Yar Mahaukaciya Complete Hausa Novel

Author :  Nainerh KD Category :  Romance

Chapter   20 / 29

57K to 60K   out of 85.2K words

idannuwanta dan kuwa ta san inda ya dosa , ya ce gaba da fadin " *a cikin su ya fi su kokarin siyan zuciyarki ne har kika shiga wanan yanayin dalilin sa?*


Kafin ta bashi amsa ya juyo wajen wanan mutumi dake tsaye jikinsa na rawa , so yake ya je gareta aman yanayin hararar da take binsa da ita ya saka shi ja ya tsaya yana sauraron wani kalar yare da AA ke furtawa dan har ga Allah shi magaganun a dunkule suke zuwan masa,


Mubasshir ya matso kusan shi cikin yanayi na tsana ya ce" kana son tafiya da matata ne? Mai ya kawo ka gidan mu Elhaj? Why zaka yi kokarin rusa min farin cikina? " Kasan wani abu kuwa? *I LOVE TS GIRL* ban shirya rabuwa da ita ba sai dai a rabani da lumfashina,




A tare suka zuba masa ido inda cikin wata murya mai ban tausayi wanan mutumin ya dora hanunsa a kafadar AA ya ce " *SHE'S MY DAUGHTER*





ba Mubasshir da su Hajiya Fadimatu ba , ni kaina sai da na wuntsula jin wanan batu......., muje zuwa ba shi Kenan ba

[12/15, 4:36 PM] ‪+234 902 472 4465‬: 🇳🇪BELLES écrivaines Nigériennes


👹 YAR MAHAUKACIYA👹 na SAJIDA










61


Yar Mahaukaciya ta zaro ido jikinta ya kwashi rawa, kafafuwanta suna kokarin kasa daukar ta, cikin gargadar murya ta ce" no, ni ? Ni? Bani da Uba, ni *Yar Mahaukaciya ce* ban sanka ba , bazan taba lamunta da kai ba ,




Da Sauri ya matsa kusanta ya kama kafadunta ya ce" tabas ke ce y'a ta daya da na malaka, ke ce ake gwada min a mafarki, ke ce, sai yanzu na tino ki ke da mahaifiyarki, idanuwanki da kalar fatar ki da karan hancin ki da yatsun kafafuwan ki da hannayan ki da tsayin ki , duka nawa ne kika yo, ina tine da ranar haihuwar ki na sauko daga jirgi na kuna waya ta maman ki tayi kirana ta kara min kukan ki a waya, u'r my life my everything, pleasz kar ki juya min baya a yanzu da Allah ya nuna min ke tun kafin raina ya rabu da gangar jikina ,





Yar Mahaukaciya ta yatsina fuska ta saka hannayenta ta cire hanun sa, ita fa wannan tatsuniyar ba da ita ba, ita yanzu haka abinda ya firgita ta ganin wanan matar mai matukar kama da Mahaukaciyar ta, sai dai ita wanan a wanke take, cikin sitirar ta take ,, mai kudi ce, mai kanshi ce,, kawai kama ce , ta dago rinanun idanuwanta daga kalon Hajiya Hafsat ta sauke su saman hannun wanan nassaran mai Jan fata a Karo na biyu ta saka hannun ta ta cire cikin kunan rai ta ce" Malan ni fa matar aure ce, taya zaka taba min kafada, na fada maka ni ban san wani uba a gareni ba koda duniya zata taru a kaina, kana mahaifina ka barmu ni da mahaifiyata a bola? Muke kwana a cikin bola ? KO dan umana tana hauka ne? KO dan muna hauka ne? Ka kore mû ne? Albishirinka a cikin bola har haihuwa mamana tayi namiji, ta tafi ta barni da shi inda duniya take jifana da nayi cikin shege na haihu, ni din nan dalilin ka da ka watsar da mu har ruwan kwata mun sha, a yanzu haka akoy wa'inda basu yarda cewar Dan Mahaukaciya na ba d'à na bane, na kasance mai bakin jini sai da Allah ya hadani da iyaye na kirki dan haka wani bazai fito min rana tsaka ya ce min wai shi abanna ne na yarda ba, *I HATE YOU* *I HATE YOU*



