gwamnatin tarayya ta tura sojojin sama don koyon dabarun tsare sararin samaniyar k'asarmu.
Ya numfasa ya ce "To magana ta wuce amma lallai ki shiga cikin hankalinki, Maigado ai kanwarmu ce idan kuka ci mutuncinta kun ci namu, aurenta da Babanku ya yi kuma ya sake k'ara mata daraja a wajenku, amma shine kika made k'afar wandon cin mutuncinta, kin manta Idan kika taba ta daidai yake da kin tabamu gabadaya tunda ba ita ya kawo Kanta ba, aure ne ya kawo ta gidanku, bayan an shawo kanta da ƙyar. Aure ya zama tilas ya yi shi, sannan zai auri wacce yake so ne, ba wai wacce ake so ya aura ba. Ki faɗawa mai zuwa wajen na ki ya turo da magabatansa, Khadijah kam tunda a can mai son nata yake aurensu za'a daura musu su tare kawai. Wallahi kada na sake na ji ko da kallon banza kin yi sake yiwa Maigado bare kuma a kai ga jallin kina jagorantar kannenki kina kitsa musu shegantaka. Ya ya ina yabon hankalinki da illiminki sai kuma ki bamu kunya? Kullum da ke nake bugawa kaninki Ammar misali ashe kin sauya halayyar k'warai kin aro ta marasa da'a masu yin fito na fito da kwanciyar hankalin iyayensu? Ki yi maza ki gyara tun ba ki fara girban shukan da kike yi ba." Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:48]
Da kuka sosai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba".
"Yauwa Aysha Allah ya yi miki albarka, Allah ya jiqan mahaifiyarku, daina kuka kin ji, ya huce komai ya wuce."
Ta yi masa godiya ta tashi ta koma d'akinta.Tana jin nutsuwar zuciya, tana da tabbacin tunda ABBA ya ce Dady ya huce to babu haufin ya huce din.
Faruku ya mike yana fad'in"Bari na wuce "Allah yasa ba zan sake zuwa gidan nan da sunan bacin rai ba Oga Asad".
Murmushi Asad din ya yi tare da ce wa "Idan ta ji faɗanku ta kwantar da hankalinta ta ajiye tsiyatakun da ta aro ba zaka sake zuwa ba mana Baba Faruku".
Suka fita waje tare. Har jikin motarsa ya raka shi suka yi musabaha.
Yana tsaye yana jallon Faruku har ya fita daga gate din aka rufe sannan ya yi ciki. A ransa yana ayyana Duk cikin family lmsu ba wanda ya more irin Faruk.
Shine bai taba aikin gwamnati ba a rayuwarsa, amma kuma attajirine na sosai.
Sannan yafi kowa yiwa iyayensu hidima da jikinsa don shine yake da lokacin kansa, kullum yana tare da Baba yana yi masa hidima. Haka duk jinyar da zai yi Faruku na gefensa yana kula da shi. Shi kad'ai ne ya yi wannan sa'ar, su kam sai dai su yi da aljihunsu.
Hak'uri da sadaukarwarsa ya sanya hatta Momi da Baba kunyarsa suke ji bare kuma su. Yadda suke yi masa kacakaca ko su share shi basa taba yiwa Faruku haka.
Ya nisa ya ce "Allah ka sake son Faruku."
Ya shiga cikin gidan har ya zauna a falon sai ya tuna ya tashi da hanzari zuwa saman.
A d'akinta ya tarar da ita tana zaune a k'asan kafet ta mikar da ƙafafuwanta da suke a kumbure.
Murya ba amo ta amsa sallamarsa.
Ya zauna a k'asan yana fuskantar ta.
"Maigado ya aka yi kuma kika dawo alhalin kin ce Sai kin haihu, Babanki ma ya jaddada mini hakan?"
Takaici ya shak'e ta. Ta yi masa shiru amma idanuwanta sun cika da k'wallar takaicinsa.
Ya yi murmushi kad'an ya ce "To ya aka yi ne? Fasawa kuka yi ne ko ya ya ne?"
Murya na rawa ta ce "Na gode da muzancin da ka janyo mini Baban Bilkisu ".
Ya cije ya ce "Wacce magana kike yi ne haka. Me na yi miki?"
Hawaye ya k'wace ta ce "Akan me zaka ce mini yini kawai za'a yi ko kwana d'aya alhalin ba hakan bane a ranka."
Ya tattaro dukkan alhini ya yaba a fuskarsa tare da ce wa "Hakan ne a raina mana. To yadda kika dinga mak'ale mini ne ya sanya na fahimci kina buk'atar mu k'ara kwanakin, da na ce zamu k'ara kuma ba ki yi inkari akan haka ba. To menene laifina dan Allah, dole na yi mike ko kuwa kin tayar mini da hankali akan sai mun dawo?"
Ta kasa ce masa uffan tunda bata da bakin magana.
Ta girgiza kai ta ce ka koya mini darasi zan kiyaye a gaba".
Ya dauke kai ya ce " Allah ya nuna mana gaban lafiya."
Ya gyara zama ya ce "Ki saurare ni da kyau ki fahimci jawabin da zan yi miki da kunnen basira."
Ta goge fuskarta da tissue sannan ta nutsu sosia alamun shi take saurare.
Ya ce "Na mayar da Laura gida kamar yadda kike so, na sallami Jummai haka Charity goba zata koma inda na samar mata wani aikin, abin da yasa ma bata tafi ba kenan tuntuni, ba zai yiwu na rabata da wajen aikinta na farko ba, sannan yanzu na sallame ta ba tare da na samo mata wani aikin ba."
Bilki dai ido ta cigaba da zuba masa.
