DIJAMAH 'YAR FULANI Ranar da Komai Ya Sauya by maman teddy

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   9 / 13

24K to 27K   out of 36.2K words

takasa maimatawa saboda kunyar sa da takeji.
Maganar da ta sauka akan kunnen sune ta sasu dakatawa daga maganan,wanda cikin daure fuska yake bin Basmah da kallo...
Cike da takun isah ha'di da ta'6a baki ta nufo su,inda nan ta hau nuna su da yatsa tana mai cewa" hmmmm matan Aliyu Haydar ko....hmmm Aliyu manyan angwaye,ashe wannan kwailan ce amaryan taka,itace er Tarbiyan er mutunci ko...yayi kyau ngd da yaudara ta da kayi,amma kasani wlh Allah baxan rabu da kai ba,sai na rama abun da kayimun...
Kallon ta baiyi ba,har ta juyaga deejamah, wanda tasaki baki tana mai Kallon basma,inda a zuciyan ta take tunanin waye wannan....
Heeehhhhh stupid get out from here....wai ke wace kalan karya ne Basma... Itadin da kk gani tafimun ke,tunda na aureta ban aureki ba.inbanda rashin xuciya mai ya kawoki ne mah...
Cike da mamakin magan ganun sa tafara dariya n najin haushi,inda nan take tafara fadin maganganun banxa game da Aliyou Hydar dan har yanda suke sex sai da tafa'da... Wani wawan mari yayi mata,Don dama Aliyu badai zuciya ba...sai da yy mata mari sau biyu,sannan yakira securities ha,di da cewa su fitar masa da Basma daga gida...
Itako deejamah tuni ta shige cikin falon ta,wanda da shiganta ta nufi bedroom din dakin ta....kasa dawo wa Aliyun yy,don bai taba jin kunyar deeja kaman na yau ba...
Deeja kuwa tayi kuka har tagaji,don sam batasan Aliyu Haydar da wannan dabi'ar ba sai a yau...
Wanda koda Aliyu yadawo da kyar yasamu ya shawo kanta ta hakura inda tabar mawa cikin ta...
______tafiya suke inda Aliyu ke sanye cikin shigarsa ta manyan kaya...wayo wata dakakkiyar shadda mai ruwan sky blue..inda deejamah ke sanye cikin wata less mai launin dark blue...sunyi matukar kyau don bakaramun da cewa da juna sukayi ba...
Parking Aliyu yy cikin sauri,wanda deejamah tace" hamma Hydar ya katsa anan,har mun xo shopping mall 'din ne...?
Kallon ta yy ha'di da kashe mata ido, sannan yace" my queen kinyi kyau..kinfi kowani rana kyau...
Kallon sa tayi hadi da cewa" kai wannan magana haka tun da muka fito kakace mun haka,koda yau xamu ha'du da Alkhairy ne...
Dariya hadi da shafa sajen sa, sannan cikkin dan sauri yace" amm bari naje na gayda aminin dad...kallon sa tayi ha'di da cewa" okay amma kayi sauri....
Murmushi yayi mata,wanda kafin yafice sai da yakama hannun ta ya manna mata kiss,sannan ya fice daga motan...hadi da nufahn inda yaga Alh.muhammad maccido....
Cike da girmamawa ya fara gishe da Alh. Maccido, wanda cike da farin cikin ganin dan nasa yake tambayansa ya iyalinsa,don yaji labrin auren nashi,sosai yy masa fada akan kulawa da hakkin mata akan miji, da hakkin miji akan mata...haka ya dinyi masa nasiha sosai akan ya kula da matansa sosai,sannan sukayi sallama...

