Author : ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category : Love
mana!" A hankali na fara kuka, nan ne kuma ko me yake ji bai da hakurin ganin kukana, shafa kaina yayi ya ce min. "Sun min laifi amma ya wuce!" Ya fada a shake nasan bai wuce ba wallahi na san shi ciki da waje, yana da zuciya. Amma kuma yadda ya ce ya wuce sai na bari a haka, ba sai fushin ya dawo nawa ba. Yayi ta fushi da ni ya daina kula ni, a daren yaji ma ya min sai na share shi.
Gari na wayewa ya bar gidan ko karyawa bai yi ba, ni kuwa da nasan kan iskanci sai da na bari ya isa ina ga ko shiga bai yi ba na sheka mishi kira ina nishi haihuwa yazo....
[12/31/2025, 8:11 PM] Maman Walid: 33
Wani irin tambaya yake min kamar ya dirko ta wayar, I swear this man go see shege promax, wata ƙatuwar nishi na sake tare da cewa. " Wayyo Allah na, wayyo cikina wayyo bayana!" Na katse kiran hankali kwance, na cigaba da abinda nake sanin zai dawo yasa na shiga kitchen na markada fruit na zuba madara da ƙanƙara da zuma na dawo parlour na zauna tare da kunna sunnah tv, ina shan fruit dina a hankali, ina kallon yadda yake kirana kamar zai shigo ta wayar. Murmushi nayi na shafa cikina da daya hannun nace. "Dan albarka gashi nan ta sanadinka Daada zai dawo gida." Ai kuwa ban rufe baki ba zai ga karar motarshi ina ga ko parking me kyau bai yi ba ya shiga kwala min kira, har ya shigo parlourn. Kallonshi nayi na ce mishi. "Lafiya?" Musamman yadda ya ga na cika spoon zan Mai baki. Mamaki da al'ajabi ya saka shi tsayawa kamar gumki. Murmushi nayi na ce mishi. "Hala mantuwa ka yi!" Daidai fitowar Umma,tawowa yayi ya zauna yana kallon Umma ya ce mata. "Umma Lubnah tana da hankali kuwa?" Itama cikin mamaki take kallona, ganin yadda na tura baki ta ce mishi. "Hala wani shirmen tayi maka?" "Kirana tayi wai bata da lafiya na zo!" Sake baki tayi tana kallona na ce mata. "Umma kawai daga gyara kayanka sai ya zama sauke mu raba, kawai gaba yake da ni, shine na rama shima ya ji haushi kuma wallahi idan bai daina gaba da ni ba, idan ban daina cin abinci ba!" Na fashe da kuka, ganin yadda nake kuka ya ce mata. "Ni ba gaba nake da ke ba, amma." Juyawa Umma tayi ya bar mana wajen, hannuna ya rike yana faɗin. "Bana son kina shiga damuwa, yanzu kin san yadda na dawo nan kuwa?" Yadda yayi maganar idanunsa sun kad'a jajjur. "I love you so much, ko yaya kika yi kasada da rayuwraki ni ne xan wahala Please kada ki kara abinda kika yi kin ji, ba fushi nayi ba, kuma ba gaba nake da ke ba, ba don kina da wannan laluran ba wallahi idan wani ne zan dauki mataki akan shi amma ke sai na ga babu hanyar da zan yi fushi da ke! " Ua zungure min goshi. Nima na saka hannu na zungure cikin ina faɗin. "Daada ya ja maka!" Rike haɓɓa ya rike yana faɗin. " Lubnah!" Kallonshi nayi Umma da ta shigo ta ce mishi." Ka hadu da sharrin Autanci." "Ni dai zan koma idan wani abu ta taso a kira ni!" Murmushi nayi ina shafa cikina. " Ubangiji ya dawo da kai lafiya ya baka sa'a da abinda aka fita nima!" Jan kumatuna yayi yana faɗin. "Allahummah Amin!" Ya fada yana sumbatar goshina, ya mana sallama ya fita.
