DIJAMAH 'YAR FULANI Ranar da Komai Ya Sauya by maman teddy

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   12 / 13

33K to 36K   out of 36.2K words

wanda ta ansa sunan ta,mai ruwan sararin samaniya,( sky blue) wanda ya zauna yy masa aikin data amshe jikin shi,wato babban riga sosai yafito a yaron sa mai tashen ku'di daji da isa da ixxah,(dolars...) cikin sauri ma'aikatan suka hau kawo masa gaisuwan su ha'di da '6acewa daga falon.wanda da fitan su ya taka har gaban deejamah wanda sai a yanxu taji wani iri,wai yau hamman nata ne yy aure...cike da danne kishin ta tace" hamma kaganka kuwa,yau kayi mun kyau sosai kafito a cikakken ango...
Murmushi yy ha'di da manna mata kiss a kan tattausan la'6'6an ta sannan yace" da gaske my queen...?
Murmushin ita tayi masa ha'di da cewa" allah kuwa,don yau kafi kowani rana kyau.🥰
Bude baki yy xaiyi maga dai² kiran Anwar na shigowa,don ana can ana ware² n neman ango,wanda en gulma da tsegumi har sun fara baxa kolin su.
Ganin ya'ki dagawa ne don shi samm bai son ganin yarabu da deejan nashi,nan deejamah tace masa"hamna ka tafi mana,kila fahh neman ka akeyi.
Murmushi yy ha'di da cewa" ni banagajiya da kallon ki ne,kin fimun ko wacce rana kyau my angel.ganin yana yoo mata xuba kuma data son hali in yafara mata sai su '6ata a wanni yasata cikin sauri cewa"ni kaga na mi'ke na baka wuri hamma, don na lura ba fitan nan xakayi ba.
Ganin ta nufi side din nata ne yasa shi dariya ha'di da mikewa ya nufi parking space...

Koda ya isah wurun daurin auren yasha fa'da wajen abokannan shi,masu yabon deejamah nayi masu xagi nayi,don wasu ma har cewa suke kai wannan masha'allh, ace yarinya 'karama tana juya mutum yakoma kaman mutum mutumi saboda gigitashi da takeyi,wai dolars meye sirrin..?
Bai basu amsa ba,illah kau da kai da yy yana mai bin su da murmushi... Wanda nan take su Anwar suka hau Angon na deeja ne.....hmmm Na deeja bada kanka a sare kaje gida kace yafa'di...haka dai suka dinga shikiyancin su suna dariya... Wanda daganan suka wuce wajen da suka shirya don ta najer da tasu event 'din.
A wannan rana Basma ta tsin ci kanta cikin wani irin farin ciki musamman da aka tabbatar mata da 'daurin auren ta da Aliyu Haydar...
Wanda event sun shirya shi yafi akirga...wanda ciki kuwa harda dinner,wanda ba'a gabatar ba sai da aka kai Amarya gidan mijin ta,wanda babban falon su duka 'daya ne,sai dai part din kowa da ban...tun da dangin Basma suka shigo cikin gidan suke bu'da ha'di da habaice² inda wasun su suke kisaka kafanki ko inah da bisimillah,don kin san fulani da mugun ta,wata ce mai irin bakin nan tayi saurin amshewa da cewa" ae munan da aka ganmu mun sha li'ilafi bb sharrin wani mahaluki da xai tasiri a jikin mu...
Jin irin habaicin da suka fara da shigowan su,wanda sunan tana falon ta ne,amma sai da tajiyo su yasata nufahn bedroom din ta ha'di da 'dauro alwala don ta gabatar da sallahn isha'i.
Bayan sun gama habaicin sune,an gama mawa amarya fanfo,inda bayan en mintoci suka fara shirye² n tafiya dinner, Basma ko irin zinaran da kwalliya n da aka sha samm ba'a magana,don ba'karamun a zaban kyau tayi ba,wannan 'katon bakin nan kuwa duka ya shige.
Haka motoci suka kwashe su xuwa hotel din da xasuyi dinner.
Wanda kamin kace kobo tuni en uwa da abokan arxi'ki sun cika....wanda tuni kowa ya gama halarta sai ango da bb shi,tun ana san ran ganin sa har aka soma cirewa,wanda Basma ko ganin bb Aliyu Haydar ba'alaman shi yasata 'daga hunnu ha'di da kama kai tana ihuu...
Wanda ganin haka yasa tuni akayi saurin kamata ha'di da nufo da ita gidan mijin ta....sosai aka dinga bata baki da ha'kuri,inda sosai abokan Aliyu Haydar suka toxarta a wajen,don ba'karamun wula'kanta su kayi ba.
Yayin da justice madina labarin na isar ta,ta daga wayarta cike da masifah dajin haushin abun da Aliyu Haydar yy a wajen taro mutanen.....amma cikin rashin sa'a ta samu wayar tasa a kashe...tsaki taja tana cigaba da banbami..wanda meenash dake gyefe tajiyo da'din sosai abun da Hydar yy mawa dangin basman da ma ita kanta basman...
Sosai taji da'din hakan,wanda ko a fuska ta ta gaxa '6oyewa.mom kuwa ganin farin ciki a fuskan meenash yasata hurhurga mata harara...

