Chakwakiyar Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Romance

Chapter   8 / 9

21K to 24K   out of 24.3K words

muka ɗawkoka a mota har muka ga wani abokin Alhaji suna rikici da wani saurayi harya "eh natina nima wannan abin har yanzu ina tina wa dashi in ji Amar kenan, be bari ma yaƙarasa ba. Amar yace... To me yafaru da ita?

Se a lokacin Alhaji Sani yayi mgn yace... "Yarin yar ammata auran dole Kuma tasha maganin ƙwari ta kashe kan ta dalilin hakan, Dama kasan tace tana son yaro amma mukuma muka ce baza mu bashi ba saboda bashi da sana'a, Alhaji sani ya cigaba da ba yani kamar haka..

To wannan shine da lilin da yasa na taso domin nazo naga irin zaman da Basma takeyi da mijin ta, in har naga bata jin daɗin zaman to zan raba auran, tin dade itama nasan tana da wan da take so, auran dole nayi mata. Cikin rikicewa da abin da zece ɗin yace.. "dama kasan tana da wan da takeso kuma ka aura mata wani? inji Amar yana tam bayar Alhaji sani

"eh nasan tana da wanda take so amma ban san waye ba "To meyasa kasan tana son wani kuma zaka aura mata wani? inji Amar. Alhaji sani yace..."Ranar ɗaurin auran ne Dasafe ita da ƙawar ta Lubna, Suna zancen nikuma nazu zan huce shine naji lubna tana cewa... Haba Basma kar ki cuci kan ki walhi nasan idan har daddy yaji cewa kina da wan da kikeso to na tabbatar baze miki auran doleba.

Alhaji Sani yacigaba da cewa... Nikuma da naji haka se kawai na shiga cikin ɗakin nasu, Amma ban nuna musu naji abin da suke cewaba, Bayan mun gai sada ita Lubnan sai nace tazo zan ai keta, bayan tazo sai nake tam bayar ta cewa abin da naji yanzu gaske ne kode ƙar yane? Lubna ta ce..."Daddy mekaji? nann take na mayar mata da abin da naji suna batun sa... To a lokacin abin da Lubnan tace shine yaɓata min rai yasa nakoreta kuma nayi ban za da maganar.

Awannan lokacin da kace Amar zai iya zuwa lahira a yau kuma yadawo to da babu abin da zai hana Amar tafiya domin kun ya da kuma tsoro. tam bayar zuciyar sa yakeyi shin meye Lubna tace! Kenan tace masa nine saurayin ta shikuma ya ji haushi? Tam bayar da yakeson yayi yakasa yaji Ali yana tam bayar Alhaji Sani. "To yaya me nene ita Lubnan tace maka? in ji Ali yana tambayar Alhaji sani.

Alhaji sani yayi shiru yana kallon Amar, Wanda izuwa yanzu har wata zufa ce take keto masa. Alhaji sani yace..."yarin yar tabani mamaki dakuma rashin tsoro domin kuwa se yan zu nake tinanin abin da tace shi ne gaskiya. Ta cemin...

To daddy idan kasan wanda take so ɗin zaka fasa aura mata wannan n? "nikuma jin haka yasa nake ganinn kamar tamin rashin kunya ne, ni kuma nace mata.. "bazan fasa ba ina so de nasan waye shi. Sai kawai naji tace min wai "To ai daddy babu am fanin sanin inde ba auramata shi zakayi ba. Ni kuma jin haka cikin tsawa nace mata tafita min daga ɗaki mara kun yar ban za.

Amar tam kar yazuba ruwa a ƙasa yasa don murna, Azuciyar sa yace.. Wai dama ashe Lubna tanada wayo haka gaskiya ta yi namijin ai ki tanada babbar kyuta a gurina. Abin da Alhaji sani yace ne yasa duk kan su suka mai da hankalin su izuwa gare shi.

Alhaji sani ya kali Amar yace..Tam bayar ka nake so zan yi kuma dan Allah ina so kafada min gaskiya, Shin ya zaman Abdul da basma yake a cikin gidan nan? domin ni walhi in har naga basa zaman lafiya to zan raba auran ne, kuma zan nemo wannan Tsohon saurayin nata in aura mata tin dade nasan shi takeso, kaga in naje furin lubna zata gaya min gaskiya.

