kaƙi Bani gudunmawa"
Malamin yace.. "Haba A'mar Dik wata nasara DaKasani A Hankali a ke samunta Amma kai naga a lama da Hanzari kake Son taka, kayi haƙuri Ka d'an ƙara jira"
A'mar Zeyi magana malamin Yace "kar ka damu. Yan zu de yakamata kumatsa kusa... Sannan ya barSu a gurin"
"ok gamunan Zuwa" Kafin Subar Gun da suke Ne Sega Tanan Da Saurin Ta Tana Zuwa Tace "Barkan kuda rana"
Kafin A'mar Yayi magana. Sadam yace "Barka yanmata me kikeso?
Basma Tace Sunana "Basma Najib Nima 1 daga Cikin student Din wannann makarantar Kuma. Ina Son.. Kakoya min Rawa ne Domin Munada gasar rawa da za muyi Kuma nima ina ciki... Sannann Kuma irin Rawar Da naga Kanayi Jiya ita Nake Son kakoyamin"
Tin Tana Cikin maga nar Sadam yake cewa a cikin Zuciyar sa. Wannann irin Zuƙeƙiyar budurwa amma Ita rawa ta keson koya Kuma Tarasan Meko amata Rawa Se namiji
Haka ita Kuma Tachi gaba da cewa "please ina son inci gasar domin Shine mafarkina"
A'mar Yace... "Nikuma saboda cikar mafarkin ki Sena bar nawa ko?
Se tace "Bafa A kyauta Zaka Din ga koyamin ba Zan dinga biyan ka please"
Sadam yace "Ok dama Biya Zakiyi. To nawa zaki din ga biya Dik Sati?
Tace "Zan dinga biyan nera Dubu 5, " yace ki'kara masa mana, Dasauri tace "to zan Din ga biyan dubu 10 Dik Sati"
Sadam yace "To shikenann badamuwa Nima abani Wani Abu"
Lubna Tace "To kafin a baka wani Abu Sekafara koyamata Tukun, Kaiba da Rawaba kai da Surutu".
Sadam Zeyi magana kenan Akakirasu Suka bar Gurin Yana Hararar Lubna , Bayan Sun Shirya in da zasu fara koya mata Rawar gobe.
ita Kuma se dariya Take tayi masa
Suna juyawa Suka Hadu da Kamal. Yace "Wato ke tauRin kaine dake ko Nace miki Matata Bazata yi rawa ba kekuma kin Dage ko to walhllhi in har nagan ki agunrawa to wallahi Se kingane niwaye.."
_________________________
*TO FA GA SABON BOOK NA FARA Me taken Muzuba muga ni Please ina bugatar Addu ar ku a gareni* *NAKUHAR KULLUM *S REZA*
*The end part 1️⃣*
*To be continue ⏩....*
*In naga ruwan comment Zan cigaba Amma in ban ga Comment ba bazan cigaba ba*
Please
Sher And
Comment
By S REZA
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: ©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
CA'KWAKIYAR SOYAYYA ♥️💘.... PAGE 5️⃣
.........Gurin da suke ya nufa Babu alamar tsoro a tare dashi, Yana zuwa ya nuna Wanda yayi wannan maganar, ya ce " me maka ce? "Shima cikin rashin tsoro ya ce.. "Cewa nayi Zata iya ɗaukar maza guda huɗu.. ai ko ƙarasawa bai yiba. Amar Ya ɗau keshi da wani Mari Wanda har sai da yaga ha'koransa guda 2 a hannun Sa, Kafin kace me, Sauran biyun Sun yo kan sa. Cikin sa'a ya 'kara kaiwa nafar kon naushi Wanda Sai da ya fad'i, Ya kamo na bayan yayi daniyar 'Dago shi Se yaji Saukar wani abu a bayan sa, Yana dubawa yaga Wannann na farko ne daya Zubar masa da ha'kora Shine yataso ze Soka masa wu'ka Shine Basma ta rigashi tabuga masa dutse akai.
