Dingishin Kwado Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Romance

Chapter   5 / 23

12K to 15K   out of 67.7K words

shi a dole sai ya ja ra'ayinta, shi bai san ma haushi yake ba ta ba.

Da ta rasa yadda zata yi da kasalar da yake haifarwa gangar jikinta sai kashe wayarta ta yi saboda gabad'aya nishinsa ya ruru mata jikinta.

[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "To ka bar komai a hannuna Ya Asad ba dai ka fada mata ba ai ka gama mai wahalan."

Daga haka suka rabu saboda damuwa da tashin hankali ma. Tawagarsa ya k'ira suka dauke shi tamkar yadda suka kai shi Nafdac office.

Abida kuma ba ta yiwa Bilki maganarsa ba ko da ta dawo, saboda ba ta so ta fahimci kamar za ta yi mata dole ne, amma tana lura da ita domin ta samu wata damar da za ta kawo mata maganar.

Kwana uku tsakani, ranar jumma'a bayan Baba Babba ya dawo daga masallacin Bilki ta zo wajensa suna hira.

A cikin hiran ne ya kalle ta yana fadin"Bilki ina son na yi wata magana da ke."

Bai ba ta damar maganar ba ya cigaba da fadin" Aure nake so na yi miki Bilki. Saboda ina son na ganki kin samu natsuwar irin ta aure, ko Abida da kika ga ban yi mata maganar aure ba ina ji a jikina Sulaiman na nan a raye kuma ina ji a jikina zai dawo in sha Allahu "

Bilki ta yi shiru kawai gabanta na faɗuwa.

"Idan har zai yiwu ina son na ba da auranki a karo na biyu Bilkisu."

Baba Babba ya sake fada mata..

So take ta ji wa kuma Baban zai aura mata.

"To Baba."

Ta amsa mishi tana son jin wane ne?

"Idan kin amince Asad zan aurawa ke. Ya zo ya duka mini da rokon na ba shi auranki, nima kuma na so ku da juna amma duk yadda na so abin idan har ba kya so, to ba zan yi miki dole ba saboda sharia ba ta ce na yi miki dole ba"

Bilki ta kalli Baba Babba ta kasa fadin uffan sai kawai ta fashe da kuka har da gunji kamar wata k'aramar yarinya.

*Surayya Dee*

[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Duk wulakancin da take yi masa bai saka ya karaya ba. Ya dinga yi mata manyan kyautuka masu gigita tunani. Ana haka ya je Dubai. Sai ga shi ya siyo mata wani murtukeken bangle da zobensa kallo daya zaka yi ka gane zinare ne sannan ya lashe manyan kudade na gaske. A lokacin Momi ta farga ta gane Asad zawarcin Bilki yake yi ka'in da na'in.

Bata nuna adawa da lamarin ba, tunda ta san Baba Babba zai yi faricinciki idan al'amarin ya tabbata, tunda auren nasu ne zai ƙara daidaita zumuncin gidan da ya shiga halin ni y'asu.

Sai da ya fara nunawa momi tsarabar Bilki. Ta ga ni da walwala a fuskarta ta ce "Amma ina na Abida kasan tana ga ni zata hau rikici tunda Bilki kishiyarta ce".

Ya yi murmushi ya ce "Rabu da ita Momi sau nawa ina siyo mata? Ina ce bara ma da na je Saudiyya sai da ta ce na siyo mata sarƙa kuma na siyo mata. Bilkin ma dan ta gane da gaske nake yi ne ba wasa ba."

Ya kammala fad'a yana shafa kansa .

"To ma sha Allah, Allah yasa rabonka ce, zan yi farinciki da hakan."

Ta faɗa tana mirmishi, ba shakka idan ya samu Bilki ta san ya gama morewa.

"Amin Momi. Gata nan tana ta yi mini tutsu ki taya ni shawo kanta."

Ya fada cikin jin kunya.

"Ba ruwanmu a ciki. Ka cigaba da ƙokari in sha Allahu za ta amince."

