Author : Nainerh KD Category : Romance
idannuwanta sai rufe su take tana cije lebenta, har ta shige bayin suka Mara mata baya
hajiya Fadimatu ta zauna Kusa da Hajiya hafsat ta ce " sister ya zakina nunawa y'ata halin KO in kula ne haka ? Kin ga fa irin wahalar da ta sha na rashin ki aman sai Ina ga bakya Bata kulawar da ya dace da ita
hajiya hafsat ta zaro ido ta ce" Lah aunty, wace kulawa kuma zan baiwa islam wace ta fice Wada kike Bata ? Kin tarbeta à lokacin da kowa yake hantarar ta, kin zauna da ita ba tare da kyama ba, kin sakata à hanyar samun ilimi, kin koyar da ita girki, kin koyar da ita tsaya, kin aurar da ita ga miji mafi daukaka à rayuwarta mai kuma zanyi mata ? Aunty ki Sani wly wly islam kece mahaifiyarta domin ni haihuwarta kawai Nayi, har kunyarta nake ji a zuciyata, Ina Jin dacin irin rayuwar da na gana mata,
Ta karashe zancen tana kokarin mayar da hawayenta
hajiya Fadimatu ta ce " karki ringa tuna baya, abinda kika aikata ba à cikin hankalinki ba kike yiwa nadama ? Haba sister ai bai dace irin haka ba, na Sani sarai islam Ina bata kulawa aman ki Sani ya zama wajibi kema ki ringa sakata à jikinki domin ba komai zata iya fada min ba, KO daman can islam akoy zurfin ciki bale yanzu da yaron nan ya yi mana haka, kina gani fa irin saurin da ta kwasa du dan kar à gane baiwar ALLAH, Dan haka muna barar hakan
hajiya hafsat ta kawar da kanta tana murmushi à fili ta ce" korafinku ya karbu
à gaskiya na san Ina jinkiri wajen posting, aman Ina neman afuwarku kun san yau da gobe sai ALLAH, abubuwan ne sai à slow, thanx à lot🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*Na*
*Sajida*
74
*Uwa Tana Iya Kula Da 'ya'ya Sama Da Goma Amma A Wasu Lokutan Sai Ka Tara 'ya'ya Goma Sun Kasa Kulawa Da Uwarsu Guda Daya!!! Yakamata Musan Cewa Abubuwa Masu Mahimmanci Da Daraja Basu Cika Maimaituwa A Rayuwar Mutum Ba... Shi Yasa Kowanne Mutun Uwa Daya Kacal Gareshi!!!
Kuma Watarana Zamu Wayi Gari Babu Ita A Duniyar Nan... Dan ALLAH Mu Kara Kulawa Da Mahaifanmu Musamman Ma Uwa Wacce Babu Kamarta A Duniyan Nan!!!
Ya ALLAH Ka Bamu Ikon Yiwa Mahaifan Mu Biyayya Ka Jikan Iyayenmu, Ka Basu Aljannatul Firdausi, Allah Ya Sakawa Iyayenmu Da Mafificin Alkhairinsa Duniya Da Lahira*
bayan ta ajiye wayar ta shaidawa mahaifiyarta aiki ne ya rike shi ashe
Hajiya Marhaba ta ce" jibi ne tsinaniyar yarinyar zata tare KO ?
Sahla ta ce"Eh mama
Hajiya Marhaba ta ce" toh duk yanda zanyi zanyi na kawo miki hadin maganin kinji ?
