all your kayan mata*
*Tested and trusted*
*Muna dafa kaza da ciccibi*
*Muna da sanyi flusher mai kyau*
08032773332.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal đź«¶đź’Ťđź’›: Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:17]
*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items*
*Egyptian abayas*
*Egyptian nighties*.
*Bags and jewelries*
*Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria*
*Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*.
# +201121544627
# +2349162662750
Mamaki mai tsananin gaske ya lullube shi. Kishi ne ko kuwa tsabar rashin mutunci ne ya sanya ta zagi Rukayya da uwarta har ma da kakarta?
Ransa ya b'aci matuk'a da gaske.
Ya mik'e ya isa kusa da ita ya ce "Wanne irin abune ya same kine kanki d'aya kuwa?"
A harzuke ta ce "Na maimaita maka kalamaina ne don ka gane a hankalina nake ko kuwa?"
Ya juya ya tsaya a bayanta ba zato ta ji ya rungume ta, ta baya, a hankali ya dinga ja da baya ya Ăsa bakin gadonta ya zauna a hankali, sannan cikin nutsuwar ya zaunar da ita akan cinyoyinsa, fad'in mazaunainta da nauyin cikinta sun danne shi sosia irin yadda yake so. Ya daidaita mata zaman tamkar wanda zai shayar da ita. Ta shige kirjinsa tana rusar kuka sosai. Ya sunkuyar da fuskarsa daf da tata, suka dinga shakar numfashin junansu. Duk da a yanayin b'acin rai suke sai da jikinsu ya amsa. Ba zato ya rik'e mata hannunta da k'arfi ta yadda ba zata iya kwakkwaran motsi ba. Ya kai bakinsa kan nata bakin ya tsoste shi da kyau a k'arshe ya gasa mata cizo. Ta kidime amma bai sake ta ba, ya sake tsosatar wajen, sannan ya sake skaar mata cizon. Ta fashe da kuka daidai lokacin ya dago da fuskarsa ya kalli yadda take kukan azabar da ya gaana mata cikin wani irin salo mai birkitarwa. Ya sake mayar da fuskarsa daf da tata ya ce "A ina kika samu tarbiyar zagin? Ki janye zagin nan ko na cigaba".
Ta ki yin motsi bare ta janye din. Ai kuwa ya sake maimatawa, dad'i da azaba suke ratsa ta a lokaci guda. Cikin kuka ta ce "Ka yi hak'uri zan janye".
Ya sake ta ya zuba mata idonsa da suka yi jawaur gabad'aya shima ya birkice da bukatarta.
Ya sassauta rikon da ya yi mata. Murya ba amo ta ce "Fitsari zan yi".
Ya sake ta ta yi maza ta sauka daga jikinsa ta koma kan gado nesa da shi ta zauna ta bude baki tana rusar kuka wiwi. Ya numfasa ya ce "Tabdi jam wato janyewa ne ba zaki yi ba shine kika ce band'aki za ki, k'arya za ki koya?" Ya fad'a yana matsawa kusa da inda take zaune. Da sauri ta sake matsawa ta ce "Na janye zagin Talatu da uwarta. Amma Wallahi ban janye na Rukayya da na Laura ba".
Daga haka ta yi wuff ta shige bayi ta rufe kofar".
Duk yadda yake cikin bacin rai sai da ya murmusa.
Ta jima bata fito ba, ko da fito a Inda ta bar shi a nan ta tarar d shi bai motsa ba.
Ta wuce shi ta zauna can gefe tana kokarin warware duvet d'in da zata lulluba.
Ya numfasa ya ce "Wataƙila dai kin manta mu gidanmu na tarbiya ne, dole ne kuma a ladabtar da duk wanda ya nemi ya yi watsi da tarbiyar da aka d'ora shi a kai wala yaro wala babba. A gabana za ki zagi matar da ta haifi wanda ta fiki, hakan bai ishe ki ba, sai kin had'a da uwarta itama?