***
Hafiz
Yau aka yi addu'ar ukun Baba Malam, Hafiz kana ganinsa kasan daurewa yake amma bashi da lafiya, a gefe guda kuwa Goggo talatuwa ce da Goggo Uwani suka saka Baban Bauchi a gaba da bashi hakuri, Goggo talatuwa ta ce mishi. "Yayan Bauchi, don Allah ka saka baki yaron nan ya sake Jalilah tunda aka ce baya haihuwa ai ka ga babu amfanin zama da mijin da ba zaka karu da shi ba, kowa yasan Hafiz ke da matsalar rashin haihuwa." Shiru yayi har ta kai aya kafin ya ce mata. "Ina Uwani?" Ta ce mishi. "Gani nan Yayan Bauchi!" Gyara murya sannan ya ce mata. " Ina ga kamar auren nan kune kuka kulla abinku?" Shiru tayi, Baban Bauchi ya cigaba da cewa. "A lokacin har rashin kunya kuka min ko?" Duk suka sunkuyar da kai kasa. " A lokacin da na bi dokin zuciya da na rasa Yarana da Mata anyi ko ba a yi ba?" Suka yi shiru, shima shiru yayi irin wnada kana gani kasan yadda yake jin zafi da ciwo, murmushi yayi kafin ya ce musu. "Ina Hafiz din?" fita aka yi aka kira shi. Ya shigo ya zauna aka kira Jalilah itama ta zo ta zauna, "Hafiz kafin na gabatar maka da abinda yake faruwa zanso na tuna maka wasu abubuwan da muka aikata da kai ko!" Kanshi na kasa yayi zuru-zuru. "Hafiz tunda muka zauna da kai na tab'a zalintarka?" Girgiza kai yayi Abba ya sake murmushi ya ce mishi. "Yarana fa?" Girgiza kai yayi, "Alhamdulillahi, Hafiz me kayiwa Lubabatu da har yanzu hakkinta yake bibiyarka?" Kasa yayi da kai yana kallon kasa, hawaye na zuba mishi. "Shi kenan ni da kai mun zalunci Lubnah da yau bani na haife ta ba, zan ta jin ciwon abin amma da Allah ya taimaka min ta samu miji irin wanda kowani uba yake fatan yarshi ta samu naji ashe bana buƙatar naki abinda ta samu, kasan Yaron nan kafin ka aureta sai da yazo min da maganar yana sonta, naki saboda ina da yakini akanka, sai na rufe idanuna da kunnena, amma da yake shi ɗan halak ne gashi nan ya dawo har da albarkan aure a tsakaninsu. Alhamdulillahi batun lubnah bata haihuwa na ƙaryata domin kai ne da matsalar ita kan sai da mu jira haihuwarta lafiya in sha Allah."
Wani irin kallon yake yiwa Baban Bauchi, hawaye na zubo mishi shi kenan ya rasa Lubnah har abada, shi a nashi lissafin idan har Mijinta ya ga bata haihuwa zai kore ta. Amma da yake lamarin na Allah ne sai gashi nan kome ya kunce mishi.
