Author : ALAƘAR ZUCI BOOK 2.docx Category : Love
abinda tayi min ba, duk abinda Hafiz yayi min Jalilah tana da kaso a cikinsa.
Wurin karfe biyar Daddah suka zo da Badr, sosai suka cika min gidan suna zuwa kowa kallon cikina yaƙe. Ko minti goma basu yi ba sai gashi. Tunda ya shigo yake hararata, dariya ya bani haka ya zo ta zauna yana matsa min kafana suna Magana da Daddah jife-jife, har kusan awa guda kafin suka yi sallama, ni dai ban tab'a sanin mai ciki tana zama abin kallo ba sai a family kumo. Shi kansa dariya yake min idan ya ga yadda nake nuna ina tsoron abinda da yake faruwa. Ce min yake ba kome zasu dai ma don ba zai dauki renon hankali ba......
[1/6, 8:28 PM] Maman Walid: 35
Haka muka yi ta fama, ranar wata laraba da yamma muna hira muka ji ihun Falilah. Sai da gabana ya fadi. Ina zaune a wurin Umma ta fita ta duba ashe har sun kaita asibiti. Haka ta dawo tana jajjanta abinda ya faru wai a bakin masu aikinta ta ji haka kawai ta fadi ba tare da kome ba. Ni dai rabona da ita tun wani zuwana awo na hango ta tare da matar Uncle Auta, ban Kuma ganinta ba, karfe shida matar Uncle Auta ta shigo suka gaisa da Umma ina kan abin sallah, ina jiran a kira sallah kawai nayi sallah, ta shigo tana shigowa kuwa ana kiran sallah, tashi nayi na gabatar sallah, sannan na cigaba da azkar, bayan na idar muka kara jajjanta abinda ya faru na Falilah shiru tayi kafin ta ce min. "Kwanaki da Turaki ya kwanta, ta zo min da wani magana ta ce min ai idan ka duba yadda turaki yake rawan jiki akanki ba hakan kika barshi ba." Kallonta nayi da kyau, kafin na ce mata. "Ina ga kamar maganar nan bata da amfani anan ko?" "A'a yana da amfani dalilin da ya kawo ni kenan, ina son ki sani nayi kuskuren da na biye mata muka yi ne!" Sanin cewa zan iya samun kaina da bakin ciki idan naji labarin sai na ce mata. "Kin san me?" Girgiza kai tayi, "ki bar labarin nan na yafe maku, ku je wallahi na yafe." Cike da mamaki take kallona. "Baki san me muka yi miki ba amma kin yafe mana?" "Idan nasan me kuka min xan ta kallonku da shi har karshen rayuwarmu, amma idan na yafe ba tare da na sani ba zuciyata zata samu natsuwa babu wnada na rike ba wanda ya rike ni. Kuma har gaban Ubangiji ban kwana da kowa a raina ba." Wannan maganar da bayi ta samar min da kwanciyar hankali.
Kasa magana tayi don na hanata ta, Umma ta zubo mata abinci, taki ci. Bayan ta bar gidan na sauke ajiyar zuciya. " Kada ki sake damuwarsu ya taɓa lafiyar cikinki."
" In sha Allah! "
Hmmm ashe tana kasa tana dabo, ita dai Jalilah abu ya ki na asibiti, dole aka wuce da ita Gombe, a can ne aka yi ta wani irin rigima da gurmi fa, na farko aka ce kishiyarta tayi mata asiri, abin tausayi yarinyar nan haka suka d'agawa iyayenta hankali, dole ta shiga wani hali, aka yi ta fama.
