Author : ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category : Love
ihun Falilah matar Ubaid muka ji tana faɗin matukar tana numfashi ni da Mijina da muka saka Mijinta aure zamu gani. "Ta gani akanta!" Ta kara da cewa. "Idan na haifu yar halak Lubnah ke da haihuwa sai dai wasu su gani!" Murmushi yayi bayan na kalle shi. "Allah ya bamu sai dai taji haihuwa!" Haka muka tattara ta muka zuba a gefe, sannan ya min kashedi na fita harkan Matar Uncle Auta itama munafika ce, kawai sai naji na samu nutsuwa hankalina kwance ba ruwana da kowa. Babu wanda ya san ina da ciki ma, satinmu uku da dawowa aka yi bikin Badriyyah ta auri wani senator a abuja, yadda bai je ba nima ban je ba, gidanmu baya rabuwa da karatun Alqur'ani, haka yasa muke kara samun kariya daga Ubangiji.
Lokacin da cikina ya shiga wata biyar da sati biyu na cigaba da zuwa ANC anan Lagos, tare muke zuwa ya rike min jakata. Duk ya lalace a jikina, haka nake zuba kafasiti son raina. Wani ikon Allah cikin bai fito ba duk yadda muke boye shi bai fito din ba, haka matar Uncle Auta ta gama Jarabar shigen min ta kyale ni. Koda na shiga wata bakwai a lokacin muka fara sayan kayan haihuwa muna shiryawa, a lokacin yayiwa Mama magana a zo a zauna da ni, yana da tafiyar da zai yi. Abba ya ce babu wanda ya dace da zama da ni kamar Ummanmu kanwar Mama itama ba laifi akwai ibada da addini. Wannan yasa ya ce ta shirya kwananta biyu a Bauchi ta tawo lagos, muka cigaba da turawa da ita.
**
Ranar wata laraba ina kwance lokacin cikina ya shiga wata takwas cib, sai ga Maman Badriyyah da Yan uwanta, Ummana tana ɓare min ayaba ina zaune don cikin ya fara fitowa. Suka shigo kallonsu nayi fuskata da mamaki. Suma ganin cikin da ya ɗan fito ne ya basu mamaki, Maman Badriyyah ta ce min. "Ke yaushe kika yi ciki?" Kallonta nayi na ce mata. "Wannan kan ai hurumin Allah ne ba nawa ba naki ba!" Shiru tayi kafin ta ce. "Shine kika haka shi aure?" Dariya nayi na ce mata. "Shi fa mijin mace hudu ne, akan me xan hana shi aure? Ai na taso gidanmu mata biyu ne akan me zan ji a raina ni daya ce tal, ai na jima da yarda da haka don ko gidan da na fito mu biyu ne." Na fada ina cin ayaba. "Amma wannan cikin dashensa aka yi?" "Da sauki tunda na Bilal Turaki ne ba na wani ba!" Daga haka suka bar gidan kowacce magana tana da amsarta, haka suka bar gidan cike da barin kunya.