Cikin wani irin yanayi mai bayar da tausayi yayi Saurin rungume ta a jikin sa dan ta dena jifan sa da wanan kalma da gwara a ce bashi da rai da ya ji ta daga bakin gudan jinin sa,




Cikin yannayin bacin rai ta kwaci jikinta ta juya da gudu tana rusa kuka ta fada dakinta ta rufo



Su duka da kalo suka bi ta , shi kuwa ya fadi nan sumame , cikin firgici suka kwashe shi suka nufi asibiti da shi inda kafin su fita Hajiya Fadimatu ta fada dakinta ta dauko macajin Yar Mahaukaciya ta ciro gashin dake makale a jiki ta bi bayan su , inda Hajiya Hafsat ta zamto tamkar kurma dan kuwa ta rasa tudun dafawa , ga koshi ga kwanan yunwa


Suna isa akayi emergency da shi inda Hajiya Fadimatu ta shiga ta office din docter ,



Basu fi minti goma ba ya farfado aman docter ya yi masa alurar baci




Suna nan zaune sunyi jigum jigum kowa da abinda yake sakawa a ransa inda AA Mubasshir ya zubawa hannayen Elhaj Muhammad Muktar ido yana auna su da na Matar sa,




Docter ne ya shigo da takarda a hannun sa ya mikawa Hajiya Fadimatu


Ta karba tayi masa godiya


Yana fita ta zauna ta Buda ta karanta , idanuwanta ta lumshe ta sauke ajiyar zuciya domin gwajin gashin Yar Mahaukaciya da Elhaj Muhammad Muktar ya nuna eh lale Y'ar sa ce, jinnin sa ce, ta mikawa Mubasshir result din



Yana karantawa shima ajiyar zuciyar ya sauke ya mike ya nufi motar sa ya shiga ya tayar sai gidan Hajiya Fadimatu ,




Tunda ta shiga dakinta kuka ne take tana rike da dan kwamin Mahaukaciya tana tina rayuwarta da ita , ta mike da niyar ta dauko zoben hannunta Wanda ta tsinta a bola ta kade kofin ruwan da ta dibo dan shan maganin ciwon kai , ai kuwa ya kwashe ta sai gata yim a kasa koshinta ya fashe ga jiri tana nan konce tana ganin dishi dishi ta kasa tashi kuma ita bata suma ba sai kuka take tana fadin" mamana



Yana shigowa ya haura dakinta ya dan konkwasa , ya kai minti biyu shiru hakan ya sa ya tura ya shiga


Hangota ya yi nan konce tana maida numfashi tamkar an caka mata yikuwa , ai wuli yayi da takardar ya nufe ta , yana isa ya talabota ya dauke ta ya dora ta saman bed dinta , ya mika hannu ya dauko dan kwalin dake yashe dan ya daura mata , warin dan Kwalin ya bugi hancinsa dan kwata kwata kin wanke shi tayi gudun kar warin jikin Mahaukaciyarta ya fita, da auri ya wular da ita yana goge hannun sa,



Hawa yayi ya dan tsaya yana nazarin yanda zai yi mata da rigar jikinta dan ya samu ya goge mata jinin da ya bata mata goshinta,


Rintse idanuwansa ya yi ya leka fuskarta ya ga tamkar baci take dan kuwa idanuwanta a rufe , ajiyar zuciya ya sauke ya saka hannunsa ya ja ZIP din doguwar rigar , hannunsa na karkarwa ya sabule rigar yana kokarin sabule rigar ta zabura ta farka tana zaro ido daidai nan aka turo kofar aka shigo



Gabanta ya yanke ya fadi haka gaban Wace ta shigo da kwarin gwuiwar ta yanke ya fadi .......





Shin wacece ta shigo? Yar Mahaukaciya zata yarda da mahaifinta? Ina Mahaukaciya ne? Shin mai sunan Yar Mahaukaciya na kirki?