Sati daya da mai da ita Gombe, na tashi da ciwon nakuda. Cikin dare haka aka wuce da ni asibiti. Tun karfe sha biyu muke abu daya har asuba gari ya waye. Ban haihu ba. Karfe tara na safe Umma tana waya da Mama ciwo ya taso gadan-gadan, dama ni da shi ne a dakin itama ta kawo min ruwan Lipton da sugar ne ta fita kenan tana faɗin. "Wallahi har yanzu!" Kawai sai jin kukan jariri tayi ta leko, ganin yadda haihuwar tazo a dakin da aka kwantar da ni kiran Nurse tayi ai kuwa sai gasu nan a tare lokaci guda na sauke mishi ƙatuwar diyarshi, jajjur da ita. Wani irin kallona yake domin bai zata zan haihu a yadda na ke din nan ba. Komawa nayi na kwanta aka gyara Yarinyar tas, sannan nima suka duba ni ko na karu babu kome.
Karfe goma suka gyara dakin har yan gidansu sun fara zuwa kafin wani lokaci labarin ya karaɗe ko ina, Ya Ado yana office aka gaya mishi ai kuwa sai gashi a asibitin. Har da Aunty Nuratu Kafaya da yarta Nasiba. Karfe biyar anan yayi musu. Daga ni har Babyn muna cikin koshin lafiya. Karfe shida na yamma aka sallame mu, muka dawo gidan duk da an yiwa yarinyar wanka acan muna shigowa Umma ta kwab'a lalle, tazargaje, ganyen magarya, ta mutsike yarinyar da shi. Ta lullube ta. Wurin karfe takwas bayan na fito wanka. Ta shigo da kayan wanka tayiwa yarinyar wanka tas, a lokacin wata budurwa da ban santa ba, ta shigo dauke da tiren abincin. "Sannu Aunty kin samu kai lafiya!" "Alhamdulillahi!" Matar Ubaid a bayan yarinyar suka shigo. "Sannu Husnah!" "Sannu ashe kin sauka!" Murmushi nayi mata yarinyar bata da matsala kamar Falilah."Alhamdulillahi!" "Nur ajiye mata taci Aunty ga abincin nan nayi miki da kaina, Allah yasa ki ci!" Murmushi nayi na ce mata. "Zanci kai!" Umma da take gyara baby ta ce mata. "Me zai hana!" Bayan Umma ta gama kintsa Baby ta fitar da kome zuwa toilet sannan ta dawo da ta zuba min abinci, na fara ci a hankali. Ina jin wani irin dad'i yanzu na gane dalilin da Ubaid ya makalewa Yarinyar na daya gwana ce a wurin girki, domin kakar yarinyar tayi sana'ar tuwo-tuwo a gadar Lagos, na biyu yar gayu ce tsaf-tsaf da ita. Ga iya magana da salo. Dole na miji ya tare wurinta.
Dama basu samu haka ba ma ya aka kare balle kuma sun samu ai magana ya ƙare, sai sha daya suka tafi tayi ta kallon Yarinyar. Bayan tafiyarsu Umma ta ce min. "Ba mamaki Mijinki ya zo nan domin na lura ba ruwansa da kunya idan yazo shi kenan idan bai zo ba ki kira ni!" Gyada mata kai nayi na kwanta. Ina me addu'ar barci yarinyar nan sai barci take. Wurin sha daya ya shigo da katon leda, sai da ya kaiwa Umma sannan ya kawo min dakina. Kallona yayi lokacin da ya kunna wutar dakin. "Sannu ko" murmushi nayi, ya fita ya dauko plat ya juye min namar. "Uncle Auta ya ce ana son kici!" A hankali na fara ci shi kuma ya koma wurin Babyn. "Kece kika haife ta?" Gyad'a kai nayi, ya dauke ta yana sumbatar goshinta. "Wani suna kike so a saka mata!" "Mammy!" "Sai dai ko Mama!" "Mammy sunanta Ummuna Aisha!" Na fada ina kallon namar gabana. Ajiye Babyn yayi ya zo ya zauna a gefena. "Thank you!" Sai naji abin wani iri, a wani lokaci maza har wani isa suke nunawa akan