Bayan ya shiga motan ne deejamah ke tambayan shi,wai hammm yaushe xamuje naga momy ne,kullum sai kayita mun magan ta,amma ban ta'6a ganin ta ba...
Shiru yy na en sakonni sannan yace" ki nason ganin momyn kenan... Tohhh ki shirya a satin nan xan kai wajen momy ki ganta..
Cike da murna tace" tohhh allah ya kaimu...
Wani dan kararen shopping mall suka tsaya inda Aliyu Haydar yy parking... Cikin takun sa na isa ya fito wanda daka ganshi kaga tsayayyan namji,wanda ya amsa sunan sa namji...bude mata side din ta yy inda cike da nastuwa tasako kafan ta,wanda da kagani xakasan da hutu da kwanciyar hankali a wajennn....
Jakarta ya kar'6a wanda a hankali ya riko mata hannun sa daya kuma yana sakale da nata...
Da shigansu wannan wurin kowa da kallon sha'awa yake binsu,don daka gansu basai anfada maba,zaka fahimci masoya ne na usullll....🤣🤣🤣
Haka sukayo siyyayr su sannan suka fito daga shopping mall din...
Fitowansu kenan dai² sobreen xata wuce ta gaban wurin,wanda sanye take cikin wani irin xin bulen hijaab...wanda gaba daya ta chanja,da ka ganta kasan tana cikin wahalar rayuwa...
Kallon² suka hauyi mawa juna...inda Aliyu Haydar yake tunanin an yahhh wannan sobreen ne kuwa,anya itace wanda yasani kuwa kodai wata ce ba ita ba...?
Kallon sa sobreen tayi ha'di da "dan yin murmushi, inda ta juya ha'di da kallon deejamah.
Wanda ita kanta deejamah kallon sobreen 'din take,tana mawa zuciyan ta tambayan wacece itah wannnan kuma...?
" cike da manaki da ta'ajibi Aliyu yace" sobreen kece,mai yasame ki? Hauka ne dake...?
Wani murmushi sobreen tayi wanda hausawa ke ce tafi kuka ciwo,sannan cike da 'dacin maganganun sa tafara cewa" yohhhh idan hauka ma ne dani ae bb abun da ya shafeka,tun da banxo niman magani wajenka ba,don haka koma me yasame ni naga bai shafeka,tun da inah da Allah, shi ne ya hallince ni,kuma shine mai jinkaina a kowani hali nake ciki,kuma kullum shi yake bani ba tare da ya gaxa ba...don haka ina da Allah to bb ruwanka dani,kok a wani hali ka gannni..
Ya mutsa fuska yy cike da wulakanci don ko a gyefen kwalar rigar sa bai damu da ganin sobreen din a haka ba...
Waigawa sobreen tayi xuwa wajen da taga deejamah, cike da 'dan murmushi tace" kece matan Aliyu ko...! Hmmm ya sunan ki...
Cikin sanyin murya dijamah tace" khadeeja.
Wow suna mai da'di,tohhh nikuma sunana sobreen, ni tsohuwar budurwan sa ce,ina maki fatan Alkhairy... Sannan don Allah ina jawo hankalin ki akan hakuri, don in kayi shi xaki ci ribar rayuwan ki,kuma duk rintsi duk wuya kar ki sake kirabu da Aliyu, domun shigowa rayuwan shi da kkyi haskene,kin gyara masa tsarin rayuwa, don haka abu daya ne xaki 'dauka da shi,shine ha'kuri...
Murmushi deejamah tayi ha'di da cewa" in Allah ya yarda...
Nan sobreen tayi murmushi ha'di da shafa fuskan dijamah, sannan ta juya ga Aliyu Haydar tace" Aliyu matar naka kuma kyakykyawa ina sonta,sai kuma tace Ina maku fatan Alkhairy, tana fa'din haka ta juya ha'di da cigaba da tafiyan ta,bin ta kallo Aliyu yy wanda a ranshi yake tunanin mai yasamu sobreen ne,tabbas may be tana da cutar rashin hankali ne.
Haka ya share ma zuciyan shi tunanin wata sobreen,inda ya bude mawa deejamah mota ta shige,shima ya xagaya ya shige side din shi,ya tada motan.