"Jalilah har dake lokacin da aka raba auren Lubnah da Hafiz, kika yi ta cewa zata sha wahala kafin ta samu miji irin Hafiz duk naji. Gashi nan Hafiz din da kike ganin cewa zata wahala kafin ta sami kamarshi." Murmushi Abba yayi kafin ya cigaba da kallon kasa kafin ya ce musu. " Yanzu Hafiz suna son ka sake ta saboda baka haihuwa?" Girgiza kai Hafiz yayi kafin ya ce mishi. "Idan na sake ta ba zata samu wanda bai kai ni ba, ta zauna da ni a haka har ta Allah ta ishe ni, nisan da Lubnah tayi min har abada babu wata macen da zan iya samu irinta." Kasa yayi idanunsa sun yi jajjur ya d'ago yana kallon Jalilah ya sakar mata murmushi, ya ce mata. "Ina fama da laluran rashin lafiya na jima ina amsar magani, yanzu ciwon da yafi damuna shine cutar hanta. Kuma ina kyautata zaton kema kina da shi, tunda mun yi mu'amalar aure da ke!" Wato da Jalilah ta fasa ihu tare da yankar jiki ta fadi, sumarta uku kafin ta farka, tana ganin Hafiz ta fashe da mugun kuka tana yi tana buga kanta da bango tare da jin kamar ajalinta ne ya zo. "Yanzu Hafiz ka kyauta abinda ka aikata?" "Abba wannan shine karshen azalumai irinmu, Abba kasan yadda suka yi ta tura ni ga na saki Lubnah. " Hawaye yake zuba mishi, tabbas yayi asara babba da ya rasa Lubnah, haka yayi ta kuka kamar yadda yake jin ciwon da yake damunsa ya d'ago kai ya ce. "Ta bani kudinta na ci na hanata, sau uku kana biya mata Umara nace ba zata ba, na amshi kudin na kashe akan matan banza ban da Jalilah da kin Allah sau nawa kika cewa zaki Jama'are, na kama miki gida ki zauna mu ta abinda bai dace ba, nayi duk abinda kike so saboda kawai mu kunttawa Lubnah ba wani, kina daga cikin mutanen da suka bani shawarar na daura Lubnah akan kwaya, idan ba haka ba zata cika min gida da Yara ashe yau don bana haihuwa kece mutum na farko da zaki fara zama da ni, kece kika hada ni da Karimah yau kece kike guduna saboda bana haihuwa, Haba ai idan na kyale ki Allah ba zai bar ni na kare rayuwata lafiya ba, gara mu karasa abinda muka fara, a jikina me ye baki yi ba, meye ban baki ba wai har kece zaki guje ni, kin ga yanzu idan duniya tasan halin da nake ciki sai naga yadda zaki kashe auren, hmmm na san haka zai faru. "
" Allah ya isa tsakanina da kai, Azzalumi dama can halinka ne ni ce zaka yiwa sharri." Jalilah ta cigaba da zaginsa da ci mishi mutunci da cewa ko me zai yi sai ya sake ta wallahi bata zama da shi." "Goggo ko na sake ta wallahi ba zata sami me aurenta ba, duk inda zata ni zata dawowa." Ya fada yana kuka yana kallon kasa. Ya cigaba da cewa. "Ko sau daya babu wanda ya daura ni akan hanyar da ta dace akan Lubnah, kowa so yake na kuntatta mata idan na cire Goggo Alti ita ɗaya ke ce min ka rike aurenka da daraja, Abba nan suke zuga ni da cewa ai morata kake don haka ka bani auren Yarka, duk yadda kuka juyawa Lubnah baya basu gani ba, nima ban gani ba, anya zan samu rahamar Ubangiji kuwa? Har wurin Dangin Mijinta na je na lalata mata suna da kome, amma da yake Allah ya kafa aurenta ba kafi irin namu na, Na gaji zuciyata kamar zata fashe idan na tuna ni da kaina a lalata lamarina, Hajiyata tayi kokarin gini min mugun nufina.......
[1/6, 8:28 PM] Maman Walid: 34
"Amma yau gashi mugun nufina ya dawo! Na zalunci kaina da kaina, duk abinda nake yi duniya ta juya min baya, ina ji ina gani na kashen kaina da kaina. Na saka dabi'ar niman mata a gaba, bani da aiki sai yadda naso, Abba kasan na tab'a kawo mace gidana ta kama mu amma." "Ya isa haka Allah ya kyauta." Baban Bauchi ya fada yana kallon yadda Hafiz yake girzan kukan kamar yaro karami, girgixa kai yayi kafin ya ce mishi. "Me kake gani zaka sake ta?" Murmushi yayi hawaye na zuba mishi ya ce mishi. "Na sake ta saki ɗaya." Ya mike s hankali, har ya kai bakin kofar fita ya juya yana kallon Baban Bauchi ya ce mishi. "Ina son Lubabatu ina sonta, ina sonta azzalumai da ni kaina mun cutar da ita, ji nake kamar nayi ta ihu ina masifar kaunarta ina kewarta da dukkan rayuwata. Kace mata ta yafe min." Daga haka ya fita a parlourn, mamaki ya kama kowa a parlourn ga dama kamar jira ake kiris maganar da aka yi a cikin parlourn har an fara lekowa ana kallon Jalilah da take ihu abinda ya janyo hankalin masu zuwa gaisuwa kenan, gidan ya rikice da tashin hankali.
