Author : ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category : Love
da kuka. "Hamma Turaki, meye laifina don akan aurenka da Zakiya? Ashe Baban Nihla ya je yana niman auren kanwar Maman Husnah Yarinyar nan walidah kawar Zakiyah. Fisabiilillahi."
"Kin san bakya son zama da kishi kika tafi har gaban Daddah kika hada min munafunci, ai ni na bada sadakin karma is bitch shine zai kashe ki, aure babu fashi." "Baby ka bani kudin hada kayan leffe please bana son wannan damar ya wuce ni, zan hada muku kai da ita in sha Allah."
"Idan har rashin haihuwa ne kema me yasa baki kara wani haihuwar ba, Yan mata zan ki kudin kayan lefe!" Wani irin mutuwa jikinta tayi ta ja kafa ta fita, kallonshi nayi cike da Mamaki. "Dama aure Ubaidullah zai yi?" "Eh kai ya jima yana son yayi aure shegiya tana hanawa na rasa gane me kika tsare mata take jin haushinki, yanxu zata ga rashin mutumci ganin idanunta ba ita yar iska ba!" Rike baki nayi ashe haka yake da rashin mutunci.
Ai kuwa ba washi gari Ubaid yazo yayi ta bani hakuri Allah sarki sai ya bani tausayi. Idan baka samu mace ta gari ba rayuwarka tana cikin garari, wani ikon Allah ni da taso ganin nayi hauka. Da na gayawa Dangina addu'a aka yi ta min Allah sarki saii ga Yadiko tazo ta kawo min maganin wanke mahaifa, da sauransu. Satinta biyu ta koma, a lokacin har na gama hada lefen Ubaid ai yadda ta min kan kara haka zan mata na itacce. Kuma na shiga gaba aka kai kayan auren, muna dawowa tayi ta hauka da ihu zata dake ni. A raina na ce ko zaki mutu aure sai anyi shi......
[12/26/2025, 4:22 PM] Maman Walid: 30
Ihu da haukar da take yi, har cikin parlourn ina jinta, hankalina yana kan abinda nake haɗawa don na sha, "wallahi idan ina raye sai ga bayanki!" Ihu da hauka iri-iri tayi shi gashi an hanata shigowa gidan, a ranar dakyar ta koma gidanta, ina jin yadda yake ihu da tashin hankali.
Da yake mijina ya tafi wani meeting Abuja sai dare zai dawo haka na hada magani gyaran jiki, wurin karfe shida ya shigo a gajiye, karban jakan nayi kallonshi. Yayi laushi na tab'a goshinsa ina faɗin. "Anya yau lafiyarka lau kuwa?" Murmushi yayi ya wuce kitchen yana faɗin. "I need water!" Na biyo bayanshi na bashi ya sha, sannan ya sauke ajiyar zuciya can kuwa ya fara wani irin tari. "Me yake damunka?" Na rike hannunsa muka wuce cikin dakina, ina shafa bayansa.. sai da na taya shi wanka duk yayi laushi. "Me ke damunka!" Masallaci ya tafi bayan ya dawo ya kwanta sai dai dama mishi kunu nayi ya sha, ina rike da hannunsa. "Meke damunka?" "Bana jin dadi ne almost 3-days kenan." Sake tab'a wayarshi nayi na ji zafi rau. "Baby you're burning! Muje asibiti." Girgiza min kai yayi yana mai rike hannuna ya ce min. "Please sir na da sweater!" Haka na wuce dakin na kawo mishi, ya saka nace mishi. "Me kake so!" Girgixa min kai yayi yana faɗin. "Bana jin yunwa." "Fisabiilillahi haka zaka zauna da ciwo?" "Hmm!" Ya ce min na rasa me yake min dad'i, duk ya rasa kuzarinsa, haka yayi ta zazzaɓi a kwanakin ya daina zuwa office sai da yayi sati s gida, wanda ya janyo aka kai shi asibitin da baya so. Ruwa suka yi ta saka mishi, wani abin mamaki sai jikinshi ya rikice sosai. Wanda ya saka ni cikin wani irin tashin hankali.