_____________________________

Aliyu Haydar kuwa bai shigo gidan ba sai can tsakiyan dare,wanda dashigowan shi,kaman a kunnen Basma don sam ta gaxa bacci,shi ka'dai Aliyun takeson gani,duda tana fushin shi da laifin da yayi mata...
Kara lelaye jikin ta tayi da mayukan datasan yafison su da turaruka masu da'din 'kamshi... Wanda dama tuni ta yakice wa'innan kayan dake jikin ta tasa wasu irin damanmun kaya masu jawo hankali da tada sha'awa( segxy dresa💋💋)
Shikuwa da shigowansa bai nufi 'dakin shiba sai na deejamah, wanda tuni tayi bacci,da shigar sa yanufeta ha'di da xama gyfenta yana mai 'dora kanta bisa kan kafan sa,a hankali yakai hannun sa ha'di da cudawa cikin gashin ta,wanda yake da taushi da tsantsi,jin irin kamshi n dake fitowa daga kan nata ne yasa shi kai hancin shi yana shakan kamshin nata...
Wanda nan yafara motsashi sosai,hannun shi yakai xuwa cikin sleeping dress din ta,ha'di da dorasu kan dukiyan fulanin ta yana me fara wasa dasu,wanda lokaci guda idon shi yaka'da na tsantsan sha'awan matar nasa.
Cikin bacci ne taji kaman ana shafata,amma kuma sai ta cigaba da baccin ta,wanda jin abun na 'kara gaba ne yasa ta cikin bacci ta bu'de idin ta,wanda da saukan sa kan nashi,nan tayi sauri mi'ke wa daga jikin shi tana mai kare masa kallon mamaki...
Cikin wata irin muryan bukatan ta yace" plzzzz my queen sau 'daya kawai....
Cike da mamaki fall a kan fuskan ta,tace " tabdijammm allah hamna ka tashi kafita konayi maka ihunnn kwarto,kowa ya xo yaganka...
Cike da zafin maganan nata yace " deeja nifah mijin ki ne ba kwarto ba,don nace hakkina nake bukata sai kice mun haka...?
Kallon sa tayi duda taji bb da'di abun da tace masa,amma sai ta cigaba da magana cikin rashin nuna nadama tafara cewa"hamma yau fahh kayo aure ae yanxu banice zan baka hankin ka ba,amryan ka ce don haka don Allah kafitar mun daga 'daki.
Ganjn yanda ta tubure kuma yasan baxai samu abun da yakeso ba yasashi don dole hakura hadi da mi'kewa yana layi yabar 'dakin nata ha'di da nufahn nashi 'dakin.
Basma ko dake kallon sa ta window don tun daga shigar sa dakin deejamah har fitar sa a kan idon ta ne,yanayin shi ta lura ta fahimci yana cikin bujata,gashi itama kuma duk wakanne don tasha magunguna wanda tun 'daxu suke tsumata,cikin sauri ta fito daga nata side 'din ha'di da nufo nashi falon,direct nufahn bedroom tayi ganin bata ganshi ba....
Shikuwa Aliyu Haydar ganin bai samu abun da yake bu'kata ba yasa shi daga shigan sa ya cire manyan kayan jikin sa,ha'di da fa'dawa kan bed din shi yana mai lumshe ido,wanda suka kuma 'kan'ksncewa saboda fitina,inda da ya rufe surar deejamah yake gani.
Wani matsanancin sha'awar ta ne ya rufe shi,inda lokaci guda ya hau juyi,yana mai danne🍌 ganin irin 'dagowan datakeyi....
Saukan mutum yaji ajikin shi,tana wani bin shi da irin romance love,wanda cike da bariki da iyawa take bin kowani sassa na jikin shi,jin takama shafa shu ne kaman wani......yasa shi saurin sauke nannauyan numfashi,don a tunanin shi deejamah ne.
Kai bakin ta tayi dai² kan nonon shi tana wani irin tsotsan su wanda ya 'kara gigita shi,bude baki yy yana son anbaton sunan deejamah amma ya kasa saboda jin sa da yakeyi a wani samma....
Cike da tafiyan tsutsa ta fara gangarawa da hannun ta har kan🍌 wanda a hankali ta fara wasa da su...ha'di da 'dara bakin ta a kai tana wani irin tsotsa sosai....
Gaba 'daya yagama ficewa daga hayyacin shi,wanda cikin muryan inninahhhh yake kirar sunan deejamah.... Wasshhhhh deeja na,xaki kashe ni da da'din kiiiiiiiii..........jin irin duniyan datake lulawa dashi ne dakuna hannun shi da yakai yana shafa wajen da yafiso taji su shafaffu yasa shi dawo hayyacin shi sakuma fahimtar ba deeja ba ne...inda nan yafara tunanin samm deejamah baxata itah yi masa hakan ba ma....
Fahimtan da yy Basma ne yasashi saurin angajeta ha'di da daka mata wawan tsawa....
Cikin firgita ta mi'ke ha'di da kuma matsowa jikin shi idon ta a rufe....cike da masifah yafara cewa tafice masa daga daki,yana mai xaxxaga mata bala'i,don tassha xagi har da ce mata karuwa, fitinanniya...
Kuka basma tasa ha'di da kara manne masa tana mai cewa" plzzzzzz Aliyu baxan iyahhhg ba....don Allah ka taimakeniiiiii....
Jan wani dogon tsaki yy ha'di da juya mata baya,wanda hakan yakuma sakata wani sanon kukan...
Inda lokaci daya tahau firar da wani irin numfashi tana gurmususu a wurin...bakin ta banda karkarwa bb abun da yakeyi.....
Ganin yana shirin jefah yarinya cikin wani hali gakuma tausayin ta ya tsirkan mai yasashi badon yaso ba,ya biye mata a wannan daren...wanda sosai yaji banbanci tsakanin ta da deejamah... Sammm kawai sai yana biye mata ne don ya gamsar da itahhh badon yanajin da'din abun ba...
Wanda a haka yayi ta ko'karin faranta mata.....

