kika Haifa bayan na Baro bola mun hadu da jarabawa kalakala Allah ya Amshi abinsa, ............... Nan ta ci gaba da basu labarin bayan fitowarta daga bola saceta da akayi aka nufi Lagos da ita, matar da ta so lalata mata rayuwa Mai sunan Falmata a yanda ta ji inyamurar nan tayi kiranta da oga, Allah ya ceceni mijinta ya dawo a lokacin, nan na samu na fice.
Elhaj Muhammad ya dago kansa da sauri ya ce" Falmata? Hajiya Falmata? Inyamura a gidan? , nan ya zaro wayarsa ya ciro hoton matarsa Hajiya Falmata ya nuno mata
ai kuwa Yar Mahaukaciya ta mike dafe da kirjinta ta ce" tabas ita ce, wannan matar ce, lokacin da ta shigo tana fadin kar na damu ba zata jima ba Dan ma boka ya ce dole dole sai mai da kar asirin da tayi shekara 15ya karye, tana kokarin aikata nufinta akace mijinta ya zo, nan ta ce a fitar da ni ta baya yanda bazai gan ni ba
Elhaj Muhammad ya shiga maimaita inalilahi Wa'ina ilahi raj'une, tabas matarsa ce kuma Yar uwarsa wace Hajiya Rafi'at ta saka baki ya aureta Ashe ita ta ruguza masa farin Cikin sa? Kai duniya abin tsoro abin a bi a sanu ce, ya dube su ya ce" ga sakayar Allah nan tun ba. Aje lahirar ba domin yanzu haka Tana psychiatric na shine tana hauka har ta kashewa likitan Karen sa sai fada yake kan aje a daukota tun kafin ya sake ta,
gaba daya suka shiga jimami Suna Al'ajabi, rayuwa kenan ko an zalince ka idan kayi hakuri Cikin ruwan sanyi Allah zai saka maka, tsoro da kaunar musulunci ya Kara darsuwa a zukatan su, kowa tasbihi yake a Cikin zuciyarsa yana wasa Sarkin da shine Sarki Wanda buwayarsa take a bayane gagara misali, ubangijin samai da kansai, Mai wuta mai aljannah, Mai bada umarnin abu ya kasance ya kasance, Mai kowa Mai komai, Wanda bai haifa ba, ba'a haife shi ba, wannan dai gagara misali,, *Allah* kenanβΊ,
muryar Sahla ce ta katse musu wanan shauki da suka shiga inda ta matso Kusa da Elhaj Muhammad mai gidan mahaifinta a wajen aiki kuma mijin kawar mamarta ta ce" Aba, ban gane ba, shin mainene hadinka da wannan mahaukaciyar Yar Mahaukaciya wace uwarta MA tayi Cikin shege balatana ita gashinan Tana fadi da bakinta ta wani zo tana Yi maka karya ka yarda har kana zubar da hawayenka, da ganin zagar idanuwan yarinyar nan ka San Yar bariki ce ba karama ba Aman har a iya sauraron ta harma a aurawa mijina ita bayan ba a San asalinta ba?
wani irin kalo ya watsa mata Wanda ya sa yata hadiye sauran maganar ta, yana Al'ajabin daman haka take? Bata da kunya har ya dauketa tamkar Yar sa ya Cikin sa yake kyautata mata? Daidai da rigimar mota da ta Dora mahaifiyarta ta kawo Karar MahaifinTa ya ki saya mata da yayi masa magana ya nuna bashi da Hali hakan ya saka aka kawo mata ashe bata da kunya? Ransa ya Kai kololuwar baci ya buda baki ya ce"""""""""""""""""""""""""""::::::::::::::::::::::::::::::::::::""""""""""""""π³πͺBelles Γ©crivaines du Niger
*'YAR π§π»*
*MAHAUKACIYAπΉ*
*_Na SAJIDA_*
65
Cikin wata irin murya mai cike da mamaki da haushin kalaman bakin Sahla Elhaj Muhammad ya ce" ashe baki da nutsuwa?
