DIJAMAH 'YAR FULANI Ranar da Komai Ya Sauya by maman teddy

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   1 / 13

1 to 3K   out of 36.2K words

ο»Ώ[01/02 8:30 pm] Maman teddy🧸: *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION...πŸ“˜πŸ–ŠοΈ*

_Kungiya masu aiki da naxari da ilimi..

πŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈ
*DIJAMAH 'YAR FULANI*
πŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈ


*Story and writting by:*
_Aysha moh'd (maman teddy...)_

Facebook@mamanteddy.com
Wattpad
Aysha maman teddy🧸
Maman teddy@gmail.com

*DEDICATION*
Dedicate to you my teddy...🧸
Wannan pagen naki ne my teddy,kiyi yanda kikeso da shi...Maman teddyn ki ne...πŸ˜…


Plz hajiya inkinsan baxakimun Comment ba,tohhh don allah karki karantamun novel...
Masu Comment Allah yabar kauna😍

*EPISODE* 1&2

______________________


..."DEJAMAR...." DEJAMAR.....!!!UMMAH NE TAKE YO KIRAN 'YARTA TA....

Dejamar dake can tayi nisa wajen wasan ta da shanayen dasuka fito kiwo...wanda suke kan shan ruwan wani rafi.....
"Kaman daga sama tajiyo muryan umman nata,wanda take can 'dan nesa dasu acikin wannan dajin...don itama tana tare da nata garken shanayen suna kiwo tare...
Jiyo muryan umman da tayi" yasata cikin sauri ta bata amsa da inworah ummah...
Wato tana mufin tana xuwa...
Cikin sauri tafara ka'da shanayen nasu xuwa inda umman nata take,don lokaci ne ta ruwa.
Hadari ya ha'du sosai,inda garin yakoma ba'kin 'kirin.iska sai ka'dawa yake...
Magana ta hauyi ma shanayen ta harshen fulatanci...inda kaman suna fahimtan abun da tace" suka kama kamo hanya,ha'di da biyo bayanta....


Gurun wata 'yar dattijuwan mata naga ta nufah,wanda take sanye cikin sa'ken ta na fulani...

Da isanta,nan matan cikin sauri tace"deejamar maxa muka'da shanayen nan mukoma ruga.
Don hadari ya taso sosai...
"Tohhh umma....!!!
" Deejah tace hadi da cigaba da ka'do shanayen.inda suka dauka hanyan rugansu....

_______________________

*RUGAR HAR'DO...*

A haka su deejamah da umman ta suka karako xuwa cikin rugarsu,wanda akafi saninta da rugar har'do... Inda ummah tasha surutun deejamah har tagaji,don sam bata gajiya da xuba,kamar tsohon ridio...tun umma na bata amsa har takoma cemata"ehmmm.....a'a

Ahaka har suka iso rugan su,inda naga sun nufah
Bukkan su,wanda naga bukkunan fulanin a kewaye da na junan su...kowanne bukkan nasu xa kagani can kasa,don duka a gajirce suke,wanda sukansu inxasu shiga sai sun du'ka sannan suke shigan shi.

Da isansu umma ta ka'da shanayen xuwa rumfan su...
Inda dijamar ta nufi 'bukkan su,don tagama gajiya,hutu kawai take bu'kata a yanxu...

Bayan ummah tagama kafe shanayen a rumfan su ne,tayo hanyar bukkan su,don har anfara yayyafin ruwa...wanda da'alama ruwan na gab da sauka ne.

Muryan yadiko taji tana cewa" shattu..."kun dawo wurin kiwon ne...!!!
Murmushi umma tayi ha'di da cewa" ehhh yadikko...dawowan mu kenan.

"Yadikko ne tace" dejama ta shige buka kenan...tohh kar dai kuman ta gobe da lumo...
Woto tanan nufin gobe daxuwa kasuwa....
"Tohhh yadiko,ae ko gobe da asuba xamu fita...don mu isah cikin garin da wuri...

Allah yakaimu goben.
Umnah tace'ha'di da ko'karin nufahn bukka.

Nan yadiko tace"Ameen,sannan kuma ki shaidama deejama fitanmu xuwa lumo da wuri da gobe...kar ta6ata mana lokaci da wannan surutun nata...
Murmushi ummah tayi inda tace"yadikko kenan,yau keda kanki kk fa'dan surutun dijahman kuma!!!hmmm ayau kuma???

Jin maganan umma yasa yadikko shigewa bukka tana dariya...

