Author : ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category : Love
muka gama ya wanke hannu ya taya ni wanke kwanon, muka fito ina cewa. "Dauko tissue please! " Wurin cin abincin ya nufa Uncle Auta ya ce masa. " Sai ka gaya mana matarka ce ta baka abinci a baki!"
"Kai dai da baka iya romantic ba, a barwa newly couples kayansu!" Ya tawo lokacin har na shigo parlourn, yana zuwa ya mika min. Na amsa tare da goge mishi ina faɗin.. "Malam gashin baki da kasumbar nan suna bukatar gyara fa." Na faɗa kasa kasa. "Tow idan suka tafi ba sai ki gaya min ba, ai tun jiya nake bin ki, amma kika share ni."
"Ok bari mu sallami baki!" Na fada ya koma wurin mazan. "Duk wannan soyayyar kafin a haihu ne idan aka haihu shi kenan sai ya zama tarihi." Murmushi matar Uncle Auta tayi ta ce mata . "Da don haihuwa ne, da tuni ya tara goma na yara. Kauna ce dai da bata tsufa ba, sannan bana jin idan zasu cika gidan nan da Yara zai fasa wannan halin shi ba bafulatani ziryan bane kuma ba bahaushe ba ne da mace na fara haihuwa zai zuba mata yaran ta ji dasu shi ruwa biyu ne.......
[12/19/2025, 8:05 PM] Maman Walid: 23
"Mu kanmu mun yarda ƙabilar uwarsa tayi tasiri akanshi. Yadda ya iya jiranta ta dawo gare shi." Sai duk suka yi shiru, kasancewarta Babba a tsakaninmu sannan muna bata girmanta daidai gwargwado.
Tun da fadi haka bata kara magana ba, sai ta yi shiru,sai dai na fahimci wani abu a nan shine matar Ubaid kamar ban mata ba, da farko na zata matar Uncle Auta ne take min kallon gani gani amma daga bayan zuwan waɗanan matan sai ja lura da yadda Matar Ubaid take bina da idanu. Bayan tafiyarsu na gyara parlourn na tattara wanke-wanke, ya rungume ni ta baya yana me taya ni wanke -wanke. "Maza biyu da suka zo nan Alhaji Ahmed da Alhaji Mohammed, abokan kasuwancin Papa ne, Alhaji Mohammed yana Cotonou da iyalinsa, shi kuma Alhaji Ahmed yana abuja, tagwaye ne su." Gyada kai nayi na juya ina fuskarshi. "Su ma wadancan tsalla tsalla yan mata da suka zo da su dama an shirya proposal ne ban sani ba?" "Ni waye ya gaya miki an shirya haka?" "Amma ai a bakinsu naji ana cewa yana Bauchi na da rowa!" "Wallahi ni ban fadi haka ba sai dai ko su." Dan dagalgala nayi tare da sumbatar goshinsa ya saka hannu ya dauke ni cak, na sumbaci goshin sannan ya sauke ni na ce mishi. "Ina ga sai na fara saka maka abu domin na lura family dinka basu da buri da ya wuce su ga an yi min karin wata mace!"na juya na na zabga mishi mintsini. " Na gaya maka wannan shine kashedina da kai wata mace sai na fille maka kai!" " Tow ranki shi dade!" Haka ya fada yana dariya, a tare muka gama wanke kayan muka gyara kitchen din tas sannan ya riko hannuna zuwa parlourn nan ma muka gyara wannan na fito na samu yana jirana. Bude min hannu nayi na shiga da sauri ina sauke ajiyar zuciya. "Ina sonka dayawa!" " Ok bani labarin ranar kika fara sona!" Biye mishi nayi muka yi ta hira shi kuma ya zuba min idanun ina bashi labari ina dariya ko ina farin ciki.
Haka muka gina kanmu, kuma muka gina rayuwarmu. Zan iya cewa tunda na fahimci tarin alkhairin da yake tattare da mijina, tafiya ta kama shi ina hada mishi kaya ya zauna yana goge kanshi ya ce min. " Ko zaki raka ni ne?" " Ka manta ina son zuwa gidan Ya Ado ne?" Shiru yayi kafin ya ce min. " Zaki iya min alfarman na dawo sai mu tafi tare?" Kallonshi nayi sai nace mishi. " Allah ya dawo da kai lafiya." Na fada ina murmushi, bana son ta ha kamar raina bai so ba, haka na shirya mishi kayansa, har na taimaka mishi ya sa kaya amma ina son zuwa na ga yan uwana, amma yadda ya nuna baya ra'ayi na share ban kuma magana ba. Bayan na gama shirya shi ya ce min. "Me zan saya miki?" "Kome ma ina so!" Daga haka muka fito ya shiga motar, bayan tafiyarshi ne nayi baki duk da ya hana su zuwa amma Amma saboda masifa sai sun zo. Na musu iso suka shigo parlourn. Na kawo musu abinda ya dace sannan muka kara gaisawa na ga sai dariya suke yan matan idan suka kalle ni, sanin zasu iya saka ni a damuwa yasa na barsu na wuce dakina. Kiran Aunty Zakiyah ta shigo ta ce min zasu zo in sha Allah gobe ita da Yaranta.