Cikin kuka ta ce "Kada ka fake da haka, kawai ka gana mini azaba ne dan na zagi matarka! To na janye na uwarsu da kakarsu amma ko zaka tsire ni ba zan janye na Laura da na Rukayya ba."
Ta fad'a cikin matsanancin kuka.
Ya yi shiru yana kallon yadda take kuka mai d'auke da shesshekar ajiyar zuciya.
Ya taso daga inda yake, ya zauna kusa da ita, ya ruko ta ya sassauta murya ya ce "Yi shiru sarauniyar shaiba, yi hak'uri."
Ta fisge cikin kukan ta ce "Ni Wallahi ba zan yi hak'uri ba sai Laura ta bar gidan nan".
Ya ce "Lallai kin shiryawa rikici sarauniyar shaiba, ga shi kuma ina kan batuna na ba zan kore ta a gidana ba".
Ta sake harzuk'a ta rushe da kuka ta ce "To kuwa ba zan zauna ba, ita ta zauna ta maye maka gurbina tunda na lura tana yi maka irin amfanin da nake yi maka!
Ya hassala k'warai da gaske.
K'warai ya ji zafin kalamanta. Laura tana yi masa irin amfanin da take yi masa? Tana zarginsa akan Lauran kenan. Wai su mata haka suke ne dukkansu? Mafi yawansu basa mallakar hankalinsu akan batun kishi. Kuma dan iskanci ma ko da zargi suke yi ba tabbas ba sai su rufe ido su yi rashin mutunci tare da d'iban albarka! Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:21]
Murya babu amo ya ce "Sa'arki d'aya cikin jikinki ba dan haka ba dan kin dandana kudarki Maigado".
Cikin kuka ta ce "To ka mayar da shi jikinka mana idan ya so ni ka kashe ni tunda ba ni da gata".
Mamaki ya lullube shi ya ce "Da kika tashin yi baki sai kika yi na rashin kunya Bilkisu? Wanne irin k'arkon kifi kika yi haka?"
"Eh!
Ta ba shi amsa a takaice.
Ya jijjiga kai ya ce "Zan kuwa goge miki shi".
Cikin kunkuni da kuka ta ce "Idan na zauna da kai ba".
Ya yi shiru yana kallonta amma zuciyarsa na suya.
Tsawon lokaci tana kuka yayin da ya zama mutum mutumi.
Haka suka kwana zuciya babu dad'i.
Sassafe ya fice bai yi mata sallama ba.
Ta yi wanka ta samu leda ta zuba dogayen rigunan Malaysianfabrics na Umm Nihla.......
Don sosai take jin dad'in saka su tunda basu da nauyi ga taushi.
Ta leka d'akin da Alti take ta ce mata ta shirya zasu fita.
Farinciki ta ya da ya kasance asabar ce don kuwa zata tafi da Farha babu wani shamaki.
Ta zuba turarunkata na Mkbees perfumes da mayunkata na lame skin ........
A motarta suka tafi.
Mamaki ya kama Alti da taga Bilki tana ta gararanba da su a manyan titunan Abuja.
A tausashe ta ce "Da alama dai tafiyar ba ta lafiya ba ce. Tunda kika dauko ni tare da Farha nasan ba k'alau ba."
Bilki bata tanka ba, tafiya kawai take yi. Alti ta kaurara murya cikin sigar umarni ta ce "Samu waje ki tsaya ".
Babu musu ta gangara ta yi parking.
Hakuri da rarrashi Alti ta fara yi mata akan ta daure ta koma d'akinta ba abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah.
Cikin rishin kuka ta ce "Ba zan iya zaman ba. Gaskiya na gaji!
Hankalin Alti ya yi tashin gauron zabi ta ce "Muje gidan Momi ".
Bilki ta kece da kuka tana fad'in yaushe zan iya zuwa wannan gidan, ai cutar da ya yi mini kenan ta ya ya zan je na fadawa Baba da Momi bana son d'ansu, na gaji da zama da shi, ta yaya zan k'i zaman gidansa na koma gaban iyayensa alhalin shi ya siyi gidan. Wayyo Allah wayyo Yaya Sulaiman!
