Chakwakiyar Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Romance

Chapter   4 / 9

9K to 12K   out of 24.3K words

yagamajin Dik abin da tace, "Sannan yakira Basma yatam bayeta gaskiya ne? Da Sauri tace "eh daddy tin jiya Naso in gaya maka amma na ban ta, Daddy yace" Tom amma fa tare da dreba Zakutafi, Basma bataso hakaba amma bayanda Tayi suka hagura.

Tafiya Sukeyi Kanta yana ga wayan ta Se danne² takeyi abun ta, inda itakuma Lubna take ta zuba Surutu, Kamar an ce tad'ago Kanta Tana d'agowa idonta yasauga akan wasu Samari su biyu A kan mashid'in Amar, Kar tasan su amma amma ta manta in da tata6a ganinn su.

Magana tayiwa dreban Akan ya tsaya Ta sauqa Ai kuwa yanemi 'kuri ya tsaya Lubana tana cewa"lafiyakuwa? Basma tace.."zaku iya jirana kokuma kuje zan sameku a cen, kokuma de, Zamuyi waya, Tana bad'in haka tafita daga motar

Me mashin ta samu tanuna masa mutanenn da zedingabi a baya har in da suka tsaya, me mashin zeyi mgn tace.. Kar kadamu Zan baka komanawane jin hakanne yasa yayi shiru. Waya ta ciro tskira Amar amma no Amsar, Shikuwa me mashin 'Kara bin mutanann da tanuna masa yakeyi.

_____SMAR
Zaune Suke Shida abokin sa wato Sadam Yana gaya masa cewa an sace masa mashin Kuma shide baya tinaninn kowa, "amma abin da mamaki, in ji Sadam Bayan ya gama jin dik abin da yace.Amar Ina zuwa yace yana barin gurin, Yabar wayar sa a gurin Bayan ya tafine Kiran Basma ya shigo waryar har sau uku amma Sadam be d'aukaba, akira na hud'un ne , yayi dede da ya iso guri da Sauri yad'aga domin kuwa katin waya Yaje siyiwa domin kiranta.

Amar naga mashin d'inka please kazo yan zu gashi ma ina bin su a baya dan wkayi Sauri, Abin da tace kenann lokacin da Taji an d'aga kiran, Cikin mamaki yace.. "Basma are you ok? "Tace please I'm ok dan Allah kazo dawuri, yace kina ta ina yanzu? Yagaya masa inda Suke sannan ya kashe wayar, Ko mgn beyiwa Sadamba Shima yafito yanemi me mashin Suka nufo gurin

A wani gurin Samarin Suka Tsaya, Da a lamar gurin ogansu sukazo. Tsayawa sukayi da Nasu mashin d'in Suna kallon su. Setaji ogan Nasu yana cemusu.. "Meya baku cire number ba mashin d'in ba? Amma kun San Wannann gangancine, Kuma kun biyo cikin gari Dashi bakuda Han kali ne? Waya kuje gurin masta yan zu yacire wannan lambar, yana nuna musu da hannu a kan su hau mashin d'in sutafi.

Dik abin da Suke Fad'a Basma tana jin su, Dataga alamar Tafiya zasuyi kuma gashi Amar bezoba Se kawai Tanufi gurin su. Tana zuwa tace.. "Barkan ku wannan Mashin d'in mune, Sekuma tayi shiru Don ganinn irin kallon da sukeyi mata , ogan Nasu ne yataso tana nufota yana cewa "ina lasisin sa Yake? Ina takardun sasuke? Basma tace.. Kamar yaya? Ogan yace.. "Idan kika nun amin ai se mubaki mashin d'in, d'aya daga cikin yaran sa yace.. "Ke megida yana Tambayar ki, kibashi amsa mana?

