shigowa dakin su ba.
Tana shiga ta kalli su Amal ta ce
"Ku je falo ku ce Alti ta kunna muku cartoon din a can Farha."
Ta fada tana kallon ta da sauri ta yi gaba tana fadin" To Mahma Noor mu ku zo je."
Sai da suka fice sannan Balki ta mayar da hankalinta wajen manyan tana kallonsu.
"Sannu da gida Anty."[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: In ji mai sunanta Bilkisu.
"Ya hutu?"
Ta fada tana kallonta.
Sai ta amsa da lafiya lau, da ma ita suna gaisawa marar kunyar ta k'arshe Hafcy ce.
Yanzu ma ko kallon Bilki ba ta yi ba, hankalinta na kan wayar hannunta
Stool din madubi Bilki ta jawo ta zauna lokaci daya tana fadin" Sannu Hafsat."
Da gayya ta yi mata sannu domin ta ji kunya, idan ita ba za ta gaisheta ba, ita bari ta watsa mata kunyar gabadaya.
Amma yarinyar nan ba ta ji kunya ba sai ma ɗagowa da ta yi, ta sakar ma matw wani kallo kafin ta amsa da lafiya kawai ta cigaba da latsa wayarta. Ta ji wani iri amma sai ta danne ta numfasa ta ce
"Bilkisu da Hafsat me ya sa ba kwa cin abincin da na saka ake dafa mana gabadaya?"
Ta tambaye su tana kallonsu.
"Muna ci mana."
Bilkisu ta amsa amma ban da Hafsat..
"Ba kwa ci, sai dai ku saka Jummai ta yi muku naku daban. Kunsan kuma ba yadda za'a yi a dora tukunyar abinci a gidan nan a hanaku. Sai mu yi d'aku ku k'i ci, ku saka a dafa muku fiye da cikinku, abincin yana yin yawa da safe sai an zubar me ya sa haka?"
Bilkisu ta yi shuru domin ita ko tana son ci sai Hafsy ta hana ta.
Hafcy kuma ko nuna ma tana jin su ba ta yi ba.
"Ba zan takura muku sai kun ci abincin da na saka aka dafa ba. Amma ina so ku sani in har ba za ku ci ba, ku fada min, sai na fad'a mata ta daina sanwa daku idan jummai ko charity kuke son su dinga dafa muku ya wadatar ba sai an yi barna da yawa ba."
Suka yi shuru ba wacce ta yi magana.
"Ina fatan kun fahimta?
"E Anty"
Bilkisu ta fada kafin ta cigaba da fadin" Ki yi hakuri Anty."
Bilki ta mike tana fadin" ba komai ni dama saboda b'arnan abincin ne ya sa na yi magana."
Har ta kama hanyar fita ta ji Hafcy na magana cikin gunguni
"Ai ko mun yi b'arnar Daddynmu ke kawowa ba wani ba "
Ta fada tana hararan ta gefen ido.
Bilki ta juyo tana kallonta da kamar za ta ce mata wani abu sai kuma ta kasa hadiyewa ta ce" Haka ne shi yake kawo wa."
Daga haka ta fice daga dakin nasu, ta koma nata ta dade a gefen gado tana fama da zafin zuciya, yarinya karama take yi mata rashin kunya amma ta kasa daukan mataki.
Ta dade zaune tana tunanin kafin kiran sallar mangariba ya tashe ta, ta shiga tiolet ta dauro alwala amma a ranta ta kud'iri niyyar ko mai za su yi ba zata sake yi musu magana ba, kamar yadda suka fada gidan ubansu ne, su yi yadda suka ga dama.
Tun daga ranar ta kawo ido ta sanya musu, duk sun manta da tara sun da mahaifinsu ya yi farkon dawowarsu gidan a gaban Bilki ya ce su yi mata biyayya su darajata idan har suka yi mata rashin da'a shi suka raina ba ita ba, amma duk Hafcy ta manta da wannan karatun, shi kuma baya yini a gidan bai san abin da yake faruwa ba, da daddare yana tare da yaran sai sun kwanta sannan yake zuwa wajen Bilki.
