Maman Walid

Author :  ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category :  Love

Chapter   7 / 28

18K to 21K   out of 81.9K words

Wani irin rigima ne ya kaure tun a Gombe har zuwa Lagos, ganin cewa idan ya bar kasar zasu kara dagula al'amurra yasa shi hakura yayi facing matsalarshi, amma fir suka ki amincewa ya gaya musu iya kar gaskiya shi bayan sonta, amma suka kafe sai dai idan zai dauki asara biyu ya hakura da shugabanci CEO ko kuma ya auri Badriyyah, domin haka ne kawai zai bashi damar zama a wuri guda. A wannan takin duk me son zaman lafiyarshi kai tsaye ya bashi zaɓi, shi kuwa da yake ya wuce tunanin su a lissafi a take ya ce musu, a raba kamfanin su dauki nasu kason ai idan sun san wata basu san wata ba, ganin yadda ya tsaya akan maganar sai dai a raba kamfanin. Da ya gama hada musu wuta tunda yasan shine karfin kamfanin, sannan su kuma suna nuna miishi, sun fi shi sanin kan Kakarsu sai ya tattara ya bar kamfanin ya kyale su tare da tura musu sakon ya ajiye musu CEO ɗinsu, . musamman tuhumar da Alhaji ELYakub Kumo ya mishi na baya son zaman lafiya da kuma rashin kunya wa yaj uwan Babanshi. Shi kuwa ya tattara kome ya bar musu, bai yi gaggawar cire abubuwan da ya san nashi ne ba, ya kyale su da fari suma sun ji dadi akan ya bar musu kamfanin amma daga baya sai suka gane cewa ai ba barin kamfanin bane matsala koda yau ya bar kamfanin zasu yi farin ciki, amma masu hannun jari a kamfanin ne suka fara bibiyar lamarin sai gashi sun mara mishi baya da cewa tunda baya kamfanin gara zare hannun jarinsu, bashi suka samu ba, Uncle Auta ne, amma hankalinsu yayi mugun tashi, gashi ya kashe wayarshi ba halin ayi reaching dinsa, duk ta yadda aza a same shi babu hanyar.

Alhaji ELYakub Kumo yayi shiru yana sauraren Ubaidullah, ya cigaba da cewa. "Idan har kuka ce sai yayi abinda ake so ba zaku taba samun kwanciyar hankali ba,sannan Bilal shine karfin kamfanin nan, baya nan amma kuma ya tsayawa kamfanin, yana nan kamfanin ta habbaka. Ku kyale shi da abinda yake so, ku bar shi ya so abinda yake so, yana son yarinyar kuma zai iya rabuwa da kowa akanta, idan kuka ce lallai sai mun bukaci ya auri wata xai aure ta amma da alamar zata rayu cikin bakin ciki don Allah ku janye ni kuma xan tabbatar da ya samu yarinyar, ta kauna ce shi." Kasa da kai Alhaji ELYakub Kumo yayi uaja jin wani irin yanayi. "Me zaka yi?" "Zan shiga maganar ne domin na samar mishi kaunarta ne." "Na baka nan da wata uku idan baka samar da alaka mai karfi da kuma shaida ba. Wata uku na cika zan daura mishi aure da Badriyyah ya dade bai bar kasar ba."

Sun tattauna sosai akan Turaki domin kuwa, izuwa yanzu kowa ganin bakin turaki yake Uncle Auta ma ya sha zuciya don fushi yake da shi, shima kuma fushi yake da kowa, ganin da gaske kowani bangaren fushi suke.

***

Lubnah

Wannan tashin hankalin na shiga bayan san sallame ni a cikin sati Ya Ado ya ce a dawo da ni, dama bai yi niyyar na bar Lagos, lokacin da muka iso kuwa kamar ya goya ni, duk na zube kamar ba ni ba asalin rama nayi wanda ya kara fitar da yanayin yan gidanmu. Dama tsawo ne damu ba jiki ba, sai gashi nan na rame sai yanci na koma kamar yar Somalia, bana magana sosai. Sai da na kwashe sati biyu a gidan Ya Ado, sannan ranar Monday ya zagayo na shirya office.