Ta rushe da kuka wiwi.
Alti itama sai ta shiga taya ta kukan, tsawon lokaci suna yi, kafin Alti ta yi jarumtar had'iyewa. Ta numfasa ta ce "Da dai za ki amince da kin yi hak'uri kin koma gidanki idan Allah yasa kin haihu lafiya sai mu tattara mu bar masa gidan. Amma yanzu kina cikin wannan hali ina za ki je? Ki daure ki haife cikin nan a gidan ubansa."
Bak'inciki ya sake turnike Bilki, tabbas cikin nan ya yi mata shigar sauri daga zuwanta gidan ta same shi.
Murya ba amo ta ce "Ba zan koma ba fa Alti gaskiya!
"To na yarda ba za ki koma ba, amma a cikin biyu Wallahi sai kin zabi d'aya ".
Bilki ta yi shiru tasan kuma tunda Alti ta rantse to dole kuwa ta zab'a.
Alti ta numfasa ta ce "Ko dai mu je gidan Baba Babba ko kuma mu je gidan Farouku ".
Hawaye ya k'wacewa Bilki ta ce "Cikin cutar da Yaya Asad ya yi mini har da shamaki da ya gindaya a tsakanina da Yaya Farouku, ta ya ya zan je na zauna a gidansa alhalin na ce bana son d'anuwansa, duk yadda yake sona ai nasan yafi son Asad da ni".
Alti ta ciro wayarta ta lalubo sunan Faruku tunda tana iya karanta wasu daga cikin kalmomin hausa, don ta yi yaƙi da jahilci tun kafin ta yi aure.
Bugu d'aya ya dauka ya ce "An buga an bar ki Altin Bilki".
Ba kuzari a muryarta ta ce "Kana Abuja ne?".
"Ina nan Alti, Allah yasa lafiya na jiki wani iri ".
Ta ce Farha me aka rubuta a jikin wanccan dogon ginin?"
A sanyaye Farha ta ce "Sheraton Hotel". Don tunda ta ga uwarta na kuka gabad'aya ta rasa kuzarinta.
Alti ta ce "Ka zo muna tsallaken sharaton hotel".
A hanzarce ya ce "Lafiya kuwa amma dai ga ni nan zuwa yanzu".
Mintina talatin da yi masa waya ya iso.
A sukwane ya yi parking ya fito ya doshi motar Bilki. Ya bude gaban motar. Alti ta ce "Farha dawo nan.".
Farha ta tsallaka ta koma baya, Shi kuma ya zauna. Juyin duniya ya tambayi dalilin kukanta da fitowa ta bar gidanta amma ta k'i magana sai kuka.
Ya numfasa ya ce "Yanzu mu koma gidanki, ki yi hak'uri, nasan kina yi to ki k'ara hak'uri, Annabi ya ce aljannar mace tafi samuwa ne idan ta yi hak'uri ta yi biyayyaa a gidan aurenta.". Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:24]
Sai lokacin ta numfasa cikin rishin kuka ta ce "Gaskiya ba zan koma ba Yaya Faruku, ina cutuwa, ni gaskiya ina buk'atar na samu gidan da zan kama".
Ransa ya b'aci ya ce "Bilkisu Baban na da rai ne za ki kama inda za ki zauna? Me yasa kuke yi masa haka ne? Ko ni nake da rai ai ba kya yi mini wannan wulakancin ba bare Baba".
Jikinta ya mutu ta ce "To ya zan yi tunda ya dage sai da ya aure ni don ya shiga tsakanina da ku".
Faruk ya ce "Bai isa ya rabamu da ke ba. Yanzu na amince ba za ki koma gidansa ba. Amma ki zaba ko dai gidana ko wajen Baba".
Cikin kuka ta ce "Zan je wajen Baba ".
Ya numfasa ya ce "To mu je." Ya fita ya shiga motarsa ya ja, sannan ta bishi a baya suka tafi. Ba kowa a falon gidan sai talabijin da take babatu, k'amshin air freshener na mkeebs perfumery da yake tashi sannu a hankali tare da sanyin a.c ya sake sawa falon ya zama gun hutawa.
