Author : Nainerh KD Category : Romance
basu kuma ya amshe abinsa kiyi hakuri Allah ya jikansa muje gidana ayi masa sitira idan kin huce sai asan yanda za'ayi aman bazan barki haka ba , kawai ta shiga tatara mayafin yar Mahaukaci�a ta dagota KO takalmi babu a kafar Yar Mahaukaciya ta kamo hanunta tana kuka itama tana kukan suka shiga cikin mota Shi kuwa ya koma ciki dan ya dauko gawar dan Mahaukaciya
Cikin mutunci aka yiwa dan Mahaukaciya sitira harda taro domin Hajiya Hawau mutuniyar mutane ce sosai aka yiwa dan Mahaukaciya adu'a inda mata ke shiga suna ta'aziya domin Hajiya Hawau tayi ruwa tayi tsaki tace jikanta ne daga kauye suka zo Allah yayi masa rasuwa ,
Ita dai Yar Mahaukaciya tana Zaune da zunbulelen hijabin Iya da tazbaha a hanunta tana ja astagfari kawai take ja itama Iya ta fada mata tace ki ringa hailala kina maimaita astagfrullah Allah ya jikansa ke kuwa ya sanyaya miki zuciyarki ya baki dangana, hakan yasa ta koma gefe daya irin yanda ta saba zamanta tayi shiru tana ta jan carbinta tana astgfari hawaye wani na korar wani ,
Konci tashi har an yi cikon satin Dan Mahaukaciya , aman har yanzu sakewa ta gagari Yar Mahaukaciya domin jira take a koreta ta kara gaba dan tasan hakan rayuwarta take KO an Nuna mata so to fa za'a kyamaceta ,
Dawowarsa Kenan daga asibiti ya nufi can cikin gidan su domin mahaifiyarsa tayi kiransa cewar tana son ganinsa , yana shiga ya tarar da ita zaune ta harde kafafuwanta ya karasa ya zauna yana kokarin gaisheta kamar yanda ya saba , cikin sauri ta katse shi ta ce " abdul wai wacece yarinyar nan? Ni dai a sanina dangin ku duk yawancinsu yan camaru ne ya akayi ita wanan na ganta a nan ? Wa ya kawota ne? Meye halakar kakarnan taka masifafiya da ita?
Abdallah ya rasa amsar da zai baiwa umansa domin ita a rayuwarta ta tsani taga an rabe su idan dai mutun ba mai arziki bane tofah ranta baya so , ya ce " am haba mom kinga nima tare na gansu bansan KO wacece bâ fa ,
Hajiya Marhaba tayi shiru can ta ce " naji can ita da jarabarta aman na haneka da shiga sabgar yarinyar nan idan kuwa ba haka ba wly sai na saba maka , kuma karka manta nayi maka mata dan haka ka mayar da hankalinka kanta kaji KO?
Abdallah ya dan Sosa keya ya ce " an gama mom please ki dena rayar da hankalinki ai itafa bazawara ce kingani ai sai bazawari KO?
Hajiya Marhaba ta daga kafadarta irin su ya shafa din nan ta Mike tana tafiya ciki gadara ,
Bayan ta tafi docter Abdallah ya kontar da kansa jikin baban kujerar dake tsakar dakin su ya lumshe idanuwansa ya ce" ina son sanin labarinki beauty ( wato Yar Mahaukaciya ina ruwanka da labarinta inji ni sajida 😏 )
Zaune take ta saka kwanon furar da Hajiya Hawau ta dama mata a gaba tana ta tunani , Hajiya Hawau ta dauko karamar kujera tayani tsegumi ta zauna ta ce " to yarinya bani labarinki kuma ki fada mini sunan ki
Hankalin yar Mahaukaciya ya tashi a ranta ta ce " Nasan idan kema na fada miki sunana Yar Mahaukaciya zau gujeni ne, ni kuwa wani suna zan fadawa iya?