Justice madina kuwa kullum gida babu xaman lafiya,don yanxu har meenash bata kallo,inda meenash sam bata damu da hakan ba,ganin abun da tau dauka baxai bille mata bane,yasata jan meenash a jiki,don tasan inda Aliyu Haydar yake da matar nasa...
Koda ta tambayi meenash nan meenash tace itah sam bata san inda ya Hydar yake da matar sa ba...jin maganan nata yasa momy fada ta dafa,inda take shiga ba nan take fita ba,nan takuma yi mata rantsuwa akan sai Aliyu ya rabu da wannan yarinyan, don Basma ka'dai ta shirya kar'6a a matsayin suruka.
Zaune Aliyu gaban momy wanda kafahn sa ke a tankwashe haka kansa a kasa.
Cike da issa masifah take masa magana,wanda duk akan xancen dijamah ne,wanda daga 'karshe take cewa" umarni ne wannan nake baka ba shawara ba,kaje yanxu kasaki wannan yarinyan, in bahaka ba toh daga yau karka kara kirana da sunan uwa gareka...
Jin maganan momy yasa cike da firgici ya 'dago kai ha'di da kallon ta na wannam lumsassun idon nasa,baki na rawa kuma cike da rudu yafara ceww" plz momy kiyi hakuri,wlh baxan iya rabuwa da deeja ba,Allah ne yasamun son ta,don haka momy don Allah kibarni nay....rufe mun baki,kaji dai mai nace maka,don haka bana bukatan wani dogon surutu tashi kafice mun daga 'daki....
Momy tace cike da masifah da bacin rai,da irin son datagani na deejamah a idon shi....
Cike da matsanan cin damuwa ya mike ha'di da fitowa daga 'dakin ta.wanda saboda tsaban tashin hankali har jiri yake gani,tayaya satin shi biyu da aure ana uku ace ya rabu da matar sa,gsky shi sam baxaya rabuda deejamah ba,don sonta a jinin sa yake...a haka ya nufi gidansa,wanda sam bai nuna mawa deejamah yana cikin wani hali ba,illah ma cigaba da kulawa da yake mata,ku ina xata yana manne da itah,don a yanxu har ma'aikatan gidan sun saba ganin hakan,don sunan masu girki na koya mata ne,amma tare suke koya,wanda su ma'aikatan kansu soyayyar tasu tana burgesu matuka...
Zaune take aka cinyarsa yana sama ta fruit salad din dake a gansu a baki,inda itakuma take lumshe ido don da'di,don tun randa ya ta'6a bata taci shikenan take kaunar abun....
Da gangar ya kai ruwan salad din bakin ta,sai ya shige da spoon din duka bakin ta,wanda yasa gaba daya ruwan ya '6ata mata baki...aeko nan ya hau yima dariya,'dan daure fuska tayi ha'di da tashi daga jikinshi ta 'ko',karin mikewa,wanda yy saurin jawota ha'di da mannata da jikinsa,inda yakai bakin shi kan nata yafara lashe inda ta'6ata da ruwan salad din,a haka ya gangaro har kan bakin ta yafara lashewa,wanda da yakai cikin bakin nan ya cafko halshen ta ha'di da tsotsan ta cike da gwanewa.....ita ko dayake batasan wannan halin mai tan nasa sai tafara tureshi tana mai kokarin kwace bakin...
Salatin da suka jiyo ne a bayansu yasa shi cikn wani irin yanayin mai cike da sha'awan ta ya saki bakin nata a hankali, yana mai kallon inda yajiyo salatin dakaman anyi mutuwa...
Karo fito da ido yy ganin justice madina tsaye tana cika tana ficci,inda cike da 'dan kunya ya dan sosa kyeya ha'di fa cewa" momy sannu da xuwa,ga wuri ki xauna...
Wani mugun kallo ata watsa masa,sannan cike da masifah tace ba zama na zoyi ba,kafini sanin abun da yakawoni,don haka maxa sallameta ta takama hanyar garin su........