Amar jin maganar yayi tam kar sauƙar aradu, Dan tsabar mamaki har rikicewa yayi yace..."Alhaji ni faaa ban san Alhaji allha ni fa "Alhaji sani yace.. "kaga ai ba wai nace zan raba auran haka kawai bane, Nasan Abdul abokin kane kuma nasan baza ka faɗi ƙarya ba, ni de Abin da nakeso shine farin cikin yarin yata.

Amar yayi shiru yana tinanin abin yi. Yan zude ga dama tasamu, yan zu zai mallaki abar begen sa, yanzu Basma zata zama tasa, yan zu wuƙa da nama suna hannun sa, jin zuciyar sa yakeyi wasai tam kar ya mallaketa.

Ali yace.."kar kaji kunya duk abin da ya ke faruwa kawai ka sanar damu,

Amar yace... "Wai dama auran nasu ba na soyayya bane? "eh walhi basu ma taɓa ganin juna ba se ranar auran, Ali ya bashi Amasa. Amar yace..."Shi yasa nake ta ganin abu buwa suna ta faruwa mana, yaci gaba da cewa... Gaskiya duk auran da bubu soyayya do le irin wannan abubuwan su dinga faruwa, yana maganar yana gir giza kai a lamar abin babu daɗi.

Han kakin Alhaji Sani in yayi dubu to yau ya tashi. Yace.."yan zude sanar mana duk abin da kaga suna faruwa a gidan kar kaɓoye mana komai, nikuma in de naji babu abin da zesa bazan tafi da ita gida ba kuma daga gida zamu huce cot domin a raba auran, ni kuma in aura mata wan da takeso suje suyi zam su cikin farin ciki.

Amar yaji wani farin ci ki haɗe da ƙarin ƙyiwa a kan abin da yakeson yi. Amar yace..."gaskiya daddy zam nasu.......✍️📝😄😄😄








*KAI JAMA'A WAI ME AMAR ZECE? SHIN KUNA GANIN KODA YAYI ƘAR YAY AURAN ZAI RABU? KU KASAN CE DA S REZA DOMIN JIN YAN DA ZATA KASAN CE....✍️*📝

*ITA ƘADDARA KOWA DA IRIN TASA, KAR KA DIN GA HANGEN NA SAMAN KA KA HANƘI NA ƳASA DA KAI YIN HAKAN ZAI SA KADIN GA GODEWA ALLAH🙏 ALLAH MUN* GODE MAKA2



End of part 1️⃣2️⃣
To be continue...


PLS COMMENT AND SHERE 🙏



This is my new numbar 👇👇👇👇👇👇👇👇
08100785178. .S REZA
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CHAKWAKIYAR SOYAYYA*💋
Story and Written..✍️
By. S REZA


*Slm masoyan Cakwakiyar soyayya. Daga wannan PAGE din zan yi tafiya saboda haka , bazaku jiniba har sai sabuwar shekara, in Allah ya kaimu, in kuma Allah yasa na dawo to zan cigaba, Ina Allfahari da masoyan littatafai na🙏🏼*



PAGE1️⃣3️⃣


................Kallon Daddy yayi sannan ya kalli Ali sai kuma ya sunkuyar da kansa sannan ya ce... "Gaskiya daddy nima abin nasu yana bani mamaki, tin da nazo gidan nan kullum a cikin faɗa suke, bama wannan ba wallahi wani abune yake bani mamaki" Da sauri Daddy ya ce.."Kar kaji komai sanar dani duk abin da kagani ko kuma kaji"

Amar ya ce " Daddy to wallahi basa kwana ɗaki ɗaya" "Ban gane ba? basa kawna ɗaki ɗaya kuma? Inji Ali yana tambayar Amar?

