Maman Walid

Author :  ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category :  Love

Chapter   3 / 28

6K to 9K   out of 81.9K words

Allah sarki sannu Lubnah Allah yasa Ubaid bata maka kome ba!, murmushi nayi domin na fahimci ni ce take nufin girgiza mata kai nayi, haka tayi ta jana da hira har nurse ta shigo tare da Alhaji ELYakub Kumo, kallona cikin fara'a yayi ya ce min.. "kin dawo daga Bauchi lafiya?" Gyada kai nayi, ya kalli Mr Turaki da yake nishin kafad'arshi tana ciwo. "Ai ya auna arziki, shi ya ce kada a gaya miki don ko jiya Adamu yana nan!" Kallonshi nayi cike da mamaki. To akan me zai ce kada a gaya min........

[12/8/2025, 11:21 AM] Maman Walid: 4

Ban me yake kokarin boye min ba, amma ni har ga Allah bana nufin kome da shi, kallo daya nayi mishi ban kara kallonshi ba, ba mamaki abinda ya faru a Bauchi. Na ji a raina ya kullace ni, don haka nayi ta kallon kasa, a haka suka tafi sallah juma'a amma, Kakarshi mace ta haɗa mishi ruwan zafi, ya shiga yayi wanka ajiye mishi kayan tayi muka fito waje. "Kana da kyau!"

Ta fada min murmushi nayi ban iya bata ba amsa ba. "Turaki tana da kirki, kuma yana da mutunci ita ba mutumin banza ba ne, amma haka suka yi mata sharri wai tana bin maza." Sai naji maganar tayi min wani irin girma, lokacin da ya fito sanye da Jallabiya ta maza, tayi mishi kyau. "Mamanta baturiya ce babanta Yarona na farko, tana da shekaru kusan arba'in amma taki aure, idan kin samu wani me hankali ki mata hanya tayi aure na san da iyayenta tana raye ba zasu barta tana gantali ba. " " Daddah don Allah ki bar tona min asiri" ya fada yana satar kallona, nima kallonshi nake, saboda yadda yake shafa mai a jikinshi turare a jikinshi ina ga ko mai dai ban ga ya shafa ba, sai body spray da asalin oil perfume, abin har mamaki yake bani daga can ya dauko blue seal ya shafa tare da taje kasumbarshi.

