DIJAMAH 'YAR FULANI Ranar da Komai Ya Sauya by maman teddy

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   2 / 13

3K to 6K   out of 36.2K words

sai ya dauko ni mudawo gida tare....

Cike da farin ciki na shirya,inda nace mawa uwani ta shirya itama muje tare,don naji da a hannun hajiyan take...

A haka muka shirya duka ha'di da nufan gidan hajiya babba...

A wannan rana ne na fahimci yanda hajiya babba ta dauke ni a zuciyanta,don wannan rana naga wulakancin da ban ta'6a gani ba...

Ciki da fara'a muka shiga falon hajiya babba, inda na sameta xaune kan 2 seater,dayan '6angarenta kuma wata mata ce,wayyayyiyar gaske,irin wa'annan matan da sukaci boko har suka gaji,wanda suke neman maza ido rufe...

Ko arzikin amsa sallaman bamusamu ba,inda cikin sayin jiki na duka har kasa na gaishe da hajiya babba.... Amma kallona batayi ba,illah ma cike da tsawa da masifah ta hau cewa"kehhh.....matsa ki bani wuri...kina tunanun xan kar6eki a matsayin suruka!!! Tohh lallai kinyi kuskure....jubiki da allah,gayyar yunwa...tohhh ni nan dakika gani,inkin malleke shi,tohh ni nafi karfin ki makirah....

Nan tanisa ha'di da kallon maccido wanda gaba 'daya maganan hajiya babba bai masa da'di ba...

Kai kuma saunawa xan fa'da maka baxan yarda wannan busasshiyar taxama suruka ta ba..amma ka kiji...tohh kutashi kubarmun gida...ranan daka amince da auren binta ne xaka iyah shigomun cikin gida....
Ku tashi kufita nace....hajiya babba tace" cike da tsawa...yayin da doc.binta ke gyafe tana sakin murmushi,itah ala dole tayi kamu da uwar miji....

Kallon ta nayi,inda lokaci guda idona ya ciko da kwallah,uwani ko ganin halin dana shiga yasata,saurin girgixamun kai alamun kar nayi kuka akan maganan hajiya babba...
Nan maccido yafara ba hajiya hakuri akan tayi hakuri,kallon shi batayi ba,illah fixgixga batare da tace mashi komae ba...

Bai kuma bin ta kanta hajiya babba ba,yajuyo ha'di da mana sallama sannan ya nufi wurin aikin sa....


A wannan rana nasha wulakanci a wurun hajiya babba, amma sam ban nuna na damu ba,inda rashin nuna damuwata yakara bakanta ran doc.binta...
Haka rayuwa ta cigaba...inda shekarata daya a gudan maccido na haifoki,kuma har alokacin hajiya babba bata daina nuna mun kiyayya ba.amma sam ban duba wannan,tunda maccido yana nuna munso matuka....a wannan shekara kuma sai danaje wurin su baba na,inda kan na haifeki sai da naje sau biyu...wanda har alokacin munawwarah bata xoba...kuma taji labarin nayi aure....a nijeriya kusa dasu....amma bashi yasa ta nemeni ba...

Ba karamun murna Abbanki yayi ba dana haifeki,inda nan take yasa maki suna NANA KHADIJA...wato sunan hajiya babba... Hajiya kuwa bakaramun bakin ciki tayi ba,dajin hauhuwa ta...

Kwanan ki uku a duniya ne,ina xaune a kan gado na,a bedroom...inda nake goye dake abayana....


Kattawan maxa ne suka shigomun bedroom ba ko salllama,fuskan su duka a rufe da wani bakin kyalle....ihun su uwani nakeji,inda nan take na hau salati...amma kafin na farga tuni wani daga cikin su ya shakamun wani powder a fuska...


Wanda tundaga nan ban kuma sanin halin da nake ciki ba,sai farfadowa nayi naga ganni a rugar har'do....