Cikin sauri Yar Mahaukaciya ta ce" a yau na hadu da abanna, ina son ya wuni Cikin farin ciki, bana son Wani abin komai girmansa ya daga masa hankali, please abanna Kar ka mayar da bacin rai Cikin bacin rai,
Sahla da ta Gama harzuka ta ce" ke ki Kali kanki ki kirayi kanki y'ar dad? No baki Kai wannan matsayin ba, ke fa almajira ce, mabaraciya ce, Mahaukaciya ce, sanan Yar Mahaukaciya,
Mubasshir Cikin bacin rai ya ce" sahla ya ishe ki haka,
Sahla ta juyo Cikin bacin rai idannuwanta sun fara rufewa ta ce" to Kai kuwa shanyaye, Da aka Koreta daga gidan namu shine ta shanye ka, ka kwaso ta ka kawo ta nan kana kawar da jarabar ka har ka goga min cuta ko? To walahil azim Baku isa ba, ni da ku mu zuba mu gani, Idan takamarta karuwanci, iya bariki ni na fita iyawa, kuma ka Sani ni sahla Dan ni kadai aka halice ka Kai Mubasshir,
Hadiye maganar tayi sakamakon dauketa da mari da ya Yi, ya Kara mata wani,
Gaba daya ido suka zaro, Da sauri Hajiya Fadimatu ta nufo shi haka Elhaj Muhammad suka rike shi inda ita kuwa ta silale nan jini ta hancinta yana zuba,
Hajiya Fadimatu ta ce " why son? Why zaka taba lafiyar jikinta bayan an Hana ka dukan koda namiji ne bare mace? Shin ka manta ne?
Elhaj Muhammad ya ja Hannun sa ganin yana kokarin sume masa ya kasa furta komai jikinsa sai rawa yake,
Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya tana adu.ar Allah ya tsagaita fushin sa,
Hajiya Rafi'at ta nufo sahla ganin tana habo harda yawu na diga daga bakinta, da sauri ta mika hanu zata taimaka mata, Aman karfin Hali da muguwar zuciya suka saka ta ja jikinta a haka har ta fita da kyar ta shiga motar ta , ta nufi asibitin yayanta tana gursheken kuka,
Dakin Yar Mahaukaciya ya nufa da shi ya zaunar da shi sanan Ya shiga bayi ya hada masa ruwan wanka Mai mugun sanyi ya taimaka masa yayi wankan, har a lokacin bai ce ufan ba, Shima Elhaj Muhammad bai ce masa komai ba, , Suna fitowa ya nufi gadon da shi ya konta , ya kuma laptop ya saka masa karatun alkur.ani mai girma sanan ya fito ya rufo masa Dakin
Yana saukowa Hajiya Fadimatu ta mike ta ce" Yaya dai? Ya suman ko?
Elhaj Muhammad ya ce" aman da kina da Cikin sa Sarki ya baki wanan tsumin ko?
Hajiya Fadimatu ta ce " haka, domin a ranar da aka shaida mana namiji ne, ya turo min da tsumin nan, to run yana yaro nake iya yina Dan gudun bacin ransa, dan idan ransa ya baci bai huce haushin sa ba suma yake, daga ya farka sai kurmancin kwana biyu
Elhaj Muhammad yayi murmushi ya ce" tsoho ya hada min yaro da rigima, Ai zamanin yaki ne ake irin tsumin nan, gashi shi kuwa baya son harkar sarautar MA, bare har yayi yaki,
Hajiya Fadimatu ta ce" haka,
Hajiya Rafi'at ta ce" wanan wani irin tsumi ne haka? Kar dai ya suman?
Elhaj Muhammad dake kalonta da mayatacen kalo tunda ta rukunkume shi a asibiti ta tayar da zaune tsaye ya ce" no akoy wata hanyar, ana saka mutun a ruwan kankara, sai a bashi abinda zai saka masa nutsuwa da yardar Allah idan ya farka zaiyi magana aman fa ba kamar da ba, sai ya kwana biyun nan sai ya saku,
Hajiya hafsat ta gyada kanta Tana ta shafa gashin kan Yar Mahaukaciya wace tayi zuru tsoron Mubasshir ya darsu a zuciyar ta, Wanda bata taba jin irinsa ba, ta kawar da kanta ya sauke ajiyar zuciya Tana tuna zako ta iya Jan ajin nan? Kar taje ta ja ya jaza mata duka(hhhh) , wata zuciyar tace mata "wani Jan ajin kuma ke da baki Kai wannan wajen ba, ke fa a kalon Yar bariki yake miki,
Hajiya Fadimatu ta katse mata tinaninta inda ta ce" Yar Fadimatu tashi ki dauki abinci ki ci please,
Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta mike ta ce" to mamana, ta nufi kicin
bayan tafiyarta Hajiya Fadimatu ta gyara zama ta zayane musu komai tun ranar daurin auren Mubasshir da ya kawo mata Fadimatul Islam har zuwa shawarar da suka yanke na