"Eh basa kawna ɗaki ɗaya, kuma nayi-nayi na san dalilin hakan amma kuma Abdul yace min babu ruwana hakan ne yasa nima nayi shiru na rabu dasu" "To shiɗin a i'na yake ƙwana? inji daddy. Amar ya sunkuyar da kai ƙasa alamar abin ya bashi takaici, sannan ya ce... "Daddy abin da nakeso daku yanzu kawai ku bari in dare yayi sai kugani da idon ku, zakuga ina zai je ya ƙwana"

Haka kuwa a kayi daddy yace tom bari Allah ya kai mu daran "Amen inji Amar yana tashi ya barsu a gurin.

Alhaji sani wato daddy, ya kalli Ali yace... Gaskiya In de abin da yarannan yafaɗa gaakiya ne to wallhi babu abin da zai hana ban raba auran nann ba, ace miji da mata baza ƙwana ɗaki ɗaya to hakan mai yake nufi kenan? "Yana nufin basa zaman lafiya kenan, hakan ma yanuna cewa tun kafin Amar yazo haka masuke rayuwar su kenan fako? in ji Ali yana tam bayar daddy, daddy shuru yayi yana gir-giza kai Alamar ran sa ya ɓaci.


*_________BASMA* bayan sun gama kar yawa tattara gurin tayi takai kicin sannan ta dawo ta share gurin, Duk abin da takeyi ran ta a ɓace yake saboda abin da ABDUL ɗin yayi mata, yan zu ace daddyna yazo amma wai bazai hagura da aikin yau ba, kuma yau baranar aiki ba. Sosai abin ya ɓata mata rai, wan katayi bayan taga gyara gida sannan kuma taɗora musu abin cin rana.

Tana kicin tana aiki taji dawo warsa, afili take magana. Wai wan da yace Zai dawo yanzu-yanzu shine sai yan zu, tin safe sai ƙarfe 2 amma wai yana cemin baze daɗeba "Haba mana amar yata ai gashi nadawo, walhi wani abune ya tareni shine yasa amma ai gani sorry kinji uwar gida, yana maganar yana kama kunnansa a lamar ban haguri.

Haka kawai yau takejin tana jin hausin abin da yayi mata, Hakan ne yasa bata kula shiba, sema ƙoƴarin ƙwace jikin ta da takeyi daga nashi, Abdul yace... My amarya lafiya kuwa inata magana kin min shiru? jin bata amsa bane yasa ya rabu da ita ya huce ɗaki domin yin wan ka.

Zau ne ne suke dukkan su'akan daynin tebul domin cin abin cin rana, bayan tazubawa ko ita kuma bata zubawa kan taba, kuma dama tin da tazo gurin babu wan da tayi wa magana, kai da kagan ta kasan rain ta'a ɓace yake. Meƙewa tayi da niyar barin gurin ABDUL Yace... "Basma lafiya kuwa ina kuma zakije? bata bashi amsa ba sai ma kallon sa datayi saikuma taci gaba da tafiya. daddy ne yace..."Yar daddy dawo kici abin cin kin ji "Nifa naci nawa tin ɗazu sabo dahaka kawai kuci kayan ku, tana gama faɗin haka tahuce tayi tafiyar ta.

Kallon-kallo aka koma yi sta kanin Ali da daddy da kuma uban ƙaiyar wato Amar. Abdul ne ya meƙe ya bita abaya domin rarrashin ta. Bayan Abdul ya fita ne, daddy yayi tagumi irin tagumin hannu bibiyunnan. kallon Amar Ali yayi yace..."Gaskiya ne maga nar ka, ga alama guda ɗaya mun gani tin dade gashi a gaban mumafa kenan "yan zude kunga alama guda ɗaya ko? Tom Allah ya kaimu anjima zaku sha mamaki.

Abdul yana shiga ɗakin yayi truss yana kallon ikon Allah, ƙarasawa inda take yayi yana mata magana, Haba Basma menene haka kuma? yazakizo ki kwanta a ƙasa kina kuka sai kace ammiki mutuwa Pls dan Allah kitashi muyi mugana kinj "nide katashi kafita min daga ɗaki kaje gurun wacce tafini agurin ka nide kabar ni nace.

