zuciyarki kamun kazar kuku idonki ya rufe, sannan da yawa mata ai ba kwa son mai mata! Da kin amince da kin gane ba abin da zai hana ni sonki, Idan an kere ki da wasu abubuwan ai ke kuma kina da k'uruciya, kinsan alfarmar k'uruciya kuwa?"
Ya girgiza kai tabbacin al'amarin babba ne.
A ranta kuma ta gasgata shi don itama ta ga tasirin kuruciyar yadda Sahal ya dinga rawar jiki akan Hawwah. Sai dai shi Yaya Asad ya yiwa matarsa adalci tunda mutuwa ce ta rabasu duk yadda ake ganin Sahal da kad'an ya girmeta to tazararta da Sahal tafi tazarar Asad da Rukayya don kuwa shekara d'aya tak ya bata shiyasa Abida take ce mata Anty Gyatum.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Da wayo da hila da gwada soyayya mai zama a zuciya sai da suka yi kwanakin sati. Ko maganar su tafi ma bata yi. Sai dai Akai akai ta kan ce Farha na can na kukan nemana.
A duk sadda ta fadi hakan kuma baya tankawa, asalima sauya fuska yake yi. Idan su Amrah sun k'irata a waya yana karba su gaisa ya yi ta yi musu tambayoyi akan karatunsu da kuma menene matsalarsu. Amma maganar Farha baya um bare um um. Jiya ma da Alti ta k'ira ta had'a su da ta ce a bawa Dady bai amsa ba, ya ce dai yana gaishe ta.
Har zuciyar Bilki bata kawo komai ba.
Ranar da zasu koma Abuja daidai da satinsu guda. Ya kalle ta ya ce "yanzu sarauniyar shaiba duk yadda kika dinga makale mini ba zai saka mu wuce gidanmu kaitsaye ba, duk kirkin da na yi miki, kalli fa yadda kika zama tamkar yanzu za ki haihu? Kawai mu wuce gidanmu washegari sai muje mu gaida su Baba mu ce musu mun shirya!
Ta girgiza kai ta ce "Daga rakiya sai na ce musu na koma gidana alhalin na ce musu na gaji ba zan koma ba, gaskiyar magana kunya ma zan ji, kawai ka bari sai na haihu din".
Ya jijjiga kai yana gasgata bata da wayo. Ban da rashin wayo akwai kunyar da ta wuce ta koma musu gidan bayan ta biyo shi ta yi sati guda tare da shi, sannan ta koma da sunan cigaba da zama a gabansu. Amma bari ya zuba ido ya ga yadda zata kwashe tsakaninta da Baban nata da ya zuba mata ido take yin yadda ta ga dama, kafin ta dawo ya mata hukuncin da zata dinga sanin me zata dinga furtawa a gabansa.
Ya rausayar da kai ya ce "Shikenan Maigado amma kada ki dinga kashe wayarki, sannan duk ranar da zaki je awo zan zo da kaina na kai ki, idan an kammala sai mu je mu na gaisa da unborn, tunda kin nesanta ni da jinsa duk sadda na so".
Ta sinne kai tana murmushin kunya da jin dad'i.
K'arfe goma na safe suka dira a airport din Nmadi Azikiwe da yake birinin tarayya. Motocin y'ansanda sun kai shida da suke takewa tsaleliyar motar da suke ciki baya. Shadaya daidai a kofar gidansu ta yi musu. Har cikin gate din motar da suke ciki aka shigar dasu, yayin da motocin yan rakiya ya ce su tsaya a wajen. Daga bakin falon ya ce "Ki gaishe su da kyau. Sai dare ko gobe zan zo na gaishe su, offiice zan wuce ana jirana da gaggawa". Ya mik'a mata jakar kayanta. Ta karba a sanyaye don so take ya rakata cikin, saboda tana sauka daga motar ta ji kuma wani abu mai kama da kunya na bibiyarta. Daga tafiyar yini ko kwana d'aya ne ta kwashe kwanaki bakwai?
