sake matsowa kusa da ita sosai ya ce "Zo mu tafi gidanmu kin ji Maigadona. So nake yau mu jijjiga gadon zinaren nan na ki da kyau. Ta so mana ai na ce ba zan sake ba, ki huce dan Allah kin sa duk ahalin gidan sun dau fishi da ni ba kuma wanda ya yi nufin taimakona a cikinsu."
Ko uffan bata ce ba. Ya gurfana a gabanta ya ce "Zo ki d'are na goyo ki, mu tafi gidanmu".
Dariya ta subuce mata, dattijo da shi zai wani ce ta ta zo ta d'are alhalin Baba babba ko momi zasu iya ganinsu. Wato dai shi namiji babu ruwansa da kunya.
Ta kawar da fuskarta tare da ce wa "Ba fa zan koma ba, ka yi tafiyarka, na riga da na gane ba zan iya wannan zaman ba. Ban iya yaudara ba, idan ma na iya ai ba zan yaudare ka ba Baban Bilkisu! Ka yi hakuri kada maganar nan ta sake cakalcakala mana al'amarinmu".
Ya mike tsaye cak. Ya zuba mini idonsa na saci kallonsa na ga har wani tsumuwa yake yi watakila da wani k'aramin d'an sanda ne ya bata masa rai da ya d'and'ana kudarsa domin ya fusata ainun.
Da kakkausan harshe ya ce "Kawai dama dai ki ce auren manufa kika shirya yi da ni?"
Ya yi mata kwarjini k'warai da gaske, tsoronsa da ta rayu da tashi ya taso mata.
Ta kasa ce wa komai.
Jin bata ce komai ba ya sanya ya sake maimaita tambayar da ya yi tabbacin amsatra yake dako.
Murya na rawa ta ce "Ba Hakan bane ko kadan. Ban same ka a yadda na zace ka bane. Na dauka ka aure ni dan kana sona kana kuma burin ka rayu da ni cikin adalci da jink'ai tare da wanke mini dukkan bak'inciki da na kwankwada. Sai dai tun tafiya bata yi nisa ba na gane manufar aurena bata wuce ace kana da iyali a idon jama'a ba, sai kuma dan ka sauke buk'atarka a duk sadda ka so. In ka cire hakan babu wani dalilin so, ko tausayina a tare da kai da na ga ni a aikace idan kuma akwai to tuna mini dan ni ban gansu ba."
Ya numfasa ya ce "Amma ai na ba ki hakuri, na ce zan gyara dukkan laifukuna, indai ba wani abu bane a ranki ai sai ki bani wata damar, idan ba ki ga sauyi ba, na amince da kaina zan dawo da ke gaban Baba babba cikin mutunci za'a yi komai tamkar yadda ya ba ni ke cikin mutunci. Da hankalinki Maigado ba za ki taimake ni ba, gabadaya fa daga Momi har Baban fishi suke yi mini. Ba akan komai sai a kan ki"
Hawaye ya b'alle mata ta ce "Saboda hakan ai na ce zan tafi na kama haya, ba zai yiwu na ce ba zan zauna da kai ba, sannan na zauna a gabansu indai ina da kunya da mutunci "
Kuka sosai ya k'wace mata, yinsa take yi tunda ga k'asan zuciyarta. Tare da ayyana dama dai ta yi hakuri ta rayu da y'ay'anta, da ta yi hakuri bata tirsasa mijinta ya sake ta ba, da yi zamanta a gidanta ta rayu da ƴay'nta. Idan mijin ya zo fine Idan bai zo bama fine. Don ta riga da ta saba da rik'e gida, dan haka ba zata gaza ba. To ko bai kawo komai ba. Tana da rufin asirin da zata rik'esu ba tare da ta ji komai ba. Amma yanzu ta bar yaranta suna ragaita a hannun yarinya k'ank'anuwa, ta zo tana hidima da yaran da suke ganinsu daidai da ita sannan babu godiya ko yabo a wajen mahaifinsu.