[12/11/2025, 3:53 PM] Maman Walid: 10

Lokacin da na isa na ga motarshi, cikin sanyi jiki na wuce office na gaida mutanen da muke mutunci, Sarah ta ce min. "Irin wannan hutun!" Murmushi nayi na wuce ina faɗin. "Bai ishe ni ba, ko zaku kara tura ni." Murmushi tayi tana faɗin. "Barka da dawowa, dai." Daga haka na wuce a hanya na ga Badr da Airah. Dauke kai nayi, na shiga elevator sai gasu nan, ban kalle su ba. "Ban da son zuciya irin na wasu karuwai taya mutumin da be taɓa auren budurwa ba kina bazarawa ki ce zaki makalewa saurayi don bai yi aure da wuri ba." Ni dai ban ce uffan ba tunda basu kama sunana ba. "Ki bar bata yawun bakinki Please! Kin ga zoben hannuna shi ya saka min na Engagement dinmu." Ta nuna yatsarta, gabana ne yayi ta faduwa har muka isa floor din muka fita ban kalle su ba, na wuce office din na sai dai kuma abin mamaki babu al'amarin nawa ne. Office dinsa na nufa, ina shiga yana fitowa shida Ubaid. "Good Morning sir!" "Morning!" Ya fada yana mai wuce ni, "Hmm Sir office din na ga kaman!" "Ki koma second floor!" "Ok! " Daga haka na bi bayansu ban bi elevator ba, na biyu matakala zuwa kasa, ina zuwa office din na ga ashe ni da Taj ne. Murmushi nayi na ce mishi."Taj Allah ya hada mu." Dariya yayi kuma zauna tare da fitar da aikinmu, na ji dadin zaman wuri guda da shi.

"Ubaid!" Ya kira sunan Ubaid. "Kana sonta?" Ubaid ya tambaye shi, wani irin kallon banza ya mishi ya wuce gaba. "Tow tsohon dan iska dole ka bari na biya bashin da ake bina." Tunda ya fadi haka yayi shiru,shi dai bai ga wani amfanin haka ba, amma haka ya kai zuciya nesa ya ga yadda lamarin zai kasance. Haka suka fita suka dawo bai ganta ba. Sai can a hanyar masallaci ya ganta da Taj, shi kaɗai yasan yadda yake ji kamar yayi tsalle ya tokari Taj. Amma saboda ya sayawa kanshi mutunci ya dauke kai.

***

Cikin ikon Allah da buwayansa abubuwan da ake son, Allah ya wanke ni Ya Hafiz ya fuskanci shari'ar inda bai boye dalilinsa ya sa nayi haka tsohuwar matarsa ce wato Karimah ita ce ta saka shi, shi yanzu ya fuskanci cewa yayi rashin adalci don Allah kotu ta mishi sassauci. Bana ce na shiga farin ciki ba, amma yankewa ya Hafiz wata biyu a gidan Yarin don ya karbi laifinsa kuma Baban Jama'are ya roki Abba da yake ta jinya ya ce ya yafe mishi, amma kuma ni tawa rayuwar ta samu tawaya.