Yaransu amma yau saboda nace ya saka sunan Mamanshi yake gode min, fita yayi ya hada min tea Mai kauri ya kawo min na fara sha a hankali, ina cin namar wurin sha biyu saura muka kwanta,. Muka sakata a tsakiyarmu, karfe biyu yarinyar nan ta ce garinta ya waye, daga ni har shi aka rasa wanda zai yi wani abu, karshe saka min ita nayi na bata nono, sannan na koma na kwanta, bayan na kwanta shi ya cigaba da kula da ita, har ta koma barci. Karfe hudu na asuba ta tashi, ya fita da ita zuwa dakin Umma itama ta daura da ita har zuwa hudu da rabi ta kawo ta na bata nono. Na koma na kwanta ita kuma ta kwanta. Dakinsa ya wuce ya kwanta sai karfe biyar ya fita sallah yana dawowa ya shiga bude kayan da aka kawo mishi last week daga Russia, duk wani abin bukata ya saya. Ina wurin karfe shida na shiga wanka ina fitowa yana hado min tea, na sha Umma ta min dumame naci, ya dauko belt ya mika min na daure cikina, na saka wata Flora gown. Ina gamawa na ya fita zuwa kitchen sai gashi da wasu bottle, Umma tana kallonshi ya mika min tare da gaya min yadda zan yi amfani dashi, ya mika min Babyn ina daura ta akan ɗayan nonon wannan da muka saka abin zuba sai ga shi ya fara zuwa, a cikin bottle din. Kafin wani lokaci ya taru na sauya mata na bata ɗaya ma, sannan Umma ta mata wanka.
"Amma nonon bai miki zafi ko kamar na asibiti." Dariya nayi na cigaba da fito da kayan da zaa saka mata. Ya shigo da fruit dakin.....
[1/6, 10:23 PM] Maman Walid: 36
Ajiyewa yayi a stool sannan ya amshi kayan ya ce min. "Zauna ki ci." Na bar mishi aikin ya cigaba ni kuma na zauna ina ci, ina kallonshi cikin kulawa. "Daada ka karya kuwa?" "Bari a shirya my queen sai na je na ci ko!" Gyada mishi kai nayi, a hankali na zame jikina ganin suna ta hira, na nufi kitchen, da kaina na fara hada mishi abinda zai ci, ina tsaka da gasa dankalin turawa naji ya rungume ni ta baya. "Yanzu aiki kika zo yi ban sani ba?" Murmushi nayi nace mishi. "Meye amfanin zaman da nake yi kana aikin kula da Mammy ni kuma sai na bawa dan Mammy abinci ko?" Janyo kujeran kitchen din yayi ya zaunar da ni yana faɗin. "Hutawa ya dace ki yi ba aiki ba." Murmushi nayi nace mishi. "Na sani amma kuma ai kafi ni buƙatar abinda zaka ci, ni ina gida ne kai kuma zaka office.!" "Inji waye ya ce zan tafi office!" "Wai kana nufin ba zaka office ba?" "Sai dai su kore ni!" Kallonshi nake a hankali, yayi murmushi. "Mace aka haifa min kuma ina fatan irinsu goma, don ina sonsu da dukkan rayuwata." "Haihuwa da wahala idan kana son sai ka ka..." Yatsarshi ya daura min akan bakina. "Never!" Dariya ya bani, lekowa Umma tayi ta ce min " ungo naki, da jegon zaki tare a jikin namiji? Kai ma ka daina shiga mana wallahi ba zan iya jegon turawa ba." Ta fada tana mika min yarinyar da take barci. "Umma jego fa ba addini ba ne, ki yi hakuri ku kyale ni a jikin Matata da Yarana, idan ma gida zaku kai su, wallahi xan bi ku. Amma batun kada ta manne min bai taso ba, Uwata ta haifa." " Wallahi ban isa ba, sai dai na kira Yaya Salamatu na gaya mata." Kallonshi nayi, a hankali na koma daki na samu tana mita, kwanciya nayi, can kuwa sai