Maman Walid

Author :  ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category :  Love

Chapter   5 / 28

12K to 15K   out of 81.9K words

babu wanda ya amsa mata, ta cigaba da cewa. " Waye ya sani ko don abin duniyarsa take bi, tunda a wannan age na shi bai zama dole ya samu haihuwa ba, tunda an gama watsar da yaran a kwaroro da lungu da sako." "Amma baki da kunya, amma Sam baki da mutumci a kan idanuna kike fadar haka? Kin manta Uwar Turaki daga titi ta wanko ki, zuwa kamfaninta bayan ta mutu kika auri mijinta, wai matar da take da boyayyen manufa ita ce yau take fadar abinda bata da sani akai." Inji Uncle Auta da ya shigo yana kallon Hajiya Zeenatu, shiru tayi tana kallon shi, zama yayi yana fadar abinda Khamis yake sannan ya ajiye takardan koran da Turaki ya mishi. "Koranshi kuka yi kenan? Haba Mujitafa, amma dai daga Bilal har Khamis Yaranka ne me yasa kake nuna fifiko akan su, idan da Bilal ne yayi haka, shima haka zaka kyale shi ne haka? Ai nasan ba zaka tab'a kin goyan bayanshi ba, ka duba lamarin idan Khamis ya bar aikin a ina zai ci-gaba da aiki?" Shiru parlourn yayi Alhaji Abbas yana rokonsa amma bai ce kome mikewa Bilal yayi ya bar su a parlourn, idan aka ce bai ji zafin abinda aka yi ba, yayi karya kawai ya san idan ba sa'a ba ya rasata kenan. Bakiɗaya yaji tsoron Allah da tsoron rasata. Haka ya shiga motar ya wuce gida. Tare da kiran Taj ya gaya mishi ya saka idanun akan kamfanin zai dauki kwanaki bai zo ba.

Tunda ya shiga gidan ya kwanta bakiɗaya yaji kome ya tsaya mishi, sallah ya samu yayi ya sha tea kawai ya kwanta. Yana nazarin yadda zai da matsala, a yanzu duk yadda zai fito da bukatarsa na aurenta abu daya ne saboda case ɗin ne zai musu rufa-rufa, duk yadda zai yi bai san yadda zai shawo kan danginta ba........

[12/9/2025, 8:05 PM] Maman Walid: 7

Washi gari

Da wuri na shirya na nufi office, ban yarda abinda ya faru ya hana ni sakat ba, na saka a raina zan tafi aikin ko don kada a ce don tazo kaina ne, ina isowa abinda na fara aikina. Takardun na fara aikinsu sannan na turawa Lauyar kamfanin da ya saka hannu, wayata ce tayi ƙara na ɗauka number Tarik Mustapha Takai, murmushi nayi na dauka ina faɗin. "Ina ka shiga kwana biyu bana ganinka?" "Sorry Baby girl na ji abinda ya faru, na turo 50% please na san Uncle zai bada sauran." Murmushi nayi na ce mishi. "Kul ka turo min kome, wato don ni ce taku shi yasa zaku kare ni? Me yasa baku tab'a yin haka akan kowa ba?" "Baby ina zuwa in sha Allah gobe zan tawo!" "A'a ka zauna ka ji ni bani da matsalar kome zan ji da kome in sha Allah." Duk yadda ya so ya tausaya min naki, bana son wani ya tausaya min bana son na ga tausayi na a idanun mutane, haka na cigaba da aikin baya. Na gama na haɗe takardun na turawa Mr Turaki, kafin kan na fashe da kuka, tare da kifa hannu a fuskana, ban san lokacin da ka dauka ina kuka ba, ina d'ago kai muka yi ido hudu da shi, share hawayena nayi tare da cewa. "Good Morning sir, na tura maka sakon zaka duba sai kayi sign zan turawa bankin UBA an jima!" Na fada ina fitowa daga table din zan wuce ya ce min. "Am sorry!" Juyawa nayi na sake murmushi na ce mishi. "Har yaushe zaka cigaba da bani hakuri? Is not your fault, haka ƙaddara take sai ta haɗa mu boat daya kuma mu fuskanci kaddara daya!" Na wuce wurin da goran ruwa yake na dibi ruwan na wuce ban dakin da yake cikin office din ya na wanke fuskana, sannan na fito na ce mishi. "Sir ka tafi babu lokaci." Kamar wanda na tura shi ya fita, goge fuskana nayi na cigaba da laptop wanda sunan Abba da kome akan file din, ina ji kamar mafarki ne, wayata ce tayi ƙara ma duba Ya Ado ne. "Lubnah!" "Na'am!" "Don Allah ko zaki duba wani sako na tura miki ko zaki iya printing ɗinsa ki zo min da shi." "Ok Ya Ado!" Haka na shiga aikin na fara, a hankali nayi ta duba takardun har zuwa wanda na gama printing sai na ga kamar na tab'a ganin takardan da jimawa, haka nayi ta kallon takardan.