Duk mai son ci gaban Yar Mahaukaciya ya turon sunan Yar Mahaukaciya ta wanan number *+22792245338* thx
[12/15, 4:36 PM] ‪+234 902 472 4465‬: 🇳🇪BELLES écrivaines Nigériennes


👹 YAR MAHAUKACIYA👹 na SAJIDA










62


*Ina matukar murna, ina farin ciki karanta message din masoya, tabas bazan taba gajiyawa da ku ba dan sai ana yi da kai ake kula ka, ni Sajida ina kara godiya ga masoya na na nesa da na kusa, harda hawayen farin cikin Ashe ina da masoya, love u ,*









Cikin tsananin firgici suke yiwa juna kalon kalo, Mubasshir kansa sai da ya dan ji dar tamkar an kama shi da wani laifin,



Cikin wata irin tafiya take takowa tana son gaskatawa idannuwanta shin da gaske ne abinda suke gani ku?

Wani irin ihu ta saki ta kama kanta ta cuje daurin dan kwalin tayi wurgi da mayafin ta nuno su da yatsar ta ta ce" Mubasshir, me nake shirin gani? Wace wanan? Ashe daman kai macuci ne? Ashe daman haka kake? Ni zaka ci amana ka kawo karuwa shinfidarka?




Mubasshir ya rintse idannuwansa ya ce " SAHLA


Sahla ta kara daga mai hannu tana karkarwa da gursheken kuka , basu ankara ba sai ji kake kwatsam ta kwadawa Yar Mahaukaciya katuwar kwalbar tiraren dake ajiye saman table , ta juya tana kokarin wawuro wani abin dukan aman har a lokacin bata ga fuskar Wace take kira da karuwa ba


Yar Mahaukaciya da taji saukar kwalba a goshinta ganin idan fa ta tsaya zata Iya halakata a kan abinda ita bata sakawa ranta cewar malakinta bane , hakan ya sa ta Mike tsaye tana haki , daidai nan Sahla ta juyo da wata kwalbar a hannunta sai dai me , idannuwanta suka yi arba da fuskar matar da tafi tsana a duniya, Wace mijinta tun kafin ya zama mijinta ta lura da irin kulawar da yake bata Wace ita da yake kokarin aure bai ba ba,


Kwalbar hannun nata ta fadi kasa inda ta bi bayan kwalbar luuuu kasa sumamiya



Gaba daya abubuwan sun yiwa Mubasshir yawa , yana tsaye ya rasa mai zai yi, tabas ya san ba'a yiwa Sahla adalci ba dan kuwa an yi mata kishiya bata sani ba, aman abin bai kai na tana zuwa ta shiga munanan kalamai ba harda fasa kai , ganin ta fadi sumamiya ce ya saka shi nufarta ya bar Yar Mahaukaciya dafe da goshi kanta na mugun Sara mata, wani katutun bakin ciki ne ya tokare wuyan Yar Mahaukaciya a ranta ta ce" Kenan ni na mutu ma KO dan baka So na? , bata san lokacin da ta ja wani uban tsaki ba ta fice ta bar masa dakin , inda ya raka ta da kalon mamaki yana tambayar kansa tsakin na raini ne KO na kishi ne?





Yana farkawa ya shiga furta sunan " *ISLAM, ISLAM*


HAJIYA FATIMATU da Hajiya Hafsat suka taso da sauri suna yi masa sanu


Elhaj Muhammad muktar ya damki hannun Hajiya Hafsat ya ce" Ai ba mafarki nake ba KO? Na ga y'a ta, na ga *FADIMATUL ISLAM* KO? Aman tamkar tana fushi da ni, dan Allah ku kaini wajen ta na gan ta , na nemi yafiyar ta,



Hajiya Hafsat ta ce" please yaya ka kontar da hankalin ka saurare ni



Elhaj Muhammad ya saka hanunsa ya cire Karin ruwan da aka saka masa, daidai nan wayar sa ta kwashi kara tana neman agaji



Hajiya Hafsat ta dauko ta dana ta Mika masa ,


Ganin number shine ce ya daga ya kara a kunnan sa yana salama , dan matar sa ta tafi harkokin kasuwancin ta , yayi ta kiran number bata shiga sai ya danganta hakan da bata samu lokaci ba


Yana karawa sai ya ji muryar namiji da harshen turanci yana tambayar idan har shi dan uwan mai wayar nan ne



Elhaj Muhammad mucktar ya amsa da " Eh matar sa ce



Daya dayan bangaren mutumin ya ce" ouf yawa Daman tun shekaran jiya muke Kiran numbobin wayar tunda aka kawo mana ita



Elhaj Muhammad ya ce" ban gane ba aka kawo muku ita? Ku din su waye? A Wace kasa ce? Sanan mai ya hada ku da ita?