"Dankari".
Ta furta a bayyane.
*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*
*07036662633*
*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*
*Surayya Dee*[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:10]
Kuka ya k'wace mata don bayan kunyar da ta yi mata dabaibayi kalaman Baban sun yi mata tsauri matuƙa da gaske , haka nan idon da su momi suka zuba musu ya sake muzanta ta ainun.
Baban kuwa bai kula da kukanta ba don sosai ya ji haushin sakarcinta ya kuma lura idan ba tausayinta ya cire a ransa ba to ba zai ga yadda yake so akan aurenta ba, tunda har Asad ya gwada masa irin wannan rashin kunyar cikin dabara, to nan gaba ba abin da ba zai yi ba, na nuna iyaka.
Da b'acin rai ainun ya ce "Ashe sadda kika zo nan kika ce mini na zubawa Abida ido ban mayar da ita d'akin mijinta ba rashin kunya kika yi mini, ba wai fad'a mini damuwarku kika yi a matsayina na ubanku ba!
Yana rufe baki ta bude baki ta rushe da kuka sosai don gabad'aya bak'in cikin Asad da kunyar duniya ne suka rufar mata.
Baba ya yi waiwaiye bai ga wani abu da zai dauka marar illa da zai makata ba.
Don haka ya zakudo ya dawo bakin kujerar sosai ya saka dukkan hannuwansa biyun ya rik'o dukkan kunnuwanta ya murd'e da k'arfi tar da fad'in "Rufe mini wannan ja'irin bakin na ki, dukanki na yi ko me?"
Ta sassauta kukan ya ce "Borin kunya kike yi tunda kika yarda kika bi miji hotel akan idona, amma kika k'i binsa gidansa. Yanzu kenan duk sadda yake da bukatarki zai zo ya dauke ki, idan ya gama sai ya dawo mini da ke tunda haka kika zabar mana ni da ke ko?"
Tashin hankali ya sanya jikinta b'ari ga kunnuwanta na hannunsa , kamar zai cire mata su, azaba ta sanya kukan ya tsaya cak, illa zufa da take yanko mata. Tunda take a duniya bata taɓa tozarta irin yau ba.
Bai saki kunnen nata ba ya ce "Ba za ki zauna mini a gida ba, yanzun nan ki k'ira babban ja'irin ya dauke ki, don na tabbatar bai yi nisa ba, ba wani office da zai je.
Sannan bana son na kuma ganin k'afarki a gidan nan har sai na bukaci ganinki da kaina. Idan kin so ki ce na yi son kai. Idan kin so ki zauna lafiya da mijinki da iyalinsa, idan kin so kuma ki gudun, ki je, ki yi zaman kanki tunda na fuskanaci taketakenki na raini a kaina. Zan zuba miki ido irin yadda nake zubawa duk wacce na bawa umarni ta kafe akan ni zan bi ra'ayinta saboda tana ganin ta yi ilimi mai zurfi".
Nan da nan Abida ta muzanta tare da shiga wani irin tashin hankali farat d'aya. Don kuwa lah shakka wannan karatun nata ne.
*Contact me*
08032773332
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*
*Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*.
Cikin kuka na sosai Bilki ta ce "Dan Allah Baba ka yi hakuri".
Murya ba amo ya ce " Zan huce da ke ne idan na ga mijinki gurfane a gabana yana yi mini godiyar ba shi aurenki da muka yi. Zan huce da ke idan kin kwantar da hankalinki tare da bada gudunmawar daidaituwar zumuntarmu. Kina tunanin idan su Ansari suka ji kina jele tsakanin gidanki da nawa gidan da sunan bacin rai zasu sassauto gabad'aya ne su sake mayar da ni ubansu?"
Cikin kuka ta ce "Baba kai ubanmu ne babu abin da zai sauya hakan ".
