Dingishin Kwado Book 3 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Romance

Chapter   15 / 23

42K to 45K   out of 67.7K words

Cikin jikinta bai rage musu komai ba illah k'ara mata zalamarsa da ya yi. Ya dinga jin kishin yadda Sahal ya kwashe shekaru masu yawa yana kwasar ganima da babbar mace irin Bilki alhalin ita din matar manyan maza jarumai ne ba irinsa da yake a lankwashe ba.

Tare suka yi wanka suka kwanta Yana shafa cikin da ya yi luf da alamu suka nuna ya yi barci.

Murya ba amo ya ce "Maigado na ji ya baje daga nan".

Ta taya shi d'ora nata hannun ta ce "Ya ji ruwan dumi, ya ji lafiyar babansa, ya yi barci".

Dariya ta subuce masa ya ce "Maigado bana son sharri fa ke dai ki fad'i gaskiya kina son a jijjiga ki kawai, ba sai kin jinginawa unborn ba"

Da murmushi sosai ta ce "Allah Dady shine ga zahiri ka ga ni, yanzu ba ya daina hautsinawa ba?"

Ya yi saki gauron numfashi ya ce "Na yarda."

Ta karya harshe sosai ta ce "Baban Bilkisu gobe idan an sha ruwa tare zamu fita ka yi askin sallah, nima a wanke mini kaina. Jiya na yi Oder din abayas a wajen Maman asalan da asala mazauniyar Eggypt din nan".

Da hanzari ya ce "Tom Allah ya kaimu, zamu je. Amma ban da kin fad'a mini ai har da yaran Sai a siyo musu daga can din".

Dad'i ya ratsata waton dama ba wani abin da zai yi?

A tausashe ta ce "Yanzu ma tunda bata turo mini ba, sai ta hado da nasun, gobe zan yi magana da ita sai Slsu zabi design din da suke so. Na gode ka ƙara hakuri da ni Allah ya tsare ka daga dukkan sharrin zamani".

Dad'i ya ratsa shi ya amsa da fad'in "Ameen Maigadona Allah ya sauke ki lafiya na k'osa na yi tozali da abin da ke cikinki k'warai da gaske. Tun ban gan shi ba ya samu matsayi mai yawa a zuciyata. Ina sonki ina son duk abin da ya shafe ki sarauniyar shaiba!

Daga haka ya latsa makunnar wutar. Ya karanta falaki da nasi tare da ayayul kutsiyu ya tofa a hannayensa ya shafe mata jikinta.Wani irin faricinciki ke tunda ga k'asan zuciyarta tare da wani irin shaukin da bata taɓa jinsa akan kowa ba sai akan Baban Bilkisu.

Ta kasa magana amma tabbas yanzu tasan ta yi aure, yanzu ne ake jiyar da ita dad'i tare da gusar mata dukkan sha'awarta. Tana jin ya sake karanto wasu surorin tsarin ya shafe nasa jikin sannan ya kwanta ya rungume ta a haka barci ya sure su.

Daga haka ya warware bai sake yi mata fushi ba. Da daddare kuwa ya dauke ta suka fice basu dawo gidan ba sai wajen shabiyun dare.

Aysha da Hafcy sun shiga hayyacinsu da ita, sun daina yi mata habaici haka nan sun fita a harkar Farha basa dukanta. Sai dai kuma basa yiwa Bilki magana.

Sun tafi a fahimtar ba haka kawai ta bar ubansu ba.

Abubuwan da yake yi a kanta ba iya soyayyar Allah da Annabinsa ba ce.

Dan haka ta samu sauk'in matsaloli amma bata jin dad'in yadda yaran suke gaba da ita. Da kanta ta fahimci duniya haka take babu wani cikakken dad'i. Wannan auren tabbas shine abu mafi dad'i gareta a yanzu. Don auren Asad ne ya fahimtar da ita akwai wani abu farinciki a duniya. A duk sadda cikin jikinta ya motsa sai Yaya Asad ya faɗo mata sannan kuma sai ta ji zuciyarta ta motsa a kansa. Zuwa yanzu babu k'insa da take ylji babu dalili a zuciyarta. Sannan ta gamsu ta fara sonsa, irin son nan mai shiga da sanɗa kafin an ankara ya yi tasirin gaske .