Mutumin ya ce" a hongkong ne , ni likitan mahaukata ne, an tsinto ta ne ta cicira kayan jikinta tana hauka a titi dan haka muke ta neman family din ta dan kuwa a jiya zuwa yau sai da ta kashe min kare na Wanda na gada tun wajen kakana ,(abinka da arne?). Ya ci GABA" dan haka kayi gagawar zuwa ka dauki wanan Mahaukaciyar matar taka tun kafin na dau mataki a kanta kuma a biya ni kare na, , yayi masa kwatancen asibitin ya datse



Yana datse Kiran daidai nan Hajiya *Rafi'at* ta shigo da tsananin firgici tashin hankalin jin yana asibiti , ita da suka rabu kan zasu je su nemi afuwar Hajiya Fadimatu tayi hakurin tarewar Hajiya Rafi'at din kafin ta shirya mata dakin Yar ta, sai ga message din kanwar ta Hajiya Hafsat tana fada mata wai suna asibiti



Tana shigowa ya juyo yana kalon ta, ai bai san lokacin da ya janyota ya rukunkumeta tamkar wani zai kwace masa ita,



Su Hajiya fadimatu suka yi gagawar FITA daga dakin tun kafin tsohuwar soyaya ta bayana kanta a gaban su





Kaji fa, in an tsufa a san an tsufa kawai ehe🤒









*Cigiya CIGIYA*



*INA BADA CIGIYAR NOVEL DINA MAI SUNA DUK KARYAR KADA TA RUWA CE DAGA BAKIN 70, 70 , 70, DAN ALLAJ WANDA YAKE DA YA TAIMAKA YA TURON TA NUMBER WAYANA KAMAR HAKA +22792245338 NA GODE*
[12/15, 4:36 PM] ‪+234 902 472 4465‬: 🇳🇪BELLES écrivaines Nigériennes


👹 YAR MAHAUKACIYA👹 na SAJIDA





63




*Haza yaumul akbar; yaumul shukur, yaumul salama! Alhamdulillahi ala ni'matil Islam*





Hajiya Fadimatu ta gyara zaman ta ta ce" Bani labarin yarinyata da mahaifanta,




Hajiya Hafsat ta zauna da kyau ta ce" George Roger ainahin sunan mahaifin Islam kafin ya musulunta, ya kasance Christa ne shi a da, lokacin da ya shigo kasar Misra, aiki ya kawo shi , irin ya shiga Wankan nan yayi sake ya bar kayansa a kofar bayin inda aka share aka tafi da su, yana fitowa ya tarar babu nan fa ya rikice ya rasa ya zaiyi domin harda pasport dinsa a ciki ,
Cikin mutanen dake jajanta masa harda aban mu, nan ya taimaka masa ya sauke shi a gidan mu domin aba akoy tausayi ,
Tafiya tayi tafiya a kulun yana Lure da yanayin rayuwar mu, tarbiyar mu, addinin mu, yanda muke cudanyar rayuwar mu cikin girmama juna , irin yanda idan zamu gaishe da na GABA da mu muke tsugunnawa har kasa domin mahaifiyar mu Yar nan Lagos ce aban mu ne na Misra, hakan ya mugun shiga ransa , gashi da tambayoyi , KO mai ya ga muna yi zai tambaya ne , mu kuwa mu bashi amsa yanda zai fahimta,
Ana cikin haka ya wayi gari da matsanancin ciwon kai harda habo , hankalin sa yayi mugun tashi domin ciwon sa Kenan habo da ciwon kai , sanan idan ya tasar masa ya kan kusan wata yana jinya ,
Aban mu yayi dabara ya kai shi asibitin aminnin sa aka bashi magunguna , yana ci gaba da sha aman sauki sai dai hamdallah kawai, hakan ya sa kulun yana konce ba damar zuwa koda palo ne balatanna bangaran su