Ya ce "Kayya Maigado ke din dai da kuma Saddiqa haka ma Ansari yakan gaishe ni idan ya bushi iska amma Sulaiman Hamida Abida Anisa da Ansari kullum da bak'incikinsu nake kwana nake tashi. Indai na mutu a yanzu tabbas suna da alhakin mutuwata, ki yi a hankali kada ki shiga sahunsu a idona da zuciyata".
Hawaye ya dinga tsere a fuskarsa a sanyaye ya saki kunnawanta ya koma cikin kujerar sosai ya jingina.
Jikin kowa ya mutu ba abin da ake ji sai gunshekin kukan Maigado da na Abida.
Abida a ran take jin zahirin wanda Baba yake so duk cikinsu daga su har su Sulaiman gabad'aya Bilki ce. Ita ya tsaya mata kada aurenta ya taɓarbare, yayin da ita ya barta ta yi yanda take so, da komai ya k'wace mata kuma ya koma tsakaninsa da ita ido ne, komai ta ce zata yi to kawai yake cewa, haka momi wannan zurun da suke yi mata tare da bata cikakken dama da y'ancin ta zaɓarwa kanta yadda zata yi da rayuwarta ke saka ta kuka kullu yaumin, tunda ta yi gardamar ba zata zauna da Sulaiman ba, aka kyaleta har yau babu wani da Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:14]
ya taba yi mata batunsa ko nuna tausayawa ga HALIN YAU din da take ciki. Yaya Asad ne kawai shima sai da ya fara zawarcin Bilki yana son ta shawo masa kanta, ya sanya yi mata alak'awarin za'a fara binciken inda yake, ga shi har matarsa zata haihu bata ji komai game da batun ba.
Ita kam tana ganin tasku da ainihin kuttun namiji. Kuka ta yi shi irin wanda bata taɓa zaton wata mace ta yi irinsa ba. Ba abin da ta nema ta rasa, amma bata samun walwalar iyayenta irin na da duk da basu taba ce mata komai ba. Amma yanzu ta fahimci tana cikin garari tunda duk yadda take a wajen Baba ya saka ta cikin wadanda suke tayar masa da hankali, suke k'ulla masa bak'in ciki. Don haka zata fara neman Sulaiman duk inda yake a duniya, idan ta gan shi kuwa sai ta shekara bata zo gidan ba sai dai waya, ko zai dinga dukanta kullum kuwa, zata yi hak'uri ta zauna a d'akinta duk runtsi. Har sai BABA ya je nemanta da kansa in sha Allah Baba ba zai mutu da bakin cikinta ba.
Tsawon lokaci suna kuka ba wanda ya ce musu kanzil. Bilki na ayyana wannan rayuwa da wahalar gaske take. Babu wani cikakken jin dad'i. Gabad'aya k'alubalen da yake cikin rayuwar yafi jin dad'insa yawa. Ba macen da zata ganta ta zaci tana da matsala a gidan aurenta.
Ga tsalelen gida, ga tsaleliyar mota, ga ingarman miji mai rike da madafan iko, ga lafiya Allah ya bata ga kuma satisfaction, ga niimar haihuwa. Amma kuma sai aka jingina mata k'alubalen fuskantar kiyayyar y'ay'an mijin da ubansu yake tsananin sonsu.
A da ta d'auka idan ta rabu da Sahal ta samu wanda zata dinga samun satisfaction to duk wata matsalar da zata zo ba zata d'auke ta a a matsayin damuwa ba.