Tun ba'a je ko ina ba ta fara jin takaicin dogon zaman da ta yi da Sahal kuruciyarta na tsiyayewa a banza. Da tasan haka al'amarin yake da Yaya Asad zata aure tun farko Allah bar shi su fafata da matarsa. Don ko yanzu da Rukayya take kwance a k'asa duk yadda suka yi mu'amala mai dadi kishinta take ji, saboda hotunanta da suke samansa da dakin barcinsa ya sanya ta haramtawa kanta kwana a d'akinsa. Kuma tabbas nan gaba kad'an zai san yadda zai yi da su dan kuwa yadda ya girke su da hannuwansa to kuwa da hannayen zai kwashe su ya sakaye a wani lokon.

Ranar sallah Asad da kansa ya tuka iyalinsa a mota zuwa masallacin kasa na birnin tarayya(National mosque) don yin sallar idi.

Sai dai motor y'ansanda tana binsu a baya don kare lafiyar maigidansu da iyalinsa.

Daga masallaci gidan Baba suka zarce.

A gaban ya'yansa da yaransa ya fito ya budewa Bilki k'ofa ta fito ya sara mata bayan ya karbi jakar hannunta. Ganin hakan ya sanya ayarin y'ansanda ma suka yi abin da ogansu ya yi tare da fad'in "Madam barka da sallah!.

Aysha da Hafcy suka ido suna kallon ikon Allah ya yin da Bilkisu junior take vedio da tsaleliyar wayarta. Don abin burge ya ya yi tare da fatan itama ta auri jami'in tsaro ya dinga saluting dibta8cike da soyayya da girmamawa a gaban kowa.

Aysha da take lauya cemm tuni ta gama lissafinta ta gano dalilin da ya sanya mominsu yin surgery wato Dady na son mata masu mazaunai da cikar kirji ita kuma bata da su. Idonta ya cika da hawaye a dalilin ta yi amannar ko momi na da rai zai nade k'afar wando ne ya auro mata Anti Maigado ya kuma sha shagalinsa da ita, a yanzu kuma da babu ranta yana holewarsa da ita a gaban kowa yake nunawa ita din ta mussaman ce babu alhini ko tunanin tsohuwar matarsa. Ta saki gauron numfashi a dalilin Su din bai gaza musu da koami ba, komai suke so haka zai yi musu, Duk kuma soyayyar da yake yiwa Bilki da suke adawa da hakan bai hana ya basu lokaci musu tattauna ko ci abinci tare ba.

Haka ma Anty Maigado bata yi musu komai ba, illah auren Babansu alhalin ya k'i anty Laura. Sannan dangin uwarsu kaf fad'a musu suke yi rabon auren Bilki ne ya kashe uwarsu.

Tunda shi ba mai ra'ayin aure aure ba ne. Amma yanzu Aysha ta fara kokwanton dan Babu Momi ne ya sanya ya aure ta. Tabbas ko ta na nan sai ya auro ta. Kuma ta yi imani takwarar da ya yi mata tun tana budurwa ba dan zumunci ba ne, dan yana sonta ne yana kuma rarrashin zuciyarta ta amince masa.

Duk zumuntarsu da anty Abida bai sanya sunanta ba. Kuma dukkansu sun san anty Abida ce favourite sister d'insa. Shiyasa take yiwa mominsu wulak6da isgili ba tare da iya yi mata hukunci ba, a karshe ma Sai Dai ya ce momin ce bata son y'anuwansa, shi kuwa duk mai sonsa to ya so Abida.

Haka ta ja jiki ta bisu a baya zuwa cikin gidan gabad'aya jikinta a sanyaye tana ta tunanin da shine ya rasu to da Momi zai yi wahalar gaske ta yi aure. Idan har kuwa zata yi to ba zata yi a kusa irin haka ba, idan kuwa ta yi shekararsa d'aya kacal a k'asa society Sai sun fitine ta da fad'in bata damu da mutuwarsa ba tunda ya bar kudi daga mutuwarsa har ta yi aure saboda tsananin fitina.