Cike da matsanan cin tsoro da firgici yake kallon momy,wanda cikin da dakiya ya kalleta hadi da cewa" momy.............

Wayyo hannu na,waiyo ido na....na gaji,kusha karatu lafiya....
Ina jin da'din Comment dinku gareni Allah yabar kauna...lov u all🥰









Maman teddy...
[01/02 8:30 pm] Maman teddy🧸: *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*

*_Kungiya masu aiki da naxari da ilimi_*


*DIJAMAH 'YAR FULANI*

Written by...:
Aysha moh'd (Maman teddy...🧸)

*Sadaukarwa ga:*
Laila moh'd
Aseem moh'd
Hudair moh'd and...
Bilal moh'd nasaudakar da wannan pagen gareku 'yan uwa rabin jiki,allah yabar mun ku....laila na pray for miji nagari,allah yakawo mana musha....🤩🤩🤩💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Episode 3️⃣2️⃣➖3️⃣3️⃣



____________________________


*~continous~*
Kallon ta yayi cikin wata irin murya mai cike da rikici yace" momy mai kika ce...
Kallon banxa tayi masa,ha'di da wurga mawa dijamah kallon tsana,sannan cike da masifah tace " au sokake na maimaitama ka kenan...?
Momyn Basma ne dake gyefen justice madina ta ta'6a baki ha'di da cewa" ae saifah kinyi ha'kuri hajiya madina, don an riga da anxauta maki 'da...
Cikin jin 'dacin maganganun momyn Basma justice madina tace" okayyyy....cewa nayi yau nakeso kasaki wannan bagidajiyar...littafin hassenart bamalli,in banda aikin mallaka,ina kai ina wannan fullatanan dajin...?tohhh in anmallake ka ni nafi 'karfin kowani matsafi ne wlh...maxa amsa ta kadda da bairo ka rubuta mata saki,don wlh baxan ta'6a xama da wata suruka inba Basma ba...tana maganan tana ciro takarda da bairo daga cikin jakarta,niko nace justice manyah...😇😎
Dan gwarar masa tayi a gabansa,don Aliyu kasa ya xube yana mai bama momy baki,akan tayi ha'kuri shi baxai iyah rabuwa da matarsa ba...
Wani tsawa justice madina ta daka mai,wanda har deejamah dake gyefe tana zubar da hawaye sai data firgita,inda momy cike da karajin murya ta hau cewa" wlh yau kasaki wannan yarinyan ko na 'daga ma nono...
Wani 'dauke wuta yy,wanda dijamah dajin maganan momy yasata 'karasawa gaban momy ha'di da cewa" momy don Allah kiyi ha'kuri karki rabani da mijina,don Allah, wlh ko wa kk so ya aura xai aurah,amma karki rabumu...
Cike dajin tsanar deejamah, momy ta hanka'data,wanda ganin dijamah tayi taga² xata fa'di ne yasa cikin sauri kuma cike da xafin nama Aliyu yakai hannun sa ha'di da riketa...
Ganin haka yasa momyn Basma salati,tana mai fa'din hajiya madina, yau ninaga lalaci,wai yarinya karama kuma er cikin daji,amma tana abu kaman karuwan data fito daga yawon bariki...?
Kuka deejamah tasa ganin yanda momyn Basma ke aibata ta,wanda cike dajin haushi momy tace"ae yau duk taxo karshe,sai taje tayi karuwancin da uban ta,Aliyu kai nake jira fah,ga bairo nan maxa rubuta mata sakin ta takoma gidan tsohon ta.
Mom ne tacigaba da cewa" wae ma inbanda aikin asiri har takan wannan yarinyan ne xaka mari Basma...!
Toh yau sai ka saketa ko na'daga maka nono....
Cike da ru'du kuma a durkushen da yake yafara rarrafawa har gaban justice madina.... Hannun sa ya 'dago ha'di da 'dorawa kan cinyarta inda bakin shi na rawa,idon sa lokaci daya ya ka'da daga fari xuwa jah,nan cike da makerkyatan murya ya fara cewa" don Allah mom kiyi ha'kuri,kar kice nasaki matata wlh inasonta,momy kitai maken kisamun albarka a cikin wannan...katse shi tayi cike da masifah da bada umarni tace" wlh yau indai ni na haifoka duniya sai ka saki wannan gayyan fitinan...don haka kafin na irga uku ka saketa.hawaye ne yafara xubowa daga kuncin sa,wanda momyn Basma ta tsaya tana kallon ikon Allah baki sake tana mamakin taurin rai irin na Aliyu Haydar amma yau akan wannan er kauyen rugar yake xubar da hawaye... Waigawa tayi inda deejamah ke a durkushe itama ta aikin kuka,wanda lokaci daya tafita hayyacin ta...
Buda baki yayi xai magana...sai mom ta hau cewa...1,2
Jin haka yy saurin dafa mom ha'di da cewa" don Allah kiyi ha'kuri xanyi abun da kk ce,amma don Allah karki min baki...
Jin haka yasa mom ta saki wata irin murmushin nasara,sannan tace" oyyah maxa rubuta,ta fa'di tana ajiye masa takarda da bairo a gaba,wanda cikin ganin duhu² jiri² yasa dau takardan hawaye yana mai kara xuba daga idon shi.
Ganin Aliyu na shirin rubuta ta kardan sakin yasa deejamah takara banxama xuwa gaban momy tana kuka ha'di da rike hannun momy tana cewa" don Allah momy kiyi ha'kuri wlh Hamma na xai aureta amma don Allah karki sa yarabu dani na rokeki....
Tsaki mom tayi ha'di da kwace hannun ta tace ke matsa ki bani waje....maxa rubuta ina jiran ka,a hankali yafara rubutun ta hanyar dora bairon kan takardan...