Wanda ya kai aka tura shi ICU, dole Mama ta zo. A cikin kwanakin nayi wani irin rama domin bana cin abinci bana kwakwaran barci. Tunda Mama ta zo take nazarin yadda yanayin mu alamata da danginsa idan ya wuce Daddah da Alhaji ELYakub sai Uncle Auta da Ubaid. Kallona tayi ta ce min. "Kina cikin abinci kuwa?" Murmushi nayi na ce mata. "Ina ci!" Riko hannuna tayi ta ce min. "Kamar kina da ciki ko?" Da sauri na kalleta babu kowa a wurin, na ce mata. "Ciki Mama?" Gyada min kai tayi, nayi kasa da kaina. Tun last week ya dace period din ya dawo amma har yanzu shiru, sai ciwon gefen ciki da yawan kasala. Na zata ko don rashin lafiyarshi ce. Rufe bakina nayi da hannuna daya na kalleta. "Innalillahi wainnalihir rajoun! Mama!" Hannu ta saka min a bakina. "Mijinki ma kamar hannu aka saka mishi, bani da tabbas amma ki shirya mu koma gida!" "Mama!" "Ba zan barki anan ba, domin shima a nan din farautar rayuwarshi ake idan har shi ba a kyale shi ba, kema ai baki tsira ba. Waye kika yarda da shi a cikin danginsa!" "Tarik!" Na furta kai hatta Uncle Auta da Ubaid ban yarda da su ba,. Kiran Tarik nayi a waya.. "My boy ina son ganinka don Allah!" "Ina nan tafe gobe in sha Allah!" "Muje gidan Adamu!" Bata gayawa kowa dalilin tafiyarmu ba, haka muka isa gida, dai naji kamar nayi kuka, idan na tuna yadda na barshi. Kusan kwana nayi da zazzaɓi, washi gari Tarik ya iso ban san me Mama tayi ba amma da safe ruwan zam-zam ta mika min muka fita, Tarik ya zo ya dauke ni. Lokacin da muka isa Asibitin Uncle Auta da Ubaid muka samu sai Kakanshi.." Jiya ina kika tafi?" "Naga kamar tana bukatar hutu shine na tafi da ita ku yi hakuri."
" Ba kome Hajiya, dama mun damu ne." Inji Kakanshi. Wucewa nayi dakin da jakar zam-zam, na shiga na same shi a yadda na barshi. Ruwan addu'ar nayi Bismillah na shiga shafa mishi, shigowa Uncle Auta yayi ya ga ina shafa mishi ya zo ya taya ni. Har muka gama ya ce min. "Addu'a ko?" Gyada kai nayi, murmushi yayi ya ce min. "Mun yi da Baffa zaki koma gida zamu tafi da shi Russia!" "Zan bi ku!" Girgiza kai yayi na ce mishi. "Ni nafi dacewa na zauna a gefenshi." Na fada ina mai fashewa da kuka, fita yayi ya bar ni a dakin, dA sauri na juya gare shi, na riko hannunshi na kai kan cikina. " Please wake up ka ji feel your baby a marana, please ka tashi we need you." Na fada ina kuka. Na rasa yadda zan yi haka na fito na same kakanshi na ce mishi." Don Allah ka bar ni nan tafi da shi, don Allah ku bar ni, na biku. Mama ki ce su bar ni kin ji Mama ki roka min shi don Allah." Kallon su Mama tayi a nutse, ta ce musu. "Ku barta ta bi Mijinta!" A yadda suka tsara babu ni, amma da yake Allah ya mata baiwar iya sarrafa kanta sai gashi sun amince. "Shi kenan ta shirya!" Haka Tarik da Mama suka kawo ni gida na shirya tsaf, sannan na hada kayana na kashe kome na gidan abincin da yake frij na kai cikin gidan Uncle Auta, sannan na rufe gidan, muka wuce asibitin. A daren muka wuce Russia, lokacin da muka isa can Russia har da Uncle Auta. Yadda aka Karbe mu yafi kome dad'i, nima damuwa da rashin hutu yasa ina sauka a jirgin na yanki jiki na suma. Haka aka wuce da mu asibitin.