Kukan da take yi, ya yi matukar tayar masa da hankali domin dai ba yaro bane ya fahimci kukane na tsantsanin damuwa. Kukane mai nuna kololuwar gajiya da kunsar bak'inciki.
Jikinsa ya yi sanyi sosai ya ce "Dan Allah ki yi hak'uri! Gaggawa fa kika yi, dama zan d'auki mataki kuma yanzu haka fa na mayar da Laura gida tunda kin ce ba zata zauna miki a gida ba. Ki yi hak'uri ki yi mini uzziri."
Ita dai bata iya bude baki ta ce masa uffan ba. Ba kuma ta ji a jikinta zata motsa bare ta ba shi amsa ba. Don kuwa ita dai ta riga ta gaji da yadda take rayuwa cikin gidansa.
Ya yi rarrashi, iya rarrashi amma bata tanka ba.
Ya gaji ya zauna yana fad'in "Innalilahi wa inna ilaihir rajiun! Ya dafa kansa da alamu suka nuna juya masa yake yi ko kuma ciwo mai tsananin gaske.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: "Murya babu amo, kuma cikin bacin rai ya ce "Da kina sona Bilki na tabbatar za ki yi hakuri da dukkan laifukana, za ki jure, bare na ce ki yi hakuri zan gyara. Amma kin kafe na tabbatar da ace Faruk kika aura za ki yi hakuri da matsalar da tafi wannan tsanani a tare shi, na kuma yi imani kin ci karo da matsalolin da suka fi wannan nauyi da tozarci a cikin aurenki da yaron can, amma ba wanda ya taba ji ko ganin kin yi yaji kin bar gidan duk da k'arancin shekarun da kike da shi a lokacin.!
Duk da a cikin kuka take sai da maganganunsa suka yi mata dabaibayi, suka nemi d'arsa mata tausayinsa tare da haifar mata da sanyi jiki magashiyan.
Bai jira jin ta bakinta ba, ya sake tsananta rukon hannunta ya ce "ki ji tausayina Maigado. Kin sani tun kina budurwa nake son ki, dan haka zancen ki ce ba dan ina sonki na aure ki ba ai tatsuniya ce kawai irin ta shifcin gizo. Don a lokacin haihuwar Bilkisu da kin ba ni dama da tuni na aure ki. Amma kika bijire mini, kika yi tamkar ba ki gane inda na dosa ba. Na tabbatar zuwa yanzu an kwashe shekaru kusan sha takwas, idan kuwa hakane ai bai kamata ki ce bana sonki ba, ko da wasa ba kuwa, domin Wallahi tunda ga lokacin har zuwa yanzu ban huta da bugawar zuciya a dalilin soyayyarki ba. Na tabbatar Ubangiji ne ya musanya mini da ke a daidai lokacin da ya yi mini jarrabawar mutuwar uwar ya'yana, tunda ya sani ya jefa mini soyayyarki mai yawa a zuciyata, idona da gangar jikina gabadaya."
Na sassauta kukan da nake yi domin yadda yake magana kasan yana yi ne cikin tsantsar k'arfin zuciya. Domin tamkar ya rushe da kuka.
Tsawon lokaci ina shesshekar kuka yayin da ya yi bakam yana saurarona. Can ya numfasa ya ce "Tashi mu tafi".
Ko kwakkaran motsi ban yi ba a karo na biyu.
Ya saki hannuna daya ya dago hab'arta ya zuba mata ido sosai, itama ta zuba masa nata idanuwan da suka yi luhu luhu, suka yi jawur tsabagen kuka.
Ya yi kasa da murya ya ce "ki yi hakuri, daure mana, ki ji tausayina, idan har ke da kike jinina kin gaza akan lamarina da yarana wa kike tunanin zata rungumemu? Ba ni dama guda daya tak idan har ban sauya ba na amince da duk hukuncin da zaki dauka. Ina son ki, ina son rayuwa da ke, dan Allah ki daina tayar da hankalinki, me yasa kike son mayar mini da abin da yake cikinki sabon maraya, zuciyata zata iya bugawa idan ke ma na rasa ki tamkar yadda na rasa Rukayya.