Oga se'kara nufota yakeyi itakuma tana jabaya, Yana wani lashe baki yana cewa.. Haba 'yan mata kiyi magana mana, ya kai hannu da niyar ta6a bakinta yaji an ri'ke hannunn, Kafin yayi magana, Amar yace.. Dan Allah kuyi hagu ri, yaja hannunn basma Suna tafiya yana cemata kar kidamu mashin d'ina ze fito,

Basma tace "baga mashin d'in ba allha muje mu kar'ba yana janta tana Wannann maganar

Sukuma ogan Nasu yana ganinn Amar yatafi da ita yakecemasa, kai yaro ai da kabar ta mun d'an mayar da yawunmu irin wannan tso'kekiyar yarin ya, Daga Gani kaima kana 'kawsar raban kako? Kai anyama kuwa zata iya, 'DAUKAR nawyin mutum 4 Kaga in Muka Mure kaima seka 'kawshi sauran, ammafa gaskiya, Kai bakada tsuciya in de har bakazo mun 'kawshi ganimaba, yana fad'in haka suka 'kawshe da wani irin dariya

Amar dik abin da sukecewa acikin kunnenn sa, Dikda suma d'in sun yine domin yaji. Cek ya tsaya, domin jin abin da Sukace na 'karshen juyowa yayi yana kallon yan da Suke faman dariya, ya kalli Basma itama shi take kallo.

Ya cire a gogon Dayake a ma'kale a hannunsa ya bata yace bana son ya 'kar ye, kijirani.... ✍️📝💪




**Tofa 🤔😃😃 inaga* *Amar Ze gama dasu 💪*
*

The end fart 4️⃣
To be continue...

*HAQIGA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️📝*

*PLEASE COMMENT AND SHER DAN ALLAH 🙏🥰,*

*NA KU HAR KULLUM S* ~REZA~
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CAKWAKIYAR SOYAYYA*


*Story and writers...* ✍️
*S REZA*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...

*I'M BACK AGAIN, PLEASE MY FANS SORRY FOR AVERTING 🙏❤*

*I* *LOVE ALL MY FAN'S* 🥰🥰



CAKWA KIYAR SOYAYYA❤
PAGE 7⃣



...........Basma Tashi tayi tanufi gurin Daddy domin Tasanar dashi komai, Amma kash!! Tayi rashin sa'a domin tunda sassafe yabar gidan bata sani ba. Amar gida yaje Sukayi sallama da Abban sa bayan yamasa fad'a akan yakula da kansa kar ya biyewa abokan banza, Dade sauran su. san nan yanufo gidan su Basma domin yin sallama da Alhaji Sani. Misalin Qarfebiyu na rana Amar yakaraso gidan, Dede lokacin Daddy yana 'ko'karin fita shi da Ali. Ganin Amar d'auke da A'kwati ne yasa suka tsaya. Bayan ya'karaso gurinsu ne yasunkuya
har kasa ya gaishe su, San nan Ya Sanarwa da Alhaji Sani Abinda ketafe dashi, Wato yasamu aiki zetafi. "Allhaji Sani yataya shi murna had'e da fatan nasara, San nan ya masa ihi'sani Suka shiga mota suga bar gidan.

Basma Duk abinda Sukeyi a kan idonta har lokacin da Amar yasa k'afa yabar gidan Taso ace sunyi sallama amma gashi ya tafi ko kallon gurin da nake ma beyiba, Har ya hau mashin d'in da Sadam ya kawo shi a kai yatafi, Fashe watayi da wani irin kuka Taji Aranta !Anya kuwa Amar yana santa? ahaka takoma d'aki taci kukan ta Iya san ranta.

*_________WASHE GARI*
Dawani irin matsanan cin ciwon kai ta tashi, Takasa walwala kana gallonta kasan akwai abinda yake damun ta, Daddy ne da kansa yaje har d'akinta yataso ta. Babu irin tambayar da beyi mata ba a kan abinda ya ke damun ta amma ta ce " Babu komai, Haka daddy ya hakura badan ya yarda ba.