To be continuedโœ๐Ÿป







#share to another groups...









Maman teddy ce....
08081202932.




this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Iwj6uv5L9np0NWOuHwBELo
[01/02 8:30 pm] Maman teddy๐Ÿงธ: *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

_Kungiya masu aiki da naxari da ilimi_


๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ
*DIJAMAR 'YAR FULANI*
๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ๐Ÿ”๏ธ

*Story and written by!*
*Maman teddy๐Ÿงธ*



Facebook@mamanteddy.com
wattpad Aysha mamanteddy
Mamanteddy@gmail.com


_Episode 5&6_


_________________________

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู…*

"Cike da wauta da yarinta dijahma tace"tohhh Adda sai kinxoh...
Nan uwani ta kuma sakin murmushi, don lokaci guda taji matsanan cin kaunar dijamahn a ranta...
" maida kallon ta tayi,akan ummah wanda take tsaye tana binsu da ido,don bata ta6a jin nadaman surutu irin na dijamah ba,da haushi kamar ta yau...
"Uwani ce tace" tohhh xan wuce ni,kuma in Allah ya yarda xan xo inga inda kuke a kwanan.
Murmushi ummah tayi,wanda ita kadai tasan manufahn hakan...inda a sanyaye tace"tohhh uwani Allah ya kawoki lfy...
Nan uwani ta amshe da amin...
Uwani bata bar wurin ba,sai da tayi ma dijamah kyautan kudi...don gaba 'daya rayuwan tasu ta tausaya masu matu'ka...
Nan ko dijamah ke ta murna,ha'di da yi mata godiya...
A hanyan su ta dawo wa,sam umma bata da karsashi,duk inta kalla dijaman ta,sai ta goge hawayen idon ta,wanda duk basu lura da hakan...
Yayin da dijamah ke can tana xuba ma yadikko bayanin wannan mata da taba shede...
A haka suna tafe suna fira,wanda kafin magriba sun iso cikin rugansu....
Nan kowa tayi cikin bukkanta,inda bintoto,take kara shaidama dijamah,anijima tafito,wasan dare a dandali...

Da shigansu bukka,bayan umma ta ajiye kwaryan su ne,ta fito ha'di da nufahn wurin da suke dafah...
Anan ta samu karyayi,ha'di da kara,ta kunna wuta,don ta girkama dijamah marori...(shinkafa)

Bata dauki wani dogon lokaci ba...ta kammala,inda nan tanufi bukkan da shi...

Bayan ta gama xuba mawa dijamah ne,tayo kiranta ha'di da bata,a cikin wata 'yar a kushi....

Cike da murna dijamah ke cin abuncin...ha'di dayo mawa umma sunbatun da'di....๐Ÿ˜‹

Umma dai banda murmushi ba'abun da take mata,don tunanin da takeyi akan uwani yafi damunta sosai,banda tunanin mafita babu abun da takeyi a yanxu...
"Dijahma da ta fahimci kaman da damuwa a tare da umman nata ne tace" umma na tunanin mai kikeyi ne,tun 'daxu!!!
"Saurin kallonta ummah tayi,inda cike da mamakin fahimtan tana cikin damuwan da dijamah tayi tace" hmmm dijamah na,maxa ki kammala cin abun cinki...inaso xamuyi wata magana...

"Murmushi dijamah tayi" inda Cikin 'dokin wata magana ce xasu yi da umman nata tace" umma tohhh,ai ma na 'koshi,wace magana ne xaki fadamun....!!!

Ruko hannun dijamah ummah tayi,inda a hankali kuma cike da sanyin murya da taushi...tace" dijah na yau xamu bar wannan rugan...