To jama'a ku taya Yar Mahaukaciya zabar sunanta don gujewa tsanar sabuwar family dinta 🤝🤝🤝🤝🤝
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
10
Yar Mahaukaciya ta gama yanke hukuncin ba Wanda zai kuma sanin labarinta domin idan ta fada kyamarta ake gwara ta boye sirinta ta nemi Mahaukaciyarta a boye daga baya idan ta ganta sai ta gudu da ita ,
Ta dago kanta ta kali hajiya Hawau ta ce " Ni dai Marainiya ce bani da kowa sai Allah ,
Hajiya Hawau ta ce " to shi mijinkin rabuwa kuka yi KO mutuwa yayi?
Yar Mahaukaciya ta ce " mutuwa yayi hajiya , domin tasan idan ta ce rabuwa suka yi za'a nemi sanin KO shi waye dan a nemi yan uwanta ,
Hajiya hawau ta ce " eyah Allah ya jikansa kar ki damu yata kinga daman ni dana daya a duniya Allah ya bani ya aure mata marar mutunci kinga tana can ciki ba ruwanta da ni , yaron ma da yake kulani bakin ciki take kinga kuwa ohon mata Allah ya bani nima yar KO?
Yar Mahaukaciya tayi murmushi a ranta ta ce ki gafarceni hajiya ki gafarceni ,
Hajiya hawau ta Mika mata furar da ta dama ta sha nono mai kauri da cukui sai abin mai take ga siga ta ce " kinga damun Dan Aljana ne wanan kwana biyu bai shigo ba mahaifiyarsa ce bata da lafiya ai har Idrissu ya kamata a gadon asibiti yaki sakinta sai da akayi da gaske
Yar mahaukaciya tayi murmushi ta ce " kai gaskiya bai kyauta ba sam
Hajiya ta kara karkata daurin dan kwalinta tace " kyaji mai yi dan Allah kinga ai ke kinsan abinda kike yi aman sauran gaba dayan su sun goyi da bayan a BArta ta samu lafiya ji suke asibitin ci ce , ai sai sun ga uwar bari kafin su yarda da magana ta ,
Yar Mahaukaciya tayi dariya domin du yanda kaso kaucewa lamarin hajiya to fa sai ta saka ka dariyar ,
Hajiya ta ce " KO ke fa to baki fada min sunan naki ba ,
Yar Mahaukaciya ta ce " sunana RAHAMU domin bata manta sunan da Baba tayi mata ba
Hajiya hawau ta ce " Rahama suna mai dadi To ni dai zan ringa kiranki da Ramatu domin Rahama haka sunan sirikata yake a gaban baban idrisu bazan iya fada ba
Yar Mahaukaciya ta ce " to hajiya ba damuwa na gode , haka suka wuni suna dan tataunawa Yar Mahaukaciya ta dan fara sakewa da hajiya Hawau domin tana kara janta a jiki
Washe gari da safe Hajiya Hawau ta shirya tacewa Yar Mahaukaciya ta tashi su je gidan su Dan Aljana su ga jikin babarsa an sakota daga asibitin,
Haka kawai Yar Mahaukaciya taji bata ra'ayin fitan ta kali Hajiya ta ce " Hajiya ki je ni na karasa aikin mu KO?
Hajiya ta ce " kai Ramatu bakya son yawo kema ga son aiki to ni dai kinga tafiyata sai na dawo
Yar Mahaukaciya ta ce " a dawo lafiya Allah ya tsare
Hajiya ta ce " Amin tayi gaba abinta ,
Bayan tafiyarta Yar Mahaukaciya ta zage damtse ta shiga sharar gidan ta share tsaf ta dawo ta zuba cleam ta wanke da ruwa da tsintsiya ta koma ta harhada kayan wanke wanke ta dawo ta zauna ta cire hijabinta ta kara gyara daurin zaninta ta zauna saman tayani tsegumi ta shiga wanke wankenta
Ya jima tsaye yana kalonta tana ta wanke wanke yana mamakin kalar fatarta har wani yelow yelow yake sakawa faratunan kafarta dogaye ba kananuwan yatsutsai bane da ita a hankali yayi salama ya shiga
Ta razana da jin salamarsa ta dago da Sauri tana konce hijab dinta daga kanta ta saka tana amsa salamar sa ,
Idriss ya karaso ya jawo kujera ya zauna kusa da tata , yana fadin sanu da aiki madame wanan aiki haka?