Deejamah ne taji cikin ta na wani mur'da mata,wanda lokaci daya taji wani irin axaba da bata ta'6aji ba yana ratsata,jin datayi wani abu na bin jikinta yasata sakin wani irin mahaukacin 'kara ha'di da sulalewa 'kasa.
Cike da xafin nama Aliyu ya isa gareta,ha'di da fara girgixata,wanda lokaci daya idon ta yakame...ga jikin ta yasaki ko ina yadago a sake.bai tsaya bin na momy ba,wanda suka tsaya suka saki baki suna kallon ikon Allah...
Sun gumana ta yayi ta hanyar daukan ta cakkk ha'di da nufahn parking space, cikin gaggawa yasata cikin mota inda mai gadi cikin sauri ya wage masa tanfatsetsen gate din gidan,wanda cikin sauri yafigi motan ha'di da barin cikin gidan ha'di da nufah da deejamah hospital....

Momy kuwa sakin baki tayi ha'di da xama kan kujera sharafff,wanda lokaci daya jikin ta yy sanyi kalau....don tana tsoron abun da xa'ace sunyi kisan kai...
Ganin karaya a tare da justice madina yasa cike da makirci mom Basma tace" hajiya madina shin kinga abun da nagani kuwa...?batare da momy ta bata amsa ba ta cigaba da cewa" kaman fahhh wannan yarinyan juna biyu ne da itah,kai bawanda ya kai fulani iskanci,ace kaman suna rukon abun...anyah ma cikin Aliyu ne kuwa...?
A hankali kuma cike da sanyin jiki momy tace" nagani wlh,kuma cikin Haydar ne a jikinta bana wani ba,don nasan halin fitinan Aliyu Haydar,ni yanxun bansan ya maxan yi ba wlh,toh ya xa'ayi na raba aure kuma gashi aikin gama yagama,dole dai mun ha'da xuri'a da itah...yanxun maiye mafita...?

Momy tace ha'di da kallon momyn Basma da tacika tayi fahmmm,wanda a zuciyan ta take cewa " tabbas baxata iyah xuba mawa wannan arxiki na Aliyu ido ba,akan me wata can xata xo taci shi ba erta ba...inah sam baxai yuwu ba.
Kallon justice madina tayi ha'di dacewa " kibar wani shirin sa Aliyu Haydar kashe wannan auren,koda xa'a rabasu tohhh kibari sai Basma ta shigo cikin gidan nan tukun,sai musan yanda xamuyi.
Yanxu kisa Aliyu Haydar ya auri basma,ta hanyar ce masa yaxa'6a daya,ko rabuwa da deejamah ko kuma ya auri Basma...