Ashe gurmi ne sosai a gabanmu domin danginsa sun ce basu yarda ba, a ina na samo ciki da zan makala mishi. Ai na bar kasar babu cikin sai yanzu da zan dawo da ciki, haka akayi ta gurmi matar Uncle Auta ta zo ina barci Ummana ta hanata shiga, kai ba sai ga yan family ba kowa yana zuwa ya ga da gaske dai ciki ne, kai karewa har Daddah Kakarshi tazo min wuni itama ta ga cikin she was so shocked, matar Ubaid hankalinta ya kasa kwanciya sai ga ta har gida, itama ina jin muryanta na ce a gaya mata nayi barci. Haka kuwa ta fita rai bai so ba. Idan nace ban yi kewar My Man nayi karya, Umma tana tsaye a kaina da addu'a da kome, da yake har Islamiyya take da shi, wani ikon Allah sai gashi tun Babyn yana cikin take bani addu'a da duk abinda xan ci ko xan fada, sauraron karatun Malamai na addini, ta hanani Gulma ko maganar mutanen da muke da matsala da su, ta hana ni saka kome a raina, idan nishadi nake ji ta kan ce min. Ki duba Islamic cartoon. Haka nake budewa nayi ta kallo har na gaji, ranar da na gaya mata zai zo ta ce min ita xata koma gidan Ya Ado na saka mata kuka na ce mata. "Wurina kika zo ba wurinsu ba, don Allah kada ki tafi!" Ganin yadda nake rigima yasa ta hakura, amma kusan tare muka yi mishi abinci, tunda muka gama na dawo parlour na zauna ta kawo ruwan zafi ta ajiye min a cikin bawo karami na saka kafana. Muna hira har zuwa wani lokaci ta dauke ta koma daki ta kara hado min wasu sinadarin kamshi ta kawo tare da cewa muje ta haɗa min ruwan nayi wanka, bayan wanda nayi haka kuwa muka je ya haɗa min ruwan nayi wanka sai kamshi mai dadi ruwan yake. Sannan ta turara min kaina, bayan ya gama ta cire min wani riga da wando, ta ce min. "Saka zaki sake shima zai ji dadin ganinki cikin kayan nan, zai samu nutsuwa ko bai yi kome ba, wani lokaci ganin mace fess yana hana namiji hango muninta, ta bani karamin mayFi na yane kaina. Sannan na fito a hankali zuwa parlour ta kara gyara gidan ta saka turare, ita kuma ta shiga dakin da ta sauka. Karfe bakwai ya shigo bayan mun Isha. Kallonshi nayi a hankali na taso ya sake jakar, ya tawo da sauri ya rungume ni.
" I miss You! " Na fada ina shakar kamshin turarensa. " Baby haka kuka kara girma? Ina Ummana?" "Sannu kai dai ka ji dadinka da fashi da makami, itama Umman ba zaka bar min ita ba!" " Tana dakinta ko?" Na gyada mishi kai, murmushi yayi ya riko hannuna muka wuce dakin tana kan abin sallah da Radio tana sauraren labarin karfe bakwai da rabi na BBC Hausa, rage karar tayi muka shiga ya zauna daga bakin kofar yace. "Umma na same ku lafiya?" Ba sai suka juya fulatanci ba, suka shiga zagina (lolz haka Baban Walid yayi min lokacin Babanmu yana raye 😱 sai su juya harshe su ta fulatanci, Allah ya mishi rahama yasa ya huta.)
Ai kuwa na tura baki zan fita ta ce min. "Zo nan Hajiya ba dake ake ba!" Ruwan addu'a na ta mika min na koma na zauna na sha, da dabino da zuma, ta ce mishi. "Anan baku sayar da rake ne?" "Akwai bari na gama sai mu fita daku bakiɗaya ku sha iska!" Haka muka fito na raka shi yayi duk wani abinda ya dace sannan na barshi yayi shagalinsa son ranshi, sannan muka fito zuwa parlourn ya ci abinci. Bayan ya gama sannan muka nufi shan iska har da Umma har gidan Ya Ado muka je ashe ta shirya zama a can sai da ta fito na ga karamin jakanta, ban san lokacin da na kama kuka ba, ja na gefe tayi ya ce min. "Mijinki ya dawo yana bukatar kulawarki, idan aka kwana biyu zuwa ranar lahadi zan dawo yanzu yana bukatar nutsuwa ne, kin ji zan dawo da in sha Allah."