Wannan mutumin anya ba dan daudu ba ne, mutum ya bata lokaci yana kashewa jikinsa kudi kamar mace, kamar yasan me nake fada ya ce min." Kina da matsala ne da ni?" Ya fadi haka daidai Daddah ta shiga cikin dakin. Zama yayi a kujeran da yake kusa da ni. " Kina ta kallona!" Ya ajiye comb din Yana gyara link din hannun rigarshi. " Bar kallona!" Dauke idanuna nayi kamar nayi kuka na tura baki nan, ji nayi ya saka comb din ya zungure bakina. " Kada ki kara tura min wannan bakin domin ina iya hakuri da tuzarancina, amma ba zan iya hakuri da tsokanata da ake yi ba." Kamar mai kunnen maciji a hankali ya mike ya koma can tare da tura min table tap ya ce. " Oya fara aiki!" Ba musu na fara aiki har Alhaji Mudansir tare da Alhaji Abbas kumo suka shigo dakin ina aiki tare da gaya mishi abinda yake a ciki, mikewa nayi na gaishe su, a wulakance suka amsa, na koma na cigaba da aiki. Magana suke mishi amma yadda yake latsa wayarshi kamar bai san suna wurin ba ya ce min. "Bani hot tea!" "Ok sir!" Na mike na shiga haɗa mishi, Daddah ta fito daga ban daki, cikin harshen fulatanci Alhaji Mudansir ya fara faɗa. Zuwa tayi ta shafa kanshi Daddah tayi cikin kulawa ta ce mishi. "Turaki wai baki amsawa kawunanki ba?" Sai da ya gama shan kamshi kamar ba zai magana ba, kafin ya ce mata. "Ni yaushe suka min magana?" Yadda yayi maganar sai da nayi kamar an goge min zero plus, sake bude baki nayi ina kallon shi bakina cike da mamaki. "Lubnah kin ji sun gaishe ni da jiki?" Kasa magana nayi sai na kalle su, sai kuma na kalle shi, me yasa yake son involved dina cikin maganarsu? Jin nayi shiru Daddah kuwa ta rufe su da fada, yadda take shiga ba nan take fita ba, wani magana da ya fada na ga bakiɗayansu sun razana. Ban san me ya fada musu ba. Amma bakiɗayansu har Ita Daddah sai da na ga ta nime wuri ta zauna tare da fashewa da kuka. Bakiɗaya suka yi ta rantse rantse, ni kaina sai nayi na tsargu balle su. Shigowar Alhaji ELYakub da Uncle Auta, suka samu rigimar Daddah ya gaya musu dalilin kukanta, fulatanci suka juya Uncle Auta ya ce min. "Taso muje na kai ki gida." "A'a ka bari zan kaita da kaina." Cikin fada Uncle Auta ya ce mishi. "Idan baka da hankali ne ya kamata ka nima, domin wannan haukar da kake ba shi dai sauya kome ba, ka zauna nan kada ka sake ka yi wani shirme da zai cutar da rayuwarta!" Duk da ba da hausa yayi maganar ba, amma na fahimci kusan a kaina ake wannan maganar. " Muje Lubabatu!" Mikewa nayi na bishi. "Lunah!" Ya kira sunan da yake kira da shi. Juyawa nayi. " Ki kula da kanki kin ji, idan wani ya miki kallon banza ki gaya min." Gyada kai nayi na fita.

Turaki

Cire duk wani daurin da aka mishi yayi ya watsar ya zuba musu idanu. "Alhaji Mudansir ka kira karen farautarka, yanzu ko kuma wallahi birnin lagos ya mana kaɗan." "Hauka kake ne?" Inji Alhaji Abbas. " Daga turu nake karewar hauka. " Yadda ya yi ta masifa da jidali zaka rantse da Allah akan wani abu ne can ko kan hatsarin da yayi ne amma ina tsabar masifa ba kan shi ba ne, kawai akan abinda Ubaid yayi ne, sai da Alhaji ELYakub ya kira Ubaid, kai an ga tashin hankali domin kuwa Turaki ya rantse idan Ubaid ya kara shiga harkan Lubnah sai an ya batar da shi. Shi kuwa Ubaid da ya ji maganar Turakin da kuma yadda ya rantse da Allah. Ya ce mishi. "Akan mace zaka rabu da ni?" Wani kallon banza yayi mishi bai kara bashi amsa ba, abin har mamaki yake basu domin yadda ya nuna zai aikata kome tabbas.

"Son yarinyar kake yi ne? Ka dai san sakatariyarka ce?" "Eh sanin haka yasa nace ya fita harkanta, saboda sakatariya ta ce."

Jin haka yasa kowa ya sha jinin jikinsa, ya kara da cewa. " Ko Taj ban yarda ka shiga harkansa ba. " Yadda ya haɗa da Lubnah da Taj wuri guda yasa suka fara tunanin cewa ai ba mamaki kawai don suna aiki ne da shi, amma Ubaid da Alhaji ELYakub ya mishi fada ya kuma juya kan Turanci ya mishi tasss domin fadar Turakin yafi ba Ubaid din. Haka suka tafi Alhaji ELYakub ya ce mishi. "Ka fita hanyar mutanen nan, sannan ka daina saka Lubnah a cikin maganarmu, ina tsoron kada su cutar da ita ne, na san kafin su san matsayinta abubuwa sun yi nisa."