Koda asuba sam bai bi takanta ba,acewan sa bb abun da xai mata da bata sashi ba,don haka ne yy wankan sa ha'di da 'dauro alwala yanufi masallacin dake kusa da su.
Sai da gari yy haske sannan ya dawo wanda da shigowansa ya tarar da ita yanda ya barta,cike da kyakyani ya hau cewa" keee Basma kinsan bafa nason kaxan ta,tashi kificemun daga 'daki tun da baxaki iyah tsaftace jikin ki ba....
Niko nace kai Aliyu bayan angama....🤭😂

Tashi tayi ha'di da nufahn hanyan privacy n shi,wanda bai ko kara kalon ta bata ya cigaba da aikin sa.
Wuraren karfe 9am deejamah ta mi'ke ha'di da nyfahn dirning don tasan tuni an kammala mata komai....
Kaman yanda tasani haka yafaru don tuni su rabee sun cika dirning din da kayan motsa baki...da na break fast.
Zama tayi tafara serving din kanta hankalin ta kwance...wanda bata lura da fitowansu ba sai dai xaman su dataji,'dagowa tayi nan suka ha'da ido da Hydar wanda cikin sauri ya iso gaban ta yayi hugging din ta,da tambayan ta ya ta kwana jiya....
Murmushi tayi bata basa amsa,illah mai da hankalin ta da tayi ga Basma wanda take ta fixfixga.a sanyaye tace sannu da fitowa kin tashi lafy....?
Banxa tayi mata ha'di da kai hannun ta fara serving din kanta,wanda Aliyu ganin haka yasa shi sakar mawa deejamah da murmushi n karki damu...inda itama ta sakar masa hadi da komawa ta xauna kan kujeran ta,kaman yanda ya saba mata kullum da kanshi yake serving din ta haka ne yau ma,don basma tayi hararan har tagaji,wanda tsanar deejamah yakuma kwantawa a zuciyan ta...
Ganin basu san ma tanayi ba,yasata cike da muryan makirci ta kalli Aliyu Haydar sannan tace' honeey ya kama naji kwanakin daxayi a daki na,don inaso muje honey moon fah...
Kallon ta yy ha'di da cewa" honey moon.?sai kuma ya yamutsa baki ha'di da cewa" deeja na bata da lafy,xan tsaya na kula da itah,da babyn datake 'dauke mun dashi...ba itace ka'dai basman ta firgita ba...har ta deejamah sai da tayi shorck da jin maganan nashi,kasa magana tayi illah mikewa datayi ha'di da nufahn bedroom din ta.
Da shiganta kuka ya ku'6'6uce mata,nan ta hau kuka tana cewa" shikenan yau xata mutu ta bar umma... Kuka takeyi tana karawa,harda shashhe'ka...wanda Aliyu ko ganin deejamah n ta shiga wani hali yasa shi saurin biyo bayan ta,wanda Basma ta zauna baki sake kan daga bisani itama kukan ya 'kwace mata, tana kukanne don ganin yanda wata yarinya 'karama kuma er daji bafullatan an ruga ta sauya shi ga ba'daya ta canja masa lissafi...
Kuka take sosai kan daga bisani ta nufi 'dakin ta ha'di da kirar momyn ta.
'Bangaren Aliyu Haydar kuwa da shigan sa bedroom din yanufeta ha'di da rungumota jikin sa yana mai aikin lalkashi,don dama yasan irun wannan rana xata xo...
Kuka take tana cewa" itahhh ya fitar mata da cikin bataso ta mutu ta bar ummah,wanda sosai hankalin shi ya tashi,don shi har ga Allah yana 'kaunar cikin deejamah n...
Da kyar yasamu ya lallashe ta da bata baki har yasamu tayi shiru...