Nann take yazube , Amar yatara su a guri d'aya, Ya ce waya turoku gurina jiya?
Cikin Tsoro Sauran Suke kallon Sa, Ogan nasune ya ce.. "Kai ne Amar?" Cikin tsoro yake Kallon Amar ganin yanda idon sa ya sake color, Amar ya ce "waye yaturoku Gurina? "Shima yana Yiwa ogan nasu tambaya a karo na biyu
Cikin Tsoro ogan nasu ya ce.. Kamal Shine ya turomu, Kuma ba mashin yace musataba, Cikin mamaki yake bin Su da kallo ya ce.. Waye kamal? Domin Shi har ga Allah Bai ma san waye kamal ba.Basma ce ta ce.. "Kamal kuma,To meye kamal d'in ya ce muku?" Ogan Nasu ne ya cigaba da bayani.
"Ya ce mun Mu biku abaya duk gurin da ku kaje, Sannan ya ce.. Wan da suke tare da ita muyi masa duka, wato kai kenan,ita kuma yace Mu d'auko masa ita mukai masa in da yake.Amar ya ce.. "To meyasa baku Sace ta ba kuka sacemin mashin?" Yana kallon Su. Ogan ne ya ce.. Eh da Mun so muyi hakan amma ruwan da a kafara ne alokacin Yasa muka rabu daku,kuma Mun sace wannann mashin d'inne Domin kar kutafi ku tsaya neman sa har a d'auke ruwa, Amma bakuyi hakan ba.
Waya yazaro yakira yan sanda domin Sutafi dasu, bayan wasu lokuta Sega motar yan sandan Sun garaso gurin, Nan take aka Saka musu ankwa akayi gaba dasu.
Amar yajuyo Gurin basma ya ce.. Waye Kamal? "Nan take ta sanar dashi, Shine wannan na school d'in nan nasu,Nan take shima ya gano shi, ya ce " Dama har yanzu yana tare da ke ne? Basma ta ce.. "Ni Wallahi har na manta dashi a rayuwata kai ma bana son kasa wannan a ranka please.
Cikin 'Dan damuwa ya ce.. To yanzu da kika biyosu nan gurin ke kad'ai in da ban zoba sun miki wani Abu kuma fa? Yana maganar yana 'kar6ar a gogon sa yana sawa a hannu, kafin tayi magana ya cikigaba da cewa, a kan mashin Zakije ki Jawo wata damuwar.Wannann mashin d'in Ina jin sa tamkar wani abune daga jikina, Duk wani Abu naka Ina girmama shi Sabuda haka kar kace a kan mashin kawai.
Jin haka yasa yaji dad'i Sannan yace.. Duk da hakan Kin yi kuskure, Kar ki'kara irin haka kinji. Cikin murna tazo dagudu ta rungumeshi ta ce.. Ina sonka Sosai Amar. "Shima rungumar ta yiyi ya ce.. Me too my baby.
Haka suka kamo hanya zuwa bakin ti-ti. Seyan Zuma basma Ta tuna da wanda ya kawo ta nan wato me mashin, Amma ta duba bata ganshi ba, Wanda tun lokacin daya ga Basma taje Gurin su sun fara Biyota kamar zasu daketa shi kuma ya tada mashin d'in sa yabar Gurin. Ganin bata ganshi bane yasa suka tafi.
Har Gurin da Ta bar su Lubna da direban su me mashin d'in ya kai su, Dama kuma ta kira Lubna ta tambaye ta suna Gurin har yanzu ko dau sun tafi?Inda Lubna ta hauta da masifa kafin ta ce mata suna Gurin. Sallama Suka yi da Amar a kan zeje gurin ƴan sandan
Domin jin abin da zai faru motar tashiga tana d'aga masa hannu Shima yana d'aga mata hannun har suka tafi. Tana kallon irin hararar da Lubna take bin tadashi Amma ko kallon ta bata yi ba har suka isa.