Shiru yayi yana jin hakan ya ja wayarshi ya turawa Uncle Auta, sakon Ubaid domin ya jima da goge number shi tin ranar da ya ce yana zarginsa, ai kuwa kamar bayan minti ashirin, sai ga sakon Ubaid yana faɗin. *Wato saboda Lubnah shine ba zaka gaya min da bakinka ba, sai dai ka turo a gaya min ka dai kula da kyau, domin mai son abinka yafi ka dabara* bai kula maganar ba. Bayan ya gama nan ma suka sake dasa wata drama shi da Alhaji ELYakub Kumo, yana tuhumar dattijon da boye mishi mutuwar auren Lubnah, wannan masifa na Turaki sai gyaran Allah, bakiɗaya dattijon ya rasa yadda zai yi da shi, ga rikon da yake da shi na cewa ai da gyara yaki gaya mishi mutuwar iyayensa yanzu ma ya kara laifi akan wani laifi wallahi idan ya kara boye mishi wani abu ba zai kara zuwa inda yake ba har abada. Tunda duk abinda yake yi baya gani. Rasa yadda zai yi da Turaki yayi ya zuba mishi idanun yadda yake rigima kamar wani Yaro karami.

***

Tunda Uncle Auta ya dauko ni, yake kallon titi yana murmushi ya ce min. "Ita rayuwa da kika ganta, tana da sauki amma kuma saukin bai kai yadda kowa yake gani ba. Turaki ya takurawa mutane dayawa musamman da yake zargin da saka hannun wasu a mutuwar iyayensa." Shiru yayi ya cigaba da tukin da yake yi har ya kusan isa gidan Ya Ado. " Ba ina gaya miki haka ba ne, sai dai zuwa ranar Monday zai dawo aiki akwai abu guda biyu a gabanki, ki yi kokarin ganin sun daidaita da abokinsa na yarinta, na biyu ki yi kokarin ganin ya fasa koran ma'aikata domin kuwa akwai abinda yake yawo ina ga ya ci a ce kin fahimci haka." Gyada kai nayi ya ce min. " Lubnah Turaki ya ce kina mishi kallon mutumin banza, wallahi ba mutumin banza ba ne shi, na gaya miki gaskiya shi ba mutumin banza ba ne koda wani zai miki wata magana na cewa wani abu ya faru a past dinsa, mutumin kirki ne da ni har mamaki bane yadda aka yi bai ajiye wata mace ba, Turaki nagartaccen mutum ne da Allah ya sani har cikin raina nake jin shi domin kuwa shekaru goma na bashi, amma ina jin shi kamar dan cikina. Kin san irin halinsa kuwa? Ko yana son abu bana tab'a fitowa ya ce yana son wannan abin amma kuma zai tsaya akan abinda yake so da haka muke gane girma da kaunar da yake yiwa abinda yake so, bana son na cika magana amma na san tunda Turaki ya shigo rayuwarki zai matuƙar wahala wani ya miki kallon banxa, na ina gaya miki haka ba ne don na tilastaki kula shi amma kece mutum ba farko da yake iya bata lokaci yana magana da ke, ko yayi fada akanki. Kace mutum na farko da ya tafi har inda kike, a idanun duniya ke sakatariyarsa ce amma a maganar gaskiya ke kin wuce yadda ake tunanina, baki ga office din an sauya fasalinsa shirinsa ce, yana son ya nisanta ki da kowa ya zama ke daya ce a gefensa. Idan har haka ne gare ki, wani aiki ne domin shi dai bakiɗaya rayuwarsa da ayyukansa kaɗan ce ta yan arewa sauran dabi'unsa na turawa ce, amma ba ina gaya miki haka don bai da ilimin addini ba, hmmm kada ki latsa shi domin zai iya goge miki lissafinki. Ki nuna mishi girma da ƙaddara domin ta haka ne zai fahimci ba dukkan mutanen duniya ba ne azzalumai." Kaina ne ya cika da magana na rasa ina zan fara shi kuma tashi matsalar kenan, bakiɗaya sai nake jin kamar anya ban so kaina ba? A hankali na d'ago kai tare da cewa.." Me yasa sai ni?" " Ce miki aka yi daukarki aiki yayi? Tun ranar da ya ganki a cikin masu niman aikin, ya yanke a ransa ko kina da aure ko baki da aure zai ajiye ki a gefensa. Sanin cewa zai iya hana ki sakat idan ya gano baki da aure kuma haka zai iya shafar aikinsa yasa muka ji gaya masa cewa ai baki da aure muka ko nuna masa Kumo tana da alaƙa da Yayanki. A yanzu da ya mai da kanshi dan gidanku ya samo labarin rashin aurenki. Yana da kyau ki kara tsayawa da gaske akansa. Idan kika ce bakya sonshi ba laifi amma shi kafin ya furta yana sonki shine aiki. " " Cab jam kana nufin ni ce dan je na ce ina sonshi? Ni fa babu wani maganar aure a rayuwata, ni babu wani damuwar wani namiji a gabana. Please idan har maganar soyayya ce ya ajiye abinsa, ni yanzu rayuwata da lafiyata sun fi min kome na duniya. Bukatar lafiyata nake don Allah kada a kara min wani ciwon da nake fama da shi.." na bude kofar na fita ban ko yi mishi sallama ba, shi wannan mutumin sai na mishi tijara kafin na samu kaina.