Haka Baban Bauchi ya bar can hankali a tashe, bai ga ma dan uwansa ba. Amma yasan yana cikin tashin hankali. A hankali yake kara godewa Allah da basu juyawa Lubnah baya ba, yadda suka yiwa Lubnah rashin adalci. Koda ya iso Bauchi yake gayawa su Mama da Yadiko, abin bai basu mamaki ba domin sun san haka zai faru. Ai ba yau aka fara ba, kuma ba yau za a gama ba.
Fatan ta sauka lafiya suka mata kawai domin yanzu shine babban damuwarsu ta sauka lafiya.
***
Lubnah
Tabbas yanzu na fahimci yadda kowacce mace take ji idan cikinta ya tsufa, wayyo Allah na, sai na ji kome ya tsaya min a rai. Duk yadda zan bada labarin hankali ba zai dauka ba, sai ka shiga wannan yanayin zaka fahimci mata jarumai matukar jarumai ne, domin kuwa kullum zan kwana da ciwon baya, mai cin rai amma gari yana wayewa zan nime ciwo na rasa, tunda na shiga 38 weeks nake fahimtar wannan yanayin. Yau ma ina kwance yana shiryawa. Tsayawa da saka agogon hannunsa yayi ya ajiye sannan ya dawo gabana ya zauna yana kallon yadda nake kallonshi, abu biyu yake damuna na farko haushinsa nake ji, na biyu yadda yake wani shiri alamar ko a jikinsa halin da nake ciki, ai kuwa yana riko hannuna na rufe idanuna sai ga hawaye sharr. Ba yau ya fara ganin wannan sabon halin nawa ba, amma ya dauka a matsayin yanayin ciki ne, tunda shekaranjiya kusan tsiwa nayi mishi, har da kuka ni ya bar ni na tafi Bauchi na gaji sai da Umma tayi ta fada kamar zata duke ni na yi shiru, sai kuma na fara kuka. Sosai nayi kuka fa sannan nayi barci, Umma ta ce mishi. "Kayi hakuri fa wasu matan haka suke idan cikinsu ya tsufa gani suke kamar basu da wani amfani a wurin namiji, wasu ma sai su ji basu son zama da mijin ina ga bata samu matsalar haka lokacin laulayi ba ne, shi yasa yanzu take maka haka kayi hakuri." "A'a ba kome ai na bincike kuma ina bin rubuce-rubucen masana da likitoci ba wani abu ba ne." Wannan bayanin da tayi mishi sai ya samu natsuwa har ya shirya ya fita, to yau ma haka yadda nake kuka duk sai ya damu. "Sorry!" Ya fada yana shafa hannuna. "Nasan kin gaji, ki yi hakuri zan kasance a gefenki har Allah ya baki ikon rabuwa da shi." Ya fada yana shafa kaina. "Na gaji!" Hannunshi ya kai bakina. "Na sani ba sai kin fada ba, Allah ya baki hakuri da lafiya kin ji." Gyada kai nayi ya rike min hannu nan tashi zaune. " Sannu!" Ya fada min, sannan ya fita daga dakin can sai gashi dauke da tire na abincin, wayarshi ce tayi ƙara ya kalla sai kuma ya cigaba da aikin da yake ya zuba min abinci ya nufi toilet ya dauko min brush, da toothpaste ya dawo. Sai da ya saka min na yi sannan ya bani ruwa na wanke bakin ya koma ban daki ya zubar, ya dawo ya taimaka min na ci abinci. Ina ci yana bani labarin aikin da yake gabanshi. "Amma ina ga yau zan hakura da shi sai gobe ayi meeting din!" "Da dai ka tafi;!" Jan