Sahla ta amsa mata ta Mike tana fadin bara ta juya kar aje yayi safiyar dawowa gidan Bata nan
Hakan kuwa hajiya Marhaba ta barta cikin tsohon daren nan ta juya ta koma gidanta tare da dumbin muguwar hudubar mahaifiyarta
Tunda ya juya ya fita bai sake saka Islam à Idannuwansa ba, domin Hajiya Fadimatu ta kasa ta tsare ta hana shi hawa saman balatana ya ganta, duk irin yanda yake fakewa da Bara ya dauko wani abin sai ta tare shi ta ce lala ba zai hau ba, hakan na matukar mahalar da shi,
Da kansa ya je gidan su Fati kawar islam ya shaida mata Auren islam aman ya boye mata mijin domin ya fi son ya zame mata surprise, auren kansa tayi mamakin sa domin Bata taba kawowa à ranta rashin zuwan islam school na kwana biyun nan haka ne ba, kuma ai suna waya Bata taba Shaida mata ba, Jin ya ce à washe gari zata tare ya sanya ta shirya da yama ta nufi gidan su AA Mubasshir,
Konce take tana baci, wannan bacin ya zame mata tamkar na rashin Lafiya, ta fiya baci à yan kwanakin nan,
Hajiya Hafsat ta shigo dakin ta Nemi gefen gadon ta zauna ta rasa ta Ina zata fara, à hankali ta saka Hannu tana dadaba bayanta
Firgigit Yar mahaukaciya ta farka tana adu'ar tashi daga baci, idannuwanta ta sauke à fuskar mahaifiyarta, da sauri ta zauna tana kalonta
Hajiya hafsat ta kawar da kanta à ranta tace " wannan ido na mahaifinki ai sai mutun ya tsorata, à fili ta ce" ni islam bacin Lafiya kike ?
Yar mahaukaciya ta ce " *Mahaukaciyata* da sauri ta rike baki ta gwalalo ido tana dan girgiza kai
Hajiya Hafsat ta jawota jikinta ta rungume ta tsam, kawai sai suka fashe da kuka irin mai tsananin nan, Wanda KO ranar da suka hadu basu yi shi ba,
Sai da suka yi mai isarsu sannan hajiya hafsat ta fara tsagaitawa tana shafa gashin kan Yar mahaukaciya, à hankali ta ce" sunan da kike kirana da shi ne à da KO ?
Yar mahaukaciya ta dago kanta ta ce " Eh, sunan da yara suke fada miki ne, nima da na tashi sai nake kiranki da shi
hajiya Hafsat tayi murmushi tana share mata hawaye ta ce" shin Ina dukan ki à cikin hauka KO ?
Yar mahaukaciya ta lumshe idannuwanta ta bude ta ce" duk da à cikin hauka kike à lokacin mama, idan zaki yi baci sai Kin jini à jikinki idan kuwa bana nan na tafi nemo mana abinci har na dawo kina zaune kina duba hanyata
Hajiya Hafsat ta rintse idannuwanta ta ce " ki yafe min *Islam*
Da sauri Yar mahaukaciya ta ce " Mama, karki nemi gafarar abinda baki da laifi, ba abinda kika yi min, Dan ALLAH ki dena tinawa
Hajiya hafsat tayi tsai tana kalonta, can ta ce " tell me, kina Son sa ?
Yar mahaukaciya ta zaro ido tana kalon mamarta
Hajiya hafsat ta ce " eh fada min,
Yar mahaukaciya ta e" wane ?
Hajiya hafsat ta girgiza kai tana murmushi ta ce" mijinki nake nuFi, kina son sa ?
Yar mahaukaciya tayi saurin rufe idannuwanta gabanta na faduwa, tabas idan ta buda makaryacin bakinta ta furta cewar Bata son Dan Aljannah sai à nada mata sarauniyar makaryatan duniya baki daya, Dan haka gwara tayi shiru shine mafi aala à gareta, sai dai tana mugun Jin tsoronsa, tana Jin tsoron haduwarta da shi, sannan tabas idan abinda ya faru da ita da shi ne Aure ta san zata wahala, Karshe ma ta mace domin ta ji azabar da Bata san akoy irinta à nan gidan duniya ba
hajiya hafsat ta katse mata tunanin da ta afka ta ce" my islam, ki buda kunuwanki da kyau ki saurare ni, ki dago muyi zancen fahimta da ke à matsayina na wace tafi kowa sanin sirinki, shin kina son Mubasshir ???