Tun da suka gama breakfast tashiga d'akin ta taci gaba daga in da ta tsaya, Ta manta da cewa yau ne Za a zo maganar sa ranar ta. Wasu motoci ne guda biyu Suka shigo harabar gidan, Motoci ne masu d'auke da Tam barin wani abu wanda nide bangane menene ba Bayan sun yi parking ne dukkanin su suka fito a tare su hud'u ne maza ukku se mace guda d'aya. Kana kallon su kasan Sun jik'u da naira, Ga wani irin Kama da sukeyi dukkanin su.

Banyan sun shiga cikin parlon ne A ka tar6esu da abubuwan marmari, Nan take suka ci abinda zasu iya ci, Bayan Angama cin komai ne Allhaji Sani ya ce" Tom masha Allah daya kawo mu wan nan rana , Duk dacewa tun zuwanku na farko muka gama yin duk abinda yada ce, To yanzu Allah yakawo mu yau da muke fatan Cika muku alqawarin da muka d'auka, wani abokin Alhaji sani da ya gayyato ne ya ce" Tom mash Allah Sabida haka muna jira daga gareku Shin kun shirya akan base mun saka bikin da nisaba ko kuma dai kuna da d'an gyare gyaren dazakuyi?

Dasauri macen Cikin su tace"Aa bamu da wani abu da yarage, mu ku muke jira san nan kuma bamaso a saka ranar da nisa. Haka kuwa akayi bayan sun bada sadaki ne aka saka ranar biki a kan wata biyu masu zuwa Abisa yarjejeniyar b'anga rori guda biyu, a haka Suka ci gaba da wani hirar akan kasuwanci .

Misalin hud'u Suka kama hanya suka tafi da fad'in cewa zasu turo yaran nasu yazo domin su fahimci juna kafin lokacin.

*___________BASMA*
Duk abinda a keyi bata sani ba tana sama d'akin daddy tana barcin dole, wanda bayan tasha kuka ne ya d'auketa.Jitayi ana tashinta amma kamar a mafarki ganin abin kamar azahiri ne yasa ta bud'e idonta` a hankali wanda suka yi jazur tasauke su a kan Lubna. Ganin itane yasa ta tashi da sauri tarungumeta tagara fashewa da kuka, ita kan ta Lubna ta tausaya mata sosai.

Bata rarasheta ba barin ta tayi seda tayi me isar ta. San nan basma ta ce" *LUBNA* yatafi wallahi yatafi ya bar ni, yazan yi? Duk cikin kuka take wan nan Maganar. *LUBNA* Takamo hannunta ta ce" please dan Allah kidena kuka haka ai zedawo Ba tafiya yayi ba yana sane dake Kuma ai yagaya miki shekara daya fa kawai zeyi yadawo please kibar wannann kukan kin ji.

*LUBNA* kallon ta takeyi tana tausaya mata` ya zanyi in sanar mata da cewa an saka ranar ta da wani? Wanin ma bamusan waye ba, anya kuwa *BASMA* zata iya jure jin abinda zataji daga bakina?,Tambayar da *BASMA* ta watso mata ne yasa hanjin cikinta juyawa "Ta ce..sun zo an saka ranar ko? Sanar da ni cewa an saka ranata kar ki 6oyemin ko mai *LUBNA*, Da gaske abin da nagani afuskar ki gaskiya ne Shin daddy ya bayar dani? Tini *LUBNA*tarasa abin da zata ce mata Se gyad'a mata kai kawai ta keyi kamar qadan gariya.

Nan take *BASMA* Tazube agurin tamkar babu numfashi atare da ita, ita kuwa *LUBNA* Metake in banda ihu da kiran sunann *BASMA. BASMA BASMA* Amma ina ko motsi batayi ....✍️📝

WAN NAN SHINE MAFARIN QADDAARAR SU GABADAYAN SU , shin kokun San waye wan da a ka saka musu Rana da Basma? shin Kun San cewa Kamal Yana Raye Kuma yace se ya au reta?
KU kasan ce da S REZA..✍️

*KUYI HAKURI* *ABISA JINA SHIRU KAWNA 2, ABUBUWA NE SUKA* *MIN* *YAWA DA FATAN ZAKU MIN UZURI* 🙏🙏🙏


The end of part 7
To be continue..✍️



*PLEASE COMMENT AND SHERE DAN ALLAH* 🙏🥰


*BY S REZA*
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: CAKAWKIYAR SOYAYYA💋❤💘
Writer by. S REZA.. ✍️

©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...