Alti da Farha ne suka shiga ciki suna sallama. Momi da take kan sallaya tana lazimi ta idar da walaha ta tsinci sallamar Alti. Kafin ta amsa Farha ta tura k'ofar d'akinta ta shiga. Nan da nan ta shafa addu'a tana fad'in "Farha kune da sassafe haka? Ta kalli agogon da yake makale a bango ta ga goma saura na safiya.
Alti ta durkusa tana gaida Momi cikin sanyin jiki.
Ta amsa a sanyaye tare da fad'in "Alti kune da sassafe haka ice ko lafiya?"
"Lafiya k'alau momi tare da ita muka zo tana falo da Yaya Faruku".
Nan da Momi ta ce "A a ba k'alau ba, tunda ta ja tunga a falo bata shigo ciki ba".
Suka fita momi na ganin yadda fuskarta ta yi ja ga idanuwa sun yi luhu luhu zuciyarta ta harba ta tabbatar babu lafiya.
Da hanzari ta isa kusa da kujerar da take yayin da Maigado ta mik'e kaitsaye momi ta jata jikinta ta rungume. Jin haka ya sanya Maigado rushewa da sabon kuka don a yanayin da take ciki so take a ce ta je gaban mahaifi ko mahaifiyarta ta yi kukan da take ta rik'e shi a ranta. Sun jima a hakan kafin Momi ta sake ta, ta ce "Zauna Maigado sannu!.
Maimakon ta zauna kan kujerar sai ta zauna a k'asa tana fad'in "Momi ina kwana?"
"Da kin zauna a kujerar ai sai tafi miki dadi Maigado".
Murya a dakushe ta ce "Babu komai momi".
Yayin da Momi ta kalli Farouku ta ce "Sannun Farouku Ubangiji ya yiwa kokarinka albarka".
A sanyaye ya ce "Ameen momi. Baba ya tashi kuwa?"
Ta ce "Har ya karya ya yi tattaki kwanciya ya ce zai yi amma ai dole ya taso".
Ta juya don zuwa d'akin Baba.
Tare suka fito da Baban kamar kullum yana sanye da farar jallabiya mai asalin tsada.
Duk da shekaru sun ja masa ainun da dan sauran kuzarinsa, ba dan mutuwar k'aninsa da takaddamar da ta biyo ba, da yafi haka kyan gani don tun lokacin bai yi cikakkiyar lafiya ba.
Alti ta gaishe shi, ya amsa da walwala, ya mik'awa Farha hannun tare da fad'in "Zo kusa da ni Bilkisu d'iyar Bilki".
Ta tashi daga kusa da Maigado ta isa kusa da shi ta gaishe shi yana tambayar ina ta baro Amal da Noor?"
Zuciyar Bilki ta doka, sai dai bata ji a ranta zata koma gidan da za'a dinga bawa yara lasisin su dinga zaginta suna aibata mata uwa haka siddan ba.
Cikin hikima Alti ta zame ta nufi kicin da ta jiyo motsin momi.
Momi ta fito ta ja Farha zuwa d'akinta inda junior yake barci don sassafe Abida ta fita zata yiwa wata patient c.s.
A nutse Bilki da Farouku suka gaisa da Baban nasu.
Ya k'are musu kallon nazari ya ce "Dukkanku ba kwa cikin walwala menene damuwarku ne?"
Cikin nutsuwa Farouku ya ce "Bilki ce ta samu matsala da mijinta, ga kuma halin da take ciki."
Baba ya yi shiru tsawon lokaci bai ce komai ba.
Yayin da dukkansu suke dakonsa.
Ya numfasa ya ce "Yau ne karon farko da kika taba barin gidan aurenki da sunan bacin rai, ban so kika karyawa kanki record din ke ce kad'ai baki taɓa yin yaji ba tunda aka yi miki aure, sai ga shi kin fara yi a inda ban yi zaton za ki yi ba. Na kuma shaida alamarine ya kerewa haƙurinki, amma da sawa kika yi Farouku ya kai miki ni gidanki da yafi mini dad'i." Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:31]
Bilki kanta na k'asa tana zirar da hawaye ta kasa magana.