Haka muka sha hira sannan muka dawo ya sayo min rake dayawa ya saka a firji, wani abu idan Babba ya hango mu yara bamu isa mi hango ba, Umma tasan ya dawo amma kada tana gidan ta hana shi sake, haka yasa ta bar gidan, ai kuwa daren ranar zuwa wayewar gari sai da muka nufi asibiti muna can aka kira shi A family house ɗinsu, ya ce zai zo. Sai da ya kawo ni gida har na kwanta ashe wai cikin zai shiga wata tara shine ya juya tunda watanin haihuwarshi zai shiga. Sai bayan tafiyarshi da na farka na daura mana light abinci, sannan ka fitar da rakena nayi ta shan a hankali.
***
Yana zaune kusan family din sun zagaye shi, Kakan yayi gyaran murya ya ce mishi." Na ji labarin Matarka tana da ciki da fatan dai ba dashe kuka yi ba? Kai taya haka ya faru bayan ance baya haihuwa?" Kallonshi yayi sannan ya sake murmushi ya ce mishi. "Ita ce bata haihuwa amma ai basu gaya maka ni bani da lafiyar da zan mata ciki ba!" "Kul Bilal!" Kakan ya daka mishi tsawa. "Ba zan ji ba, meye matsalarka da labarin da suka baka, ba kai ba duk wnada ya nime sheganta min Yarona sai na gaya mishi magana, ni ba danka ba ne baka haife ni ba, ku kyale ni nayi rayuwata bai zama dole na zauna da kowa na."
"Ina bayanki Turaki ai na gaya mata tun ranar nace ciki tun kwanciyarki ni na ga haka amma nayi shiru kuma da ya gaya min watannin cikin nayi lissafi ciki ai ko baki fada ba naki ne don haka ki kyale kowa ki rike iyalinki tafi miki kowa anan da suke niman bayanki!" Inji Daddah, dama yasan za'ayi haka ya mika musu takardan sauka a matsayinsa tare da cire hannun jarinsa, ya ce musu. "Ba yau na gama shirina ba, na zare hannun jarina nima zan gina kamfanina na kaina don Allah bana son tashin hankali da fitina, sunan Mahaifina zai saka na ambace ku a matsayin nawa bayan nan Matata da Yarona sun ishe ni, daga haka ya mike...........
(Na gode sosai Allah ya karo zumunci, ga shi nan daya kuka samu don Allah kada ka rena)
[12/30/2025, 10:24 PM] Maman Walid: 32
*KUYI HAKURI NI NA FIKU SON NA GAMA WALLAHI DOMIN NS GAJI SOSAI*
Sun matuƙar razana basu dauka zai iya rabuwa da su ba, don haka ba. Haka ya bar gidan, zuciyarshi babu nadama ko danasani domin haka da yayi yana ganin ita ce adalci da zaiwa kanshi ya nisanta kanshi da su, ba tare da yaji zafi ko haushinsu ba, lokacin da ya iso gida ina kwance a dogon kujera kallonshi nayi ya karaso dab da ni ya zauna yana kallona. "Sannu kin ji!" Gyada mishi kai nayi ina faɗin. "Kai ma haka bari na kawo maka abinci." "A'a barshi kawai!" Ya fada yana shafa kaina. "Ina sonki!" Murmushi nayi na ce mishi. "Na sani!"
"Thank you da sanin haka!" Murmushi nayi ina jin wani irin kaunarshi yana kara fuskana. D'ago kai nayi na kalle shi a hankali, kafin na ce mishi. "Me ya faru!" Kallona yayi yana murmushi ya ce min. "Ba kome!" "Wani ya ba'ta maka rai, na san halinka, na san kanka da kanka yadda kai baka isa sanin kanka ba, ranka ya b'aci ba haka ne ba." Murmushi nayi na ce mishi. "Ban san me ya b'ata maka rai ba, amma ina me baka hakuri kayi hakuri ka yi hakuri, ka yi hakuri. Idan kana cikin fushi Babynmu ma haka!" Na fada ina janyo hannunsa akan cikin. Murmushi yayi ya daura dukkan hannunsa biyu. "Ba kome!" Na san ba haka ba ne, amma kuma ganin yadda ya sake sai nayi murmushi, kwana muka yi ni dai nayi barci farkon dare zuwa can dare na farka na ga yana zaune ya jingina da allon gadon. "Baka yi barci ba ne?" Murmushi yayi ya ce min. " Ina kallon yadda kuke barci ne ke da my love!" Murmushi nayi na gyara zaman da nayi ka sauka a gadon, na wuce ban daki nayi fitsari, ashe dama ciki idan ya tsufa haka ake fama da fitsari. Ko atishawa nayi sai ya zubo min haka yasa bana iya rike fitsari ko kaɗan ne.