Ita kuwa tana zaune tana zaman jiransa wani lokacin ma barcinta take yi tunda ta fara fahimtar Kakar hak'urin da zata yi a nasa gidan.
Wani dare ya shigo d'akinta ya tarar tana ninke sallaya da alama shafa'i da wuturi ta idar. Ta cire ƙaton hijab dinta na gunis collection . Sanye take cikin rigar barci ta garari fara kal wacce umm asala mazauniyar Eggypt ke kawo su Nigeria....
Cikinta ya fara turowa ta sake budewa ta kasa. K'amshinta na mussaman na tashi ko ya ya ta motsa. Shima ya yi wanka sanye yake cikin hadaddiyar jallabiya ruwan madara. Kamshinsa ya cika mata kofofin hanci.
Ya matsa daf da ita ya rungume ta a hankali ya ce
"Maigado ki rika zama tare da yaran nan da haka ne za su shaku da ke.".
Ba ta ce masa komai ba illa to domin ita bata son ta fara magana ahalin yanzu, ga cikin jikinta ba ya son hayaniya yanzu abu kadan zai bata mata rai, ta fara jin za ta yi kuka, sannan yana saka ta hassala nan da nan amma duk da haka tana ta daurewa.
Tunda ya yi mata magana ta ke dan fitowa suna zaman hiran amma ba mai sako hira da ita to gwara ma Bilkisu, amma Hafcy yi take tamkar bata san da ita a wajen ba, da ubanta kawai take hira.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Har suka kammala ayyukan Bilki na zuba idon ganin Aysha ta fito ta tanka ko ta ce sai an yi mata girkin dole. Sai ta ji shiru. Ta dinga ganin ashe ma rashin motsa kwanjine ya sanya suke yi mata cin kashi.
K'arfe shida sun kammala komai an shirya abinci abinci a saman tsakiya inda suke shan ruwa gabad'aya. Bilki ta fito a wanka ke nan ta ji ana bude mass get. Gabadaya gida ya kaure da k'amshin spice's din girki na Amreesh spicy Kano....
Ga kuma k'amshin tuararukan Dubai masu tsada na tashi sannu a hankali cikin burner.
A takaice dai gidan tamkar aljannar duniya ne.
A takaice ta shirya cikin bubu abaya ta elsisi Mai zuwa da mayafinta wacce itama dai a wajen mazauniyar Eggypt din nan uwar Yan biyu ta yi order din ta Umm Asalan da asala mai rigunan kasaitaaccun Mata.....
Ta saka hularta da ta ce da rigar. Ta ajiye mayafin akan gado. Ta dauki sallayar tare da mayafin ta sauka zuwa inda zasu sha ruwa don da shi da ita da yaran Syke Shan ruwa gabad'aya tunda aka fara azumi yaunkuma na biyar zasu kai.
Abin jin dad'i Shi yake jansu sallah.
Sallar Isha da asham kuwa a can k'asa suke yi ya jasu tare da dukkan ma'aikatan gidan maza da Mata.
Zamanta da shi ta gane ba shi da girman kai ko kad'an sannan Yana da kyakkwar mu'amala da na kasa da Shi. Rashin faraarsa ba ya hana shi kirki da saukaka mu'amala da jama'a.
Kawai inda take ganin rauninsa ta fahimci tamkar yana cikin mutane masu tsananin son ya'ya.
Amma sai bata wani ganin laifi tunda bata ga wani abu da zaisa ta tuhume shi akan son ya yi yawa ba. Dama ba yadda za'a yi ka haifo d'a ace baka sonsa.
Ta sauko daga samanta, shi kuma ya hawo dan haka suka hadu a tsakiya. Ya cire hularsa ya sara mata da taushin murya ya ce "Ranki ya dad'e sarauniyar shaiba ya ibada?"