Yar mahaukaciya ta dago kanta still idannuwanta à rufe kanta à Sade kasa cikin wani irin yanayi ta gyadawa mahaifiyarta kai tana nufin eh
hajiya hafsat ta ce " Alhamdulilah, kin san mai zan fada miki ? Aljannarki zaki je nema, ki Sani islam akoy da babu mijinki shugabanki ne, Lafiya da rashinta kyautatawa à gare shi ya zame miki wajibi, da fara'a KO babu kokarin kwontar masa da hankali na rataye à wuyan ki, yi Nayi Bari na Bari islam, à yanzu yanda mijinki yake da iko à saman ki KO mu da muka haife ki Bamu da shi, ki Sani idan kin gyara auren ki kin gyara lahirarki, shi kuwa gyara aure shine biyaya ga mijinki, Islam baki da sama da mijinki duk abinda ya saka ki yi kiyi shi banda Wanda ya sabawa adinin musulunci, Tsafta, girki, tsaftar gidanki, komai ki rike da hanu bibiyu, tsananin ki da kishiyarki kyautatawa, *Islam, Islam, Islam* sai da ta kirayi sunan sau uku taci gaba *Islam* duk ranar da kika je gaban boka KO malan kika durkusa da bukatar kan mugun nufi ga abokiyar zaman ki KO à kawar da hankalin mijinku à kanta KO wani mugun nufi ni mahaifiyarki ban yafe miki ba, ki Sani babu wani makami KO kariyar da ta fi kiyi alwallah ki tsarkake kanki ki fadawa ubangijin ki, ke kece shaidar abinda ya faru à kanki kinga à yanzu Allahn nan shi dai ya ga bayan ta, sannan yaci gaba da kare ki, kiyi ta hakuri da zaman gidan miji domin yau da gobe sai ALLAH,
haka mahaifiyar islam tayi ta Bata shawarwari kan rayuwar aurenta, da mahinmancin hakuri da barnar shirka, har lokacin jikonta yayi, da kanta ta karba ta jika islam tana kara koyar da ita yanda zata kula da kanta tun tana Jin kunya har ta sake sai dai tayi dariya KO ta rufe idannuwanta
suna fitowa suka zauna tana caje mata kai Fati kawarta ta shigo da gudu tamkar karamar yarinya
rumgume juna suka yi suna ta murnar ganin juna,
fati ta ce" kawata yanzu mamanki take fada min wata magana, Dan ALLAH yanzu AA ne mijinki ? Daman ba yayanki bane kika ce yayanki ne ?
Yar mahaukaciya ta ce" ke hajiya bakya zama sai tambayoyi ? Kinga mamana nan tayi mata nuni da Hajiya hafsat dake murmushi tana kalon su
Fati ta ce" Lah kinga kuwa kuna kama wallah, ta duka ta ce" mama Ina yini
Hajiya hafsat ta amsa fuskarta cike da fara'a, Daidai nan Elhaj Muhammad ya shigo da salamarsa yana fadin jama'a Ina cigiyar My princesse nd my wife
Hajiya hafsat ta dago kanta ta ce" du sun bata
da sauri ya ce" ALLAH ya kiyaye, plz koda wasa kar ki kuma ambatar sunan Bata à gabana plz, koda wani abina ne ba'a gani ba ki ce" aban islam wannan abin ka sayi wani plz maman islam
Hajiya hafsat cikin murmushi ta ce" Aban islam kaga kawarta fa,
sai à lokacin ya juya yana kalon su ya Mika hanu ya kamo islam Ya jawota yana gyara mata gashin kanta ya kali Fati da tayi sharan tana bukatar karin haske à sunan *Islam* da kuma wannan mutumin da farin su iri daya shi da *Rahma* harda kwayar idannuwansu,
🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🙈🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*Na*
*Sajida*
75
*Watarana manzon Allah S.A.W. ya gama ibada yana addu'a Yana cewa Allah ka yafema sayyada Aisha R. A. zunubbanta da wanda ta sani da wanda bata saniba Da wanda tayi yanzu da wanda zataiyi nan gaba duk Allah ka yafemata ashe sayyada Aisha tana ji sai taji wani irin dadi sai tace: Ya RASUULULLAHI (S.A.W.) na gode sai Manzon Allah yace wannan addu'ar dana yimaki. Itace nake yiwa AL 'UMMATA A kowace Sallah. Allah ya karawa ANNABI daraja tare da wasila da farila à aljanar firdausss*