Ashe ba hakan ba ne, mutum na girma matsalolinsa na sake bunkasa, matsalar y'ay'an mijin da babu uwarsu babbar jarabawace da ba mai gane girmanta sai wadanda suke cikin matsalar, gara yaran masu uwa, idan har sunada tarbiya Kuma suna mutunta uwarsu AI dole su mutuntunta Matar ubansu, Idan kuwa basu da tarbiya basa mutuntata uwarsu ai shafawa Kanka ruwa zaka yi ka Koma gefe ka yi kallon yadda sakayyar rayuwa zata hau kan kowa. Da ace Rukayya na da rai suke mata irin haka, to da ita kuma a kanta zata rama iyashegensu tunda itace abokiyar burminta, idan y'an arziki ne sai su kiyaye ta. Amma yanzu ba yadda zata yi sai fatan Allah ya kawo musu miji su je suma su fara fuskantar yadda rayuwar take, tunda haka rayuwar take kowa hak'uri yake yi da yadda k'addara ta zaba masa. Allah dai yasa mu wanye lafiya kawai.
Cikin muryar umarni ya ce "Ki tashi ki koma d'akinki, Alti na gidan Faruku sai jibi zata dawo matarsa ce ta je biki shine ta je ta taya yar aikinta kula da yara.
Jibin ko gata direba zai kawo ta tare da d'iyarki".
Ta kasa tashi tsabar kunya da nauyin da jikinta ya yi mata na tausayin Baba. Gabad'aya k'arfin hali yake gwadawa akan su Yaya Hamida da suka share shi.
Cikin kuka ta ce "Dan Allah Baba Yaya Faruku ya raka ni".
Murya babu amo ya ce "Ba zai raka ki ba, shi ja'irin mijin naki ya zo ya dauke ki, ko ki shiga ki dauko mukullin motarki ki tafi ai kinsan hanya".
Sai lokacin Momi ta ce "Alhaji da dai ka yi hak'uri ya kaita din, ba zata iya tuki cikin nutsuwa ba, kuma ta inda aka hau, ai ta nan ake sauka. Shi ya kawo ta ranar da ta yi yajin, yanzu don ya mayar da ita ai babu komai, daure dai Alhaji kada ta tafi ita kad'ai."
Baban ya ce "Yadda ta fito haka zata koma, ina ce a gabanmu ta wuce ta bi miji uwa duniya, don zata koma gidansa ita kad'ai sai ya zama abin jin nauyi? Kin san Allah Asad na k'ofar gida yana jiranmu ni da ita. Ai wannan abin da ya yi sakone mai harshen damo ya yi mini, kin ga ai ya fahimtar da ni da yaren da na ji shi har cikin k'wanyata.
Momi ta kasa magana don gabad'aya kunya Baba yake bata a gabansu. Yayin da shi kuma ko a jikinsa yake ta nanata rashin kunyar Bilki da rashin mutuncin Asad.
..
Sai lokacin Yaya Faruku ya bude baki ya ce "Baba da ka yi hak'uri dai na rakata, Allah bar shi idan na gan shi a wajen ko a hanya sai na ba shi ita su tafi". Save Restricted Contents Bot, [Sep 25, 2025 at 20:17]
Baba ya jijjiga kai tare da fad'in "Oh oh ikon Allah sai mutuwa ta d'auke Babanku ni kuma aka bar ni ina ganin waki'a iri iri Faruku!
Cikin tausayawa Yaya Faruku ya ce "Allah ya jiƙansa, kai kuma Allah ya baka ladan hak'uri Baba ".
Murya babu amo ya ce Ameen Faruku! Allah ya yi maka albarka, ya yiwa dukiyarka da zuri'arka albarka, kai kadai gayya ne Faruku.
Abida da Bilki suka yi tsuru tsuru don kuwa gabad'aya jikinsu ya sake yin sanyi tare da sha'awar ina ma sune Yaya Faruk. Kafatalin gidansu Yaya Faruku abokin kowa ne maza da mata kuwa. Duk wanda yake son yi shawara ta sirri to ya tuntubi Yaya Faruk. Har yanzu da shekaru suka rufar masa shiga cikinsu yake yi ana hira ana tafawa. Idan kuwa aka ha fishinsa to lah shakka ba k'aramin al'amari bane kai da wuya ma. Duk yadda rikicin Ladi farms ya yamutsa hazo wani mahaluki bai ji tarinsa akan batun ba. Shi dai kula da lafiyar baba ya mayar da hankalinsa tare da da kwantar masa da hankali akan ya yi hak'uri kowanne d'anadam akwai inda Allah yake jarabtarsa don gwada k'arfin imaninsa, haka nan shi kad'ai ne bai nunawa su Sulaiman b'acin rai ba ko da kuwa a fuskarsa, don ko Munira da take da kusan irin halayyarsa an fahimci fishinta a wanccan lokacin.