Ta murmusa tare da mika masa hannunta na dama ta ce "Alhamdulillahi, ya aiki dafatan dai yau baka ji k'ishin ruwa sosai ba?".
Ya sumbaci hannun sannan ya ja ta zuwa tafkeken falon da suke zama.
A ciki ya tarar da yaran har kananun. Ganinsu bai saka ya sakar mata hannu ba sai da ya kaita kujera ta zauna. Ya dunkule hannunsa na dama alamar jinjina ya ce "Sannu da k'ok'ari Maigado gabad'aya k'amshin girkinki na daban ne wani irin k'amshi yake bayarwa da ba'a jinsa a ko ina sai a girkinki."
Dad'i ya ratsata don kuwa tana matuƙar son ta ji yana yabon ta, sannan shi a gaban kowa yaba mata yake yi ba ruwansa da yara
Sai da ya ga ta zauna sosai sannan ya juya ga yaran ya karbi gaisuwarsu. Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Ku bani mintina goma na watsa ruwa".
A ranta kuma tasan spice's din Amreesh babu na biyunsu wajen k'amshi da fitarwa girki dandano na mussaman.
Aysha na kishigide wayarta na hannunta ta gefen Ido kuwa Bilki take kallo. Haka kawai ta ji wani abu ya mintsine ta ganin yadda ta yi kyau ta haska maroon din rigar da take jikinta. Sannan cikin jikinta ya fara turowa ana ganinsa duk kuwa da ya bi jikinta. Sosia ta ji ciwon da ya ce wai k'amshin girkinta baya jinsa a ko ina sai a gunta. Wato har na mominsu kenan?
Ta yi k'aramin tsaki tabbas ba zasu shirya da Anti Maigado ba mussaman da dazu ta nuna mata iyakarta a gidan ubanta. Bari a sha ruwa itama ta nuna mata tasirin y'a a wajen uba.
Mintina shabiyar ya fito sanye da jallabiya coffee k'amshinsa ya baibaiye su tun kafin ya shigo.
Yana shigowa ana kirian sallah.
Suka yi addu'ar buda baki sannan suka hau cin dabino da inibi ga kuma kankana da ruwan roba da ya yi raba don sanyi.
Suka dan huta sannan ya jasu sallah.
Bayan sun idar suka fara cin soyayyar doya da kwai da kuma ferfesun kaji sai kunun gyada, da shayi. Ga kuma su samosa a gefe. Sai kuma farrar shinkafa aka dafa da kayan lambu irinsu kara's, pea's, da koren wake da za a ci da soyayyiyar miyar kaji. Ga hadin salad mai kyau. Ga kunun aya mai dad'in gaske.
Duk abin da kake son ci shi zaka zuba da kanka. K'ananun ne ake zuba musu zabin da suke so.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Sannan har yanzu girkinsu suke sawa a yi musu. Basu fasa yin yadda suke so a kicin ba.
Bilki ta rasa yadda zata bullowa lamarin sai kawai ta ce a daina girki da su, ta rika dafa iya su da su Amal su kuma Jummai ta dinga dafa musu abinda suke so, hakan kuma da aka yi shike nan Bilki ta samu zaman lafiya, ba ta shiga harkansu suma ba sa shiga tata, tana zuwa wajen aikinta suma suna zuwa makarantatsu tunda dama hutun da Hafcy ta samu ba mai yawa ba ne . Bilkisu ma a sati biyu da suka shud'e ta fara zuwa makarantarsu Hafcy ta samu gurbin karatu zata karanta pharmacy, dan haka sai dare suke haduwa, idan kuma sun hadun Bilkisu za ta gaishe ta amma Hafcy matsewa take yi tamkar bata ganta ba.
Al'amarin Hafcy na matuƙar ciwa Bilki tuwo a kwarya, kawai hak'uri take yi, don ba zai yiwu ta biyewa yarinya k'ank'anuwa ba. Amma dai tabbas ta gama tabbatarwa jarabawar aurenta da Asad yaransa ne don sune zasu hana ta zaman lafiya.