A babban falon ta tarar da dadynsu da dukkan tawagarsa sun gurfana gaban Baba da Momi da suke zaune a kan kujera.

Itama ta durkusa gefen Bilki tana mik'a tata gaisuwar.

Baba ya dinga addu'a da fatan Allah ya karbi ibada. Yayin da jikin Bilki ya yi sanyi tana hasaso ita nata mahaifan babu ko d'aya.

A hankali y'ansanda suka fice suka bar iya ahalin gidan. Tuni kuma an cika musu gabansu da cimaka iri iri. Abida ta fito sanye da gown ta Malaysianfabrics...... Ta yi kyau sosai duk ba kwalliya ta yi ba junior na biye da ita cikin shudiyar tsadaddiyar shadda.

Aysha da su Laura suka dinga gaishe ta cike da girmamawa. Dama haka suke kaffa kaffa da ita tunda ba ta yi musu.

Ta isa gaban Yaya Asad ta yi saluting d'insa ta ce "Barka da sallah Baban Bilkisu I.G.P din gobe da yardar Allah ".

Dad'i ya kama shi ya mike ya cire hularsa ya yi saluting dinta ya ce "Barka dai Abidan Baba k'anwar Bilkisu ".

Bilki ta kalle su cikin shauki da tuna baya, ta sani Yaya Asad da Abida wata irin kaunar juna suke yi ba kad'an ba, tamkar dai yadda suke ita ta da Yaya Sulaiman.

Karon farko Abida ta sunkuya ta cicciba Bilki ta yi saluting dinta ta ce "Yaya Maigado barkanmu da ibada".

Dad'i ya ratsa Baba Babba yana jin had'uwar kan mutanen ukun nan za'a ji ci lagon gabar da ta yi k'arfi a tsakanin ya'yansa da na Baba k'arami.

Shiyasa tunda al'amarin ya faru Bai sake barci cikakke ba Sai bayan auren Bilkinsa Asad. Wannan auren shine tsanin yin sulhu da afuwa a tsakanin ya'yansa da na k'aninsa. Don kuwa gidan Asad zai zama kowa na da alaka da gidan kaitsaye. Shiyasa kullum sai ya yi musu addu'ar Allah yasa albarka a cikin aurensu ya kuma dauwamar da shi.

Da dabara Abida ta janye Bilki suka yi d'aki.

Ta ce Maigado cire mini wannan bubu abayar na ganki sosai. Wato watannin aurenki watannin cikinki, ke Maigado ki rage had'ama".

Dariya ta k'wacewa Bilki ta ce "Ni da kika raina kya fad'a mini haka mana, alhalin shi ya kamata ki tambaya ki kuma jingina masa had'amar."

Abida ta ce "Ke da shi dai sak kun dace halittarku d'aya. Na taɓa jin matarsa na faɗawa wata aminiyarta cewar shi mabukaci ne na sosai ita kuma tsaka tskai ce. Kin ga kema tuni na san mabukaciyar ce kin ga ai abu ya yi kyau dole na jiki shiru babu wani borin ba Kya sonsa."

Kunya ta lullube Bilki don ta san gaskiya Abida take fad'a.

Can ta nisa ta ce "Bilki na fa k'osa wanccan birkitattancen yayan naki ya dawo, na k'osa k'warai da gaske ki faɗawa mijinki nima irin halittarmu d'aya da ku, an fara bincikem inda yake kamar yadda ya yi mini alk'awari ko kuwa na fara fita nemansa da kaina?"

Idonta ya ciko da k'walla.

Na yi shiru amma dariyar da ban shirya ba ta k'wace mini. Na ce "Ni wacece ta ce mini ita dakhila ce ne?"

A hassale ta ce "Abida ce amma sadda na fad'a din AI ban gane kaina ba, yanzu kuma an rataue ni shekaru uku ai dole na k'osa tunda raine da ni".