Ya zarce da fad'in "Yanzu za'a samo sabbin masu aiki, kin ga wanda za suzo basu saba da yara ba, bare su dinga girmama umarninsu sama da na ki."
Ta dan ji dis amma ta maze ta ce "Tom amma da ba'a kawo wasun ba, tunda dai akwai ma'aikata da yawa. Ga masu shara da wankewanke da goge goge, ina ganin hidimar girki a bar mini tare da taimakon Alti zamu yi komai" .
Ya ce "Kina iya shiga kicin duk sadda kike so, amma gaskiya ina son na ga ina da chef a gidana."
Zuciyarta d'aya ta ce "Ka manta nima girke girken na karanta? Sannan Alti ta iya girke-girke kala kala na ban mamaki".
Ya daure fuska ya ce "Alti ai ba zata dawo mini ba, tunda ta biki kuka tafi bata hana ki yi mini yaji ba, to na dakatar da ita. Wani irin al'amari ya daki zuciyarta. Nan da nan idonta ya ciko da hawaye ta ce "Baban Bilkisu ya haka kuma? Alti fa bata da kowa a duniyar nan sai ni, tun haihuwar Faruku muke tare da ita, yanzu idan an sallame ta ina zata je dan Allah?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 26, 2025 at 11:51]
Ta je koma ina ne".
Ya fad'a a dake.
Bilki ta zuba masa ido tana ayyana abubuwa masu yawa, ba k'aramin artabu zata sha da wannan mutumin ba lallai.
Ta tausasa harshe ta ce "Amma tun kafin mu yi aure sai da na ce Baba ya fad'a maka da ita zam zo gudun irin haka fa".
Kaitsaye ya ce "Na amince a farko ne ba tare da na yi tunanin komai a kanki ba. A yanzu da na gane inda kika dosa a kaina ba zai yiwu kuma na bi yadda kike so ba. Wallahi ba dan Baba ba, da kinsan kin zage ni a gabana. Amma tunda dole wani ya ci albarkacin wani na hak'ura na k'yale ki, amma Alti da Farha su zauna a gidan Baba wajen Momi."
Wannan karon bayan bugawa zuciya har y'ay'an cikinta sai da suka motsa da k'arfin gaske. Ta fashe da kuka mai tsananin gaske.
Takaici har makoshi. Cikin fitar hayyaci ta ce "Na rantse da Allah ba zan yarda ba, kawai ka sallame ni, dama ba sona kake yi ba tun filazal, ka samu abin da kake so shiyasa kake fito mini da halayya iri iri. Ko tafiyar nan da ka yaudare ni muka dade da kana sona ai ba zaka mini sanadin da zan muzanta irin haka ba, ka cigaba da cin zalina yadda ka saba tuntuni ".
Ya yi murmushin da babu nishadi ya ce "Ai da muka je din ba dole na yi miki ba, yanzu ma kuma ai ban daure ki ba, sai dai ki sani idan kika yi kuskuren sake saka k'afarki kika bar gidan nan, sai kin yi kuka na gaskiya don kuwa za ki dawo ne ki tarar da wata a cikinsa".
Kuka ya tsaya mata cak, ta zuba masa ido a maimakon ta ji tsanarsa yadda take ji a da, sai bata ji ba, ta kasa gane me take ji a ranta game da shi tunda babu so, kuna babu kiyayyar.
Ta tuna yadda suka rabu da Baba Babba da yadda ya tabbatar mata tashin hankalinsa ace bata zaune lafiya da mijinta, farincikinsa da burinsa bai wuce ace ta bada gudunmawar da zai daidaita zumuntarsu ba, bugu da ƙari Baba ya ce" Ba zai huce da ita ba sai ya ga Asad tsugunne a gabansa yana yi masa godiyar auren Bilkisu da aka ba shi. Wanne irin nauyi Baba ya dora mata, wacce irin biyyaya yake son ta yi, wanne irin dabaibayi Baba ya yi mata?
Zata yi komai, zata jure komai amma ban da rabata da Farha. Haka nan ba zata rabu da Alti ba har sai Faruku ya girma ta damka masa amanarta, shi take rikewa ita, yadda ta ci wahalarsa da rainonsa da ikon Ubangiji zai rik'e ta akan tsufanta a lokcin da zata fi koka rashin y'aya' da dangi.
Hawaye face face a idonta ta ce "Ayyah Baban Bilkisu amma alk'awari bai ce hakan ba. Magana biyu ba taka ba ce. Ni fa zan iya rabuwa da komai da kowa amma rabuwa da Farha mutuwa ce kad'ai zata gitta a tsakaninmu".
Ya sake harzuk'a ya ce "Asad ya rabaku alhalin ba mutuwa kika yi ba. Ai tunda kika gwada mini wulakanci kala kala akanta to ba zan zauna da ita ba. D'iyar Sulaiman ta fi ta kowa saboda rashin kara da wulakancinki ya kai k'urewa."
Ta yi sakare tana jin wani irin abu na mamayarta ashe shi a haka ya fassarata?
Murya ba amo ta ce "A haka ka dauka kenan? Ni fa Wallahi mantawa nake yi ba ni na haife ta ba. Gaskiya ni ba haka a raina, ban yi zaton zaka mini irin wannan fassarar ba, haka zalika ba zan iya rayuwa babu ita ba, na tsallake na bar y'anuwanta a Katsina amma ita kam tabbas ba zan iya ba. "
Ya sake girgiza kai ya ce "To zan ga yadda za'a yi na zauna da waɗanda bana son zama da su a gidana kuwa".
*Na gode sosia da soyayyarku ga rubutuna*.
*Na gode da uzzirinku*
*Surayya Gwaram*
✍️