Ganin kalon na fati ya saka shi yin dariya ya ce" i'm Muhammad, nine aban islam, yayi nuni da Yar mahaukaciya
Fati ta ce" abanta fa ? Sis ??? Ta kali Yar mahaukaciya
Islam tayi murmushi ta ce" yeah, ni ba marainiya bace, wannan shine abanna, sannan wannan momyna, ni kuma sunana na gaskiya Fadimatul islam,
Fati ta ce" waouh, kenan hakane, waouh sister inai miki murnar ganin iyayenki, yanzu maman AA ta fada min komai to du sai nake Jin zancen tamkar wani Sabon zance,
Islam tayi murmushi ta kama hannun fati ta ce" haka Allah ya tsara, kinga Zo ki ga
Suka yi gaba, inda su Hajiya hafsat da mijinta suka ci gaba da tataunawa kan tarewar y'arsu kwaya daya da suka malaka à gidan duniya
Tunda garin ALLAH ya waye ake ta shige da fice a cikin gidan, masu gyaran dakin amarya na kanfanin Imran spécial aka dauko suke gyaran bangaran Islam, gado uku akayi mata kowani daki da nasa, kujerunta seti biyu na arabian da kalar na sarakai, ado� ash da fari ne ake tsara dakin da shi, komai ya ji zanzan,
Tunda yama tayi mahaifiyar Sahla ta Zo à sadade ta kawo mata maganin wajen bokan inda suka hada hadaden j'yaourt mai cike da na'a na'a sai kanshi yake ta dauko sabon caraf mai kyan gaske suka zuba dan madaidaici ta zuba maganin ta girgiza ta saka à firij Hajiya Marhaba ta juya bayan ta kara jadada mata ta tabatar ya sha fa,
Bayan salar magarib gaba daya familyn na zaune inda na hango wani a
hasken yadi fari kar sai Sheki yake, sheshekar kuka na tashi sai muryar namiji na adu'a , Yar mahaukaciya ce tsugune à tsakiyar falon inda Hajiya hafsat, hajiya Fadimatu, hajiya hawau, hajiya Rafi'at, Aunty habiba, Sai Elhaj Muhammad dake adu'o'in neman tsari ga Y'arsa, wace zai sadata da gidan mijinta à wannan lokacin,
sosai sukai mata nasiha, suka kuma nuna mata mahinmancin Hakuri da kuma ilar rashinsa,
Kuka suke su uku à bayane wato *Fadimatul islam, Fati, da kuma hajiya Rafi'at* su kuwa iyayen suna share hawayen su,
Makota da abokan arziki suka fara cicika motoci inda mahaifin Islam ya murje Idannuwansa ya dauko sabuwar motarsa ya kama hannun y'arsa tana kuka ya nufi mota da ita akayi amaryar koko da Fati kawarta,
Su suka fara isowa inda Elhaj Muhammad ya damka mata alkur'ani mai Girma ya kama hannunta ta shiga Gidanta da adu'a à bakinta,
Sai da ya sadata da dakinta ya kuma yi mata gargadin karta yi sake da adu'a sannan ya juya ya baro gidan zuciyarsa cike da raunin kukan Islam
duk irin azarbabin masu rakiyar amarya Hajiya Rafi'at ta kasa ta tsare ta hana kowa shiga bangaren islam, haka kowa ya hakura ya juya da santin falonta da sauran dakunan da suka leka, aka bar islam da fati da hajiya Rafi'at kanwar mamarta
konce yake saman makeken bed din dakinsa yayi rigingine Idannuwansa a lumshe, yana matukar mamakin irin yanda zuciyarsa ke azalzalarsa da ya je wajen islam tun kafin yan rakiyarta su juya, yana mamakin dokin da yake, cijewa yake tun karfinsa
Cikin takun yanga take takowa cikin dakin takalman kafarta na fitar da sauti kwos kwos kwos, uwargida kenan wato Sahla sai zuba kanshi take ta sha make up din yaudara,
Tafiyar tsutsa ta shiga yi masa tun daga wuyansa har kirjinsa, sosai sakonta ya fara caza shi domin daman à dane yake,
Idannuwansa ya buda ya sauke su à fuskar Sahla gabansa ya fadi, domin à lokacin mumunan aikin da ta shirya masa ya fado masa à ransa,
Murmushi ta sakar masa sannan cikin yatsina ta ce " wani irin ango ne mai baci karfe takwos bayan an kawo masa amarya à dakinta ?