Sai da nayi kwana biyu ina barci na farka, koda na farka Aunty Herlim na gani a gefena. "Lunah sannu kin farka?" Gyada kai nayi ina murmushin karfin hali. "Ya Jikin shi?" Na tambaye ta ina kallon dakin, murmushi tayi ta ce min. "Yana dakinsa." Gyada kai nayi na rufe idanuna. "Kwanaki biyu kina barci!" Kallonta nayi na ce mata. "Kwana biyu?" Gyad'a kai tayi tana murmushi. "Amma babu inda yake ciwo na kira likita?" Gyada mata kai nayi, danna abu tayi sai ga nurse sun zo, tare da likita a bayansu, bayan an gama duba ni suka min tambayoyi, na basu amsa. "Ki huta zaa yi miki scan nan da dare!" Bayan sun fita na shiga wanka, na fito nayi sallah. Sannan na wuce dakinsa. Lokacin da na shiga naga sun daura mishi karfuna, zama nayi na dafe kaina. Ina kallon yadda ya koma lokaci guda, wani irin kuka nake ina kiran sunan Allah, tunawa nayi da kayan da nazo da shi, na kalli Aunty na ce mata. "Ina goran ruwan da yake jakata." "Yana gida zan saka a kawo miki!" "Ina so yanzu nan!" Haka ta bar Asibitin, bayan minti ashirin sai gata, dauka nayi na shafa miishi a jikinsa da ko ina. Da dare na je aka yi min scan sannan anan aka gano cikin sati biyar da kwanaki shida, hawaye ne ya zubo min, na koma dakin ina kallonshi yana barci. A bisa ka'ida ba za a zauna da shi ba, amma saboda yadda suka ga koma suka bar ni, sallah biyar sai na saka shi a cikin addu'a. Idan dare yayi kuwa sai gari ya fara haske nake komawa gefensa na kwanta ina kuka har nayi barci.
Ban sare ba, ban tab'a give up ba. Addu'a na saka Allah a gaba. Ruwan zam-zam din na karewa na gayawa Auntynsa suka nimo min har da ganye magariya, anan ne na ga ikon Allah, na kuma. Yarda akwai sihiri a tare da shi, tunda ya kwanta baya motsi numfashi ma da taimakon inji yake yi, amma ina fara ayatul shifa, ya fara motsi. Tunda na fara sai nima na fara jin wani irin abu yana yawo a kaina, idan na kwanta barci zan ga kamar aka bina da gudu. Sau biyu na ga haka, sai na kira Mama ina kuka na gaya mata. "Bar kuka haka, ki tuna akwai wanda yake bukatar kulawarki bayan Turaki, ki tuna da abin cikin ki ko ba don kanki ba, in sha Allah zan taya ki daga nan." "In sha Allah Mama!" Na fada ina kuka, tayi min nasiha sosai sannan ta kara min addu'a sosai.