Yar Mahaukaciya tayi murmushi tana kara gyara zaman hijabinta
Ya ce " ina masu aikin gidan ne?
Ta ce " ai an aiki biyun kasuwa dayar kuwa tana baya tana wanki
Ya ce " ai kuwa sai an karo muku masu aiki KO?
Yar Mahaukaciya ta dago da Sauri suka yi ido hudu kuwa ta kawar da kanta ta ce " ina ma aikin gidan yake ai ni kadai ma na isa nayi shi
Docter ya girgiza kansa ya ce " tap ikon Allah ai bazai taba yiwuwa ba hutawa kawai zakiyi
Yar Mahaukaciya ta ce " hum , a ranta ta ce hutu fa lale KO a mafarki
Ya lura bata cika magana ba aman tana da girmama mutane yana son yi mata tambayoyi sosai aman sosai yake jin nauyin hakan bai san dalili ba haka yayi ta zama har ta gama wanke wanken ya dauke kondon kwanonin yayi kicin da su ita kuwa tayi murmushi ta dauko tabarma katuwa ta shinfida masa ta dauko kwarya da ludayi ta zauna ta a saman yar kujerar nan ta s�iga dama furar , s�ima waje ya nema ya zauna yana kalon yanda take aiki bata da alamun gajiya tana gama damawar sai ga Hajiya hawau ta shigo gidan da salamarta
Yar Mahaukaciya taje da Sauri ta amshi ledar dake hanunta tayi daki da ita fruits ne ta sauye ta wanke ta jera rabin a frij ta debo wasu saman tire da wuta ta fito tana fitowa taga Hajiyar na zaune saman kujerar tana kara dama wata furar a hanunta , gefenta Idriss ne zaune yana shan wada ta dama masa idanuwanta suka ga wata kafa fara kar cikin wani bakin takalmi mai shegen kyau takalmin uwa na sarakai domin kalar adon sa ji tayi bazata iya kalon mai takalmin nan ba hakan yasa a hankali ta ajiye fruits din a kusan Hajiya Hawau ta Mika hanu tana fadin Hajiya kawo na dama miki mana
Hajiya hawau ta ce " aa yar gidana wanan damun sai ni da kaina kowa ya dama baya sha sai ni din nan da kike gani ai ta Dan aljana ce da nake baki labari , ta kuma kalon dan Aljana ta ce " Dan Aljana kaga yartawa da nake fada maka
Bai dago ba bai kuma ce kanzil ba itama haka kawai ta kasa koda dago kanta bare ta kale shi , jin takun tafiyar hils da wani kalar tiraren yasa ta bada hankalinta kan kofar shigowa
Wata budurwa ce ta shigo ta sha mahaukacin hils mai shegen kyau kai ita kanta abin kalon ce domin haduwa iya haduwa ta hadu ga kamshi tana zubawa batayi salama ba kawai shigowa tayi sai da taga idriss na zaune sai naga ta saki murmushi ta ce " Brother daman kana nan har momys take neman ka?