Cikin mama ki yake kallon ta jin abin da take cewa, ban gane ba mekike nufi? cikin kuka tace... "Bayan kafita ankira'a wayar ka akace wai ana neman ka a office kuma kace min cen zakaje, sannan kuma kace min yan zu zaka dawo amma tin safe sai ɗazo fa kada wo? Tana gama maganar tafaɗa jikin sa tana rushewa da wanin sabon kukan.

Cikin mamaki yake kallon ta, to shi waye ya kira shi! yace...Ni a ka kira? yana tam bayar ta "to zam maka ƙaryane tabashi amsa "tashi kije ki ɗauko min wayar. Tashi tayi tafita domin ɗauko wayar, Abdul mamaki yakeyi to ma wai waye wanda ya kirashi kuma ai shi tin ɗazu yana office amma bari ta kawo wayar ya gani.

Da sallama ta shigo ɗakin tana nufar in da yake meƙa masa wayar tayi tana kallon sa. Dasau ru ya karɓi wayar yana bude ta, kurin da in mutum ya kira kokuma a ka kirashi zai gi yanufa, abin mamaki, Gaba ɗaya ma yau babu wan da ya kirashi, Dama kuma shi bashi da a boki koɗaya in kaga yana waya to shida daddynin sane kokuma wasu daga cikin ma ai katan sa. Nuna mata wayar yayi yace... Basma kin gani a yau ma babu wan da ya kirani ta wannan layin, yana nuna mata wayar, itama cikin mamaki ta karɓa taduba.

Basma tace kuna fa walhi an kira ka kuma nice da kai na na amsa kira, cikin wasa yace... Kode tsabar kishin nawane yasa kika manta kina ce ko ankirani ne? "Ai ni yanzu nadena kishin ka tin dade kai ma baka kishi na "Nidin ne bana kishin ki? yana tam bayar ta? tace "eh mana tin dade gashi ni ina kuka kai kuma bakayi "to yan zu dan mutun yana kuka kai ma in kayi shi ne kayi kishin sa? yana tam bayar ta, ita kuwa tace "eh mana ai haka shine cikar masoyi duk abin da masoyin ka yayi kai ma kawai sai kayi "tom yan zu bari nima in kama kukan. Nann kuwa shima ya buɗe baki ya fara kukan ummmm aaaa. Ita kuwa me take in ban da dariya.

Haka tsakanin mata da miji sai Allah, a haka de suka shirya kamar komai bai faruba. Shikuwa Abdul wannan abun yana ransa, shin waye yakirashi daga office? kuma shi yasan yau tin da yafita yana office bai je ko ina ba, Haka de yake ta tunani a kan abin.

*____________AMAR* Murna ya keyi yakusa kama aikin sa, yan zu idan Allah ya kai mu dare daddy ya tabbatar da abin da na gaya masa shi kenan Basma tazama tawa, wani ɗan ƙaramin ihun daɗi yayi yana tsalle a kan gadon sa. Gaskiya ina son Basma ina mata son da babu wani magaluki da zai iya mata, kuma ni walhi babu ruwa na da Auran ta in de har daddy ya gano su to nide wuff! zan yi da ita abuna, wani abu ya tina sai kuma yayi shiru. Shin ma yan zu idan daddy yaraba su kuma yaji ance nine tsohon saurayin ta an ya bazai zargi wani abu ba! shuru yayi yana tinani, jan zuwa wani lokaci yace.. Nasan abun da zan yi bazai gane ba.

Zau ne suke duk kan su domin cin abin cin dare. Abin da yabasu mana ki shine, Basma da Abdul sai raha sukeyi suna cikin farin ciki gashi kuma sun zauna a kusa da junann su. Ali da daddy suma abin ya basu mamaki, amma sukayi shuru da bakin su kamar babu komai. Shi kuwa Amar abin haushi ya bashi ganin yanda suke ta dariya har da wani man nuwa jikin sa.