gashi da abincin, ya kawo duk yadda take mita sai gashi ta barmu mun ci tare har ya fitar da kayan na kwanta aka saka room heater, barci yayi gaba damu. Wurin karfe daya sai ga Alhaji ELYakub Kumo haka aka ƙara gyara yarinyar aka fitar da ita, na shirya cikin abaya, shigowa dakin yayi ya tsaya a bakin kofar tare da jingina da kofar, yana min wani irin kallo daga kasa har sama. Murmushi nayi mishi. Matsowa yayi ya rungume ni, " thank you!" Murmushi nayi na ce mishi. "Da aka yi me?" "Da kome kin yi min kome, kin bani kyauta daga gare ki, kin min kyautar da ba kowacce zan samu daga gare ta ba, na gode sosai na gode sosai na gode. Please kada ki musu murmushi me tsadar nan, yake zaki musu kin san yadda nake jin zuciyata tana wani irin pounder kamar zata buga." Murmushi nayi haka ya riko hannuna muka fita har wajen. Muna isa parlourn na zauna a daya daga cikin kujerun, na gaishe su. "Sannu Lubabatu!" Murmushi nayi ina satar kallonshi. Shima kallona yake yana magana da fulatanci, ban tab'a ganin kyautar gwal a zahiri ba sai akan Mammy, box din ya mikawa Uban ya bani, sai kudi dollars. "Gashi nan ki saya mata pampers wannan na barka na ne." Sai da suka dauki minti arba'in sannan suka mana sallama, komawa ciki muka yi na kwanta na huta, dauke yarshi yayi wurin karfe ya kawota lokacin ciwon ciki da ake bayan haihuwa ya dame ni, sai fama nake kamar zan mutu. Ganin haka yasa shi shirya ni muka wuce asibiti,muna zauna aka kwantar da ni, allura suka min da drip aka min. Wurin karfe goma da rabi muka dawo gida.
Washi gari da safe sai ga Jasminah da Yaranta, tunda suka zo suka mannewa Babyn da suke kiranta Boɗɗo, kowa sonta yake ni kuma Jasminah muna dakin, zuwansu ya sa shi tafiya Office a can ma ya kira ni ya kai sau goma, har ya dawo gida kirana yake, lokacin da ya dawo na kai mishi, ina shiga dakin na same shi yana cire takalmi, karasawa nayi na ajiye mishi abinci, sannan na shiga taya shi ya cire kayan, tausayi ya bani kamar wani maraya. "Sorry!" "Yau duk nayi kewarku!" Rungume shi nayi tare da shafa kanshi, "Sorry baby mun yi kewarka."
Ban tsaya biye mishi ba, na hada mishi ruwan wanka, sannan na fito na saka shi dole ya shiga wanka, ai kuwa yana shiga na gyara kayan sannan na ciro mishi kayansa na saka turare na ajiye mishi. Ina me barin dakin, lokacin da na koma yana cin abinci yana ganina ya mika min hannu yayi na isa wurinsa, zama nayi ina kallonshi. "Ina sonka!" Murmushi yayi tare da sumbatar goshina, ya cigaba da cin abinci. Yana gamawa ya rike hannuna a cikin nashi, mun jima a haka ya ce min. "Kin san Allah!" Kallonshi nayi, "da kin haihu da Hafiz ko!" Kallonshi nake a hankali ya ce min. "Da har abada ba zan daina kukan cutar da yayi min ba, Alhamdulillahi Ubangiji ya min kyautar da ba zan iya saya ba, ya bani d'a guda daga gare ki, iya wannan nayi mishi nisa, sannan ni ne Uban Uban Yaranki ni daya da Yarana zamu more ki, ba tare da mun raba da wasu ba, babu wanda ya riga Yarana iya su kaɗai zasu kalle ki su ce Mamarsu ce su daya ba tare da wasu yaran ba, iya wannan ma babban sa'a ce da nayi, kai Alhamdulillahi Alhamdulillahi