Haka nayi ta tafiyar da rayuwata ina kokarin recovery, amma idan na tuna wani abun da ya faru sai na ji na kasa sukuni, yau ma da wuri na zo aikin. Sai dai Hajiya Khaulatu ta zo har kamfanin. Gabana yana faduwa na isa office dinmu.. "Lubabatu ko? Ki zo muje!" Nace mata tow, na bi bayanta har zuwa tsohon bangaren, muna zuwa wani office din da na ga bakiɗaya KUMO FAMILY ne, lokacin da na shiga sai jikina ya fara rawa kai na a sunkuye ina kallon kasa. "Gata nan gara ku gaya mata tun wuri." "Kin san anyi baikon Turaki da Badr?" Kaina yana kasa ban iya basu amsa, "baki ji bane?" "Na ji!" "Ok me yasa kike bibiyarshi?" D'ago kai nayi na ce musu. "Ni babu abinda ya hada ni da shi!" "Karya take yi, Momma tana bibiyarshi!" Inji Airah, kaina a sunkuye ina jin wani irin yanayi. A hankali suka yi ta cin mutuncina, tare da gaya min magana har da kirana daddiro wacce ta kaso aurenta, kai magana mara daɗi da mai daɗi yau na ji shi har da cewa. Talauci ya sa Yayana ya nima min aikin a kamfanin. Ban san wanda ya gaya mishi ba, sai gashi su uku shi kaina a sunkuye ya shigo. "Me yayi kuke cin mutunta? Me tayi da zafi haka?" Shiru suka yi a hankali na ce mishi." Tambaya suke min, kuma na basu amasa. Ba Mr Turaki ba, wani ma da ya shafe shi ba zan kara kulawa ba, don Allah ku yi hakuri. " Daga haka na fita a office, duk yadda yaso nayi magana shi, amma naki. Abin bai kara bashi mamaki ba sai da na gama abinda nake na isa office din na kai mishi kome da kome, da zan fita Ubaidullah ya ce min. "Mrs Jama'are ki yi hakuri!" Dariya nayi na ce mishi. "La ba kome wallahi." Na fita.

Akwai wani abu da Ubangiji ya shirya shi yasa ya fito da wannan lamarin yan uwansa da ita yarinyar sun matsa min, duk da bama tare kamar da amma a yanzu na fahimci akwai wani abu da yake tsakaninmu me karfin gaske wnada ya sa ni da shi ko daya bai ga daya ba zai jira ya ga wucewar daya. A yanzu haka ko motarshi ce ban gani ba sai naji abin a tattare da ni.

Wata guda da dawowa daga hutun dole, tafiyar gaggawa ya kama shi zuwa Russia, ban sani ba tafiyar ta dare ce, sai da na isa office din na ga ban ga motarshi ba, a fari ban damu ba, sai a bakin Sarah nake ji yayi tafiya, wunin ranar nayi shi babu sukuni, duk da shakuwarmu tayi baya, amma kuma akwai wani irin abu da ya ratsa tsakaninmu da ni na yarda da cewa ina jin wani abu a kanshi. All day nayi shi ne bani da kuzari, sannan a gefen Ubaid idan zan tafi zai dauke ni zuwa gida. Izuwa yanzu ja fahimci wani abu girmama amintarsu da kuma yiwa juna adalci, a yan maganar da muke da Ubaidullah ya fahimci waye Mr Turaki, da kuma irin abinda yake da ra'ayinsa. Na kuma gane dalilinsa nayi yin wani abubuwan. Wani bin idan yana bani labarin dariya nake domin nafi jin nayi dariya, wani kuma nayi ta jin tausayina. Ubaid ya shiga jikina ta hanyar labarin Mr Turaki, yayinda na saki jiki da shi har ina bashi labarin sanin da nayi mishi da na gaya mishi ni sai yanzu nake iya kallonshi ma, dariya yayi ta min ya ce min. "Shi yasa kika ce yana da zubin Gardawa ko?" Dariya nima nayi nace mishi. "Ka bar rigima tayi barci!" "Eh kai amma ai Turaki ko lokacin muna matasa kaf Riyad babu na biyunea domin dan gayu ne." "Ai fa na ga yana son gayu kamar mace!" "Kuma gashi nan dai."