Idriss ya dago kansa daga kwaryar furarsa ya dan kaleta yace " sauran kice mata ina nan
Tayi murmushi bata gaida hajiya Hawau ba bare ta gaisar da Yar Mahaukaciya Wace take kalon takalmin kafarta tana mamakin yanda akayi ta hau saman sa , ta nufi wajen wanan mutumin mai cike da korjini tana zuwa ta saki murmushi ta ce " Honorable barka da warhaka
Sai yanzu Wanda aka kira da honorable ya dago kansa ya zabga mata harara , da Sauri na furta ya Salam na fadi ba shiri ba ni kadai ba Yar Mahaukaciya kanta gani nayi ta zaro idanuwanta tana kalon wanan bawon Allahn
Shin wanene Dan Aljanar da Hajiya Hawau ke fada tana karawa? Wacece wanan budurwar da ta shigo meye halakarta da Irdriss? Mai yasa bata gaishe da Iya ba? Muje zuwa daga Yar mutan niger
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
11
Aunty Amnoor inai miki murnar gama novel dinki *Naga Rayuwa*
Aunty UMMIEXY barka da gama *HISABI*
Allah ya kara kwarin ido da zakin hanu amin💋💋💋💋💋💋💋💋
Dagowar kan da yayi , yayi daidai da kalonsa da Yar Mahaukaciya tayi gabanta ne ya yanke ya fadi da Sauri ta sada kanta kasa a ranta ta ce " to shi kuwa wanan mutun ne KO aljan? Daman akoy mutane kalar haka? Shi kuwa wanene?
Muryarsa ta tsinto ya furta kalma uku Wace bata san mai yake nufi da ita ba
Yana kalon budurwar da ta shigo ya ce " are u crazy?
Ta girgiza kai gwuiwa a sace ta juyo wajen Hajia Hawau ta ce " hi grandma
Idriss ya ja tsaki ya mike da furar sa ya kali Yar Mahaukaciya Wace take ta al'ajabin maganar dan Aljanah kamar yanda Hajiya ke kiransa da shi ya ce " sister taso ki ga sakon nawa na shige ance mom na kirana
Yayi ciki Yar Mahaukaciya ta bi bayan sa
Hajiya Hawau ta gama dama furar kai KO ni sai da ta ban sha'awa irin yanda take daukan ido ta mikowa Dan Aljanah ta kakabe zaninta sai tura baki take tayi cikin dakinta ,
A hankali wanan budurwa ta ja kujera tana fuskantar Dan Aljannah cikin raunananiyar murya ta ce " Mubasshir please manan kayi hakuri ai na gaisheta
Sai da ya gama jujuya furar yana ta tinanin wanan sabuwar mai aikin ta Hajiya ce ta dauko kwaryar da aka dama masa furar a ciki shi fa yaki jinin yan aiki yana kyankyamin harkokinsu baya son KO kadan su rabi abincinsa gashi kuma furar sai fizgarsa take , maganar Budurwar nan ta maido shi daga tunanin da ya tafi ta ce " *Mubasshir* ka amsa min please nace kayi hakuri
A hankali ya dago idanuwansa ya sauke su a saman fuskarta suka yi ido cikin ido da Sauri ta kawar da kanta domin duk tsatsauran halinta bata san ya akayi take shakar hada ido da Mubasshir ba ,
Cikin fadafada ya ce " *Sahla* ki gane ni fa ba zan kwashi marar tarbiya ba , a kulun ina fada miki ki kiyayi rashin kunya , idan baki girmama macen da ta haifi mahaifin ki ba fada min zaki girmama tawa kakar kuwa? Da da ranta nasan har sai kin taka ta domin kince kina kyankyamin tsofafi, ki gane darajar tsohuwar nan da kika raina yasa har nake iya kalonki har nake kula ki kin fi kowa sanin KO wanene ni nafi karfin ajin ki aman ina jin kunyar wanan tsohuwa da nake kalo tamkar kakata ke kuwa Allah yayi miki rahama kina kaucewa , so bara kiji ni bazan lamunci shashancin nan naki ba idan har bakya mutunta manyan ki to fa tsakanina da ke horo ne kawai ba wani Abu
Cikin tsoro da kalamansa ta ce " I'm sorry honorable nayi alkawarin mutunta ta kayi hakuri please karkayi fushi da ni
Ya dago kansa yana kalonta gaskiya shima ya san yana son Sahla domin kyakyawa ce ajin karshe , sai dai abinda baya so a tatare da ita raina mutun sam ita ta raina mutane ta tsani ta shiga lamarin mutun indai ba ta yarda da shi ba hakan kuwa harda kakarta Wace ta haifi mahaifinta ,
Wacece Sahla?????