Ummah ma shiga nata bukkan tayi,imda ta cidda dijah...kwance kan tabarman kaba...




*Cikin garin gombe...*

Wani minister ne naga mutane da 'yan jaridu sun rufe shi,inda kowa yakeson yasamu yayi magana dashi....
Sauran mutane kuma najiyo suna mae kirari dacewa..." ALH. Mohammad maccido...macccidon Alhairy...don kirarin dasuke masa kenan.
"Wata ce daga cikin 'yan jaridun tayi saurin kae masa tambaya,ta hanyar cewa" ranka yada'de don Allah xumu iyah sanin dalilinka,na xama babu mata, kuma babu 'ya ko 'da a wannan matsayinka da kake kai a yanzu na minister of petrolium????





Bari nabar ku haka naga irin taku Comment din...




*TO BE CONTINUED....*



*#SHARE TO ANOTHER GROUPS...*





*MAMAN TEDDY CE....*
080881202932.
[01/02 8:30 pm] Maman teddy🧸: *MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION...πŸ“˜πŸ–ŠοΈ*

_Kungiya masu aiki da naxari da ilimi..

πŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈ
*DIJAMAH 'YAR FULANI*
πŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈπŸ”οΈ

EPISODE 3&4

*Story and writting by:*
_Aysha moh'd (maman teddy...)_
facebook@mamanteddy.com
Wattpad Aysha maman teddy🧸
Mamanteddy@gmail.com



*DEDICATION*
Dedicate to you my teddy...🧸
Wannan pagen naki ne my teddy,kiyi yanda kikeso da shi...Maman teddyn ki ne...πŸ˜…


Plz hajiya inkinsan baxakimun Comment ba,tohhh don allah karki karantamun novel...
Masu Comment Allah yabar kauna😍


______________________


Alh.maccido kuwa jin wannan tambayan da 'yar jaridan tayimae,nan take yasa shi ka'duwa,inda lokaci guda ta tado masa da tsohon famin dake cikin zuciyan sa...
Kasa bata amsa yayi,don dama bae shirya basu amsan kowani tambaya ba,balle kuma wannan tambayan nata...wanda kullum da tunanin iyalin nashi yake kwana da shi yake tashi.

'Daga mata hannu yayi,alaman baya da lokacin bata amsan ta,inda nan take jami'an tsoron da ke bayan shi,wasu a gaban shi,sukayi saurin rufamai ta hanyar dakatar da 'yan jaridun...nan take kuwa 'yan jaridun suka hau...hayanin yansu ta hanyar cewa" don allah ranka ya da'de minti 'daya mukeso muyi magana da kai...
Wannan 'yar jaridan ne takuma cewa " don allah yalla6ai ka bani amsan tambayata...haka dai kowa yake jefo nashi maganan.inda ministern yakasa ce masu komai...wanda nan take excout din shi suka bu'de mai motan da xai shiga.aiko da shigan shi jami'an tsaro da sojoji da 'yan sanda sukayo bayan shi...sauran mutane kuma suka cigaba da mae kirari ta hanyar cewa" Allah yakara kwana...maccidon mu,maccidon Alkhairy....
Haka suka dinga ihu,dae irin ta matasa,don kafun yabar wurin saida yayi masu Alkhairyn da yasa ba,kuma da suke mai kirari a kan sunan...
Niko sai da nakuma maimaita sunan,ina jin jinawa,kunsan suna linxami....hmm maccidon Alkhairy... Duk wanda ko akasan shi da abu...lallai yayi Alkhairy n ne har yagaji....tohhh Allah yabamu Alkhairy....

'Bangaren ummahn dijah kuwa da shiganta bukka,ta cidda dijah,kwance akan tabarman kaba...inda tuni ta jingine sandan ta,ta fulani a gyafe...
Xama ummah tayi ha'di dacewa" miyatti allah dijahma...yau kinga mun dawo ruga,ruwan sama bae bugemu ba.
'Dagowa dijahma tayi daga kwancen da take,nan ta kara matsawa kusa da umman nata,sannan tace"ehhh ummah,yau allah ya taimakemu...
"Ummah ne tace" dijamah bari na dama maki fura da nono kisha,don nasan kina jin yunwa yanxu ko!!!
"Dijahma ne tayi saurin cewa" ehhh ummah, kaman kinsan yunwa ko nakeji...
Dariya ummah tayi inda nan tace"taya baxan san abun da dijamah na takeso ba!!!
"Dariya dijamah tayi,inda nan takuma cewa" ummah nonon da aka dafah yaune....
Ehhh dijah na...bari na dama maki yanzu...
Batare da dijamah takuma cewa"komai ba,ta cigaba da kalllon ummah,wanda take aikin dama mata furan.