Rashin lafiyarsa sai ta shafi kowa tun ba ma sisterna Rafi'at, kulun muna yi masa adu'a

Wata safiya muka shirya muka shiga dan mu gaishe shi sai muka tarar yana ta kakafewa , hakan ya mugun tsoratar da mu , da gudu na juya dan neman agaji ita kuwa ta matsa ta zauna ta dafa kan NASA daidai inda ya fi rikewa tayi bismillah ta karanta masa salatil allahnabiyi kafa daya sannan tayi masa wala haula wala kuwata ilabilah har kafa tara,
Cikin ikon Allah tana sauke hannun ta tamkar ta sauke da ciwon , nanauyan baci ya yi gaba da shi


Ya kusan awa uku yana bacin nan inda muke zaune mun kewaye shi muna ta yi masa adu'a ya farka

Daya bayan daya yake bin mu da kalo inda ya kafe Rafi'at da kalo , abinki da nasara sai ji muka yi ya ce" I LOVE YOU,


Ido muka tsaro inda ya Mike da kyau ya tsuguna gaban aban mu ya ce" Tabas na yarda da adinninku dad, ban taba tinanin cewar musulunci ya kai haka ba, tabas musulunci rahama ne, musulunci haske ne , ya hade hannayensa ya ce " *Ina son zama musulmi*

A Ranar munyi murna marar adadi, bayan Aban mu ya tabatar da eh lale da gaske yake ba kokonto a cikin ransa ya dauke shi Ranar juma'a ya tafi masalacin juma'a da shi inda Duban musulmai suka shaida shigar sa musulunci aka daura masa aure da Rafi'at ,

Cikin ikon Allah bayan shekara guda da yan watani aka biyo bayan sa daga America inda ya shirya ya bisu ya gama hada koman sa ya juyo


Bayan shekara hudu har a lokacin bai samu haihuwa ba, a nan suka shirya har ni muka je garin kakansa na wajen uwa Wanda yake a raye a lokacin,
Da zuwan mu an karbe mu hanu bibiyu , a nan aka nuna masa dukiyar mahaifiyarsa sai dai fa da sharadin idan bai dauki Rosemond a matsayin mata bazai dauki dukiyar ba harta da hotunan ta,

Cikin fushi ya ce baya So su rike , aman Rafi'at ta tsaya tsayin daka kan sai ya amince KO da rabon su ga kwon su ne a duniya

Hakan kuwa aka yi bayan ta musulunta da kyar aka aura masa ita muka koma da ita Misra

Aban mu yayi murna haka mama , shi kuwa Muhammad yana matukar mamaki inda Farida bata taba nuna bakin halinta ba

Cikin haka aban mu yayi rashin lafiya Ashe na ajali ne , Allah ya karbi abinsa,

Bayan yan watanni muka tataro muka komo Lagos da zama dan kuwa kwata kwata mun dena jin dadin zama a Misra


Konci tashi arzikin Muhammad ya kara habaka inda ya tsaya tsayin daka dan ganin ya inganta mana rayuwar mu ta fanin ilimi ba'a magana sosai muna jin dadin rayuwa da shi

Ana tsaka da haka ciki ya bayana a jikin Rafi'at, zo ki ga murna , hankalin kowa saï ya koma kanta inda a nan bakin halin farida ya fito dan kuwa kiri kiri ta nuna ta tsani Rafi'at

Cikin ikon allah ta haihu lafiya inda aka saka mata sunan *Fadimatul islam*

Yarinya tana cikin gata Wanda fada miki shi To fa bata lokaci ne , hakan ya kara tunzura zuciyar farida ta taba kama kuncinta ta ja daidai mahaifinta ya shigo, a Ranar mun ga tashin hankali dan kuwa da kyar aka amshe

20 / 29