Ya amsa da Allah yasa tunda kowa na ba shi k'warin gwiwa ai sarewa bana shi ba ne yanzu.

Bai tafi ba, yana zaune yana dakon isowarta.

A falo ta tarar da shi, shi kad'ai, fuska babu sukuni ta zube sosai ta gaishe shi tare da yi masa sannu da dawowa. Daga haka ta doshi k'ofar da zata shige ciki ta nufi d'akinta. Takaici ya mak'ure shi.

Ya bude murya ya ce "Maigado ke nake ta jira, zo ki ba ni mintina goma mu gaisa nasan a gajiye kike."

Kan dole ta dawo ta durkusa har k'asa daga gefe tamkar basarake gaban basarake. Ya yi tsam yana jin wulakanci ne kawia yake Sawa take yi masa irin haka.

"Maigado tunda na yi tafiyar nan nake ta mafarkinki. Yau kuma sai na yi mafarkin kin haifa mini boy".

Ta tsuke fuska sosai ba ta tanka masa ba.

Ya nisa ya ce "Wannan bacin ran fa? Ki daina yi mini haka mana dan Allah!

Ya tura mata k'aramar leda mai kyau wacce take d'auke da tambarin United Arab Emirates.

Ledar kanta abin sha'awa ce bare kuma kayan cikinta.

A sanyaye ya ce bangle da ring ne suka birge ni na siyo miki su a Dubai kin san k'asar suna da gold sosai".

Da k'yar ta bude baki ta ce "Na gode ".

"To ki bude mana"

A hankali ta ce "Ina fama da indigestion afuwan zan shiga ciki".

Ya mike da sauri yana fad'in "Sai na sake zuwa Maigadona".

Washegari kuma ya dawo da Kaya fal leda na Farha da su Amrah.

Da girmamawa ta ce "Hidimar fa ta yi yawa Baban Bilkisu dan Allah ka daina".

"To ni ai ba ke na siyawa ba. Ya'yana ne babu ruwan ki a ciki."

Sai ta kasa yin magana dole dai kanwar na k'i ta yi masa godiya.

Tunda ya dawo ta kuntatawa kanta ta daina walwala. Idan zai kwana yana k'iranta a waya ba zata dauka ba.

Idan ya zo gidan kuwa bata yarda su kebe. Ganinta ma sai idan ta dawo yana gidan to dole ya ganta, nan ma sai ta gabatar da uzzirin band'aki zata shiga. Daga haka kuwa ba zata yarda ta fito ba.

Abida ta Fara kufula da alamarinsu, yana tsananin son Bilki, ita kuma tana tsananin k'insa. To ya hak'ura mana shi da ake ta yi masa tallan y'anmata zabga zabga ma.

Wajen shadayan dare ta k'ira shi a waya. Da kaushin murya ta ce "Dan Allah dan girman Allah Yaya Asad ka hak'ura da Bilki haba na gaji da wulakancin da take yi maka."

Asad ya yi shiru yana jin ta.

Kafin ya sauke numfashi yana fadin" Abida ina son Maigado irin son nan mai wuyar a bar shi".

"To yaya Asad za ka yi ta bin ta ne tana maka wulakanci? Da girmanka da darajarka!

Abida ta fada cikin hassala.

"To ya zan yi! Allah ne ya jarabace ni.".

Idan ba za ki taimaka mini ba kar ki ce na daina bin Maigado Abida."

Ya fada kamar zai yi kuka, sai ya bata tausayi.

"Ya Asad tunda har ka yi mata magana ba ta amince ba, Baba ma ya yi mata magana ba ta ji ba to mafita daya ne yanzu ya rage."

"Mene ne mafitan Abida?'

Ya tambaya a sukwane.

[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Ya Faruku ne. Shi ne kadai mafitar da ta rage maka. Idan kuma ka gwada a bangarensa ba a dace ba to ka rabu da Bilki ba za ta amince ba Wallahi."