Hawaye ya sake balle mata domin tabbas ya bata tausayi ta yadda ya raunana kwarai da gaske. Ta kuma gasgata shi mutum ne mai k'arfin zuciya na gaske.
Ya zaro tissue a aljihunsa ya hau goge mata hawaye yana ce wa "sorry Maigadona, very sorry!
Murya babu amo ta ce"Zan kwanta sai da safe"
Ya ce "Na dauka fa zamu tafine Sarauniyar shaiba! Ta girgiza kai ta ce "ka yi hakuri kaina ciwo yake yi, kasan kuma likita ya ce na dinga yin barci a wadace."
Nan da nan ya hau gyara mata gadon da shimfidarsa take a hargitse. Ta bishi da ido tana kallon yadda yake gyara mata gado mutumin da zai iya ajiye zaratan yan sanda dubu su yi masa.
Amma da kansa yake yi cikin rawar jiki da son ta ga gwanintarsa.
Ya dawo kusa da ita ya ce "za ki shiga bayi ne?"
Kai ta girgiza tunda fitowarta daga bayin ke nan ya shigo.
Ta mik'e ta d'ingisa ta hau gadon domin ji ta yi ƙafar ta yi mata tsami.
Ya tofe ta da addu'o'i tare da shafe mata jikinta. Tana jinsa yana ta faman laluben k'irjinta dan ya gane sune weak points ɗinta. Ilai kuwa nan da nan jikinta ya amsa ta nemi birkicewa. Sai kuma ta yi jarumtar saka hannu ta make masa tare da ce wa "Bana so, da iyayenmu a tare da mu kake yi mini haka?"
Ya mike daga durk'ushen da ya yi, murya babu amo ya ce "Na tafi Maigadona ki yi hakuri ki huce so nake gobe na zo mu tafi gidanmu. Kin san ba ni da juriya akan ki Balqees ki taimaki yayanki kin ji".
Ta gyara bargon sannan ta ce "Ni fa ba zan koma ina kallon yadda ka zuba ido yara na mini yadda suke so ba, ba zan koma kana daukan alamuran da suke hakkinane kana basu ba. Wannan shine gaskiyar magana ".
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Ya fesar da iskar damuwa ya ce "Amma na ce "Zan gyara ko? Akan me ba za ki ba ni dama ba? Na gamsu na yi kurakurai, na kuma yarda zan canja menene kuma ya yi saura indai ba tada zaune tsaye kike so ba!
Ya fada cikin fishin da yake ta danne shi kar ya k'wace masa.
"Hmm" kawai ta furta dan kuwa ba yarda zata yi ta koma ba, sai an baje maganar nan a gaban manya. Ta riga da ta fahimci kawaicinta ba zai yi tasiri akan lamarin yaran nan ba. Ba wacce take mamakinta irin Hafcy. Yarinyar da shekarar da aka yi aurenta yar yayace, tare da tuna irin soyayya da take a tsakaninta da Hafcyn har su Aysha amma wai yau sun yi girman da suke ganin bata kai ta zame musu uwa ba.
Sun washi su bude ido su ga babansu ya shiga al'amarinta ko dakinta. Tunda dangin uwarsu sun zugesu, tare dafad'a musu rabon aurenta ya kashe musu uwarsu.
Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba.
Ta idar da azahar ke nan ta koma gado k'arfe shida na asuba.
Wayarta ta dinga gumza(vibration).
Ta saka hannu ta duba ganin Baban Bilkisu ne ya sanya ta ajiye wayar ba tare da ta amsa ba.
Amma tana katsewa k'iran ya sake shigowa.
Ta dauka ta yi masa sallama murya babu amo.
