Maman Walid

Author :  ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category :  Love

Chapter   28 / 28

81K to 81.9K   out of 81.9K words

irinta ne.

Rayuwa ta bani abubuwa dayawa, a lokacin da ban zata ba, a lokacin da naso abubuwan ban samu ba, yau dai gashi ni ce cikin Alkhairi da kwanciyar hankali.

***

Bayan shekaru biyar ..

Hafiz kuwa jinya ya sha kamar zai mutu don zai da ya kwanta a bayara can asibitin kutare da masu tarin fuka, anan ta sha jinya Jalilah da aka kashe auren guduwa tayi ta shiga bariki. Aka nime ta aka rasa, wannan abin yayiwa Goggo talatuwa ciwo, a cikin wannan yanayin Allah yayiwa Goggo Alti rasuwa, lokacin Yarana suna da shekaru uku, Nana taka da shekaru hudu da rabi, haka muka zo har Jama'are kowa ya ganni sai ya tambaya anya nice kuwa, murmushin gaske nake gani a fuskar dangina da yan uwana da suka tsaya min, mun hadu da Hafiz ganin yadda Ajmal yake tsalle a jikin Abba Amjad yana jikin Ya Umar da Nana a gefen Ya Ado, Anum a cinyar Ya Tahir abin sai ya sake shi jin kamar na shi ne Yaran, haka ya bar cikin mutane ya koma can bayan gidan yana kuka, domin idan da xai bada labari tow duk wnada ya gayawa Ya auri Lubnah ƙaryata shi za ayi, yau gata da Yaranta da Mijinta, da yau ace sun haifi ɗa da ita da yanzu ana alakanta shi da ita amma yanzu sai zai ace tsoho.

Ko wancan watan yaji labarin yadda Karima tayi mummunar hatsari tana can asibitin Mahaukata, yaran da kuwa an kwashe su ba a san inda aka kai su ba.

Kwanan mu goma sai ga Turaki a Bauchi, yazo yayi ta mita wa Mama da Yadiko. "Fisabiilillahi yaushe Lubnah zata girma ne? Sati daya na bata amma ta kara kwana uku, nasan yanzu kusan har magana sun yi da Hafiz yayi ta nunawa mutane ita as tsohuwar Matarshi."

"Kai ai baka da matsala sai na kishi, idan bai nunawa jama'a ita tsohuwar matarsa da yayi wasa ya rasa ta, ai kai abun alfahari ne ace yau ga matar da ya rasa saboda sakarcinsa." Inji Yadiko sai kuma ya shafa kai yana murmushi. "Kuma fa haka ne fa!" Haka ya gama musu iyayi, sannan ya bar gidan ya tawo gida. Na gama abincin dare, ina wanka ya shigo har ban dakin.

Zan iya cewa zane ni yayi amma zanewar kauna, haka muka fito cike da kaunar juna. Sai da muka yi sallah isha sannan muka fito parlourn muka ci abinci da yaran, sannan muka yi hira na shiga da Yaran cikin dakinsu na kwantar da mazan gado daya matan gado ɗaya. Sannan nayi musu addu'a.

Kafin na dawo dakin ibada wato dakin mijina, yana ganina ya kashe aikin da yake ya tashi ya kashe wutar dakin sannan ya muka bude wutar kaunar da take rura zukatarmu.

Washi gari.

A group naje jin Hafiz an tura shi asibitin ƙwaƙwalwa na jahar Kano wato saboda halin da yake ciki da ake tsammanin hauka ce, ni da kaina nace damuwa ce, domin domin ita kadaice zata zarar da shi, haka, dayawa cewa suke hakkina ne y kama shi, don haka ya kare da hauka.

Satinmu uku muka wuce da Yara Lagos. Don ma yaran nan gidan Ya Ado suke tafiya hutu ko can KUMO FAMILY. Hankalin zuriar KUMO ya kwanta. Ita kuwa Falilah matar Ubaid an ce wai asirin da tayi kokarin yi min ne ya koma kanta ko ma Yaya ne Allah ya kyauta. Matar Uncle Auta muna shiri da ita. Domin ko lokacin bikin yarta Dada haka muka tsaya a matsayin kawayenta ni da Amaryan Ubaid, ai kuwa sai muka hade kanmu yadda kansu yake haka.

Yarinyar daga Lagos muka kaita abuja, aka sha biki wata shida a tsakanin aka yi bikin Taj. Shekara biyu da auren Dada aka yi bikin Yar Ya ado a Bauchi a lokacin ina goyon mai sunan Ya Ado, wanda muke kiranshi Annur.

Ana gama bikin mijina ya sako ni gaba muka dawo Lagos. Wato idan Turaki yana bina a Sannu ji nake I'm melting domin ni kaɗai nasan gajiyar da nake samu a tare da Mijina, ni daya nasan waye shi. Ina son mijina ina kaunar Mijina kuma nasan shima yana sona Sosai. Dirin motar shi naji na fito ya shigo, isa gabanshi nayi na amshi jakarshi. Ina murmushi nace mishi. "Barka da dawowa ya hanya ya aiki?" Jan kumatuna yayi yana faɗin.. "Alhamdulillahi na same ki lafiya ina Yaran suke?" Murmushi nayi na yi nace mishi. "Naa tana gidan Ya Ado, Amjad yana gidan Taj, Anum da Ajmal suna can wurin Dadda dani sai auta ne a gida, janyo ni yayi yana faɗin. " Ke dai ki ji tsoron Allah ki daina kiran Auta domin wallahi akwai shida na zuwa na gaya miki goman nan dai sai kin dire min su! " Murguda mishi baki nayi nace mishi.." tunda a ruwan sha ne ai sai ka dura min. " Na shige dakin biyo ni yayi yana faɗin. " 'Aa ba a ruwa ake sha ba, amma bari na gaya miki yadda ake shan shi." Ya fada yana rungume ni ta baya na fasa ihu karami cikin jan hankali.

Alhamdulillahi anan zan tsaya da labarin Lubnah. Da yake cike da alakar Zuci soyayya da rikita rikita, Na gode sosai da wa'danda suka biyo ni a labarin nan, Ubangiji ya kara hada mu a wani labarin mai sunan......... Fatan alkhairi son so Fisabiilillahi......

28 / 28