Da muryar kuka Bilki ta ce "Dan Allah Baba ka ja masa kunne akan zubawa yara ido suna cin mutuncina amma baya iya tsawatar musu da sunan tausayinsu."
Baba ya tausasa harshe ya ce "Na yi masa, zan kuma sake yi masa, kuma idan har kika koma ba ki ga canji akan mu'amalarsu da ke ba, kaitsaye ki faɗawa Faruk zai kawo ni har gidan. Ko ki k'ira ni kaitsaye ki fad'a mini ko ki faɗawa mominku."
Ya kalli momi ya ce "Dauko mata zamzam din nan na d'akina".
Momi ta tashi da sauri ta nufi d'akinsa.
Ya ce "Kina tashi a barci ki fara shansa, idan za!ki kwanata ma ki sha, In sha Allah za ki haihu lafiya kuma abin da za'a haifa zai zama mai fikira.
Momi ta fito d'auke da babbar robar 5litr cike da zamzam ta bata.
Faruku ya mike ya ce "Kawo na dauka ai zata yi miki nauyi".
Ba musu ta bashi.
Ko sallama bata yi ba ta juya ta tafi Momi ta bude murya ta ce "Ki k'ara hak'uri kin ji".
Yayin da Baba ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa.
A fili kuma ya furta "Allah ya daidaita al'amarin da kansa, Yara na neman fasa mini kai da zuciya."
Murya babu amo Abida ta ce "Dan Allah Baba ka yi mini nasiha mana".
Ya nisa ya ce "Abida ai na yi miki a farko kika tankwabar da ita da sunan an taɓa ni, wanene Ni da ba za'a taba ni ba? Kinsan me yasa aka jarrabe ki akan Sulaiman da ɗansa?"
Ta girgiza kai tana rushewa da kuka na gaske.
Tausayinta ya tsirga masa, don kuwa ya shaida Abida ta gama yin tub'us, tun tana boyewa har abin yafi k'arfinta. Ya ce "Alfarmar aure kika keta, ba abin da Allah yake saurin yin hisabi akansa irin cin dukiyar maraya da keta alfarmar aure. Auren nan fa da kike ga ni Ubangiji ne da kansa ya kewaye shi da dokoki iri iri bai barmu da ra'ayin kanmu ba! Ko da na haife ki, ai mijinki yafi ni iko da ke, kin yi fishi saboda sun yi k'arata. Sai kika kasa gane uwarsu ce ta yi k'arata ba su ba. Su kuwa tunda ta haife su babu yadda zasu yi da ita, da kin yi hak'uri Abida Sulaiman sai ya zo gabana ya bavni hak'uri. Wallahi saboda Aurenki ya tsira na kafa muku sharadi ke da Usman duk wanda ya yi inkari akan hukuncin Munira ban yafe masa ba a cikinku, baki yi magana ba tabbas amma kin yanke alaka da Sulaiman a lokacin ba ni da lafiya. Bana sanin me yake faruwa, ban san kina tare da mu a Abuja ba, sai da kika yi wata guda.
Lokacin da uwarsa ta rasu anan na ce miki ki yi hak'uri idan munje ki zauna a d'akin mijinki, ki koma gabad'aya ki zauna tunda ba sakinki ya yi ba, sanadin hakan sai a samu daidaito, zai zo har nan tare da y'anuwansa su ba ni hak'uri, na tabbatar Sulaiman zai yi haka. Amma kika dinga rusa ihun ke zuwan ma ba zaki yi ba. Dole nine