Ni dai dad'in yadda aka jarrabi ta akan Yaya Sulaiman nake yi don kuwa a bayyane yake tana da tasiri a cikin y'anuwanta tunda ta sauko ta huce da mu, to fishin kowa ba zai ma abin damuwa ba tunda hatsabibiyar tasu ta yi laushi irin tub'us din nan. Sai dai Bilki ta san da sauran rikici a gaba don Yaya Sulaiman ya fusata da ita takaddama ce mai tsananin gaske zata sake Tashi. A ranta ta dinga addu'ar Allah ya shiga don kuwa ga ni take ba k'aramin jan Abida zai yi a k'asa ba.

[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:31]

*Surayya Dee*

Hakurin nan dai shi Bilki ta bawa Abida.

Tare da adduar Allah ya bayyana shi.

Sai azahar suka tafi nasu gidan su ya'yansu.

Daga kan Bilkisu, Amal da Noor basa bata matsala don kuwa tunda ta zane Hafcy suka sake nutsuwa.

Yayin da Aysha da Hafcy har ma da Laura ido ne a tsakaninsu. Suna yin yadda suke so a gidansu. Yayin da ta koma gefe take kallonsu.

Bilki na zaune tana cin hadddedn kulikulin da ya Asad ya koya mata ci na Ummiel foods 08036355535....wayarta ta hau kuwwa. Ta dan murmusa ganin sunan Baban Bilkisu ke yawo a fuskar wayar.

Ta dauka da walwala ta ce "Baban Bilkisu ka sauka ne?"

Da take yana cikin tawagar da suka raaka Shugaban Yan sanda na k'asa (I.G). Zuwa jihar Sokoto kan sha'anin tsaro.

Jiya suka tafi, yau kuma zasu dawo.

Ya ce "Eh mun sauka sai dai zamu fara raka oga gida. Tuwo nake son ci, ki mini da kanki if possible Maigado".

Da kanzagi ta ce na shinkafa ko na semo?"

Na fi son na masalina fa".

Cikin hanzari ta ce ka samu Baban Bilkisu. Allah ya kawo ku lafiya".

Ta mike ta nufi kicin ta shiga store ta fito da garin masalina leda d'aya. Kad'an zata yi tunda yaran basa ci. Manyan kuma abin da suke so suke sawa a yi musu.

Ta bude murya ta k'ira Alti. Ta iso tana fad'in me kike so ne Mahmah?"

Daidai lokacin Laura ta shigo kicin din. Ta bude sink tana wanke hannunta.

Bilki ta ce "Baban Bilki yake son cin tuwo ya ce na yi masa da kaina."

Farinciki ya bayyana a fuskar Alti a dalilin ta fara gamsuwa Bilki ta fara son mijinta, nan gaba zata dawo da hakurinta ta yadda zata jure duk wani k'alubalen zamanta a gidan.

Don gabad'aya Alti a ankare take da ita kada ta yi musu sanadin da zasu bar wannan aljannar duniya tunda ta gane Bilki irin mutanen nan ne da basa neman hujja a so ko a kiyayya. Idan suna son mutum to suna sone da dukkan zuciyarsu duk kuma nak'asun wanda suke so zai zama an amsa uzziri. Idan kuwa basa son mutum komin kirkinsa da abin duniyarsa basa so, dole a k'yalesu.

Da azama ta ce "To da me zan taimake ki?"

"Ki fito da kaza ki wanke, ki silala mini, miyar ayayo zan yi masa ".

Alti ta ce "Yanzu kuwa. Ta bude firiza.

Laura ta fice tana jin takaicinsu gabad'aya ya kamata. Tare da tunanin yadda zata b'ata girkin tunda kishinta take yi sosai, so take a ce itace a gidan tana bada umarni ayi ko a bari. Amma ya tashi ya dauko bazawara yana b'are b'are a kanta. Ta fice ba wanda ta yiwa magana illa tafiyar tak'ama da take yi. Bilki ta jijjiga kai tana ayyana al'amura masu yawa, idan su Aysha suna yin dibar karan mahaukaciya da ita tana hakuri tare da zuba ido to lah shakka Laura ta yi kad'an. Amma dai zata sake daurewa tunda idan ta yi magana Alti balbale ta zata yi da fadan ta koyi rashin kawaici.