Cikin sauri dijamah tace" ummah ina xamuje...maeyasa xamu bar wannan rugan!!!
Ko xaki kaini wajen abban na ne...?
Kwallah ne yafara xubo mawa umma shattu,inda tafa cewa" a'a dijamah bawurin Abban ki xamu ba.
A salima saboda shine xamu bar wannan rugan har'do a daren yau,wanda batare da kowa yasani ba...
Rigima dijamah tafara samawa umma,inda take cewa" umma mai yasa bakyason naga Abbana!!!mai yasa xamu rabu da su yadikko...mubar rugan mu...
Umma ni naji banason ganin Abbana,amma karmu bar su bintoto da yadikko,aradu banason tafiya na barsu....

Kuka dijamah tasa,inda umma ta jawota jikin ta,tana share mata hawaye,ha'di da cewa" dieejah yau xan baki labarina da na mahaifin ki,wanda in kinxa6a mucigaba da xama,a wannan rugan shikenan sai mu xauna...

Dajin haka nan take dijamah ta mike da kwancen da take a jikin umma,nan cikin sauri da 'dokin son jin labarin umman nata tace" yeeehhh umma na,yau xaki gayamum iyayen ki kenan,dakuma labarin Abbana.!!?

A hankali umma ta 'daga mata kai,wanda a zuciyanta take cewa yaro yarone...Allah sarki ita gata tana nan tana 'dokin ganin mahaifinta da dangin sa,hmmm kosu suna 'yan ina oho...don wanda ya'ki ka,baxai ta6a sonka ba...

Nisawa umma tayi ha'di da gyara xama,sannan tafara da cewa" kaman yanda kika sani....
Sunan Aishatu... Wanda nasamu sunan shattu daga cikin rugar har'do.....

________________________


Kuma ni ba bafullatana bace,kaman yanda kika sani,ko ince kika sanni acikin fulani....
A salina buxuwar agadas ne ce,'yar asalin garin maliy......

Mu hudu allah yaba iyayena,inda nake da yayyu maxa guda biyu,saikuma yayata mace wanda take da suna munawwarah.

Saikuma yayyuna maxa akwai,sama'ila saikum tanimu,wanda nice 'yar autan su mai suna Aishatu...


Na kasan ce 'yar gata,kuma 'yar lele a wajen mahaifina.kasancewar nice auta...sosai nake samun kulawa...duda ba karfi ne dashi ba.


Duk inda baba na xai tafi tare dani yake xuwa...
Don haka gaba daya garin mu ba wanda bai sanni ba...don shiyasa innaga yanda kike mu'amalanki da mutane,dakuma yanda kowa ke nuna maki so,sai intuno da kaina a baya...don yanda kk ganki,kowa naki ne,tohhh haka nima nake a yarinta ta...


Banyi ilimin boko ba,amma inada na mahammadiyya,duda kasancewan mu buzayen agadas bamu damu da ilimin zamani ba,munfi damuwa da ilimin mahamdiyya...saikuma kasuwan cin mu...


Don haka tun ina yarinya nake sana'ar sai da abunci..inda nake kaima mawa ba'ki,wanda sukaxo daga kasashen kusa damu...kaman nijeriya da sauransu...


Muna son muga 'yan najiriya sun xoh 'kasan mu,don ganin su muke kaman wasu hallittu na daban...saboda sha'awa...inda a haka nake sana'ata kuma kowa yasanni da yanayin dabi'ata da kowa,inda anan na ha'du da mahaifinki,wanda asalin sa daga nijeriya yake,kuma cikakken attajiri ne ko alokacin,inda ya mallaki abubuwa da dama,don bakankanin arxiki yake dashi ba...


Kuma cikakken 'dan jarida ne...wanda shine dalilin dayasa yaxo garin agadas...don harkan jaridan sa ne yakawo shi...
Wanda yake da suna......










To be continued....โœ๐Ÿป













#share to another groups....