Basma ce tace... Wai daddy baka bani labarin Anty Zainab da kuma litil dina bafa? tana kallon daddy "Ai busu san nann muka zo ba, kin san halin shi in da yasan nan zamuzo ai da sai mun zo dashi, in ji daddy yana bata amsar tam bayar ta "to daddy kuba mu shi mu zaina da shi mana, cewar Abdul yana kallon daddy? daddy yace.."Ai muma shi kaɗai ne a gaban mu badan haka ba ai da tini mun baku shi "Amar takira sunan sa a han kali ganin yagi cin abin cin sai jujjuya cokali yakeyi a cikin abin cin...

Me yake damun ka? naga tin ɗazu baka fara cin abin cin ba sai tinani kakeyi. Amar lokacin da yaji muryar ta acikin kun nan sa sai da komai na shi ya tsaya na dan lokaci kadan, yanayin yan da takira sunan nasa sai yaji tam kar yau tafara kiran sunan nasa, sai yaji tam kar tafi kowa iya kiran sunan sai yaji tam yace dan Allah ta ƙara kiran sunan koda sau ɗaya tak amma ina bazai iya ba kode inc "Amar lafiya kuwa kake yaƙara jin muryar ta a karo nabiyu wan da tasa tsikar jikin sa tashi "Bako mai walhi ina tinani wani abu ne.

daddy ne yafara tashi yace musu sai da safe, shima Ali yabi bayan sa. Bayan ɗan wasu dan lokaci shima Amar ya tashi da niyar tafi sai kawai yaji Abdul yace jirani mutafi, sai da ya kama hannun ta ya man na mata kiss sannan suka tafi shida Amar izuwa ɗakin kwanan su. daddy da Ali basuga lokacin da yayi mata kiss ba, sai ganin lokacin da Amar da Abdul suka shige ɗaki daɗaya ita ma Basma tashi ga ɗaki.

Daddy zama yayi a ƙasa daɓas zaman yan bori, Sannan yace.. Walhi ta tabbata basa zaman lafi naga ni da idona, Ali ne ya ɗaga shi domin su shiga ɗaki sayi maga nar a cen. Ali yace...Yan zu Yaya menene abun yi? Cikin fishi daddy yace.."babu abin da zai hanani raba auran nan, ita kadai Allah ya bawa yaya na kuma namasa alƙawarin zan ri ƙeta amana.

Amma yan zu in zo in mata auran dole to wallahi bazata saɓuba. Daddy yace... Yan zu kasan me zamuyi? Ali ya ce.. "A'a ban sani ba, amma ga wata da bara Daddy yace.."ina jinka Ali yace..."gobe idon Allah ya kai mu zan ce mata haƙorina yana min ciwo, Kaga zata ce muje asibitin ƙawar ta wato LUBNA tin dade ance itama anan tayi aure kuma har tasamu ai ki a cikin asibitin, kaga idan mukaje sai mu tam bayeta waye wan da Basma takeso a baya kaga in ta gaya mana mukuma sai mu nemo shi, Amma fa kar mu bari Basman ta sani sai de muyi mata bazata, kaga in a ka samo shi sai kawai a'raba wannan auran sai mu aura mata wance. Kaga in a kayi haka shikenan kar muje mu rasa ta.

Cikin jin daɗi da wannan maganar daddy yace haka za ayi kaga kuwa in mukayi haka kowa ya huta. Ahaka zuka tsyar da maga na, Sai a lokacin han kalin daddy ya kwanta.

*YAU TAKE RANAR LITININ* Bayan sun karya ne Abdul ya tafi office. Ali ne yasamu Basma ya tsa ramata duk yan da suka tsara jiya da daddare, ita kuwa Basma tace... "Allah sarki Allah ya bada lafiya, yan zu kun san wani assbitin ne wan da zakuje na hagori? tana tam bayar su, dede lokacin Amar yafito shima "a'a bamu sani ba zade muje muyi tam baya, da sauri Basma tace..."A'a basai kun jewani kuriba ai Lubna ta nann a garin nan kuma likitan hakorice saboda haka bari in baku Address ɗin ta, haka kuwa akayi bayan ta basu sai kuma ta kallin Amar tace... Amar kaje karaka daddy kaga kai ma sai ku gaisa da Ita, Kafin ya bata Amsa daddy yace masa? yau bazaka je gurin ai kin babe? Amar yace..."Eh yau babu da ai ki

8 / 9