Sai da Alti ta dora ta ce "Da su Amrah nake yin waya, d'an nawa ya ce mini suna tafe cikin satin nan".

Bilki na dauraye tukunya ta ce "Haka suka ce mini dazu, zasu biyo matar k'anin babansu zata zo wani aiki, wai da motar ofis zata zo kuma zata yi kwanaki biyar."

Cikin nutsuwa da k'ware wa suka shirya masa tuwon da lafiyayyar miyar ayayo da aka burge gudar kaza a cikinta.

Ta hada masa salad don ya samu daidaito a cikinsa.

Ta shirya masa a falon saman da suke shan ruwa. Sannan ta zarce nata saman don yin wanka da kintsawa.

Ta bata lokaci tana shiryawa sosai ta yi kyau. Farha ta kalle ta ta ce "Mahamah kina da kyau fa! Kuma na ga fuskata irin ta ki ce, nima zan yi kyau kenan?"

Ta murmusa tare da fad'in "U are so beautiful Farha, kina da kyau ma fiye da ni".

Dad'i ya sanya Farha yin dariya har da tafi. Bilki ta kalle ta ce "Ki je wajen su Noor Dady yanzu zai dawo kada ya yi fadan bai gan ki a gunsu ba".

Ta fice a guje don kuwa ya fad'a mata idan bata zama a samansu to babu ita a zuwa London wajen Yaya Khadija.

Sanye take cikin super wax karshen tsadar, doguwar riga free size haka ayi ta babu ado illa tsadaddun stones da aka watsa a rigar. Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:35]

Ta yi kyau har ta gaji, ta yi fari, fata ta yi taushi k'warai da gaske. Zai yi wahalar gaske ka kalle ta sau daya baka sake na biyu ba.

Tana tafe k'amshi na alfarma na biye da ita. Gabad'aya samanta ya karade da k'amshinta.

Cikin nutsuwa take sauka zuwa inda tasan zai yada zango. Sai dai turus ta yi cikin tsananin alajabi a dalilin yadda ta tarar da Hafcy da Laura suna zaune suna cin tuwon da ta ajiyewa maigidan. Aysha na gefensu tana cin salad a bowl.

Bak'inciki ya turniƙe ta. Daidai lokacin kuma aka bude gate din gidan tabbacin ya iso kenan.

Da tsananin b'acin rai ta ce "Wa ya baku izinin taɓa abincin nan?"

Kaitsaye Aysha ta ce "Abinci a gidan nan kuma har sai mun nemi izni?"

Yayin da Laura ta ce "Mun dauka namune tunda daddy yana son mu dinga cin wanda kika saka aka dafa."

Yayin da Hafcy uffan bata ce ba.

Bilkisu tana d'akinta yayin da su Amal da Noor da kuma Farha suka yi waje don taro Dady.

Bilki ta kalli Laura ta ce "Ke ki tsaya a matsayinki kada ki yi kokarin wuce iyaka, idan su sun xama dole su zauna ke fa? Babu dalilin zamanki tare da mu".

Aysha ta ce "Ai kuwa zamanta daram don a tare da mu ta rayu".

Yayin da Laura ta fara kukan an mata gori. Daidai lokacin kuma ya iso inda suke shi da yaran.

Ganin Laura na kuka su kuma sun yi cirko cirko ya sanya shi tambayar ba'asi. Hafcy ta yi fit ta zayyane masa kanun labari ta sigar da ba zai ga laifunsu ba. Ya kalli Bilki ya ce "Kada ki damu don sun ci, idan sun rage zan ci sauran, idan kuma babu bari na saka charity ta yi mini wani abin, kada wannan cin abincin ya zama abin damuwa. Takaici ya mak'ure ta. Ta kasa ce wa komai a dalilin sun cinye gabad'aya tunda dama dauri uku ta yi, ta saka masa guda biyu ta zubawa Alti d'aya tunda itama masoyiyar tuwon ce, kuma tun lokacin ta zauna a kicin din ta ci bare ta dauko masa na Altin.

15 / 23