Kiran wayar Ya Ado nayi na ce mishi. "Ya Ado a ina ka samu takardun nan?" "Yanzu na saka Ibrahim da yazo daga kaduna ya turo min!" Hawaye ya zubo min. Na ce mishi. "A dakin Abba aka samu kenan?" "Eh a nan aka samu!" "Kin san shi kika ce?" "Bari xan kira ka an jima!" Ka kashe wayar na fashe da kukan da ya fi farko, nayi ta dukar table din gabana, wannan wacce irin masifa ce, nayi ruined family na bakiɗaya. Me yasa na kasance azzaluman, suka nayi a kan kujerar nayi ta buga kaina da bango domin ta haka ne zan ji sanyi a raina. Ina kuka ina ji kamar gara na mutu ko zan wuta, rike ni yayi tare da cewa. "Ya isa haka!" Janye jikina nayi na fashe da kuka bayan kifa kaina da gwuiwata na ce mishi. "Nayi ruined rayuwar family, na saka kowa cikin tashin hankali, Ni ce na aikata kome ni ce nayi kome. Don Allah ka saka a rufe ni saboda useless halina, gashi nan family suna suffering a kaina. Abba yana can cikin wani hali, Mama da Yadiko sun rasa inda zasu zauna, gaya min me nayi haka? Ni saboda ni kowa yana bakin ciki. Saboda ni, ina ji kamar na mutu ma kowa ya huta idan bana raye kowa zai yi farin ciki." Yadda nake zaune a kasa haka yake durkushe a gabana, "ki yi hakuri!" Ya fada a hankali, "Ba laifinki ba ne, ƙaddara ce idan kika ce zaki kalubalenci ƙaddararki kamar baki yarda da Allah ba ne, put Allah a gabanki kome zai zo da sauki." Dafe kaina nayi na cigaba da kuka ina jin shi, a hankali na mike tare da hada kome na tattara sannan na ce mishi. " Excuse me! " Na bar shi a durkushe, ganin yadda na fita da sauri ina kuka zaka ɗauka mutuwa aka yi min saboda kukan da nake sosai, ina ta son bin elevator amma na ga zai bata min lokaci stair na bi, shi kuma yana fitowa ya biyo elevator kusan a tare muka iso yadda na fito da sauri, "ki dakata hakan" cak na tsaya ina jiranshi, "muje na ce!" Ya fada a kausashe, haka na bi shi har wurin motar ya bude min na shiga. "Daga yau na dakatar dake zuwa aiki sai na nime ki!" "Sir don Allah kada ka hana ni zuwa Bauchi!" " Na yanke hukunci!" Kuka na saka mishi ya da ki gaban motar, wani irin tsoro ya kama ni na ce mishi."am sorry Sir!" Kunna motar yayi ya bar kamfanin yana tuki har asibitin. " Kin san Allah, idan kika yi wani abu da zai nuna kin san dalilin faruwar lamarin a will deal with you, don haka just keep follow me and my order, kin ji ko?" Wallahi yadda ya bude min idanun sai na ji bakiɗaya ya cika min idanu, kasa nayi da kai tare da gyad'a mishi, murmushi yayi mai sauti ya ce min." Good gurl koma yayi tsanani maganinsa Allah." Haka ya fito y bude min muka shiga Asibitin, yana gaba ina bayanshi ban san an sauya musu daki ba, sai da ya jagorance ni, har inda aka mai da su. Hancina na fara ja ya tsaya cak nayi karo da bayansa. " Ka yi hakuri Sir! " Juyowa yayi ya ce min. " Bana ce kada ki yi kuka ba?"gyada mishi kai nayi. Ya sake cewa. "Ki yi hakuri kin ji zan yi handle kome in sha Allah." Gyad'a kai nayi, sannan ya ɗan matsa kaɗan ya bani wuri muka cigaba da tafiya, har muka isa, yana zuwa ya mikawa Ya Ado hannu suka gaisa, tun daga nan suka fita, zama nayi na saka Mama a gaba ina ta kuka har, Mama ta gaji ta rufe ni da fada, can sai gasu nan sun dawo Ya ado ya ce min."Zo muje!" Tashi nayi na bishi, shi kuma ya zauna yana kallona, tunda na bi bayanshi wurin motarshi na isa shida su Ya Tahir, tambaya suka fara min akan takardan, na shiga bashi amsa, har zuwa yadda aka nasan takardan. Cikin wani irin damuwa na kalle shi,