Nayi murna sosai nace su zo da niyyar kwana yaran tunda basu gari. Ina gamawa na fito parlourn. Matar Uncle Auta ce ta shigo tana faɗin."ku wasu irin jakuna ne? Ku wasu irin jahilai ne? Kun dauka tafiyar da yayi Da badr wani abin arziki ne, shegu yan marasa kunya da mutunci." Tayi musu tas, "wai don Mijinki yayi tafiya Da badr shine zasu mai da shi babban al'amari."
"Sune da wahala na yarda da Mijina sannan ni ba mahaukaciya ba ce bana saka karfi akan kome idan ya ce zai kara aure yayi wallahi bani da case da shi sai dai duk wacce zata aure shi ni ce na bude shi a leda babu Macen da zata gaya min waye shi." Tunda na fadi haka na ga sun yi wani firgita. Murmushi nayi na ce musu. "Ni saka kishi ne, ba ji kishi ba ce. Turaki da yana da buri da ra'ayin tara mata hala da nazo a ta hudu, idan kun iya ku kama kanku idan baku iya ba, ku cigaba ni bani da energy da zan yi fada akan namiji domin mijina mijin mace daya ce, idan kuka ga kaddaran wata mace ta ratsa to in sha Allah rabo ce ta kira ta, daga yau kada na ƙara ganin kafar kowacce yar iska s gidana idan ba haka ba, between ni da lu xa a damu matsala." " Ai ki kyale su sai na gayawa Turakin!" " Akan me zaki gaya mishi, sun yi na farko yayi musu fada na biyu ya dake su da yake jakuna ne, na uku na shiga cikin lamarin, kun zo ku hada mu fada tow ta Allah ba taku ba, wallahi kun yi karya ku shirya da kyau domin Allah ya bada sai dai ku yi Hakuri sai na kona fuskar yarinya idan ta kara shigo min gida idan kuna ganin wasa ne Allah ya dawo da ku gidana zaku gane baku da hankali!" Yadda na musu tass suka fita kamar munafukai.
Wannan yasa na samu sauki amma na dan shiga rud'ani da naji labarin yana tare da Badriyyah, har dare bai kira ni ba haka na kwanta zuciyata babu dad'i, gaskiya kishi masifa ce haka nayi ta juyi har sha biyu na dare, karshe na tashi nayi sallah nafilla ina addu'a na fara jin barci haka yasa na tattara na koma gado. Kafin barci yayi gaba da ni, karfe shida na safe kiransa ne ya tashe ni don kiran sallah asuba ban ji ba, haka na tashi ina mai amsa mishi bayan mun gaisa nace mishi." Ya hanya?" Ya amsa min da " lafiya lau!" " Nayi ta jiran kiranka jiya amma baka kira ba!" Na fada a shagwab'e. " Kin san Allah kada ki d'aga min hankali, kin san yadda na bar garin nan!" Tab'e baki nayi na ce mishi."Sallah zan yi!" Na katse kiran, haka kawai sai shaidan yana min wata huxubar tsiya, haka nayi sallah na yi azkar ya kara kirana. Dauka nayi ya ce min. "Please muyi video call;" kashe kiran nayi na bude datana. Na shiga imo shi ya sauke min apps din Wai yafi sauƙin kiran idan baka kasar. Can kuwa sai ga kiranshi. Dauka nayi ina kallonshi. Haka kawai nake jin haushinsa. "Yan mata nayi miki laifi ne?" Murmushi nayi na ce mishi. "Ba kome." Sai yayi ta kallona. "Da gaske ban miki kome ba?" Girgiza kai nayi, buga kofar dakin aka yi, na ji yana cewa. "Waye?" Abinda na ji kenan. "Hamma nice badr ban dakina ruwan ya tsaya ne!" Kallona yayi na dauke kai. "Tafiyar har da ita zata ga likita ne." "Ban tambaye ka ba!" Na gaya mishi. "Ki tsaya!" "Ni kitchen zan shiga ina da baki!" Na fada ina mai mikewa zan kashe wayar ya ce min. "Ki tsaya." "Me kake bukata? Ina ga ai na sallame ka sannan ita wacce take magana ai lokacinka take bukata." Na katse kiran, ba zan kara shiga damuwa akan wani namiji ba, haka yayi ta kirana amma naki dauka asalima kashe wayar nayi na shiga aikin gidana baji ba gani, kusan da yake raina a b'ace yake aiki kawai nake har da su wnki a washing machine, bayab na gama na koma dakina na kwanta ina da miya a frij. Shi na fitar idan suka zo sai na dafa shinkafa da dodo.