Cikin taushin harshe tamkar ba shine ya tafi da fishi ba jiya. Ya ce "Maigadona tafiya ce ta kama ni kwatsam zuwa Calabar dan Allah, dan Allah na roke ki, ki raka ni domin kowa da matarsa za shi. Ki mini wannan rufin asirin sarauniyar shaiba. Na gamsu na amince idan mun dawo nan zan dawo da ke ba gidana ba" .
Ta yi shiru tana tunani tare da nazarin yadda zata ce wa su Baba zata yi masa rakiya alhali ta ce musu ta gaji da zama da shi.
Ya tausasa harshe ya ce "Pls sarauniyar shaiba ki kubutar da ni kunyata a idon magauta. Taron karramaq manyan jaruman tsaro za'a yi ki taimake ni, alk'awari na yi zan dawo da ke inda na d'auke ki."
Ta numfasa ta ce "To me zan ce wa su Baba?".
Da sauri ya ce "Kawai ki fad'a musu na roke ki za ki raka ni Calabar za'a yi bikin karrama mu".
To yaushe za'a dawo?
Yini ne kawai, ya yi tsananin gaske ne a tsallaka gobe".
Ta saki ajiyar zuciya ta ce "To".
Dad'i ya ratsa shi yana ganin nasara a k'udurinsa.
Ya ce "Ki shirya jirgin k'arfe goma na safiyar nan zamu shiga. Zan sanarwa da su Baba. Me da me zan dauko miki?"
A sanyaye ta ce "To".
Dan gaskiya ta yi missing d'insa da kalolin jagwalgwalonsa masu tsuma zuciyarta da gangar jikinta gabad'aya.
Ta zarce da fadin "Sabbin abayas din nan da ka siya mini a wajen Umm Aslan mai Egyptian abayas har da rigar barcin nan da ka ce ta yi maka kyau".
"Na gane su, rigunan barcin ma ai kamar a wajenta ne ko?"
Ya tanbaye ta a hankali.
"Eh duka a wajenta ne lokacin da muka je Eggypt, ka tuna har da su jewelleries da su jakunan mata na k'asaita".
Ya amsa da fadin"Ai zan sake siya miki wasu don ina matuƙar son products din da take siyarwa dukkan kayanta da wahalar gaske ka ga irinsu a wani waje."
+2349162662750
+201121544627
A hankali ta furta na gode.
Tare da fad'in zan yi barci ko na 1 hour ne ".
Ya ce "Amma ki tashi kafin takwas don ki shirya, zan zo kafin tara kin ga kafin mu isa iyafot ma tafiya ce mikakkiya."
Murya babu amo ta ce"To"
Alarm ta saita ya tashe ta k'arfe 7:45, ta ajiye wayar a gefe sannan ta gyara ta yi kwanciyarta.
Bata fita ba sai da ta yi wanka ta shirya tsab , cikin jikinta ya bayyana alamun ta fara nauyi ke nan. Sosai ta yo kyau, filazal bata rabuwa da materials din Umm Nihla. Don sosai take jin dad'insu bare yanzu da ta yi nauyi ba abin da take sanyawa sama da su, shafal suke babu zafi babu takura. Gasu farashinsu daidai da aljihun kowa ne.
Yanzu haka ma tattaunawa take yi da ita akan ta dinga turo mata daga Malaysia ta dinga siyarwa a Abuja tunda duk wacce ta ganta da shi sai ta tambaye ta a ina zata same su?" Gara kawai ta dinga sarowa tana siyarwa.
Malaysianfabrics raina kama ne.
7020695644.
Tana rike da jaka da ledar kayan da ta zuba, sai kuma ta fara tunanin yadda zata fadawa musu zata yi masa rakiya zuwa wani gari.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Kan dole ta fita ta tarar da su a falo. Ta zauna a kan kafet yayin da su suke kan kujera.
Cikin nutsuwa ta gaishesu. Sai kuma ta kasa cewa komai.
Cike da kulawa Momi ta ce "Ki je ki zuba abin karyawa a kicin ya ce zai zo ya kai ki, ki ga likita daga can zaku je Calabar amma yau zaku dawo".