Kaman yanda kuka sani labarin ta ku'di ne,mai bukata xai turo #100 MTN idan kuma VIP ne #200 kacal.trasfer #200....
Duka ta wannan number๐Ÿ‘‡๐Ÿป
08081202932/09137392680









Maman teddy ce๐Ÿงธ
[01/02 8:30 pm] Maman teddy๐Ÿงธ: Typing....๐Ÿ“ฑ




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION...*

_kungiya masu aiki da naxari da ilimi_


*DIJAMAH 'YAR FULANI*


_Story and writting by..._
*MAMAN TEDDY๐Ÿงธ*

Episode 9&10

Facebook@maman teddy.com...
Wattpad...Aysha maman teddy...
Mamanteddy@gmail.com....

*~GARGA'DI~*
*_Ban yarda wani ko wata suyi amfani,wajen juyamun labari tako wani siga ba tare da sani na ba.yin hakan kuskure ne..._*
Wannan labarin 'ki'kirarrene,babu fasahan wani acikin ta,inkinga tayi shige da rayuwanki toh akasi aka samu...๐Ÿค—


*DEDICATION*
*Dedicate to you Aysha Abdulkarim...(momy kg...)salmah Aliyu...(momy show...)wannan pagen taku ce...kuyi yanda kukeso da shi...kaddai ku manta maman teddyn ku ce...๐Ÿงธ*

Ina maku barka da wannan rana mai albarka...

ุงู„ู„ู‡ู…ู‘ูŽ ุฃูŽุจู’ู„ูุบู’ ุนู†ู‘ูŽุง ู†ูŽุจููŠู‘ูŽู†ุง ูˆุดูŽูููŠุนูŽู†ุง ูˆุญูŽุจููŠุจูŽู†ุง ุฃูุถู„ูŽ ุงู„ุตู„ุงุฉู ูˆุงู„ุชุณู„ูŠู…ู ุŒ ูˆุงุจุนุซู‡ู ุงู„ู…ู‚ุงู…ูŽ ุงู„ู…ุญู…ูˆุฏูŽ ุงู„ูƒุฑูŠู…ูŽ ุŒ ูˆุขุชู‡ู ุงู„ูˆุณูŠู„ุฉูŽ ูˆุงู„ูุถูŠู„ุฉูŽ ูˆุงู„ุฏุฑุฌุฉูŽ ุงู„ุฑููŠุนุฉูŽ ุงู„ุชูŠ ูˆุนุฏุชู‡ู ููŠ ุงู„ู…ูˆู‚ูู ุงู„ุนุธูŠู…ู

ุฌู…ุนุฉ ู…ุจุงุฑูƒุฉ ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

Allah kasa mana abarkan wannan rana,kabamu ikon aikata abu mafi kyawu a rayuwan mu,ka nisan tamu da shirrin mutum,ko shaidan....Ameen ya Rabbil ixxaty...๐Ÿคฒ๐Ÿป

*_____________________________*


Bu'de idon danayi akan na yadikko ne,wanda take tsaye akaina...tana min firfita ta da wani langa langa abun fifita...gyafe guda kukan dijamah nakejiyowa,inda wasu daga cikin fulanin suke ri'ke da itah...

Ganin na bu'de ido,yasa yadiko cike da farin ciki,ta hau godiya ga allah, ta harshen su ta fulatanci...

Bin su kawai nake da ido,don bana fahimtan abun da take cewa"...

Magana tayi takuma ta harshen fullo...inda cikin hanxari wata mata tayo cikin bukkan,ha'di da isowa gareni har inda nake kwance takawo mun deeja...a hankali kuma cikin hausan ta wanda bai fita tafara cemun"ki bata nono take bu'kata tun jiya,sai yanxu muka samu kika farfa'do....don haka maxa kibata ai ma tayi ha'kuri...

Babu musu na Amshi deeja nafara bata nono,inda a raina nake tunanin ta yadda wa'innan mutanen suka tsiratar dani daga wannan axxaluman mutanen,wanda bansan wanda ya turosu wurina ba.