Wanda tun daga nan komai na rayuwanshi da deejamah ke tafiya cike da so da 'kaunar juna,don yace mata samm baxata mutu ta bar umma da shi ba,zata haifah masa yara su rayu tare...
Itako Basma kaman yanxu ne ma ta da'da lalacewa" don gaba daya tasaka mawa ranta kishi sosai,wanda labrn cikin deejamah yakoma har kunnen justice madina... Sosai ta kira Aliyu Haydar tana masa fa'da a cewanta baxata ha'da xuri'a da deejamah ba,ya gaggauta xuwa a xubar da cikin...
Da tohhh yabi momy don yasan xuga ne ta mutane....wanda a haka rayuwa na cigaba,komai gaba yakeyi,ranaku na gudu...watanni kuwa sunyi mana nisa.....

Deejamah na gani da ciki tsirere a gaba,wanda girman cikin na kaina ya bani tsoro....gyefe guda Aliyu Haydar ne cikin shigar sa ta kamala,wanda yakuma kyau da kwarjini,nan naga ya rungumo deejamah ta baya wanda da'ala ma magana yake fada mata na kwantar da hankali...
Kuka deejamah tasa ha'di da cewa" wlhhh hamma na banason tafiyar nan taka, sai inajin kaman wani abu xai faru in katafi....kuka ne yakuma kwace mata,inda cikin sauri yakuma rungumeta ha'di da cewa" sowie my dear baxan da'de ba a America...just 1 weak xanyi na dawo mu cigaba da rainon babyn mu kinji....?
Murmushi tayi ha'di da 'daga masa kai,wanda a hankali ya kuma kissing din ta,sannan ya kai hannun shi ha'di da shafa cikin jikin deejamah n,wanda Basma dake mota tana son rakashi airport nan take cewa" a zuciyan ta xan baku kowani lokaci ne kuyi ta sallaman karshe,don Aliyu Haydar ka rabu da deeja kenan har abada..

Haka ya dinga yi mata abun da baya gajiya,har sannan don kanshi ya nufi motan inda cike da kewan mijin nata take 'daga masa hannu...

______________________________


Tunda ta koma falon ta takejin cikin ta na mur'da mata,wanda take ta juyi cike da dauriya don ita a tunanin ta samm ba haihuwa ba ne.
A haka ta '6ata a wanni wanda ya kaima ko 'daga kafa bata iyayi,ga muryan ta yy rauni ko daga shi bata iya yi...tana cikin wannan halin ne Basma ta shigo...wanda cike da mugun nufi ta isa gaban ta,a hankali ta duko har gaban fuskan deejamah wanda ita bama tasan inda kanta yake ba,dryn mugun ta tayi sannan tace" yau rana tace deeja,kisa mawa ranki daga yau kinyi sallama da Aliyu Haydar da mako waye don har iyayen ki yanxu haka nasa aje a 'karar mun da rugar taku baki 'daya,don yau xaki fahimci banbancin tsakanin talaka da mai ku'di.... Hawaye ne ya fara bin kuncin deejamah don bb bakin mgn...mama hinde ne tashigo,wanda cike da makirci Basma tace" keee wa kk,xo ki taimaka kusamun ita a mota na kaita hospital....
Cikin sauri da rudu mama hinde ta nufo su ha'di da kama deejamah suka saka ta a mota.... Wanda kafin su isa tuni Basma ta kira justice madina ha'di da shaida mata nakudar da deejamah keyi,wanda nan take duk wani mugun nufin da tsanar deejamah yakau a wannan lokacin, don cikin axama ta dau mayafin ta ha'di da nufahn asibitin da basma tace mata suke.