Ashe wannan dan alakar har nan kaiwa matar Ubaid, ta tashi hankalinta ta hana kanta sakat da rikici da rashin son zaman lafiya, rigimarsu har da yaji a lokacin da Jasminah take gaya min naji ba dad'i don haka da ya zo ya ce zai kai ni gida na ce mishi a'a yaje kawai. Amma ina haka suka zugo ta zuwa kamfanin, tazo tayi ta zubar da mutuncinta a gaban jama'a, a ranar na ji kamar anya babu bakin Uwa a kaina ko nace Bakin Abba baya bina? Ace duk inda na zauna sai na zaman lafiya. Korafi suna shigar a kaina, akan lallai sai na bar aikin. Uncle Auta da Ubaid suka ce basu suka dauke ni aiki ba, su jira wanda ya dauke ni. Duk da yadda suka kunno min wuta bai kai wanda aka kuna a ransa ba, tunda bakiɗaya kwanankinsa goma sha biyu sai gashi, ranar wata Laraba ya dawo. Dama tunda na je aka hana ni shiga na dawo gida ina kwance gidan na kowa Mama ta koma Bauchi ita da mijinta dama, yan gidan na kowa. Mai aikin gidan ta min magana na sauko ina da bako. Kamar ba zan fito na sai na saka hijab domin nayiwa Wasim tsiya yazo ya kai ni wurin saloon ɗin budurwanshi, ya ce min to na xata shine don daga baya naji na son fita, ai kuwa na sauko kasa ban san shi ba ne,sai da na shigo parlourn. Sai da zuciyata tayi wani irin tsayawa, na yarda soyayya gaskiya ce, domin bakiɗaya zuciya ta ce tayi wani irin tsayawa cak. Kafin ja janyo numfashina a boye na wuce kitchen na kawo mishi ruwa, ya ce min. "Bashi na zo sha ba." Kura mishi idanun nayi, kafin na dauke kai na zauna a kasar kafet din ina wasa da bakin hijab dina. "Meye alakarki da Ubaidullah?" Ya zo gabana ya zauna, murmushi nayi ina wasa da yatsuna. "Ina tambayarki kin yi min shiru?" Murmushi nayi mishi. "Wato ga mahaukaci?" Dariya nayi mishi. "Ka yi hakuri babu abinda yake tsakaninmu!" "Tow ki ji da kyau kin kashe mishi aure!" Wani irin zabura nayi tare da dafe goshina. "Ni kuma?" Mikewa yayi yana faɗin. "Idan kina son zaman lafiya ki zo ki wanke kanki!" "Babu inda zan je, tunda har ga Allah ban san kome ba! Sannan su masu ganin cewa ina tare sai su ne su yi tayi!" Wato ashe wannan maganar ya bata mishi rai ya shiga kallona wani irin kallo irin na haushi da takaici, kafin ya saka kai ya fita, har ya je bakin kofar yace min. "Kada ki sake na rigaki zuwa office!" "Ni babu inda xan kuma zuwa , ga takardan ajiye aiki nan jira na baka ka kai musu abinsu dama aikin kai ka ɗauke ni, kuma nace bana yi don ma ka sani na samu aikin koyarwa a wani makaranta!" Tinda aka fara wannan rigimar na gayawa Ya Ado shi kuma ya ce ba zai ina nima min aiki ba, domin idan yayi haka zaa ce da nufi a cikin lamarin ko zaman da yaudara. Amma ina gayawa Aunty Nuratu Kafaya ta ce nayi shawara zata nima min aiki a wani makaranta. Ai kuwa ban gayawa Ya Ado nace mata xan tafi sai CEO din mu ya dawo.

Ban san cewa haka yake da fushi ba sai da na ce mishi ya jira na dauko mishi takardan barin aikin, na zo wucewa ta gabanshi, ya fisgo ni gabanshi. "Kul ki hada ni da wani ko kishiya zaki min dole sai bayan idanuna, wallahi sai na shayar dake mamaki!" Kura mishi idanun nayi kafin na ce mishi."Ni dai na gaji ka gaya min me kake so na biya ka abinda ka min oho dama ance muna zaman dadiro ko? To gaya min inda zan zo na baka jikina idan zai wanke maka zuciya da asarar da