Ban kara ko kiranshi waya ba, Mama kan ta gaya min yadda aka yi hatsarin ni ban wani damu, domin na lura da yadda yake son cilla ni cikin damuwa da bani da iko da shi, ranar Sunday da yamma sai gashi da Yaran Jasminah, ai kuwa suka ga lallen hannuna wai suna so, dariya nayi musu na hada su da abubuwan da muka zo da shi har da tuwon madara da illoka, kalanda, da su halaka kwabo da mitimis. Yadda na ga yana kallona na san sakona ya isa rage shi kenan ko inda yake ban kalla ba sai da zasu tafi na raka su.. niman idanuna yake lallai mu hada idanun amma naki fir, sai na ga kamar yana da damuwa. Tun a farkon haduwar anan Lagos nake yawan ganinsa cikin damuwa, amma ban san me yasa nake ji a raina ba zan iya duk abinda Uncle auta ya ce ba. Domin nima mace ce ina da pride taya zan wulakanta kaina saboda kawai ya fahimci rayuwa?.....

[12/8/2025, 9:33 PM] Maman Walid: 5

Ranar Monday kamar ba zan fita ba, haka na shirya na nufi kamfanin don yanzu bana son ma Ya Ado ya kai ni da kaina nake tafiya, bayan na isa kamfanin na samu yana da baki da hannu Taj ya min alama na shiga na fito, ina fitowa na ga mutumin yana ta wani haɗe rai. Shi na lura duk lokacin da maza a wuri na zo yayi ta wani tsiro da mugun hali kenan. Haka na kai kaya na fito na same shi, da alamu basu gama abinda zasu yi ba ya sallame su. "Eh Taj har sun tafi?" Danne dariyar da take cinsa yayi yana kallon ogansa tare da nuna min shi da idanu, dauke kai nayi na ce mishi. "Har kun gama kenan?" Banza ya bawa ajiyata yayi tafiyarsa, ai kuwa don na kular da shi na biyewa Taj muka yi ta hira har muka isa sama, raka ni office dina Taj yayi muka shi ta hira. "Baka aikin yi ne?" Yadda yayi maganar yana bina da wani irin kallon, wanda matukar baka fahimci Yaren kallon ba zaka ga kamar wata yare ne amma tabbas kallo ce mai ratsa zuciya da hade da gangan jiki. Janye idanuna nayi saboda yadda zuciyata take wani irin pounder kamar zata fito waje, jikina har yana rawa, sake d'ago kai nayi muka yi ido huɗu, tabbas akwai Yaren da baki bata isa fitar da shi, haka zuciya bata iya fesar da shi, dole a barwa idanun aikinta domin kuwa yare ne da iya nan zaka iya fahimtar shi, janye idanuna nayi a karo na biyu, yana tsaye rike da mug, da alamar tea yake sha. Kasa aikin na tsaya nayi shiru ina wasa da yatsuna akan laptop. Sakon da ya shigo na duba shi ya turo sakon, yau kuma azumin magana yake min, ban ɗauki wayar ba na kalle shi, lumshe idanunshi yayi ya bude a karo na biyu, murmushi yayi sannan ya juya yana barin kofar na dauki wayar