Manage with this plz.....












Maman teddy....
[01/02 8:30 pm] Maman teddy🧸: *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊️*

*_Kungiya masu aiki da naxari da ilimi_*


*DIJAMAH 'YAR FULANI*

Written by...:
Aysha moh'd (Maman teddy...🧸)

*Sadaukarwa ga:*
Laila moh'd
Aseem moh'd
Hudair moh'd and...
Bilal moh'd nasaudakar da wannan pagen gareku 'yan uwa rabin jiki,allah yabar mun ku....laila na pray for miji nagari,allah yakawo mana musha....🤩🤩🤩💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Episode 3️⃣4️⃣➖3️⃣5️⃣



____________________________


~*Continues*~

"Momyn Basma ne ta cigaba da cewa" wannan shine ka'dai mafitan da nake ganin mana,amma kiyi tunani kema...ta 'karke maganan tana mai kwantar mawa da justice madina kai,na irin makiran matan nan..
A sanyaye justice madina tace" hakan xa'ayi dole,don bamu da mafitan da ta wuce wannan...
Shiru tayi,wanda a hankali take bin falon da kallo,wanda aka narka mai dukiya har ya gaji da kyau da walwali dakuma kayatuwa...
Komai na falon mai launin blue and milk ne,wanda hakan yakuma 'kara haska ka dakin sosai,fa'din ko irin kyau da falon yy basai na fa'da ba...
_(don kun san falon mai kudin novel..)_
Haka momy tayi ta bin komai da kallo,wanda ita kanta momyn basma ke mamakin arzi'kin da aka xuba mawa wannan bafullatanan dajin.
Haka suka gama gyetsinin su,sannan suka fito ha'di da barin gidan,wanda mom kecike da ta'ajibin tayanda sam batasan Aliyun da wannan estate din ba.🤔
Mama hinde dake gyefe tana binsu da kallo,wanda duk abun da akayi a gaban idon ta ne,haka har fitan su,goge kwallan idon ta tayi,wanda zuciyan ta fal tausayin deejamah da Aliyu Haydar ne,nufah kitchen tayi tana mai tunanin halin da dijamah ke ciki,inda take addu'a n kar Allah yasa wani abu yasami deejamah, Allah ya tashi kafa'dun ta...don in wani abu yasameta batasan yanda mijin nata xaiyi ba.
'Bangaren Aliyu Haydar kuwa,da isan su Asibiti,cikin gaggawa nurses suka kar'6a deejamah,wanda cikin sauri wani babban likita da'ake kirar sa da doc.Aryan ya fara aikin sa cike da gonewa don daidaituwan tsayuwan numfashin ta...
Wanda cikin ikon Allah ta farfa'do,inda nan sukayi mata allurai,inda ciki harda na bacci.
Da fitansa Aliyu Haydar ya nufo sa,wanda kafin yace" masa wani abu tuni Aliyu yafara jero masa tambayoyi....doctor ya jikin matata,ta farfa'do...!!! Mai ya sameta...???
Murmushi doctor Aryan yy ha'di da cema Aliyu Alhmdllh mun samu nasarar daidai tuwan numfashin ta,but ka biyoni office nayi maka bayani.
Hamdala Aliyu Haydar ya hauyi,wanda haka suka nufi office din doc. Aryaan.
Da shigan su office din ta xauna akan kujeran dake pacing din na doctor Aryan din...
A natse yafara magana ta hanyar cewa" kaman yanda na fa'da maka, ansamu nasara tohhh hakane,don matan ka tana dauke ma da cikin ka na tsawon wata 'daya da kwanaki,kuma Alhmdllh don bawani abu da yasami cikin dake jikin ta,sai dai tana cikin firgici sosai,wanda hakan xai iyah haifar mata da wata matsalan...
Cike da farin cikin magan doc.Aryan yace" deejamah na dauke da gudan jini na kk nufi,kai masha'allh da wannan albishir

9 / 13