Wurin karfe sha biyu Uncle Auta ya zo da Matarshi, Ni abin sai ya dame ni. " Ni fa ba fushi nayi ba, amma shi yana ganin kamar nayi fushi ne? Lallai fa ita ai yar uwarsa ce, sannan ko babu kome akwai aure a tsakaninsu akan me xan bawa kaina wahala kan namiji, ni zama da kishiya ba bako bane a wurina, idan zai kara aure wallahi ni ban isa na hana ba, shi yake ganin haka babban tashin hankali ne, na taso naga gidanmu mata biyu ne haka yasa na sakawa raina duk inda aure ya kai ni tow akwai wata ko na samu wasu, amma wallahi ni ban ji kome ba!"
"Ok me yasa kika kashe wayarki?" Murmushi nayi na ce mishi. "Nasan halinsa yanxu zai ta ƙoƙarin sai ya gamsar da ni akan yana da gaskiya, bayan ni nasan yana da gaskiya. Idan ya cika son sai ya min bayani zan iya jin behind the scenes yana yin wani abu ne, shi namiji ne ya kamata ya tsaya akan kafarshi. Ba laifi ba ne ya gaya min gaskiya amma bana son a kan kaina na yiwa Mijina kallon wanda ya kasa." " Na gamsu da maganarki amma ki kunna wayarki wallahi zai iya hana iyayenmu zaman lafiya sai ya saka su zo na gaya miki gaskiya idan kin yarda. "
Kunna wayar nayi sai ga kiran ina dauka ya ce mishi. " Yanzu nake shirin kiran Datti da Daddah! " " Da kuwa baka kyauta." Nan muka shiga hira su Uncle Auta suka bar gidan, muna gama wayar na kashe, sai ga kiran Aunty Zakiyah, wai suna kofar gida na zo an hana su shigowa, haka na fita na shigo dasu, muka zube a parlourn, muka yi ta hira a dauko musu abinci suka ci, sannan muka yi sallah La'asar bayan nan ya kira ya ce." Ya nake jin muryan Yara sun iso ne?" Nace mishi eh , daga nan suka yi sallah, zan iya cewa daga nan muka shirya dai dare Ya Ado ya zo ya dauke su, ya bar mun Takwaran Mama,har da uniform dinta na makaranta.
Na ji dadi haka na cigaba da kula da gidan, sai dai duk lokacin da muke waya sai naji muryan Badr, kusan kamar da gangan yake zama kusa da ita. Kawai sai na sakawa raina matuƙar zan ji muryanta zan kashe wayar. Shima kuma ya gane idan zai yi waya da ni, sai dai ya bar inda take. Ya ce min ganin likita take amma da na bude data na ga hotonsu ana ta sakawa a status. Ba karamin ƙoƙari nayi da na danne zuciyata, na zuba mishi idanu. Har ya dawo cikin ikon Allah ranar juma'a, suka zo gidana ta nuna min ta fita da mijina, dauke kai nayi kamar ban san me yake mun zafi ba, amma na san yadda nake ji. Tunda na tarbe shi ban kara bin ta kanshi ba, sai dare na rufe kofana. Tunda ya kaita bai dawo ba sai sha biyu saura da ya dawo ya samu kofata a buɗe. Yayi bugun duniyar nan nayi kamar ban ji ba, washi gari ban fito ba sai karfe tara, na wuce kitchen yana parlourn yana karyawa. Nayi kamar ban ganshi ba. Wallahi ba zan iya hakuri akan wannan ba, domin yadda tayi ta min iskanci tana kallona tana dariya. Yafi kome yi min zafi. Ina tsaye ina fitar fa abincin jiya da bai ci ba, ya bar min na zuba musu ruwa, shigowa yayi ya ce min. "Jiya ni daya na kwana!" Shiru nayi domin abinda yake bakina idan na fada sai ya kusan suma, haka yasa na ciza bakina sai da ya fashe. Sake bakin nayi a hankali na wuce na hado kayan tea na daura a tunkaya.. "Lubabatu nayi wani abu ne?" Murmusa mishi nayi ina faɗin. "Me ya faru?" Na tambaye shi. "Amma naga kamar kina wani abu da ban saba gani ba ne." "Ok ba mamaki kai kake ganin haka;" na fada a takaice ina nufar inda tukwane suke, na wanke na juye miyar na dumama. Sannan na wuce na dauki plat da cokali na jera abincin da kome da kome, sannan na nufi hanyar waje ya amshi tiren na koma na juye ruwan zafin, na nufi parlourn na zauna a hankali na fara ci. Da cokali ɗaya. "Ina cokalina?" Kallonshi nayi sannan na ce mishi. "Wannan abincin ba zai ishe mu ba;" "kamar ya? Naga abincina na ne na jiya." "Ai ya koma na kowa da kowa!" Na fara ci a hankali fir na hana shi. "Wai meye matsalarki ne?" "Kai ne?!" Na bashi amsa, "kai ne matsalata idan ina da wata matsala kai ne. Idan zaka auri Badriyyah lafiya lau, amma kawo min ita ko zuwa ka zauna sai sha biyun dare wallahi ba zan yarda ba, kashe nayi maka yasa na rufe kofar gobe ka kara dawowa min gidan rufe shi zanyi.;" na mike xan tafi ya dawo da ni na zauna yana murmushi, "kishi haka lunah........