har hannuna yana rawa na duba me ya turo min. *Idan ba zaki iya aikin ba, zo na nuna miki wani abu* murmushi ne ya subuce min, nayi ta juya wayar. "Ina jiranki" haka ya kara turo min, mikewa nayi na fito. Na same shi a bakin elevator, yadda yake kallona sai na kasa takawa, domin kafafuna sai suka fara rawa kamar wacce ta dauko wani abu, murmushi yayi ya juya min baya a hankali na tawo har zuwa elevator, na shiga cikin na tsaya a can tare da sunkuyar da kai. Wayarshi ya dauko ya fara latse-latse har muka iso kasa kafin ya mika min wayar amsa nayi na ga Mamana, sakawa nayi a kunnena. "Mama" na gaishe ta, sannan muka fito ina wayar da ita, ina bin bayanshi har muka fito. Har muka isa wurin motarshi ashe bude motar yayi na shiga, ya rufe sannan ya koma ya bude bangarenshi muka bar kamfanin tare da barin yan gulma, suna ta leke. Sai hira nake da Mama ina bata labari, duk na shirme ne itama biye min tayi murmushi da yake dauke akan fuskarshi. Haka muka yi ta tafiya ni kaina bana ce ga inda muke ta yawo ba, mun fi awa daya da Mama a waya kafin muka yi sallama, na ajiye mishi wayar a hankali, ina mai cewa. "Kayi hakuri! Na cinye maka kati!" Bai ce min kome ba, sai ma juyowa da yayi zuwa kamfanin, amma sai da ya tsaya a wani eatry ya saya min abinci, sannan muka wuce kamfanin, lokacin da muka shiga kamfanin, Taj ne bude mishi kofar motar ya fito nima ya bude min tare da kwashe kayan abincin, muka shiga cikin kamfanin. "Ke!" D'ago kai nayi kawai matar nan ta watso min ruwa a kofi. Ji nayi ya fisgo ni, ruwan ya zuba a kasa. Kallonshi na tsaya yi baki sake. "Ki kula ba ko da yaushe ake tafiya zuciya sake ba, ki kasance kamar kunama me shiri a koda yaushe, gyada mishi nayi ina jin kamar na zura da gudu, a hankali ya sake hannuna sannan ya kalli Badr da take zare idanu, murmushi yayi ya cewa Taj. "Wuce da ita!" Muna barin wurin sai jin karar mari nayi tass. "Bana ce ba ruwanki da ita ba?" "Hamma ko kashe ni zaka yi wallahi ina sonka ba zan daina sonka ba, kuma idan baka daina fita da ita ba, gaba ruwan battery zan zuba mata." Murmushi yayi ya fisgo hannunta har waje ya ce mata."i don't like you." Fashewa da kuka tayi tana kallonshi. "Hamma don Allah ka rufa min asiri ina sonka!" Murmushi yayi ya cigaba da tafiyarshi yayi ya barta a wurin, yadda kowa yake kallona sai ta muzanta, abinka da wacce saba da kallon idan abu ya same ta ba, ta wuce bangaren office din Babanta da gudu, har tana faduwa, koda ta isa ta zube a kan gwiwarshi tana wani irin shashekar kuka da fitar

3 / 28