kumatuna yayi ya ce min. "Ina kan magabata!" Bayan na gama ya kai kayan waje, ina zaune ina kallon kofar, bai tashi shigowa ba sai da wata Indonesia gown har da top ga material din roba ce tana budewa idan aka saka, ajiye min yayi ya mika min hannu, murmushi nayi na mika mishi nawa ya riko ni a hankali na sauka a gadon ina murmushi. Dan rungume ni yayi sannan ya sake ni, ya kuma riko hannuna muka wuce ban daki. Da taimakonshi nayi wanka muna fitowa ya taya ni shafa mai a jiki ba wani mai bane blue seal ne, ina gamawa ya bani comb na tace kaina, ina gamawa ya riko hannuna muka fito parlourn girgiza kai Umma ta ce. " Na shiga uku ni Aminatu! Anya ba zan koma Bauchi na bar ku da mugun abu ba." Murmushi yayi kawai ya koma dakin ya gyara sannan ya fito, dakina ya wuce ya shiga ciro kayan baby yana shiryawa, jin shiru na tashi na nufi dakin na same shi yana saka pants. "Me kake yi?" "Ina shirya kayan haihuwar ne!" "Nace maka haihuwar taxo ne?" "But ai an kusa!" Gyada kai nayi, na zauna ina nishi.
Ajiye kayan yayi yazo ta gyara min zama, ina murmushi nayi, ina son nayi magana amma ya hana ni, bayan ya gama ya riko ni zuwa parlourn. Kitchen ya shiga ya haɗa min fruit ya kawo min parlourn Umma tana kallonmu, wayarshi ce tayi ƙara ya ɗauka yana faɗin. "Barka ds safiya Abba!" Kallonshi nayi ina murmushi. Mika min wayar yayi, "Barka da safiya Abba!" "Yawwa ya kike?" "Lafiya lau!" Na fada ina jin shi, "Hafiz yana son baki hakuri amma baya samun number!" Kallon Turaki nayi gyad'a min kai yana murmushi."Abba duk abinda zai fada ya kafada maka, ina haka yafi saboda ba dad'i idan shi ya fahimci wani abu a tsakanina da Hafiz ko nice ba zan ji dadi."
"Eh haka ne shi yasa na fara kiranshi, don ina son ya san Hafiz Dan." Daga can naji Yadiko tana faɗin. "Ba dai kashe mata aure zaka yi ba? Dan uwa aiko mahaifa daya suka haɗa dole kowa ya kama gabanshi, idan don ta yafe mishi ne ta yafe a kyaleta ta ji da kanta." Daga haka muka yi sallama da shi, ina kallon yadda ya kafe ni da idanu. "Waye ne shi?" Yadda yayi maganar sai ya bani dariya, jan kumatunsa nayi na ce mishi. "Kai mana!" Na fada ina murmushi, jan kumatuna yayi haka muka cigaba da hira har na samu aka kira shi ya fita, wurin karfe daya bayan nayi sallah aka kira da wani number, ina dauka na ji muryan mace ce. Nayi mamaki bayan nayi shiru can na ce mata." Ban gane ki ba." "Eh ba daki gane ni ba, dama nima na samu number ne a wani wuri." Kashe wayar nayi don zan iya dura mata zagi, can ta kuma kirana. Dauka nayi ta ce min." Ban san ki da wulakanci ba, ki yi hakuri Jalilah ce."
" Kina lafiya? " " Lafiya lau! " Daga haka muka yi shiru bakiɗaya kowa ya rasa yadda zai ce, domin wani irin nauyin da muka yiwa juna, can ta ce min." Dama na kira na gaishe ki ne!" "Ok na gode!" Na kashe wayar, ba zan mata da