Mubasshir ya tataro dukan kokarinsa dan ganin ya ja Sahla à sabon salon barikin da ta fido dan tunkuda shi à rami,
Jawota yayi ya hade bakinsa da nata ya shiga tsotsa Idannuwansa à lumshe
Gaba daya ya kashe mata jiki, ita kanta ta san à wannan fanin ita din ba kowa bace wajen AA,
Hudubar mahaifiyarta ta fado mata à ranta, hakan yasa ta zare bakinta da sauri tana fadin" Ya Salam, huby plz tashi na raka ka bangaren matar ka bana son ka shiga hakinta KO kadan
Mubasshir ya kuma jawota ya ce" mai yasa zaki katse min rabar jikinki ne ? I need u, plz matso gareni
Sahla ta Mike da sauri tana fadin kai Hiby baza'ayi haka da ni ba, so plz bara na kawo mata dan yaourt din na tarban amarya da na Adana maka rabonka ka sha ka Isa ga amarya domin yau darenta ne,
Tana gama fadar haka ta juya da murmushin yaudara à fuskarta
,
Mubasshir ya rintse Idannuwansa ya ce "tabas yau daren amaryana ne, sai dai kin cuce ni Sahla
Bata dauki wani lokaci ba sai gata dauke da caraf din da kuma kofi kwaya daya
tana zuwa ta cika kofin ta zauna ta mika masa tana fadin" oya daga bakinka na baka ka koshi mu tafi na raka ka
mubasshir ya sakar mata murmushi ya daga bakinsa yayi bismillah ya rufe Idannuwansa ya ya................................😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳😳🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*Na*
*Sajida*
76
*Ya UBANGIJI ALLAH ka karbi tubanmu,Ka wanke zunubanmu,ka amsa addu'o inmu,ka tabbatar da hujjojinmu,Ka shiryar da zukatanmu,Ka tsayar da harshenmu akan gaskiya,kuma Ka cire duk wani mugun tunani daga zukatanmu.Mun sani, kuma munyi imani, shiriya, kariya da rahama duka naKa ne.Ya Allah,Ka samu acikin inuwarka alokacin da babu wata Inuwa sai taKa, Ya Allah Amin,summa Amin*
Rintse Idannuwansa yayi tare da yin bismillah ya fara shan yaourt din da Sahla ta kawo masa yana tunanin yanzu koda gubar ce haka zata didika masa ya sha,
Har ya kusan shanyewa sai ya gumtse à bakinsa ya tare da hannunsa ya cire kofin ya jawota jikinsa ya hade bakinsa tamkar zaiyi kissing dinta
Idannuwanta ta zaro Jin ya zuba mata yaourt din da nufin itama ta sha,
Da sauri ta janye kanta tayi bayi da gudu tana kokarin amai domin har ta hadiye wani,
Murmushi ya saki ya Mike a nitse ya bi bayanta ya jingina kansa da jikin bayin sai da ta gama amanta sannan ta juyo,
Gabanta ne ya fadi ganninsa à tsaye yana kalonta
Mubasshir yayi yannayin damuwa ya ce" Sahla Lafiya ? Kyankyamina ne kike ?
Da sauri Sahla ta zaro ido ta ce" kyankyaminka fa ? No wly KO daya
Mubasshir ya tsareta da ido ya ce" to ya akayi kike kakari haka ? KO dai kin hadiye wani Abu à ciki ne ? KO da wani abin à ciki ?
Sahla ta kuma zaro idannuwanta tamkar mujiya ta ce" wani irin da wani abin à ciki ? Kana nufin zan saka maka wani Abu da zai cutar