Ya nisa ya ce "Menene matsalarki?"
Ta kasa ce masa komai, Farouku ma ya yi tambayar duniya, amma bata ce komai ba sai kuka mai tayar da hankalinsu".
Baba ya ce "Ai kin yi k'uruciya Maigado, da zaki taho da kin sa ni kin had'o da Amal da Noor amma sai kika tsame y'arki a cikin y'anuwanta alhalin ni kika saka na fad'a masa za ki je masa da ita, na fad'a masa ya kuma ce ya amince zai saka ta cikin jerin y'a'yansa, yanzu dan kun samu matsalar da ba sakinki ya yi ba sai ki watsar masa da y'ay'ansa k'ananu ki taho da taki kad'ai? Anya kuwa! Wannan ba halayyarmu ba ce, ba mu da wannan halayyar ta banbantawa."
Kukan Maigado ya tsaya cak. Domin kuwa iyakacin gaskiyarsa yake furtawa wanda ta yarda babu son kai ko na zuciya a cikinsu.
Take kuma ta gamsu ta yi kuskuren barin yaran mussaman da su basu yi mata laifin komai ba.
Ya nisa ya ce "Ki zauna zuwa yamma idan mijinki ya tuntube ni, ko Farouku to za ki koma a yau din nan. Hakan ma dan na ga yanayin da kike cikine ya sanya zan barki, ki d'an huce. Amma da yanzun nan za ki koma inda kika fito".
Ta shi ki je dakinki ki kwanta ki yi barci kafin Dr Abida ta dawo".
Ta yunk'ura da ƙyar ta tashi ta nufi ciki yayin da Baba da Farouku suka bita da kallon yadda ta aune ga ciki ya habaka tamkar a lokacin zata haihu.
Sai da ta k'ule sannan Baba ya nisa ya kalli Farouku ya ce "Ban da k'uruciya ma a wannan halin da take ciki me zai saka ta bar d'akinta?
Faruku ya ce "K'ure ta ya yi ne Baba ai Maigado mai hakuri ce kowa ya shaida hakan".
Baban ya nisa ya ce "Ai kuwa zai hadu da fishina Wallahi akan Maigado zan yi matuƙar sab'a masa, bata son aurensa amma ya dage ya matsa sai da ka shawo masa kanta shine tun auren bai je ko ina ba zai fara tayar mata da hankali?"
Baba ya yi tambayar yana kallon Farouku tamkar shine Asad din.
Farouku ya saukar da kansa k'asa ya ce "Ka yi hak'uri ni kaina ban ji dad'in al'amarin ba, zan fad'a masa gaskiya idan ya yarda shikenan, idan ya yi wasarere da matsalar kwabarsa ce zata yi ruwa."
Sai shadaya sannan Faruku ya yi sallama da iyayensa akan da yamma zai dawo.
Abida bata dawo ba sai azahar. Junior da suke wasa da Farha ya ruga ya rungume ta. Yayin da Farha ta yi mata sannu da dawowar ba tare da bar wasan da take yi ba.
Ta kalle ta ta ce "Ke da wa kuka zo?"
"Da Mahma tana ciki tana barci".
Abida bata kawo koami ba, tunda Maigado na da ciki don ta yi barci ba komai ba ne.
Ta leka d'akin Momi ta fad'a ta dawo sannan ta shiga dakin Maigadon.
Ta idar da sallar azahar tana ninke sallaya.
Ta ce "Maigado kin ga yadda fuskarki ta yi kozai kozai kuwa, me ya same ki haka?"
Ta yi k'arfin halin ce wa "Ba komai.
Jikin Abida ya yi sanyi a dalilin ta gane ba k'alau ba.
A sanyaya ta ce "Bari na je na yi sallah na dawo ".
Da ta yi sallar ta dawo ta tisa ta a gaba