Satinsa daya cib da dawowa Umma ta dawo gidan, muka cigaba da zama. Ranar Laraba muka tashi da labarin rasuwar Baba Malam, mutuwar ta kaɗa ni domin ni dai rabona da na saka shi a idanuna tun lokacin rabuwarmu da Hafiz, addu'a muka mishi. Umma ma tayi waya da Mama bayan nan bata kuma magana a kai ba. Muna zaune Umma take cewa. "Ai abinda kakanku yayi zaman kuruciyarshi sai dai ace Allah ya kyauta. " Kallonta nayi na ce mata." Da fatan ba wani abin asha yyi ba? " " Kodaya yadda ya azabtar da matan kawai abin a tausaya musu ne. Allah ya musu rahama." "Amin Ya Allah!" Daga haka bata kara cewa uffan ba, abinda na fahimta shine bata son tayi magana akan mamaci ne, wanda a wannan zaman abinda ya zama ruwan dare kenan, mamaci na mutuwa imma a kafa dandalin tattaunawa akansa, ko kuma ayi ta wasu abubuwan da basu dace ba. Ban san ya aka yi ba, washi gari ya ce zai wuce Bauchi da Ya Ado, ban yi magana ba sai bayan tafiyarsu ina kitchen Umma tana parlour, muka ji dirin mota a kofar gidan, gabana ne ya fadi, jin muryan mutane dayawa yasa na fito a hankali na wuce daki na dauko katon hijab dina, daidai ana buga gidan, Umma ta buɗe musu cikin girmamawa, suka shigo parlourn fuskata a sake na tarbe su, murmushi suka yi min jikinsu a sanyayye. Na dawo parlourn na zauna ina mai gaishe su a hankali Umma ma ta gaishe su sannan ta wuce kitchen ganin xan mike ta ce min. " Zauna abinki!" Na koma ka zauna, ina kallon Alhaji ELYakub Kumo, ya ce min. "Lubabatu!" Nutsuwa na tattaro bakiɗaya na mai da shi kansa cikin girmamawa. "Mun zo bikon Mijinki ne, tuntuni muka so zuwa amma gudun kada ya bar kasar yasa muka jinkirta har sai da baya gari muka zo, shiru dattijon yayi kafin ya ce min." Mun kasance masu matukar son kanmu da zuciyarmu, amma tunda ya iya hakura da mu na san ba karamin girma kike da shi a cikin rayuwarshi ba, mun zo nan domin bashi hakuri idan da hali ki gaya mishi yayi hakuri mun yi kuskure." Kallonshi nayi rayuwa tana zuwa a yadda bamu zata ba, haka zalika imanin mu yana iya rauni ko akasin haka, abin da na fahimta Bilal shine madubin Kumo Family, idan suna son su yi kwalliya ko ado suna buƙatarshi.