Bayan ummah tagama dama mata ne,tamika mata ha'di da cewa" toh gashi dijaman umman ta.maxa kisahnye.
"Tohh umma miyatti...
Kafin ummah ta bata amsa nan takuma cewa" ummah yaushe ne xaki dafamun marori...!!!
Wato tana nufin shinkafah...
"Murmushi ummah shattu tayi" inda cikin sanyin muryanta irin na fulani tace"gobe xan dafa maki marori,kinsan gobe da fita lumo...don haka acan sai na siyo maki...inmun dawo ruga mu dafah ko!!!
Umma ta 'karke maganan cikin kafe dijamah da ido.
Nan cike da farin ciki da 'doki dijamah tace"umma da gaske gobe da lumo???
"Murmushi umma tayi" ha'di da cewa" ehhh gobe da yawo ko!!!
Nan dijahma takuma dariya ha'di da cewa"lahhh umma ae baxani yawo ba,xan tsaya na saida maki da nono...kinga masamu sha'de da yawa koh!!!
Dariya ummah tayi ha'di da cewa"ehhhmmm dijamah kenan,kicemun dai kina farin ciki xaku ha'du da binttu acan...
Bawae xamu samu shade ba(wato ku'di)
Nan dijamah ta hau dariya,ganin ummah ta gano dalilin farin cikin da takeyi....
Haka ta amshi furar ha'di dafara sha,tana kuma xuba mawa umma surutu.

__________________________

Washegari da subahi ummah ta shirya dijamah,don su fito lumo da wuri...
Inda dijamah ansha dige dige na fulani...fuskan nan yasha jan jambaki da ba'kim kwallli...
Haka suka kama hanyar lumo dake cikin garin Adamawa....
Ummah na gaba,yayin da yadikko da dijamah ke tafe suna xuban da suka saba,don yadikko biye mawa dijamah take intana surutun ta,don umma wata xuvin har dariya ma yadikkon ke bata,intana biyemawa dijamah n.

A haka suka isah,kasuwa.inda da isan su wannan kasuwa,kowa ya hau dijamah... Dijamah
..!!!
Don gaba 'daya mutanen kasuwan ba wanda baisan dijamah ba.
Yayin da kowa ke kaunarta musamman yanda take surutun ta dakowa,koda bata sanka ba...infact dijamah irin wa'inan yaran ne masu shiga ran mutane...kowa nasu ne..
Tun da ta isah ta bar wurin umman nata.inda tuni sun game da bintutu...wanda nan take suka nitse cikin firansu da suka saba.da tsokanan mutane fa'da.



A haka kafin 'karfe uku,tuni kwaryoyin nonon da suka fito dashi ya 'kare...don haka ummah ta fara niman dijahma don su 'dau hanyan komawa rugansu.
Dijamah....!!! Dijamah....
Nan ummah tahau kiran sunan dijamah, wanda dijamah dajiyo kiran umman nata, yasa tayi saurin amsawa,ha'di da nufota...don tasan rugansu xasu koma yanxu.

Kaman daga sama umma taji wata murya ta kira sunan ta da" Hajiya Aisha...
Cikin sauri umma tajuyo ha'di da kare ma mekiran sunan nata kallo...
Tabbas baxata manta da uwani ba,a rayuwanta...
Cikin sauri uwani ta nufota...ha'di da share kwallan idonta..
A hankali umma tace" uwani kece,ashe kinan na.
"Uwani ce cikin tausayama ummah tace" ehh nice,dama kina nan hajiya ta!!!kinsan halin da ko.....
Saurin 'daga mata hannu umma tayi" sakamakon xuwan dijamah...
Shiru uwani tayi,inda nan ta maida kallonta ga dijamah,wanda ke raba ido kaman mae laifi...
Kama tagani sosai da mahaifin dijamahn.
Inda cikin murya can kasa tace"wannan yarinyan kine...itace khadijan dana sani!!!
Goge hawaye umma tayi,inda cike da dauriya tayi murmushi wanda tafi kuka ciwo....
Nan tace"ehhh itace dijamah...
Nan take uwani ta rungume dijamah, cike da farin ciki,inda a xuciyanta take kisima abubuwa da dama.