Bilki bata san ce wa Hafcy lafiya ba ce sai da Aysha ta kamalla kwas dinta ta dawo gidan anan ne ta tabbatar da Hafcy ba ta yi mata komai ba. Ta dauka Aysha da take babba za ta fi su hankali mussaman yadda idan sun je hutu Funtua tana makale da ita tunda Abida bata kula yara.
Tundaa ta dawo gidan komai ya fara sauyawa, kai tsaye ba ta yi wa Bilki rashin kunya amma ta zuge yaran har da Bilkisu mai dama dama yanzu ta kasa gane kanta. Su Amal kuwa tana dawowa duk ta kwashe kayansu ta mayar dakinta ta raba su da Farha, duk Billki ba ta yi magana ba amma lamarin ya ba ta mamaki sannan ya daure mata kai.
Kuma ta koma ita ke yiwaa yaran komai.
Alti ke yi musu abin kari da wanda za su tafi da shi amma tana dawowa ta ba da Umarnin jummaia ce za ta dinga yi.
Alti ta yi mata magana ta ce "Mahma kada ki bari ta raba su Amal da Farha. A sanyaye ta ce "kyale su kawai ai su gidan ubansu ne ita kuwa fa? Ubanta ya yi nisa nice nake zaman uwa da uba a gare ta dan haka ki dinga yi mata kawai". Ta kamalla maganar da kuka don gabad'aya ta fara gajiya.
Ta koma kawai ta zama yar kallo shi kuma megidan bai san wainar da ake toyawa ba. Duk tsiyar Hafcy bata taba nunawa akan Farha ba amma tunda Aysha ta zo ta tisa mata yarinyar da hantara da zare ido da dukkan alamu Aysha bata son Abida duk yadda aka yi. Idan ita basa sonta to Farha fa? Kuma idan yaran basu san ba ita ta haifi Farha ba, to Aysha ta san Abida ce ta haife ta. Abida kuwa uwarsu d'aya ubansu daya da ubansu. Amna gabad'aya ta hana su Amal kulata daga Bilki har d'iyarta Aysha ta takurasu matuk'a da gaskeq .
Tun Bilki na mamakin lamarin har ta fahimci Aysha dai kishi take yi da ita mai tsananin gaske.
Sannan dangin babarsu sun fad'a mata rabon auren Bilki ne ya kashe uwarsu. Bayan haka ya k'i auren Laura wacce ita yafi cancanta ya aura don kanwar Momi ce da ta girma a hannunta ba zata taba cutar da su ba. Sannan ba zasu zama bak'i a gidan ubansu ba.
Da haka suka sake cusa mata kin Bilki tare da kud'irewa sai sun matsa mata ta bar musu gidan. Antinsu ta shigo tunda wata kusar ai tafi wata.
Da yake da iliminta cikin ruwan sanyi ta baza makaman yaƙin musgunawa Bilki.
Ana cikin haka aka shiga watan azumin ramadan. To da wuri megidan yake dawowa in dai yana gari ya yi bude baki tare da iyalinsa da haka ya saba tun filazal.
Ganin haka da Bilki ta yi ya sanya karbar ragamar girkin buda baki sai dai a taya ta don kama wasu ayyuakan don kwadayin samun ladan ciyar da mai azumi.
Don haka tun azahar suke shiga kicin ake Fara hidimar abin shan ruwa tunda ba iya cikinsu suke yi ba har da ma'aikatan gidan.
Amma ga mamakinta sai Aysha ta saka Charity da Jummai yin wani girke-girken na daban.
Karon farko da Bilki ta taka birki akan ba za'a yi wani girki ba matuƙar tana kicin din.
Sannan abin da aka yi shi kowa zai ci.
Aysha ce ta ce "Na yi fa Anty".
Jummai ta fadaa dan tsorace.
Kaitsaye Bilki ta ce "Ki ce mata na hana ina aiki a kicin din".