Kasa nayi da kaina, kafin na ce musu. " Zan mishi magana zamu zo in sha Allah." "A'a ba sai kin wahalar da kanki ba, iya shi ma ya isa idan ma ya amince ko bai zo ba wallahi haka ma ya ishe mu." Kasa magana nayi ina ta kallon kasa, "mun yi mishi laifi ne, kuma da yayi fushi bamu ga laifinsa ba." Tabbas ba zan mata ranar ba amma yaki gaya min, tsohon ya ce min. "Bai gaya miki ba ko?" Murmushi nayi na ce mishi. "Zaman da ba na karewa ba, babu amfanin zurfaffa bincike akan abinda ruwanka a cikinsa, ya koya min sanin matsayina, ya koya min jiran ya bani labari, amma abinda ya shafe ku da shi ya koya min zama kurma kuma bebiya, sannan ya gaya min ni makauniya ce a duniyarshi, abinda ya dace na sani shi kaɗai, labarin shi kaɗai ya bukaci na ajiye mishi, bai goga muku bakar fainti ba, a kodayaushe ya ajiye kome naku a cikin zuciyarsa. Don Allah kada ku gaya min kome a bar kome kamar bai faru ba, nima ba zan taɓa gaya mishi na san kome ba, zan yi ƙoƙarin na shiga lamarin amma ba zan ce na san kome ba, zan kara girman alakarku a zuciyarshi iya wannan shine abinda nasan zan yi. "
" Allah ya miki albarka! Ya sauke ki lafiya idan har kina son haihuwa a wata ƙasa ki yi magana a kai ki can ko haihu har da katin dan kasan yaro sai a yi mishi, sannan an jima za a kawo miki masu kula da ke da abinda zaki haifa." Inji Alhaji Mudansir Kumo, akwai abinda suka mishi da ya musu tawaye, murmushi nayi na ce mishi." Na gode Abba nan ma yayi aiki kuwa zan iya ba kome, murmushi yayi yana faɗin. "A'a dai mu idan bai miki ba ma za a nima miki professional Nanny!" A raina na ce ko ba Nanny ba, anya ba wani abu ya faru ba, yadda suka yi ta cika ni da addu'a da alkhairi sai naji kaina har yana motsi. Murmushi nayi kawai har suka bar gidan ina musu godiya, bayan tafiyarsu na dawo parlourn muka zauna ni da Umma, "dangin Mijinki basu miishi wani abu ba kuwa?" "Nima ina tsammanin haka, Allah ya kyauta!" Muka kama namu sabgar.
Wunin ranar mun yi waya da shi, da yamma da suka isa gidanmu, haɗa mishi kayan haihuwa har da cewa na jira shi kada na haihu baya kusa, dariya nayi da dare ni da Umma muka kwana, karfe bakwai na safe aka kawo min abinci daga can gidansu, Umma ta karba amma bata bani ba ita kaɗai taci ta ce min. " Ba zaki ci ba, bamu san me ya haɗa su ba, wannan lokacin rayuwarki da na dan cikinki yana da muhimmanci. Don haka ko zasu Shekara dari suna turo miki da abinci ba zaki ci ba." Haka umma ta hana ni barcin, ina gani ta ci ta ba masu aikin gidan ni ta hana ni, karfe biyar muka yi tuwon alkama miyar ayoyo da stew, karfe shida suka iso gidan, nayi murna da ya dawo haka nayi ta hidima da shi, bayan isha yana parlourn yake aiki hankalina yana kan Whatsp muna magana da Aunty Hindatu, na juya ba kalle shi, kamar zan mishi magana sai nayi shiru, lokacin kwanciyarmu kuwa muka yi wanka a tare muka fito, duk hankalinsa yana kan cikina, daura kanshi yayi akai, ni kuma ina zaune na jingina bayana da allon gadon. Ina shafa kanshi na ce mishi. "Kasan duk wnada aka bawa hakuri an zalince shi ne?" Kallona yayi da kyau, a hankali nayi ta tausarshi har ya kalle ni, irin kallon tuhumar nan nace mishi "kai dai da hukuma ne za a sha azaba a hannunka. Kayi hakuri sun gane kuskurensu ka yi hakuri ka ji, Baban Baby." Zuba min idanun irin mamakin da na bashi. Tashi yayi zai fita na ce mishi. "Idan ka fita ni da Baby zamu shiga damuwa ka yi hakuri ko don albarkancin Baby ka yafe