Gaskiya Basma abin da ki keyi wallahi Babu 'kyau Yanzu gashi kin samun fasa zuwa gurin da mukayi niya Saboda wani banzan dalilin ki.Lubna ce take wannann masifar ganin Basma ta sa Sun dawo gida, Cikin Sanyin murya basma ta ce .."yanzu haka daddy yana nan yana jiran dawowar mu in yaga mun dad'e kin san zeyi fad'a.Lubna ko magana ba batayi ba ta wuce ciki ta barta.
...............BASMA
turus tayi tana kallon mutanan da bata san suwaye ba tayi tana kallons u a parlon, Cikin mamakin abin da yakawo su gidan nasu ta bisu da gaisuwa amsawa duk sukayi suna kallonta, Kusa da daddy ta je ta zauna Domin jin abin da ya kawo mutanan,amma kash tayi rashin Sa a domin tana zama sukuma mutanan suna cewa.. "Tom Muzamuko ma se in mun dawo,kuma munji dad'in yanda kuka amshi bu'katar mu mungode sosai"cikin fara'a daddy ya ce.."masha Allah bakomai ai yanzu an zama d'aya ya tashi ya raka su izuwa gurin motar su.
Basma babu abin da ta fahimta acikin zancen su, Hakan ne yasa bata bawa maganar wata muhimmanci ba ta cigaba da harkarta .Har cikin d'aki taje ta samu daddy ta ce ..daddy me yakawo Su gidan nan naga kamar nasan su ko daddy? Daddy cikin san yaga ya faran ta mata ya ce.. eh kin sansu amma tun kina yarinya domin tunda kika girma ba suzo ƙasar nan ba sai wannan karan, Kuma yanzum ma sun zone da abin arzi'ki.
"Daddy me suka zo yi?" Basma ta tambaye shi domin ita jikin ta yafara bata ba lafiyaba, "daddy ya ce.. Sunzo ne da batun Suna son abasu auranki ga yaran su, Kuma mun amince domin yaran d'an manyane, Yanzu haka yaran ya daga cikin manyan yan kasuwa da suke cikin 'kasar nan, yajuyo yana kallonta ya ce.. daughter in kin auri yaran nan zaki ji dad'i kuma ni burina kenan Saboda haka na yarda da mutanan kuma nace jibi suzo se ayi maganar domin nasan na isa dake baza kibani 'kunyaba ko my daughter? Ya ƙarasa maganar yana kamo kumatun ta yana ja.
Basma tun da daddy ya fara maganar ta tsaya tana kallon sa cikin mamaki, Aure kuma! Cikin zuciyarta take cewa, to ma wai haka a ke aure bansan mutum ba to bama wannann ba karatuna fa? anya kuwa daddy yasan me yake cewa kuwa! Jin ana ja mata kumatu ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, Ta ce..daddy "aure fa kace? "Daddy ya ce.. "eh aure nake nufi domin mutane sun fara magana a kanki wai nine na hanaki haure Bana jin dad'in abin da dagin suke cewa a kaina da kuma ke. Yay maganar hawaye na zubowa daga fuskar shi, yacigaba da cewa...Suna zagina sosai nikuma ba wai aure ne bana so kiyi ba, inason in samu wanda zai ri'kemin ke da amana ne kuma inason ki auri me arzi'ki domin kihuta, Hakan ne yasa na za'bamiki shi yaran yan kud'i sosai kuma bawai kud'in baban sa bane kudin sa ne zaki ji dadin zama shi kin ji daughter? Yana kamo hannunta.
Basma wannan shine karo nafar ko da taji tausayin daddy, Shine karo na farko da takasa musa abin da ya ke cema ta kuma gashi tasan abin ba me yuwa bane tasan baza ta amince ta auri wani ba in dai ba Amar ba , to amma meyasa ta kasa yin musu? Tambayar da ta keyiwa zuciyar ta kenan. Maganar daddy ne yadawo da ita daga tunanin ya ce... Jibi za suzo tare da yaran se kuyi magana kin ji, in sha Allah zaku fahimci juna dashi , haka tana ji tana kallo daddy ya tashi yatafi amma taka yin musu kuma zuciyar ta takasa amin ta da maganar daddy, haka itama cikin sanyin jiki ta tashi tabar gurin .