"Lokacin muna tare da shi." Shiru nayi daga bayana ya ce min. "Calm down, babu abinda za ayi miki." Ya fada bayan ya karaso ya tsaya a gefena. "Sorry Barista, kada ku ɗauka na muku shishigi Please ku bita a hankali." Yana fadar haka ya wuce wurin motarshi ya shiga, wani irin fargaba yasa na rufe fuskana cikin shashekar kuka na gaya musu yadda aka yi har nasan takardan, "ban san cewa haka zai faru ba, ni dai na gaya mishi na san yadda Abba yake sign, sai ya ce min na gwada mishi, nayi mishi ya kuma je ya ga na Abba sak da irin wanda na mishi, bayan wasu lokuta sai ya kawo min takardu yadda yake azazzzalamin na saka mishi hannu wallahi ban tab'a sanin cewa irin wannan fraud zai aikata ba, don Allah nima ku yanke min hukuncin, wallahi " na fada ina wani irin kuka me cin rai. Idanun Ya Ado yayi jajjur ya ce min. " Me yasa Lubnah? Kin san yawan kuɗin da ake bin Abba kuwa?" Zuciyata ta ce ta tsinke na kalle shi a matuƙar razane, hawaye wannan na koran wannan ina girgiza kai na ce mishi." Ka rufa min asiri, wallahi ban sani ba, don Allah kada ka gaya min mutuwa zan yi." Na fada ina durkusawa a wurin, domin a rud'e nake don yadda zuciyata take tsinke kamar zata fado, zai sake magana Ya Tahir ya ce mishi. "Ya isa haka yanzu ba lokacin magana ba ne, taya abubuwan da aka rasa zai dawo ake magana." "Koma cikin asibitin muna zuwa!" Inji Ya Ado, haka na mike a hankali har na koka can nesa da su Mama ina kallonsu idan har su Mama suka san nice nayi wannan aikin har abada ba zasu daina tsanata ba, zasu jima suna jin zafina, sai yanzu na fahimci me yasa Hafiz yake cewa ba zan tab'a tsere mishi, ashe wannan abin da ya aikata ne, dafe kaina nayi da hannu bibbiyu ina jin tsanar kaina da bakin cikin wannan halin nawa zama naji an yi a gefena, da sauri na kalle shi. Mika min goran ruwa yayi yana kallon yadda nayi zuru-zuru, a hankali na d'aga goran na sha sannan na sauke ina me rufewa, kaina a kasa ina kallon goran. "Gobe su Hindatu zasu tafi, na ce su tafi da ke!" Kallonshi nayi a hankali na dauke kaina, ina kallon kasa. "Yanzu kayan sun riga da sun shiga cikin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY, har an yi musu stamp ko?" Na tambaye shi, kura min idanu yayi kafin ya ce min. "Eh!" "Nawa KUMO PROPERTIES take bin mu?" "Ba wani kudi me yawa take binku ba!" "Kamar ya?" "Eh kasancewar kayan gwanjo ne har na mai da musu kudinsu," kallonshi nayi cike da mamaki murmushi yayi ya ce min." Ba wani dayawa ba ne, kudin ruwan da yake ciki ne kawai yayi yawa, Alhamdulillahi an biya dukka." Shiru nayi ina ta wasa da yatsuna. "Yanzu ya za'ayi kenan, a cikin gidajen da kumo ta rike ko za a sakawa asalin gidanmu kudi mu saya?" Murmushi yayi ya gyara zama ya ce min," idan kika ce a baku ma dukka dukiyar me sauki ne?" Ya ciro wayarshi da sauri na kwace wayar na ce mishi." A'a! " " Yes idan har zaki yi dariya ba wani abu ba ne maza ci abinci." Akwai wani abu da na kasa ganewa akan shi, yadda ya saka Ni cin abinci. Ya Ado da Tahir suka iso. " Mr Turaki!! " Hannu ya saka a bakinshi, suka yi shiru nima kallonshi nayi ya ce min." Ci abinci! " A hankali nake ci ina kallonshi, na kasa dauke idanuna a kanshi, sannan na kasa daina cin abincin ba, a hankali na ajiye spoon din. " Na koshi!" "Good!" Ya dauki sauran yana ci, yana faɗin. "Ba kome yake bukatar ayi magana akan shi ba, je ki wurinsu Mama."