A hankali komai yake dawomun,inda nan take na hau xubar da hawaye mai dacin gaske...

Yadikko ne ta dafani ha'di da bani baki,akan komai na dauke shi a matsayin kaddara...

Haka na kwana uku a cikin rugar har'do,inda kullum wannan fulanin suke dawainiya dani da kuma kehhh deejamah...

A wannan rana da muka cika kwana uku ne,mai gari wanda yake yayane wurin yadiko,yayo kiran na...

Haka na isah wurin mae gari,inda anan yake shaidamun da yanda suka ha'du da ni,kuma da yanda suka taimakeni a hannun.
Bayan sun bar dani gidan maccido, basu tsaya dani a ko'ina ba,sai a kusa da wannan rugan...

Inda su mai gari na hanyar ta dawo wansu ruga daga cikin gari...nan suka ga wannan mutayen na janye da ni...abunka ga mara gsky,ako'ina sai ya nuna kansa...

Kunsan fulani ba tsoro..cikin tsawa da kuma hausan su wanda bai fita,su kace" waye wannan,mai kuke anan wajenn...

"Cikin muryan 'yan ta'adda suka maida ma mai gari da magana ta hanyar cewa" kai tsohon najadu bar wurin nan,kasheta xamuyi,inkuma ka6ata mana rai mu ha'da da kai...

Cikin xafin ran sunan da suka kira mai gari yace"tohhh bari kugani,xare sandan su duka sukayi,inda suka nufi wainnan 'yan ta'addan...
Ganin fulanin sunnufo su,kuma sun san bafillatani ya kasheka ya kashe banxa,musamman irin na daji irin wa'innan,yasa su saurin sakin ummah,inda sukayi wurgi da deejamah,suka kwasa da gudu ha'di da shigewa ta cikin dajin...

Bun bayan su sauran xasuyi,nan mai gari ya taresu,hadi da cewa" su barsu,suyi saurin ceton ran wannan bayin Allah...

Haka ko sukayi,inda da shigowan su,cikin ruga.suka sauka a bukkan yadikko...a haka sai da aka kwana guda sannan umma ta farfado...

Nan mai gari ya nisa, ha'di da tambayan ummah daga inda ta fito...
Shiru ummah tayi,don ita sam batasan ko'ina a nan najeriya ba,ita dai tasan tana najeriya...

Nan ta basu amsa da daga nijeriya take...
Shiru mai gari yayi,kan daga bisani yace" ae nan duka sunan shi najeriya...amma wani gari muke nufi kike?

Ganin umma bata da Amsa yasata cewa" ni ba 'anan nake ba,ni 'yar asalin garin agadas ne,aure ne yakawo ni nan.

Nan na xauna ta fara basu labarina komai da komai...

Sosai mai gari da sauran mutane suka tausaya mun,inda nan suka shaidamun suma basu san birni ba,kuma basu gane daga inda nake ba,saboda sunfi rayuwansu a cikin ruga...

Haka mai gari yace"na kara hakuri na xauna tare dasu har Allah ya kawo ranan da xan ha'du da dangina,ko miji na...

Sosai nayi farin cikin xama da su...fulanin kirki.
Kewa daya nayi,shine kyewan baba da guggo,sai kuma halin da maccido yake ciki a yanxu...amma duk inna kalleki sai naji gomma da allah ya barni dake...

A haka nacigabada rayuwa a wannan ruga,inda a haka kika girma a cikin wannan ruga.
Kuma su yadikko su suke maki fulatanci,kinji yanda akayi kk iya yaran fillo,don ni ban iya ba...sai dai na biku da ido,amma yauda gobe xaman tare yasa har na fara fahimtan wasu abun...

Nisawa umma tayi ha'di da kallon dijamah,wanda kuka takeyi sosai,tausayin ummah yagama kamata,cikin sauri ta mi'ke cike da yarinta tafara cewa"ummah ki tashi mugudu,kar su abbana suxo su tafi damu,hajiya ta turo aka shemun ke...