Shiru ya yi kafin ya ce" Kina ganin idan Faruku ya yi mata magana za ta amince?

"Tabbas domin nan duniya Bilki tana ganin girmansa da mutuncinsa, sannan komai ya yi mata umarni tana yi, amma idan dai har shima ka tura shi ba ta amince ba am sorry to say Ya Asad ka haƙura da ita kawai."

Tafaɗa cikin ba shi tabbacin haka.

Shi kuma ya ce mata ya yi mata alkwarin idan har ya turo Faruku ba ta amince ba to zai hakura da ita.

Da haka suka rabu da Abida. Da maganar ya kwana a cikin ransa gari na wayewa, ya kira Faruk ya ce masa ya zo gida ya same shi yana son ganinsa

Faruku bai kawo komai ba tunda daman yana kiran shi a gida su zauna su tattauna.

Sai dai yau ya ga bambamci domin Asad ɗin wani mazurai ya fara yi masa yana tsare gida sannan ya fara masa wasu tambayoyi.

"An ce mini yarinyar nan Maigado na jin maganar ka ko?

Sannan idan ka bata shawara tana karɓa?"

"Haba kwamishina ba girman ka ba ne. Wannan muzaran fa? Faruku ne fa? Ka yi maganarka kawai in sha Allahu ina tare da kai."

Ya Asad na jin haka ya gyara zama yana fadin" Faruku ba za ka taimake ni ba, tunda dai tana ganin mutuncinka, ka taimaka mini na samo kanta, kana ganin ina zaune ba mata kuma burinku na yi aure, itama tunda ba mijin gwara mu haɗu mu sanya Babanmu farinciki, tana ta wahalar da ni, na kuma san idan kai ne ka ce kana sonta, ba za ta yi maka haka ba, kuma tunda har ka ambata ka bar mini ita, ka taya ni mana ni na same ta, ko hankalina zai kwanta ina son ta Allah ya sani an jarabce ni akanta. Ina son ta kuma zan cigaba da son ta har abada, wallahi zan rike ta amana da gaskiya, kuma na yi maka alkawarin zan sanya ta farinciki. Don Allah ka taimaka mini Faruku na aminta da kai a cikin y'anuwana na sake jin ce wa kai na musamman ne daga lokacin da ka hakura da ita saboda ni, ka haramtawa kanka ita saboda ni, na kuma shaida ka yi mini kara da kyautatawa mai yawa"

Hankalin Faruku ya tashi idanuwansa suka kawo k'walla.

Ba domin Asad ba, da shima ba gudu ba ja da baya akan Bilki sai dai ya shaida kuma ya san ce wa Aasad ya fi shi sonta, ya fishi buk'atar mace a kusa da shi, ita ma kuma tana bukatar namijin da zai so ta ya kula da ita, ta samu gidan da za ta huta wahalarta ta baya ta shafe daga tunaninta.

Nan take ya ce masa kar ya damu ya ba shi lokaci in ya yi magana da Bilki zai neme shi domin ya ji yadda suka yi.

Asad ya yi ta masa godiya har ya ji kunyan shi ya ɗan daɗe a gidan suna hira kafin ya yi masa sallama ya tafi yana fita ya kira ta a waya suka yi magana. Ya fad'a mata zai tura mata wani adireshi za ta zo gobe da yamma ta same shi akwai wata maganar da za su yi tunda asabar ce babu aiki.

Bilki na ta murna kamar an biya mata hajji, a tunanin ta yaya Faruku ya gaji da boye boye zai bayyana mata sirrin zuciyarsa kwana ta yi farinciki ita dai fatanta ta rabu da maitar Yaya Asad.

Washegari bayan la'asar Bilki ta sha kwalliya ta yi kyau har sai da Abida ta zolaye ta da cewa ko wani bazawarin ta samo musu? Sai ta ki magana ta fice tana ta dariya farincikinta ya kasa boyuwa.