...............AMAR
Abba Gani ya na kallon abban nasa cikin son jin me zai cemasa abba ya ce.. "Takardun ka natura izuwa gurin wani professor Dayake *ABUJA,* kuma ya duba yagani ya ce in turaka domin takardun sun yi kyau. "Cikin farin ciki ya ke kallon abban nasa da ya rage masa a duniya wanda ba yason 'bacin ransa ,Wanda akansa yake yin duk wani abu domin gobensa, ya ce... Abba wallhi naji dad'i sosai shima abban dad'i yaji yana ƙara jin 'kaunar d'an nasa a zuciyar.
Numbar Basma yafara kira domin yayi mata albishir da cewa burin sa ya kusa ciki. Kira d'aya ta ɗaga amma kafin yayi magana ta riga shi da cewa.. Amar kana ina ina son mu had'u yan zu? "Yanzu ina gida nima dama a 'kwai abin da zan gaya miki. Basma ta ce.. To yanzu ina zamu had'u, Amar ya ce.. Zaki iya futowa daga gida? Cikin sauri ta ce.."eh zan iya , nan take yace mata ok tom kizo gurin Shagon Sadam ina gurin yanzu haka ok ta ce sanan ta tashi da sauri.
Tunani take yaya zata fita daga gidan nan! Nan take dabara ta fad'o mata da sauri ta fito falor tana zuwa ba kowa sai little, Dasauri ta kamo hannun sa ta nufi d'akin ZAINAB. Tana zuwa ta ce.. Anty little zai rakani gidan su Lubna zan 'kar'bo wayana naman ta da ita a gidan su? "Kasan cewar gidan bawani nisa yasa anty "zainab cewa.. To kuyi sauri domin yanzu Daddy yafita kin ga ba yason yarinka ganin ku a waje kiyi sauri kin ji tana mata hargaɗi da hannu a kan kar su dad'e. ok Basma tace tan kama hannun sa suka bar falon Sai da tabi ta gidan su Lubna Domin taraka kafin suka tafi tare.
Basma da Lubna Sun riga Amar zuwa inda suka samu Sadam agurin. Bayan sun gaisane Suka samu guri suka zauna , Kafin Amar yazo Basma Ta kwashe duk abin da sukayi da Daddy ta gaya mata "cikin mamaki Lubna ta ce... To yanzu me abin yi? Tana tambayar Basma? Basma ta ce ..shine nima ban saniba, Bansan yanda zai dauki maganar b... Kafin tagarasa Sai gashi ya karaso , kai da ka ganshi kasan yana ciki. Farin ciki.
..............AMAR
Yana gan ku cikin wani irin yanayi , To nazo muku da labari kuna sonji, Cikin farin cikin da yakasa 'boyuwa a fuskar sa yake wannan maganar. "Amma jin abin da Basma ta ce ne yasa ya tsaya cak agurin yana kallon ta.
Basma ta ce... Yaka mata muyi Aure Amar , wannan kalmar yaji daga sama tafito daga bakin Basma, Taci gaba dacewa... Saboda kaga jibi masu neman aurena zasu zo gidan mu, kuma Daddy ya amin ce musu, kuma nina ji a jikina daddy na bazai yarda muyi aure da kai ba please dan Allah Amar muje wani guri muyi auran mu Ta karasa tana kuka kamar Ranta zefita .
Amar ya ce..Aure kuma Ban gane ba? Yana tambayar ta
Cikin kuka ta ce.. Amar bana bukatar ina zaka kai ni ko kuma ina zaka ijiye ni ni dai burina dan Allah muje muyi Aure, Bayan soyayyar ka bana bukatar komai a gareka player.