Sahla itace auta a wajen hajiya Marhaba wato kanwar Idriss , Hajiya Marhaba tayi ta samun ciki tunda yarintarta sai dai cikin ikon Allah cikin yana barewa cikin haka Allah ya bata cikin idriss ta haifi abinta cikin koshin lafiya , bayan sa ma sai da tayi barin biyu kafin ta samu cikin Sahla , tun bayan haihuwar Sahla shikenan tamkar anyi ruwa an dauke Hajiya Marhaba bata kuma samun wani cikin ba hakan yasa suka dauki son duniya suka dorawa matar manya lakabin da Sahla tayiwa kanta Kenan , tarbiyar Sahla ba kwaba ba tsangwama , makarantar sai taga dama take zuwa , kawayenta duka yayan manya ne , Sahla ta kasance Doguwwar mace fara ga shegen kyau masHa Allah ga iya Jan aji ga yanga kai Sahla da ba dan halayenta ba sai nace goma ce cifffffff sai dai kashhh irin wanan gata da ta samu ya saka bata ganin kan kowa da gashi , baba KO karami zata takaka san ranta domin tasan abinda ta taka
Abinda ke hadasu fada da Hajiya Hawau irin yanayin shigarta da kuma sangartar ta idan fa hanya ta hado su sai dai ita ta rakube ta fice sanan ita ta fice hakan yasa sam basa jituwa suke yar tsama , hakan nayiwa Hajiya Marhaba dadi domin taki jinin sirikar tata abu ya hana tayi maganin ta Elahj domin yana matukar kaunar jangom lakabin da take kiranta da shi Kenan ( ya Allah ka tsare mu amin )
Abu daya yake saka Sahla dan sadakawa soyayar Mubasshir da ta wayi gari ta tsinci kanta a ciki tsundum hakan yasa take dan rage wasu abubuwan a cikin halayenta domin shi bazai lamunci rashin mutuncinta ba idan kuwa ta rasa shi tasan ta tafka asara ( tofah )
Ci gaban Labari
A hankali ya aje furar domin sai ya deba da niyar kaiwa bakinsa sai ya mayar da ludayin yana matukar son ya sha furar nan kyankyaminsa ya hana shi ya sauke ajiyar zuciya ya mike yana saita agogon hanunsa ya dan dubi Sahla kasa kasa ya ce " ki kaiwa hajaju furar nan ki fada mata na koshi , sai tomorrow ya juya ya saka kansa gaba yana tafiya cike da isa tamkar dan Sarki
A hankali tana kalonsa har ya fice daga harabar gidan ta sauke nanauyar ajiyar zuciya ta lumshe idanuwanta ta ce " i love you My man i really love u ta kuma lumshe idanuwanta ta ce " zaka soni ne a hankali domin nasan dan ni kadai aka yi ka , ta Mike ta saka kafa ta shure furar harda hararan kwaryar tayi waje ta nufi motarta dan tasan a yanzu ya bar unguwar tana iya fita
😌😌😌😌😌😌😌😌😌
🇳🇪Belles écrivaines du Niger
*'YAR 👧🏻*
*MAHAUKACIYA👹*
*_Na SAJIDA_*
13
Karfe biyar da rabi Mai gadi yayi salama ya gaida Hajiya Hawau ya sheda mata ga Mutumin da Idriss yace a bari ya shigo idan ya zo ,
Hajiya hawau ta amsa masa ya juya inda aka yiwa Malan yunus shinfida a banban falon dakin Hajiya Hawau a nan za su ringa yin karatun kulun har ita hajiyar ,
Cikin ikon Allah kulun sai Malan Yunus Ya zo da yama sunyi karatun arabi da Yar Mahaukaciya yau har sati uku Kenan sosai take fahimtar hukunce hukunce na musulunci gaba daya ,