Haka na kara kai mi, amma kuma idan na tuna akwai Allah sai na ji bana tsoro. Haka na cigaba da na shi, Turaki bai da Uwa bai da Uba, nice abu biyu zuwa uku. Jasminah tana Kano, bata san me yake faruwa ba. Nan kuwa dangin Uwarsa ba musulmai ba ne. Haka na tsaya ba dare ba rana, ina addu'a. Aunty Hindatu ta kira ni ta min jajje take gaya min anyi saukar Alqur'ani da yanka, Abba yasa an tara almajirai, sai na fashe da kuka. Sannan an raba namar sadaka gida gida, abinci kuwa har kofar fada aka kai aka rabawa almajirai. Sannan anan ware tsangaya uku akai abinci da ruwan sanyi aka raba. Nayi kuka kamar raina zai fita, sati daya aka dauka aka addu'a, sati na zagayowa ya fara farkawa, wani bin idan ta bude idanunsa har da tashi da karfi kamar zai tashi sama, sai anyi mishi allurai yake komawa barci, na kira Mama na gaya mata, ta ce min. "In sha Allah za a ci nasara!" Likitoci kuwa cewa suke miracles ne yasa ya dawo rayuwa domin sun fara tunanin a cire mishi abin numfashin ya tafi ya huta.
Alhamdulillahi ko kafin satin ya farka ya zauna da daram, ranar da na ga haka kuka na saka tare da rungume shi. Shafa bayana yake yana murmushin farin ciki. Ban kyale shi ya wartsake ba na daura hannunsa akan cikina. Na gyada mishi kai. "Alhamdulillahi!" Ya furta a hankali, hawaye na zuba a idanunsa yau na ga yana zubar da hawaye ya ce. "Zan zama Baba daga gare ki? Thank you for choosing me to be a Daada." Rungume shi nayi ina cewa. "Thank you for made me a mother!" Hade goshinmu yayi yana faɗin. "Thank you Lunah, thank you for saving me, thank you for protecting me. Na ganki a mafarkina, kin kare ni kin hana kowa ya cutar da ni, thank you for be in my side. Lunah!" Rufe mishi baki nayi ina faɗin. "Ya isa ka huta kayi sallah." "Jikina yana ciwo!" "Bari idan muka koma gida ayi maka hayakin habbatu saudat." Murmushi yayi yana shafa cikina. Haka na taimaka mishi yayi wanka da alwala, ya zo ta gabatar da sallah. Bayan ya idar ya ci abinci, sannan na bashi addu'ar da nake shafa mishi. Ya sha na kara shafa miishi, yans murmushi ya kwanta. Kwanaki hudu yayi aka sallame shi, muna zuwa gida na hada mishi ruwan addu'a yayi wanka sosai. Bayan ya fito na mishi hayaki da Habbatu saudat, ba sai gashi yana gurnani ba. Can ya tashi ya fara wani irin abu. Yana niman kamani amma yayi baya, na cigaba da zuba garin habbatu saudat, duk da na razana amma kuma aka na fahimci kamar abin da yake tare da shi yafi ni razana, tari yayi ta yi har ya zube a kasa. "Ki godewa Allah kina da shi a gefenki, Allah yana gefenki, ba wurinsa aka turo mu ba wurinki ne, wurinki aka turo mu amma muka kasa gane hanyar inda kike shine muka shiga jikinshi, shima abinda yasa muka shiga bai yi azkar din yammaci ba ne, ke kuma kina cikin addu'a koda ba kya ibada. Ni dai ki bar ni na tafi domin an daure ni ne da addu'ar da Iyayenki suke miki!" Kallon wulakanci nayi mishi na ce mishi. "Sai dai ku tabbata a haka kamar yadda ka bawa mijina wahala haka zaka kare ba zan kyale ka ba!" Ihu da kururuwa yayi ta yi har Auntynshi tazo, na cigaba da addu'a zata yi magana na ce ta je kawai. Haka na cigaba da addu'a da ruki'a, sai da na wahalar da shi har yana cewa zai mutu na kyale shi, ya fita ta atishawa. Yana samun damar barci na mishi alwala na gyara mishi kwanciya. Na kira Mama na gaya mata, ta ce min." Akwai abubuwan da aka hada muku dukkanku har da cikin jikinki ya za ayi?" " Kada ki damu zan turo Tarik."