Da isan su cikin sauri likitocin suka amshi deejamah ha'di da 'ko'karin bata taimakon gaggawa,wanda basma dake waje da momy don tuni tazo,kuma sosai ta rude a cewanta deejamah karamar yarinya ce,sosai momy ke mawa deejamah addu'a r sauka lfy...
Wanda basma cike da isa da mulki ta nufi office din wani babban likita,wanda da'alama shine xai amsa haihuwar deejamah....
Zama tayi a daya daga cikin kujerun office din, wanda jiki na rawa ya hau cewa sannu hajiya...
Dan ya tsina fuska Basma tayi ha'di dacewa,abun dake tafe dani shine " xan baka kudi kimanin 5 million...amma so nake ka kashe mun wannan yarinyan mai haihuwa,ina son ka halakata da ita da 'yan ko 'dab da xata haifah duka....
Cike da mamaki doctorn yace" hajiya wannan fahh babban aiki ne.....
Cike da izzah tace" nasani kuma dole kayi,in ba haka ba,sai nasaka ka a fitina n da sai kayi gidan yari...idan kuma ka amince ga miliyan biyar nan gara'6asa,idan kuma ka bijere tohhhh xaka ha'du da makircina...
Da jin haka nan likita n yace" haba hajiya ae wannan 'karamun aiki ne...yau nayi maki alkawarin kashe wannan yarinya,xan kasheta da ita da yaran da xata haifah,don munyi scaining ba daya bane a cikin nata...yayi dasuke shirin fitowa mukuma xamu dannan su da karfin tsiya sukoma don dole,kinga ko daga nan da ita dasu duka sun gama yawo...
Wani wawan dry Basma tasa ha'di da xube masa rafa² ta dari biyar² tana cewa" wannan somun ta'6i ne...cikin axama likitan ya hau gdy, sobreen da taxo don sanar masa da halin da mama ke ciki,jin mgn da Basma keyi yasata cikin hanxari nufahn labour room ha'di da neman inda aka kwantar da deejamah ,shiko doc. Emma mikewa yy ha'di da nufahn labour room don ganin halin da deejamah ke ciki....amma cikin rashin sa'a da isar sa sai kukan babies da ya xiyar ce shi,nurses din da suka amsa haihuwan nata ne yadaka masu tsawa ha'di da cemawa 'daya tafita 'dayan ta tsaya...
Da fitan watancan nan docton ya hau labarta mawa nurse din irin aikin da xasuyi,wanda cikin sauri suka fara aikin,don da'alama sun saba yi dama...


Cike da mamaki dakuma rashin yarda deejamah ta kalli doctor n da yace baxai mata aiki anan ba,sai sun shiga privacy.... Haka ta bisa,wanda ita kuma watancan ta tsaya da jariran tana tunanin yanda xata cika umarnin Basmah...

Ganin doctor n nashirin yimata wannan allurar ne yasata cewa" likita wannan alurar meye kuma...?
Cikin daurewan fuska ya 'dago ha'di da cewa" allurar mutuwa ce....

Cikin tsoro da firgici deejamah tace" allurar mutuwa kuma doctor, don Allah ka taimaka mun kabarni na rayu da "ya'yana,bayan nan umma na bata da kowa sai ni...kayi ha'kuri don allah,kaga ban maka komai ba.
Wani wawan dry yasaki ha'di da cewa" wata umnahn naki,matan da yanxu an tura asa ma bukan su wuta....don haka ki kwantar da hankalin ki natsu suma ya'yan naki kashe su xa'ayi,don haka kema kasheki xanyi yanxu...kuma xancan baki mun komai ba hakane,ni ma sani akayi kuma bakowa bace illah basmah....
Nufahn ta yy yana mai shirin danna mata allurar,wanda cikin sa'a ta kauce ha'di da daukan wani 'karfe ta buga masa akai......

cikin hanxari sobreen ta nufi labour room inda aka kwantar da deejamah xa'a amsa haihuwan ta acan....wanda da isan ta taga wannan nurse na 'dora filo akan daya daga cikin babyn namijin... wanda

12 / 13