Amar ya ce .. To sai naga ace za ayi aure yanz..."kafin ya karasa ta ce Amar in dai kud'ine matsalar ka zan ji da komai tana kallon shi cikin hawaye.
Amar yace "wai kud'i "kafin yayi maga ta ce .. To menene matsalar ka? Tana bin shi da kallon wanda izuwa yanzu kukan takeyi, ganin yayi shiru ne tace.. "Shin Amar kana sona? Zaka aureni?"
Amar a karo na farko da zai runguume ta ganin irin kukan da takeyi , ya ce ..tabbas zan aureki, kuma zan baki duk wata kulawa da bakiyi tunani ba , tana jikin sa har yanzu kuka takeyi , tanajin damuwar ta tana raguwa, Ta ce ... Ina sonka Amar ina 'kaunar ka ,shima abin da yake fad'a kenan har zawu wani lokaci Sannan ya saketa.
Sannan tace ya a kayi da su Kamal. Yace ban je gurin ba har yanzu amma nasa wani abokina a kan maganar shima police ne. Batace komai ba har ya rako su gunda zasu shiga keke napin sannan suka koma shida Sadam .
Duk wannann abin Da a keyi , lubna da Sadam suna gurin amma babu wanda ya iya cewa komai domin Lamari. Na sune su biyu.
Amar ya ce.. Sadam Wallahi da matsala shin kasan abin da abba yace min? "Sadam ya ce.. Aa, Nan take ya 'kwashe duk yanda sukayi da abban sa ya gaya masa ,
Sadam yace. "To meyasa baka gaya mata ba? "Amar ya ce... To tayaya zan gaya mata acikin wannan halin da take ciki ni yan zu ma wallahi ban san abin yiba
Sadam ya ce ..Amar wallahi Basma tana sonka kuma son da ta kemaka ne yasa tace kuyi aure please dan Allah kar ka bata kunya pls
Amar yace ...sadam bari zan yi tunani a kai ..daga haka babu wan da ya kara magana har suka bar gurin ....✍️📝
*YAU A KE YIN TA ANYA KUWA HANYAR DA BASMA TABI ZATA 'BULLE KUWA ,. Shin Amar Ze yarda ya bar aikin da baban sa ya sama Masa , ya auri Basma ,. Shin waye Wanda DADDY YAZA BAWA BASMA,. KU KASANCE DA... S REZA*
HAQIKA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️📝
the end of Part 5️⃣
To be continue..✍️
*ALQALAMI S REZA✍️*
*PLEASE COMMENT AND SHARE DAN ALLAH 🙏🥰*
~BY SALIS M REZA~
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: CAKWAKIYAR SOYAYYA❤❤
NA
S REZA ✍
©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*
_{Al'umma Writers Ƙungiya 'Daya Tamkar Da dubu Farin Cikinmu, Mu Faɗakar Da Al'umma Domin Su Farfaɗo Su Gane Gaskiya Al'umma. Sai Don Al'umma Allah Ya Ba Mu Ikon Fadakar Da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826
بسم الله الرحمن الرحيم...
**DAGA, S REZA*
*Wannan littafin yana da sar'ka'kiya yana da hargitsi 'kunshir ya, fahimta mu cigaba domin kuwa, Sai kun bi ni a hankali cakwakwakiyar soyayya. Ba a *ma fara komai ba fa ku kasance da S REZA** 🙏
________________________________
HAPPY MAULUD 🕌
❤CAKWAKIYAR SOYAYYA❤. PAGE ⚓️ 3⃣
...Sun riga shi 'karasawa gurin, Amar yake ce mata "Abin da nake so da ke, Shi ne. In ya zo kar ki ji tsoran shi, ki zare masa idanu, ki gaya masa magana babu abin da zai iya. Ya cigaba da ce mata, kin ga can ya nuna mata. Ɓarin hannunsu na dama, ta bi hannun da kallo, ta ce "Na gan su me za su mini? Ya ce Ba za su bari ya yi miki komai ba."
Basma ta ce"Ni gaskiya tsoro nake