(Kuyi hakuri na gaya muku gaskiya bani da lafiya wallahi gudun kada na tafi break ku ce ban kyauta muku ba yasa zan muku koda daya ne, ku yi hakuri kun san yadda nake typing amma wannan karon bana jin dadi sosai?! Arewa gobe xan kara muku update telegram maybe sai Sunday in sha Allah)
[12/29/2025, 7:53 PM] Maman Walid: 31
Na fada mata tare da rike hannunsa, kwantar min da hankali Mama take tana gaya min magana me dad'i, hawaye ne ya zubo min, na ce mata "in sha Allah ina tare da shi, ba zan tab'a ja da baya ba." "Allah ya miki albarka, ya sauke ki lafiya. Ki kula da addu'a da azkar!" Daga haka muka yi sallama, na tsaya sosai da addu'a bs dare ba rana, a bangarenshi kuwa sauki ake samu, sati daya da muka yi magana da Mama sai ga Tarik, kusan nafi kowa murna, haka muka yi ta amfani da magani na fara mishi amfani da su, Alhamdulillahi sai gashi lafiya ta samu har an koma duty, bakiɗaya ya koma irin iyaye mazan nan masu matukar damuwa da Yaransu. Tun da yaji na shiga wata na uku ya tattara kaunar duniya ya daurawa cikin, da yake gani kamar bai da wani sama da shi. Tun daga nan na fahimci irinshi, da cikin ya shiga wata hudu nan na kara yarda da cewa zuwa yanzu Allah ya min arziki da ya bani shi a matsayin mijina, domin fita goma shiga goma, zai daura kanshi akan cikin yayi ta bashi labari, surutu kala kala. Ni kuwa motsi kaɗan zai tambaye ni me nake so.
Har ga Allah na gaji da zaman garin, don haka cikin da ya fara tasawa na shiga wani irin yanayi na son gida musamman abincin gida, tuwo, fate, dambu da kwadon zogale, ranar da na tashi da son taliyar murji ban samu ba da mai da yaji, karshe indomie na dafa na jikata tayi manya manya naci da mai da yaji, da dare kuwa ina kwance naji ina sha'awar awara da mai da yaji, kuka ne ya zo min ganin yada nake shiga damuwa Kakarshi da Auntysa suka saka shi gaba ya shirya mana dawowa gida, shi a lissafinshi kada mu dawo gida a kara cutar da abin cikin tunda sun ga ba nasara akanmu, murmushi nayi kawai nace ni dai gida.
Haka muka gayawa Mama zamu dawo na gaya mata ranar da zamu dawo. A bakinsa nake jin ta turo aunty Hindatu da Aunty Innah da Zakiyah aka gyara min gidan suna gari ma su zasu karbe mu, bai yarda ya gayawa kowa zamu dawo ba, sai dai ganinmu aka yi ranar wata Alhamis da safe muka iso. Uncle Auta da Ubaid sai da suka mishi tsiya, wani ikon Allah ko Yayuna Mama bata gaya musu ina da ciki ba, tace dan duma ne ba aboye shi. Nayi kiba daga sama da kasa, suka yi ta min tsiya ko ciki ne nace su taya mu da addu'a. Duk wani abinda muke bikatA an kawo a gidan babu abinda na rasa sai dare suka bar gidan,karfe tara ya shigo shi ɗaya. Ina daki na ji shigowarshi. Fitowa nayi na same shi yana zaune yana shan ruwan zam-zam. Murmushi nayi na bi kitchen na dauko dabino da ya'yan zaitun ka kwalba, Mama tayi recommended din akan ina ci, bude min jikinshi yayi na shiga cikin na zauna tare da kwantar da kaina a kirjinsa. "Baby ya My love yake?" "Idan na haifi Baby sai a koma Madam ko?" "Waye ya gaya miki haka?" "Kai mana!" "Kada ki min sharri!" Ni dai ban ce kome ba, na cigaba da cin zaitun din har na gama, muka shiga hira. Da yake bamu ta kowa ta kanmu muke