Horn da moton bayan su,ya hauyima uwani ne,yasata cikin sauri tasaki dijamah, ha'di da cema ummah"hajiya...a wani ruga kuke anan?
Umma ne ta tsaya kameΒ² don sam bata son,wani yasan inda take,ita da 'diyar ta ta...
Kaman daga sama taji dijamah na cewa" A RUGAR HAR'DO muke.....
Gaban umma ne ya fa'di,inda lokaci 'daya tahau tunanin abun da xatayi akan lamarin.


Nan uwani tayi saurin cewa"insha'allah my deejah xan kawo maku xiyara,nida Abban ki....

Cike da matsanan cin farin ciki dijamah tace"lahhh dama nima da baba!!!...irin na bintoto...?

Tausayim dijamah ne yakama uwani,inda nan take ta 'daga mata kai alaman ehhh,sannan tacigaba da cewa"kwanan
nan xakiga Abbanki...

Don da xaran yado kasan nan xaiji wannan kyakykyawan albishir,wanda ni kaina nasan bani kadai xan samu Alkhairy daga gareshi ba,har mada sauran mutane...wanda basu mason da xancen yana da iyali ba.....



_______________________

To be continued....✍🏻




Naji Comment dinku,ina godiya da nuna kaunaπŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”
Allah yanarmun ku....πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–








#SHERE TO ANOTHER GROUPS....





KAMAN YANDA KUKA SANI,WANNAN LITTAFIN TA KU'DI CE.....#100 MTN....
IDAN KUMA VIP NE,#200.
TRANSFER #200
TA WANNAN NUMBER...08081202932/09137392680










MAMAN TEDDY CE....🧸
[01/02 8:30 pm] Maman teddy🧸: Typing....πŸ“±






*πŸ”οΈDIJAMAH 'YAR FULANI....πŸ”οΈ*


Story and writting by:
Aysha moh'd (maman teddy...)

Wattpad mamanteddy🧸
Facebook@mamanteddy.com
Mamanteddy@gmail.com...

*__________________________*

*EPISODE 7&8*


"Umma ne tacigaba da cewa" bakowa ne mahaifin ki ba,illah jounalist Muhammad maccido...kuma 'dan asalin garin gombe ne....
A sanadiyan aikin sa ta jarida ne,allah ya ha'damu da shi,mutum mai yawan kyauta,tausayin talakawa kullum tsakanin shi da talakawa sai dai son barka...
Sanadin xuwan sa garinmu shine,yana son sanin wasu daga cikin al'adinmu na buxaye...

Don haka koda yasamu wasu daga cikin 'yan uwan mu na maliy,sai suka ce akawosa wurina.

Acewansu nice mae si
Surutu,kuma xan fa'da mai har abun da bai tambayeni ba...don ni kaina nasan alokacin nan,ni 'yar fa'di ba'a tambaye ki bane...

Haka aka taho da maccido inda nake sayarda Abuncina...a dandali.

A ranan shi kanshi sai da yagaji da surutu na ko da ake fa'da mashi...don ban barshi ya tafi ba,sai da na sayar da abunci na tasss tukunnah.

Don shima nasan inna dawo xan kara 'dora ta la'asar ne...

Tun daga wannan rana kullum mahaifin ki,wanda mukai mai lakani da suna maccido sae yazo wurina a dandali...inda nikuma nayi ta koromai jawabin rayuwan mu ta buxaye...dakuma yanda ba 'dauki karatun boko da wani mahimmanci ba...sosae Yakejinn da'din yanda nake bashi labarin mu...inda nikuma bawai saboda wani abu bane nake fa'da mashi,illah saboda ganin ana haskoni a cikin television...a haka sha'kuwa ta fara shiga tsakanina da muhammad maccido...

Inda daga baya soyayya ta shiga tsakanin mu da shi...
Sosai muke son juna,inda ni dai kawai son shi nake.amma nasan ba aurena muhammad xaiyi ba,duda irin son dayake nunamun...
Ammma sam ban kawo wai muhammad maccido da gaske yakeyi xai aureni ba...dakuma
Saboda nasan halin 'yan nijeria,insunxo kasarmu haka xakaga suyita cewa"suna san yara,amma duk yaudara ce.
Don daxaran sun tafi 'kasar su,shikenan sun manta da sun ta6a son wata buxuwa...tohhh da wannan yasa ban samawa raina auren muhammad maccido ba...musamman shima,wanda ko a 'kasan nasu ansan da xaman sa.


Ana gobe xai koma 'kasan su nijeriya ne,duk nadamu don nasan shikenan rabuwan mu taxo tsakanina da shi,amma damamaki sai naji yana cewa"inya koma gida,nan da sati xai turo iyayen sa akan maganan auren mu...