Ta yi shiru tana tunanin ni ya ce mata zasu kwana d'aya zuwa biyu. Su kuma ya ce musu tafiyar yini ce. To ko dai basu fahimta ba ne?.
Ta furta hakan a fili.
Na tarar da Alti na dama kunu mai aikin Momi na soya dankali turawa dan Jos wanda kaitsaye dukkan ahalin suke siya duk abin da ya shafi dankali d doya da kuma kalolin vegies daban daban ta hannun Haj Rumanatu shugabar Raudatul Jannah foods Jos.
08065530483.
Kai dankalin Jos duniyane don shine asalin dankali mai dad'i.
Da girmamawa ta ce Mamah ina kwana?" Ta amsa cikin mutuntawa don kuwa dattijuwa ce sosai fiye da Alti.
Da azama ta dauko plate ta zuba mata wanda ta kwashe.
Ta sake dauko bowl ta zuba mata ferfesun kaji.
A dining din da yake kicin din ta zauna dan haka da ta bata sai ta ta cika katon kofin tangaran da kunun gyada. Tana fadin "na sanki da son kunun gyada".
Bilki ta murmusa ta ce "Na gode kuwa".
Cikin nutsuwa take karyawa. Sai da ta kammala ya iso. A gurguje ya gaisa da su Baba a dalilin lokacin tashinsu ya kusa. A sanyaye ta yi musu sallama ta wuce sukuku, tamkar marar gaskiya. Haka kawai take jin wani irin yanayi na takura a tare da ita. Ba dan tana kewar jagwalgwalonsa ba da ba inda zata bishi.
Sallar azahar a hotel d'in da suka sauka suka yi. K'afafuwanta suka d'an kumbura kad'an saboda dogon zaman da ta yi.
Da suka idar ya zauna ya dinga matsa mata k'afafuwanta sannu a hankali. Yana yi fad'in "Sannu Maigado."
Yayin da take jin dad'i na ratsa ta tunda ga tafin k'afar har kwanyarta saboda dalilai biyu.
Na farko ta yi kewarsa ba dan kad'an ba, na biyu kuma ta yi amannar shi baya cikin masu biye biyen mata.
Sosai ya tsiyayarata da ruwan kanta ya mantar da ita wai fishi take yi masa.
Kwanansu biyu suna holewarsu tamkar kwanakin farkon amarcinsu.
Kwanansu biyu bata ga ya je ko ina da sunan taro ko meeting ba. Tunda suka dira d'akin hotel din bai fita ba, tunda babu masallaci a wajen sai sune idan sun ga lokacin sallah ya yi yake janta su yi tare. Wannan zaman da suka yi sun shaku da juna ainun, zuciyoyi sun huta, sannan kuma sun kashe wa juna k'ishin kewar junansu.
Kwana na uku tana kwance a k'asan kafet ta yi filo da cinyoyinsa ta ce "Baban Bilki yaushe zamu koma ne tunda na lura ba wani aikin da ya kawo ka?".
Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Marmarin jihar Cross River ne ya fitine ni kinsan birinin mai dad'i da kyau, shekarar da aka yi aurenki aka dawo da ni jihar nan, a lokacin ina cikin tsananin gaske a dalilin rashinki sai gabad'aya garin ya yi mini kunci a dalilin zuciyar a kuntace take. Ban wani ji dad'in zaman ba, shekaru biyu na fara warwarewa sai kuma aka tura ni jihar Ebonyi. Shine yanzu na dauke ki don na rayu da ke na wasu kwanaki a garin da na yi ta kukan rashinki a boye babu kakkautawa ".
Ta murmusa ta ce "Hmm ai cuta ta ka yi, da baka bayyana da k'arfinka ba, ka tsaya yin raragefe, ni sai na dauka tsoron matarka kake ji, nima kuma ga ni na yi a lokacin ta fini ilimi da shekaru, ga yara ta haifa maka ai wahalar gaske zan sha idan na shiga cikinku".
Ya ce "Ke dai kada ki fake da wannan kawai Baban Su Amrah ya yiwa