Ubangiji ya gama min duk wani arziki a duniya, Aisha Bilal Haris Kumo, Aisha Turaki, ke ni fa na gama Sa'a, Ubangiji ya sallame tun daga nan na sannan Allah ya sallame ni, Ina godiya ga Allah da ya min wannan kyautar da babu wanda ya isa ya ce shi ya bani, babu wanda ya isa ya min gori sai dai ya ce min ban samu haihuwar da wuri ba, Alhamdulillahi." Yayi hamdalla ya kai sau nawa yadda yake maganar yana kara jajjantawa kanshi irin wannan kyautar da Allah ya miishi, har na gaji na bar dakin na wuce dakina. Mika min waya Umma tayi na saka a kunne, daga can Mama ta ce min." Wallahi kika sake ya kara dirka miki ciki zaki sani wato ke wacce irin sakarya ce kin biye mishi sai nanike mishi. " Yadda Mama take faɗa kamar na je nayi wani abu da shi, sai na kame kaina ban kara biye mishi ba, karshe da ya ishe ni sai na tura mishi sakon don Allah kada ya damu da rashin kula shi, mu biye musu a wannan lokacin, a bisa al'adar bahaushe ana kwanaki uku, a ranar aka kawo mana gero buhu ɗaya, rabin buhun barkono, citta rabin buhu, kanunfari rabin buhu kome sai da suka yi shi na alfarma, sai zabbi guda talatin, lokacin da Umma ta gayawa Mama, addu'a tayi kawai tasan yanzu kan Allah ya bani gidan auren da rufin asiri. Da yamma sai ga kan saniya a gyarenta aka saka a firji, iya haka da ya faru ya kara min wani irin yanayi na musamman.
Washegari Aunty Zakiyah tazo, ita da su Aunty Innah, Wai Aunty Hindatu sai ana gobe zasu tawo, ita da Sunyi Simah. Cikin kankanin lokaci gidan ya fara ciki, Aunty Raliyah ma tana hanya, tare da Yadiko duk sai naji kaina ya kara girma. Yayuna sun min adalci sun turo matansu, shima sai godiya yake ta mana, ana jibi suna ya kira ni na hada mishi kayanshi, ya tattara ya koma gidansa na Agege, sannan muka samu damar sakewa su na bar musu dakina da sauran dakunan na koma dakinsa na kwanta, a ranar da Aunty Hindatu suka iso har da su Yadiko aiki aaka yi ta yi kamar zasu tashi saboda aiki kawai.
A ranar wuni nayi a wurin gyaran kai da lalle shi yazo ya kai ni, sai da muka biya ta gidansa na agege sannan muka wuce ana gama min muka dawo gidan bai dawo da ni ba sai dare anan muka yi wanka muka ci abinci yayiwa yarshi wanka ya gasata, ina sanye da rigar wanka kallonshi nake nace mishi. "Anya zaka iya aurar da Yarka kuwa?" "Zan iya mana, a duniya babu wata Y'a mai darajar Nana Fatimah amma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya aurar da ita, don haka zan iya kawai mijin zai ga dan iskan Uba ne domin ba zan iya kwana biyu ban ganta ba ne.......
[1/7, 8:05 PM] Maman Walid: 37
Ban san me zance akan son da yake yiwa yarshi ba, amma tabbas kaunar ta kai wani mataki da baya iya boye shi, haka ya gama shiryata yayi sallah sannan ya tattaro ni zuwa gidan, harara yadiko ta watsa min ni dai na wuce kamar wata munafuka zuwa wurin Yayuna, a wannan daren anyi hira sosai, washi gari a can family house ɗinsu aka yi raddin sunan domin ya fita da wuri ya kira ni ya ce min zasu tafi radda sunan Yarinyar, yadda ya sha wanka zaka rantse daurin aure zai je. Wurin karfe tara sai ga manyan raguna a gyare aka kawo min guda biyu, mu