Hmm wannan rana nayi matu'kar farin ciki,wanda rabon da inyi irinta ni kaina na manta...

A haka mukai sallama da shi,inda da nadawo gida ne abun duniya ya dameni,don nasan da wuya su baba na su amince...

Musamman dana tuna da yaya ta,munawwarba yanda ta auri wani sojah a najeriya... wanda turosu akayi nan kasan mu,amma tun da akayi mata auren nan da shi,bamajin ko labarin ta...
Kuma ba bawai mara hali ta aura ba,don Lokacin da tayi aure da mukaje 'yan kauye muka xama...amma tun da tayi aure so daya ta ta6a xuwa garinmu,wanda alokacin dana ganta ni kaina ban gane taba saboda yanda ta chanja,ta dawo kaman baturiya abin ka da farar fata...daka ganta kasan bata cikin wahala...amma halinta bana 'dafan iyaye ba ne sam.
Tun da taxo sau dayan nan bata ',kara dawowa ba har wannan lokaci,wanda koda ta haifi 'dan ta na farko,sai dai mukaji labari,don bata fada ma kowa ba...
Rayuwanta yakoma irin ta turawa xiryan,don tsakanin ta da kowa sai dai ido...idon ma baya ganin ta.

Kuma munawwarah tun asalin ta bata damu da karatun mahammadiya ba,amma na boko kuwa itace sahun gaba,dun haka da tasamu gidan miji ta cigaba da karatun ta,duda ban mae takaranta ba.

Wannan dalilin yasani kasa mawa su guggo magana...
A haka har lokacin da muhammad maccido yafa'damun xai turo iyayen sa yayi,wanda aranan da yace"bai karya alkawari ba...yako turo iyayen sa.dattijon arxiki.

Don sam basununa kyama a garemu ba...
Sunan baba na baisan da maganan ba ne,amma sam bai nuna masu bai sani ba.. Kuma haka ya kar6esu cikin mutuncin mu na 'yan maliy...

Koda yaji maganan su,da abun dake tafe dasu,bakaramun farin ciki baba yayi ba.
Sai dai da suka nimi a tsaida magana ne yace"masu yanaso sunyi hakuri yaji ta bakin yarinyan tukkunnah...

Batare da damuwa ba,sukayi ma baba na sallama,akan cewa xasu dawo bayan mako guda.

Inda bayan tafiyan su ne,baba yasameni akan nasan da maganan muhammad maccido???

Ba tare da wani abu ba nace" masa ehhh...tunda baba yaji haka yasan na amince da muhammad maccido kenan.

Don haka guggo da baba sukasamun albarka sosai,kuma nayi matukar mamaki akan amincewan nasu...don ban kawo ba.

A kwana a tashi satin da'aka tsayar ta dawowan iyayen muhammad maccido yayi,kuma a wannan rana suka dawo...wanda ba'a 6ata lokaci ba suka tsayar da auren mu bayan watanni biyu masu xuwa...

Tun daga wannan rana soyayyar maccido yasamu wuri ya'kara xama a cikin xuciyata...wanda haka muka 'kara sabawa da kuma son juna fiye dana baya...

Guggo har mamakin da yanda kullum maccido yake xuwa hanyar kasarmu take,inda haka yakuma kwantar mata da hankali sosai...xullumin da takeyi akan auran namu ya ragu.

Don ayanzu tasan maccido ba'karamun kauna ta yakeyi ba...gakuma yanda yanda ya 'dauki guggo da baba...abun sai dai sam barka...

A kwana a tashi ba wuya gai rai,kuma mai nisan kwana...don auren mu yanxu tini ya matso... Don yanzu auren mu saura kwana uku kenan
..

Guggo tana ta zuba ido ko xataga xuwan munawwarah,amma shiru babu itah babu labarinta...wanda a haka har ranan 'daurin auren mu yaxo....ranan da baxan ta6a manta shi a rayuwata ba...a wannan rana ne,dubban mutane kuma manya tsakanin nijeriya da agadas suka shaida daurin aurena da maccido... Inda kowa kagani a wurin fatan Alkhairy yake....

Bayan kuma 'daurin aure ne,dangin maccido suka xo akan yanxu a lokacin xasu wuce dani xuwa nijeriya...