[12/21/2025, 3:54 PM] Maman Walid: 24
Ya fahimci raina a fusace yake kuma a kufule nake, sai ya fara cin abincin har ya cinye yana murmushi. " Babu wata mace da zata shigo min! " " Waye ya sani ita fa virgin ce ni kuma fa?" Rike bakina yayi yana faɗin.
"Ba ruwana da Virgin ko rashinsa, ke nake so ba budurcinki ba, ke nake so ba fuskarki ba, ke naso ba wani abu ba, soyayyarki halitta ce daga Allah, zan so ki zan kaunace ki zan kuma kare ki, sannan zan hana ki kuka, zan saka ki murmushi da farin ciki, hannuna kawai zaki rike na cika wannan alƙawarin da na miki" kura mishi idanu nayi a hankali naji hawaye na zuba min zuciyana ya karaya, tsoron kada shima ya min halin Hafiz na fara kuka wiwi karshe na bar mishi parlourn zuwa dakina ina kuka. Shigowa dakin yayi ya same ni ina zaune sai kuka nake, durkusawa yayi a gabana. "Tsoron me kike ji?" Girgiza kai nayi ina shashekar kuka. " Yar uwarka ce, ni kuma bare, akwai lokacin da Alakar zuci baya tasiri sama da dangantaka. Idan ba zaka zauna da ni ba ka gaya min na tafi ka ji, don Allah kayi hakuri ka ce min na tafi wallahi." Wato wani irin rungume ni da yayi tare da buga bayana. "Shiiiiii" yayi ta fada min sannan ya janye ni a jikinshi yana share min hawaye. Murmushi yayi yana faɗin. "Kin yi kyau, ina ganin mace tana kuka bata kyay amma ke kuka kyau yake miki? Ji wannan hancin don Allah!" Wato ba iya rarrashi ya iya ba, hatta dauko wani abun da zai mantar da ni fushin da nake yi sai da ya raba ni da fushin, sannan ya janyo hannuna muka fita parlourn, wani abu da na fahimta tun kwanakin da muka yi na sati ɗaya a gidan, Malamina ba mutu me yawan shan ruwa bane, idan ka ga ya sha ruwa to bukatar haka ce ya taso mishi, kuma idan dai sha ruwan yana sha dayawan gaske ne yadda idan ja shiga hannunsa bana marmarin sake fadawa hannunsa, domin duk sauran kwanakin da yayi da ya dawo daga tafiya bai wani damu da ya fanshe su ba. Wannan abin sai ya tsaya min a rai na daura mishi ayar tambaya. Me yasa bai damu da ya bukace ni ba.
Domin ban san cewa haka tashi halayyar yake ba, ranar haka muka kwana duk da ina son ya bukatar shi amma sai na lura kamar shi yafi bukatar hutu, don gefena can ya je ya kwanta. Kuma yana kwanciya sai barci. Ban iya barci ba daren nan haka nayi shi ina juyi domin na sha abubuwa wai irin miji zai dawo nan na gyara jikina. Sai dai kash babu abinda ya faru, tashi nayi a hankali na wuce dakina. Kusan kwana nayi ina juyi da naga abin ba zai kare ba, na tashi zuwa ban daki nayi alwala na fito, na gabatar da sallah nafilla, har dai da na fara jin barci na koma gado na kwanta.
Da asuba da ya farka ya ga bana dakin, sai da yayi wanka sannan ya shirya ya tafi masallaci, bai dawo ba sai da gari ya fara haske. A lokacin da ya shigo ya same ni akan abin sallah, ina azkar zama yayi na ga fuskarshi kamar akwai damuwa da gajiya ya kalle ni. Na shafa addu'a, na gaishe shi bai amsa ba, ni kuwa na share na tashi na fara nad'e abin sallah. Ina tsaye naji ya rungume ni ta baya yana faɗin.. "Matar Turaki, jiya sai da kika saka ni barci