Tashi nayi na bar wurin ya ce musu, " zauna San." Ya nuna musu akan su zauna. Sai da ya ci abinci ya goge hannunsa. "Kun ga sakon kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY ko?" Gyada kai suka yi, " gobe muna da board meeting, Hindatu ta wuce da Luna Bauchi, gobe idan muka gama meeting din zan tura muku sako. Ita kuma abinda ya sa na ce ta koma can, saboda wasu abubuwan zasu faru kai ma baka tsira. " Daga haka ya mike, ya musu sallama.

Basu tab'a fuskantar crisis a kamfanin ba kamar wannan lokacin, idan har kana niman dan kasada, Turaki ya dauki wani irin kasada, abin da yake so dole sai anyi zama da duk masu hannun jari a kamfanin ayiwa Lubnah sassauci, xa a dawo mata da 75% na kayan Abba sannan zata yi aiki a kamfanin na tsawon shekaru babu albashi, shine yake son ayi vote a cire aikin nata, sannan yana bukatar goyan bayan kashi hamsin da biyar na masu hannun jarin, ta haka ne zai samu goyan baya, shi kanshi kudin da zai biya kamfanin domin a sake kayan ba karamin kudi ba ne, don ma Allah ya taimaka akwai dukiyar mahaifiyarsa na wurin kakanshi, wannan ya taimaka, ya bada kusan rabi da kwata shine 75 yadda za a dawo da kayan Abba cikin ruwan sanyi. Amma koda yayi haka bai zama dole ya iya haka ba, domin sai da goyan bayan abokan kasuwancinsu. "

Don haka ya koma ya samu Jasminah da Uncle Auta da Ubaid wanda shima ya shigo cikin tafiyar, domin yasan kaf duniya babu abinda zaka yi yanzu ya burge Turaki kamar ya goya mishi baya akan Lubnah, da ya zauna yayi nazari sai ya ga babu riba, don haka ya zauna yana zaune aka fara tattaunawa, a daren suka yi ta tura sako da kiran masu hannun jari da rokon alfarma sannan suka gaya musu akwai sako su duba, kafin dangin mahaifinsa su san abin da yake faruwa mutane hudu din nan sun gama kome basu bar gidan ba sai karfe biyu na dare, kwanciya yayi a parlourn. Maganar gaskiya zuciyarshi ta gaji a yanzu fa ya dace ace ya ajiye iyalinsa na kansa ne...........