Nayi kuka sosai da naga a ranan shikenan na rabu da baba na da guggo... Inda guggo ke tamin nasihohi masu ratsa zuciya...
A haka muka biyo jirgi har cikin garin gombe,inda da saukanmu garin dangina suka ce baxa'a wuce dani gidana ba sai anfara kaini wajen surukata,wato mahaifiyan muhammad maccido... Kuma itace kaka a wurun ki...




____________________________

Koda muka isa gidan su muhammad ba'karamun mamakin gidan mukayi ba...don a wannan lokaci in akacemana gidan shugaban 'kasane tabbas ba xamu musaba...dan gidane nagani kuma na fa'da,girman sa kuwa nayi maki yanda xaki gane tafi rugar har'do baki 'daya....

Gaba 'dayan mu muka xama 'yan 'kauye,kauyen ma irin wanda suka fito daga daji,badaga cikin mutane ba...

A haka wasu ma'aikatan gidan suka yimana iso har cikin tankasheshen falon hajiya babba...inda anxuba kayan alatu kaman ba'asan ku'din suba,don dukiyan da'aka xuba a falon bakin bama xai iyah fa'da ba.don masalta maku sai yasa na 6ata shafuffuka ban gama ba...

Wasu daga cikin dangin nasa kuwa ban da ya mutsi babu abun da suke bin mu dashi,yanda kasan basuga mutane ba.wasu ko daga cikin su nan take suka kar6emu hannu bibiyo...inda sukayi mana sannu da isowa.kuma anan take suka umarci ma'aikatan hajiyan,wato masu hidimtamata akan suka wo mana kayan motsa baki...

Sannan wata dattijuwa ta shiga don tasanar da hajiya babba isowar mu gareta...

Haka ma'aikatan ko suka dinga kawo mana kayan ciyeΒ² wanda sai da suka cika gabanmu tam sannan suka fara kawo mana gaisuwa cike da girmamawa.

Cikin wannan ma'akatan gidan kuwa harda uwani...wanda muka ha'du da itah a lumo...

Toh kunsan abunka ga 'yan maliey babu dukiya ammma kuma akwai girman kai,dajan ajin kansu.don haka babu wanda ta kalla abun da aka kawo mana...

Niko maman teddy nece tohhhπŸ€”'yan maliey kenen babu dukiya sai girman kaiπŸ˜‡πŸ€ͺ

Hmm du haka muke,amma ban ga kaman hassenart bamalli ba,marubuciyan RUYUWAR AFRIDAH hmm itace tabiyo su xiryan bata yarda da raini baπŸ˜…πŸ€ͺ,amma tana dason wanda yasan darajartaπŸ˜‡,kuma badai isah da ixxah ba🀨😎,niko nace"mallawan maliey kenen....tun fil'axim akan haka aka sanku....πŸ˜πŸ˜…
Hmmm yohhh niko nace"tohh ni maman teddy ko yanake ohoπŸ€”

Kune dai kukasanni,don haka basai nayi sharhi baπŸ€—

Kar dai ku manta maman teddyn kuce....πŸ˜…πŸ˜

Haka su ummah shattu suka dunga xama,amma hajiya babba bata da alaman fitowa...don su basu san wainan da ake toyawa ba,don hajiya babba nacan ana fama daitah akan tafito wajenmu,amma sam ta'ki futowa,acewanta ita sam baxata ha'da xuri'a da bugaje ba.

Ganin haka yasa wannan dattijuwan fitowa daga 6arayin hajiya,inda take shaida mana cewa"hajiya babba batajin da'di,kuma kuma ta samu bacci ne...nan ta karke maganan dacewa"amma nan da gobe dakanmu xamu xo mukawota wurin hajiyan...

Godiya su innata sukayi,inda haka muka mi'ke ha'di da nufowa gidana...

Sosai muka yaba da tsarin gidan,dakuma girman sa,don ba'karamun mamaki mukayi daganin irin wannan gida ba.
Ni kaina ban kawo cewa"maccido nada wannan mahaukacin dukiya ba...

Tun daga wannan rana,muke xaune cikin lafiya nida mahaifinki...sosai yake nuna mun so da kulawa,inda ya samun ma'akata masu yawan da xasu ringa'ka mun hidima...
A cikin su kuwa harda uwani,wanda ya daukota daga gidan hajiya babba.

Sosai muke zaman lafiya da ma'aikatan gidana...don ni macace mai yawan surutu da barkwanci...don haka suke tsananin kaunata...

________________________________

Sati na biyu da aure,maccido yace mun xai kaini na gaida hajiya,kuma acan xan mata wuni,in yadawo wurin aikin sa

1 / 13