Wani garden ne inda Ya Faruku ya tura mata nan ta nufa da taimakon map ko da taje ma ya riga ta isowa.

Bayan sun gaisa sun yi hira sannan ya gangaro kan batun da ya zo da shi.

"Bilkisu."

Ya kira sunan ta ta amsa cikin dakewa.

"Naam"

Ta amsa cikin shauƙi.

"Kina da burin sake komawa gidan uban ya'yanki?"

Kai tsaye ta ce masa "a a ba ni da wannan fatan har abada."

Ita fa murna kawai take yi anzo wajen. Yau Ya Faruku zai furta yana son ta. Ita kuma yana cewa yana sonta za ta amsa, ta kuma ce ya faɗawa Baba Babba sati daya ma ya isa su yi auransu.

Ya faruku ya yi shuru yana kallonta kafin ya ce" Kin tabbata kin hak'ura da Sahal?"

Ta sake ba shi tabbacin ita fa ta hakura sannan ta kara da cewa.

[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Ni fa Ya Farouku ba ka san ma wata mgana ba. Ko Alti ba ta sani ba. Aurena da Sahal ya haramta. Saki biyu ya yi mini ni kuma na saka shi ya karishe mini dayan saboda wani dalilina da ba sai na fada maka ba."

Jikin Ya Faruku ya sake yin sanyi ya kalle ta yadda take kallon shi tana mirmishi. Jira kawai take yi ya furta ta amince masa.

"Bilkisu!

Ya sake k'iran sunanta a nutse sosai.

"Na'am"

Ta amsa cikin zakuwa.

"Maigado idan na yi iko da ke za ki yarda na isa na yi din ne! Ba za ki ga na so kaina ba?"

"Ba wannan tsakaninmu yaya Faruku ka isa da ni kada ka yi kokwanto"

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Ina so na bada aurenki "

Bilki ta yi kaseke tana kallonsa saboda ba haka ta yi tsammanin ji daga gare shi ba.

"Ga wa?"

Ta tambaya cikin mamaki k'warai da gaske.

"Ga Yayanki Asad"

Hawaye suka kece mata, ta kasa magana saboda ya shammace ta irin sosai din nan ".

"In dai kin aminta da kaunar dake tsakaninmu. To ki sani ba zan cutar dake ba, ba zan yi miki sanadin wahala ko tozarci ba".

A wannan karon kasa amsa masa ta yi.

Ya sake tausasa harshe cikin rarrashi ya ce "Ki duba ni, ki amince ki karbi auran nan da zuciya d'aya ki jira ki ga yadda Ubangiji zai karrama rayuwarki."

Bilki ta fara kuka mai sauti tana fadin" Ya Farouku me ya sa ba kai ba?

Me ya sa ba ka ce kai ne za ka aure ni ba ? Kana cutar da ni. Tun ina budurwan kasan ina son ka, kai ma na san kana sona amma saboda wani banzan dalili ka haramta mans cikar burinmu. Yanzu kuma bayan na dawo ka daɗa ja na a jiki ka sanya mini sonka da mararinka, ina ta tunanin ce wa wannan karon zan same ka mu yi rayuwa tare. Zuciyata tana girmamaka tana sonka, shi ne za ka zo mini da wannan maaganar alhalin ina jin nauyinka. Ni dai gaskiya tunda ba sona kake yi da gaske ba, to kawai mu bar shi a hakan, ka bar batun mutumin can".

Ta gama fada tana kuka wurjajan kamar wata karamar yarinya.

Hankalinsa ya tashi ya ji ina ina ma da ace zai iya da shima ya murza hularsa ya fito zawarcinta amma kuma ina ba zai iya ba.

"Bilki ki yi hakuri don Allah ki saurare ni".

Ya fada cikin karfin hali kafin ya cigaba da fadin.

"Ba ki ga gwara na zauna a matsayin danuwanki yafi akan mu yi aure ba?