..." Tass naji ya kwashe ni da mari, wallhi sai da na nime jina da ganina na rasa. Na kura mishi idanun cikin wani irin kaduwa da tsoro nayi baya. "Ni zaki nunawa jikinki don ina bin ki?" Murmushi yayi ya ce min," kin yi kuskure amma zan bi yadda kike so amma ba ta wannan hanyar ba, ina da kudin da zan saye ki na gaya miki ni sayanki zan yi siyanki xan yi kuma ki saka idanun! "

"So what? Don ka saye ni ina ba kai ka halicce ni ba? Kuma marina da kai yi ban yafe ba, don bani da karfin da zan rama, da kake cewa zaka saye ni ba iska na kuma ba zaka tab'a samun nasara a kaina ba, Iyayena ba kwadayayyu ba ne, idan don kuɗinka da ka ke ganin ka saka yasa kake tunanin zaka saye ni kayi kuskure. Da shiga cikin wannan Masifaffen zuriarku gara na koma gidan tsohon Mijina duk lalacewar masa tafi kashin shanu, ka je can ku kashe kanku mutane da basu da imani. Idan don raina ne ba zan tab'a zama cikin azzalumai irinku ba, kai ma bibiyar rayuwraka ake." Cikin fushi ya bar gidan. Na fashe da kuka a wurin wallahi ba zan taɓa shiga rayuwarshi ba, ba zan shiga ba gara ma da Allah yasa na koma gidan Ya Hafiz.

Cikin wani irin gudu yake bai kallon gabansa,a garin shan wata kwana ya daki babbar mota, tuni motar shi tayi wani irin tsalle, ta fada can yayi wani irin juyi motar tayi sai da ta fadi sau uku kafin ta dungura da kanta, haka yasa mutane suka taru a kan motar aka fara ƙoƙarin ceto rayuwarshi...........

(Hegiya mai kan doya ta kahe shi)

[12/12/2025, 7:52 PM] Maman Walid: 11

Dakyar aka fitar da shi a motar aka wuce da shi asibiti, bayan na dauki wayarshi aka kira Auta, aka gaya mishi halin da ake ciki. Ai kuwa hankalinshi ya tashi. Ya gayawa Ubaid kafin wani lokaci sun isa asibitin. Hankalin sun a tashe, duk wanda yake makusancin Turaki ya zo asibitin. "Yaushe ya dawo da yayi hatsarin?" Babu wnada ya iya bawa Uncle Auta amsa domin hatsarin ya zo musu bazata, sai bayan awa biyu aka fito da shi, yana barci ba wani ciwo ya ji ba buguwa, anan suka wuni zubur har dare koda ya farka sallah yayi, anyi tambayar duniyar nan akan ya fadi dalilin hatsarin yayi shiru bai gaya musu ba, amma kuma buguwar da yayi a kanshi sai da dare yayi jini ya balle mishi ta hanci da kunne, sai a lokacin aka san ya ji babban rauni a kanshi, abin tausayi Daddah cewa take. "Zaki tafi kamar Babanki ko? Zaki tafi kamar Aisha da ya bar ni da kai, kada ki don Allah." Haka aka sauya mishi asibiti a daren zuwa babban asibitin Lagos ana isa suka shirya mishi aikin gaggawa domin idan jini ya taɓa kai zai iya samun matsala, basu fito ba sai karfe shida na safe, aka fito da shi kanshi ya kumbura.

***

Wurin karfe tara na safe, ina kwance tun jiya da ya tafi nake jin tashin hankali, ban kyauta ba sam ina jin haka a raina amma ina tsoron kiranshi kada ya gaya min magana ina tsoron kada ya ce na gama gaya mishi magana zan kira shi na ce mishi me? Wayata ce tayi ƙara na ɗauka a hankali na saka a kunnena. Idanuna a lumshe. "Lubnah baki da labarin abinda ya faru ne?" Jim nayi na san cewa zai bani labarin an kore ni ne don haka na ce mishi." Allah yasa haka shine mafi alkhairi, na gode da haduwa da kai, ka taimaka min sosai shima Ceo ba zan manta

7 / 28