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Cikin kyawawan plates din ralzaplace suke cin abincin.08109544470
Cikin nutsuwa suke ci a hankali ya fahimci Aysha da Hafcy Basu zuba komai ba. Tun kankanar da suka sha da ruwa basu taɓa komai ba. Ya ajiye cokalin hannunsa. Da kulawa ya ce "Aysha, Hafcy bakwa cin abinci what's wrong?"
Suka yi shiru nan da nan idon Aysha ya cika da k'walla ta zuba masa ido take ya gano kuka take yi sannan bata cikin sukuni. Tausayinta ya kama shi yasan mominsu ta tuna tunda sun saba da ita suke zama irin haka, bana kuma ba da uwarsu ba dole hankalinta ya tashi. Atausashe ya ce "Menene?"
Da rawar murya ta ce "Dady kasan bama cin doya da aka soya da kwai ni da Hafcy, sannan ni bana cin kaza.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: https://youtu.be/j7_u1udYqDI?si=Jg27RDNS9GcXtCOJ
*Dingishin KWAD'O*
*Book4*
*Na*
*Surayya Dee*
*Dan Allah masoyan rubutuna ku daure Ki cicciba mini labarin nan ta hanyar yi mini likes a YouTube.*
*Gasa ce da yawan likes da za'a fitar da gwarzon labari*.
*A daure a mini like an saki episode 1-3 wadanda suka yi Allah ya saka musu da ALHERI, waɗanda Basu yi, a daure a yi, Ubangiji ya taimakemu gabad'aya.*
Kuma duk abincin akwai kaza a ciki."
Da sauri ya ce "Hakane to ai da kin fad'a mata tunda bata sa ni ba ".
A nutse kuma a hankali ta ce"Na saka Charity ta yi an ce ba zata shiga
Cigaba
kicin ba, na tura jummai tunda ita mai sallace an ce ba zata yi ba, dole abin da aka girka shi zan ci, alhalin mu ba haka muka saba ba."
Ta fad'a tana goge hawaye da tissue hannunta.
Ya juya ga Bilki ya ce "Maigado ki dinga bari ana yi musu duk abin da suke so. Yanzu charity da Jummai ai kusan zamansu suke yi tunda sun san me suke so. Mun Saba rayuwa kowa yana cin abin da yake so ne ba takura ".
Mamaki ya hana Bilki magana.
Ya tashi daga kusa da ita ya koma kusa da Aysha da Hafcy da suka koma gefe. Ya dinga rarrashi tamkar yara k'ananun akan su yi hak'uri su ci snacks kafin charity ta yi musu abin da suke son ci kada yunwa ta illata su.
Idonsa ya yi ja tamkar ya taya su kukan.
Bilki ta sandare tana kallonsu gabad'aya ma ta rasa me zata ce.
Ya danna k'ira shashin ma'aikatan. Charity din ce ta dauka. Cikin harshen turanci ya ce "Ta zo yanzun nan".
Mintina uku ta iso ta gurfana gabansa. Ya ce "Me zaku ci?"
Hafcy ta ce "Fried yam da onion soup ma is ok. Tunda yunwa muke ji. Aysha da ƙyar ta ce "Ki yi mana dambun kuskus da zamu ci anjima".
Ta amsa a ladabce ta mik'e. Abincin da bai ci ba kenan don yana kusa da su har aka kawo musu farar doya soyayya da miyar albasa.
Daidai lokacin kuma an fara k'iran sallar isha.
Amal da Noor suna ta kallonsu tare da Farha. Bilki ta yi sukuri tana kallon uba da ya'yansa yana ta yi musu sannun jiran da suka yi don ga ni yake yi yunwa ta ci ta cinye su.
Bilkisu junior kam ta ci abinda da Bilkin ta girka babu musu ko inkari ita bata da matsala kawai yayyen nata ne suke tursasata akan ta bijirewa Bilki.
*Pay1k via* 2384876855
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*
08032773332
*Don smaun cikkaken labarin a telegram*
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: [Sep 17, 2025 at 11:27]
49
Bayan sun idar da salla sundawo Aysha ta ce "Dady na san kana son