Goge kwallan idonta umma tayi,inda ta kamo hannun dijamah ha'di da cewa" a'ah deeja ba hajiya ce ta turo wa'innan mutane ba,nima bansan waye ba...
Sannan kuma dama ayau xamu bar wannan rugar har'do...

A hankali umma ta mi'ke ha'di da nufahn kasan gadon karan bukkan,inda ta fito ma wa da dijamah kayanta na saken fulani guda uku...
Sai kuma nata kala biyu...
Saida su ka tabbatar da kowa ya shiga cikin bukkan sa,sannan suka fito ha'di da barin rugar har'do...
Tafiya sukeyi suna waiwayon wannan ruga,inda suke tunani ranan da wowansu wannan ruga...

_____________________________


Tafiya suke cikin dare,inda a haka suka isah tasan cikin gari.

Batare da umma tasan inda xata ba,ta kutsa kai cikin wata mota dataji ana cewa"Adamawa...

Shiga sukayi,inda saida dijamah ta ganta a cikin mota,ta hau tambayan umma tana da shede ne...
Nan umma ke shaida mata,tana da kudin da uwani ta basu,dakuma wanda sukayi ciiniki a lumo...

Safiya tayi masu ne,acikin garin Adamawa,inda dijamah cike da farin ciki take bin garin da kallon sha'awa...

Sai da umma tasha fama,sannan drivern ya amshi kudunta,don kudin nasu bai kai ba...

Ware ware ta suka hauyi,inda wasu samari ganin suna wareยฒ yasasu tambayan inda xasu?

Batare da wani tunani ba,umma tace"ruga...!!!

Shiru sukayi inda suka ce,wani ruga kenan mama?
Rugar ya windo....ko rugar surbajo....
Nan umma tace"Rugar surbajo....
Nan suka sa su umma a abun hawa,ha'di da biyan masu kudin,wanda badon kowa suka biya ba,sai don dijahmah....

Gaba daya dijamah tagaji,ga wani irin mahaukacin yunwa da takeji,tun tana daurewa har takasa,inda a haka suka isa wannan ruga,...bayan sun sauka daga abun hawane,suka fara takowa daga 'kasa,don isah cikin wannan ruga,wanda tafi rugar har'do wayewa...

Nishi dijamah ta hauyi samaยฒ inda umma cike da ru'du tafara wareยฒ n ruwa...amma sam babu ruwa a wurin,wulkawn mutum ma babu bare,ruwan.


Tun dijamah na fitar da numfashi,har ta kasa,inda lokaci daya numfashin ta ya 'dauke...kuka umma tasa ha'di da kiran sunan dijamah...amma sam babu alaman numfashi a tare da itah...


Daiยฒ wasu tsofaffin fulani,wanda da'alama mata ne da mijinta,sukaxo wucewa....
Cikin axama matan tayo inda umma ke a durkushe,nan ta hau tambayan ta daga innah take???

Kasa magana ummah tayi,illah cewa da umma take" don allah ku taimakamun kar dijamah ta mutu,'ya ta ce....
Duka ta harshen fulatanci suke maganan.

Wannan tsohon ne yayi saurin ci6an dijamah ha'di da nufah cikin ruga da itah,wanda da isan su suka nufi cikin bukka ha'di da kwantar da dijamah...

*_____________________________*

*Cikin garin.....*
*GARIN ADAMAWA*


Wani tan'kasheshen gida ne na ganj,wanda girmansa yasa turawa ke kiranshi da estate house...

Gida bakaramun gida ba,wanda girman sa.ma,baxai fasaltu ba...
Sojoji kuwa xasu kai kimanin fiye da 50 xuwa sama,ko wannan su na kewaye da wannan gida...wanda da 'alama tsaron gidan sukeyi...licrout da sauran securities,wanda ba sojoji ne ka'dai ke tsaron gidan ba....