(Ku yi hakuri yau nayi baki ne)

[12/10/2025, 11:24 AM] Maman Walid: 8

"Hmmmm!" Ya furta a hankali, ai yanzu kome ya lalace, domin bai isa ya ce zai tun kari. Maganar aurenta babu shi tunda yanzu yasan duk abinda zai yi cewa za ayi don yana da alaka da abinda ya faru ne. Washi gari har da makara tun yana Sallah asuba da ya dawo madadin ya motsa jiki sai ya kara kwanciya, har sai da aka yi ta buga mishi kofar parlourn ya farka ya shirya a gurguje, a lokacin da suka isa kamfanin dayawa masu hannun jari a kamfanin sun iso shi yake da kashi sittin da biyar amma yana bukatar goyan bayansu a kowani hali, Tarik ya gani tsaye yana murmushi, ya ji dadin ganin Tarik domin shima zai bada nashi gudunmawarsa, amma kuma ta wani gefe yana bala'in shakkar kada Tarik ya kuma shige mata, gaskiya yayi farin ciki amma kuma gefe guda yana bakin cikin da zuwan Tarik domin yanzu zai dagula mata lissafin da yake ƙoƙarin daura mata, haka yayi ta bin manyan baki yana musu godiya domin bai kawo zawo bashi hadin kai har haka ba, ai kuwa daga nan suka wuce asalin conference hall din da suka shirya don baki. Haka kuwa suka hadu bakiɗaya, babban adduarsa ya ga Uncle Auta da Kakanshi, kuwa wurin minti goma da fara faron suka shigo da yan uwan Babansa, ajiyar zuciya suka sauke aka fara meeting din, cikin ikon Allah da girmamawa, ake gabatar da kowacce bayani da kuma dalilin taron, har aka zo wurin da ya kawo maganar Lubnah, shiru hall yayi da yake ba shi yake bayani ba, Taj ne. Ya cigaba da cewa. "Idan har da muna son yin gaban kanmu ne da ba zamu tara ku a nan ba zamu yi gaban kanmu amma manufar ita ce mu samu haɗin kan kowa yadda zamu fitar da sakamakon kome, sannan yarinyar bata bukatar tayi aiki a kamfanin mun dauki duk wani abun da ya dace, wannan Madadin kamfani muna niman abokan hulda su bamu damar basu 75% na abinda aka karba daga gare su, zamu biya kudin sauran kuma zamu rike izuwa reshenmu da yake garin Gombe!"

Shiru aka yi Alhaji Mudansir ya ce. "Gaskiya ban amince ba, idan har sai lallai anyi haka tow sai dai a kada kuria idan ka fimu tow shine zamu amince idan kuma baka fi mu ba, zaka hakura da tsarin jin kai ga dan kamfani sannan zata cigaba da aikinta, ai ƙaddara ce kuma tana kan kowa." Bai san me Alhaji Mudansir ya taka ba, amma kuma sai yayi zuciyarshi ta karaya, kuma abinda ya fada din sai mutane suka bashi goyan bayan haka, dakin taron ne ya samu halartar Hajiya Sameerah da Hajiya Khaulatu, sai Khamis da Badr, Mimi da sauran yan gidan kumo da suke garin lagos, suna tare da Alhaji Mudansir, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yadda suka taru kuma duk sun zauna, bakiɗaya sai ya karaya. Chairman na kamfanin wanda ya kasance Alhaji ELYakub Kumo, yana kallon

5 / 28