Ana iya yin aure a rabu duk matsananciyar soyayyar da take tsakani kuwa. Amma duk lalacewar zumunta ba'a rabuwa gabad'aya, ba yadda za'a yi ace mini tsohon yayanki ne, saboda har abada ba za'a rabu ba, duk hargitsin rayuwa kuwa. Ina sonki sosai, ina kaunar ki har cikin zuciyata ina mana fatan Allah yasa mu cikin masu soyayya saboda shi wanda sakamakonsu aljanna ne. Sau tari rayuwa tana zuwa mana ba yadda muka tsammace ta ba. Ba sai mun yi aure ne cikar soyayya ba Bilki! Don kuwa ina tabbatar miki ko kin rasa kowa a duniya ki ji a ranki kina da ni ".

Jikinta ya yi laushi zuciyarta ta narke mussaman yadda ta ga k'walla ta cika idanuwansa ga soyayyarta ta bayyana a cikin idanuwansa da gangar jikinsa gabad'aya.

Hakan da ta ga ni ya sake sanya kukanta ya tsananta ta dinga goge hawaye da majina da tissue.

Yayin da jarumtar Yaya Farouku ta k'wace don kuwa hawayen shi ma yake yi ba tare da ya ankara ba. Ya yi maza ya zaro tissue ya goge idanuwansa.

Tsawon lokaci sun kasa ce wa komai, fama kawai suke yi da tafasar zuciya. Sai shine ya sanya jarumta ya ce " Ya kike ganin za a yi yanzu Bilki?"

Cikin shakewar murya ta ce.

"Ni kam wannan bawan Allah ya matsa mini. Tsakani da Allah ya zalunce ni! Ya je ya nemi wata mana. Dole sai ni, tsofai tsofai da shi zai ce yana sona "

Ta faɗa cikin taɓara da shagwabar da ta sake narkar da zuciyarsa.

Dariya ya yi kafin ya ce" To ban da abin ki Maigado ai ni da Asad ɗanjuma ne da ɗanjummai ni nake binsa fa, shekaruna da nasa gaf suke ai".

Cikin shagwaɓa ta ce "Ni ina ruwana ko ka girme shi ni dai kai nake so ba shi ba."

Ya kalle ta yana sake yin dariya kafin ya ce" Maigado ba kara, ba ki ji kamar zan ji wani iri ba, a gabana kike kushe Kwamishina?"

Tana hararan shi ta ce" Oh Yaya Faruku nuna mini kake yi wata kusan ta fi wata ko?

Da sauri ya ce" Ba haka nake nufi ba Bilkisu ki yarda da ni".

[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "To yanzu ya ke nan kin amince na ba shi auranki?"

Tana tura baki tace" ya ci arzikin ka, ba dan ina sonsa ba"

"To na gode da nake da arzikin da zai ci. In dai zaki zauna lafiya ki ba shi farinciki ki mutunta shi, ki girmama shi ai kin gama mai wuyar son da yake yi miki ya isa ya rike auranku."

Haka ya zauna yana ta faman lallashintaa da ban baki har ta saki jiki ta ce ta amince.

Sai gab da mangriba duka suka bar wajen kowa ya shiga motarsa, kafin su rabu sai da ya sake jin ta bakinta ta ce ta aminta.

Tana mota ma kafin ta kai gida sai da ya kirata.

"Bilki kin aminta da kwamishina ba sauya magana?.

Kaitsaye ta ce" Na amince yaya Faruku."

"To zan turo shi "

Ya faɗa yana yar dariya.

"To amma ka faɗa masa bana son wannan k'ananun kaya da yake sanyawa ya ci zanzaro ala dole shi bai tsufa ba. Ka fada masa ya saka native wears gaskiya."

Ta faɗa tana tura baki kamar yana ganin ta.

Dariya mai k'arfi ta k'wace masa sosoa.

"Abida ta koya miki iya shege gaskiya"

Ya fad'a cikin dariya sosai.

[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "E mana da girmansa amma sai ya wani tsuke sannan

5 / 23