Jiniyan jami'an tsarone najiyo daga bayana,wanda yasani saurin jirgawa daga bakin tan'kamemen gate 'din danayi nisa wajen kallo...

Wasu motoci ne ke biye dana GEN.SUFYAN TABAWA...
Inda motocin sun kaifi 15 ke bin yanshi,wasu a gaba wasu kuma a baya...

Bayan anware tankamemen gate 'din ne,nayi saurin shugewa...daga ciki...


Hmm gidane wanda daga waje ashe banga komai ba....arxiki nadaga ciki....

Bude mawa hajiyan nashi mota akafarayi,inda sauran securities suka bude ma sauran side dun...

Cike da ixxa da jida issa da dukiya ta fito,tana ciko wuya...wanda kayan dake jikinta kadai ya isah yasa katafi duniyan tunani....jikin nan kuwa ta ko'inah yasha zinarai....

Niko nace"JUSTICE MADINA KENAN..

Uwar gida kuma amarya a wurin General sufyan tabawa....

Fitowa yayi cikin shigarshi ta alfarma,inda ya juyaga 'yar tasa wanda saukan su kenan daga 'kasan,nan yace mata"welcm back to nijeria my kid...!!!ya kika ga new house 'din mu na nan?

"Ya tsina fuska yarinyan tayi,inda cike da mulki tace" ba laifi dad,amma kayimun laifi guda 'daya...

"Kallon ta justice madina tayi,hadi da cewa" okay my baby mai yafaru,mai kuma ya6ata ran baby na...ta fa'di tana sakin mata 'kayataccen murmushi...wanda bamai ganin sa,sai 'yan 'ya'yan nata...

Cikin basarwa a kuma wula'kance" 'yan nata tace" dad yace mun kid...bayan ni ba kid bane yanxu,ko mom baiga na'kara girma bane...?

Don haka yabani ha'kuri.
Nan ta karke maganan ha'di da turo 'yar mitsilan bakin ta.

Cikin rayuwansu ta 'yan cin da suka saba,dad yayi dariya ha'di da shafa kan 'yar tasa,sannan yace" eyyah sowie my dear meenash...baxan karaba...

Justice ne tayi"murmushi, inda meenash tayi wani barander da xai sada tada sitting room...batare da tace" ma dad komai ba...

Bin bayanta sukayi,inda ma'aikatan gidan ke auki 'kame masa,yayin da wasun su ke kaimasu gaisuwa...

Basu ta kansu ba sukayi cikin falon tasu,wanda tagaji da kayan alatu da more rayuwa...

Ganin babu meenash,afalon yasa justice haurawa saman stairs,don tasan can tayi,yayin da a zuciyanta take cewa"ohhh meenash 'yar daru kenan...har yanxu fushi take,ala dole batason nijeria...

Kaman ko tasani zaune ta samu meenash a kan wani super cushine,inda 'yan aikin part 'din ke xube a gabanta suna kwasan gaisuwa da mata barka da dawo wa.

Kallon su batayi ba,inda take cike take batsewa...

"Justice ne tayi saurin nufo inda take,ha'di da xama gyafenta,ta jawota ha'di da xaunar da itah a jikinta.

A hankali kuma daiยฒ kunnen ta,ta hau yima magana.inda batare danaji abun da tace ba sai dai maganan meenash naji tana cewa" No mom bana son nan 'kasan,kawai mukoma Abroad plz....

Kuma innan kasan nada da'di mai yasa ya Aliyu bai dawo ba....????











To be continued....โœ๐Ÿป













Kaman yanda kuka sani,wannan littafin ta kudi ce,haka ne,xaki turo #100 ma wannan numbern...idan VIP ne #200 transfer #200 duka ta wannan number...



MTN....xaki turo ta nan 09137392680.

Idan airtel

2 / 13