I love all my fans😍





Ca kwakiyar soyayya❤
PAGE 6⃣

..........Tafiya yake yana tinanin abin yi, Shin idan suka gudu da ita su kaje su kayi aure to shi kuma karatun safa? Kuma gaskiya ina son ta ina sonta, bazan iya jure wani ya aureta ba mutu'kar ina raye.

Horn yaji ana masa tabaya Har sau huɗu amma beji ba se a nabiyar ɗin.

Ya na juyowa su kayi ido huɗu da Ali, da mamaki Ali yake kallon sa yace.. "ina kake kallo haka ana tayi maka horn amma shiru? Amamar yace .."walhi ban jiba Sorry. Allhaji sani da yake cikin mota yaga an tsaya kuma yasan halin Ali da surutu, hakan ne yasa ya leƙo yana yiwa Ali magana akan suzo su tafi. Shikuwa Ali har ya fara yiwa Amar surutu in da yake cema sa "tare muke da abban Basma, in gida z aka kazo mu 'karasa" Ammar yace .."aa nagode nima yanzu zan ƙaraso."

Ali ya na shiga motar Allhaji Sani yace .."kaida waye a waje?" Ali yace.. "nida Ammar ne yaran da ya ke ko yawa Basma rawa." Alhaji Sani yace "gida zeje? "Eh waigida zeje in ji Ali, Alhaji Sani yace .."to kace masa ya shigo muta fi ai kuwa haka a kayi da kamar yayi ƙarya yace ba gidan zeje ba kuma seya fasa ya shiga suka tafi.

Sun shigo layin unguwar su kenan suka hango taran mutane a wani 'kofar gida, dama kuma megidan abokin Allji Sani ne, kasan cewar babu ta in da motar tasu za tabi tahuce ne yasa suka tsaya, dikkanin su fitowa Sukayi daga cikin motar domin jin abin da yake faruwa.

Suna ƙarasowa sukaji , wani ɗan saurayi agurin yana cewa .."Wai me kake nufine nifa ban ganeba? "Alhji Sani Yana zuwa gurun abokin nasa yaje yace.." mlm Bala mayake faruwane? Wan da a kakira da mlm Bala ya ce "wai wannan yaran ne yace yana son binta wato ƴar sa kenan, yaci gaba da cewa.. Wai in be aureta ba. Kafin ya ƙarasa Saurayin ya tare Shi da cewa.. "Ina son Auran ta kuma itama tana ƙau nata ku tam baye ta kuji yana nuna gurin da yarin yar da a ka kira da binta take.

Alhaji Sani cikin Sanyin murya yacee..."Yaro na yin soyayy ba kuskure bane, amma kuma yin aure bada izininn uba ba wan'nan shine kuskure, ya ciga bada cewa Saurayin , shin mene ne aikin ka? Yatam baye shi, Saurayin yace .. "Na kammala Degree, ya bashi amsa a ta'kaice. Alhaji sani yace.. Wato Degree, To da Degree zaka ciyar da ita? Saura yin yace ''yan laɓai idan na samu ai kin base komai ya tafi de de ba."

Alhaji Sani yace "Shin kai baka yi tunanin yanda a kayi a karene ta har takawo hakaba? A makaran ta me tsada a ka sa mar mata da iliminta, dik mutumin da ze iya haka to yasan yanda ze ta fiyar da gidan sa. Shin bama wan'nan ba kai yanzu a haka zaka iya tafiyar tan da iyali bakada ai kin yi , yaka mata kayi tinani dan saurayi. kafin Saurayin yayi magana sejin akayi yarinyar tace.."to ai ni ma ina son sa kuma mu bama bu'kar tar dik wanan'n abubuwa" cikin mamaki mutanann gurin suke kallon ta , Sannann alhaji Sani yace.. "Yan zune ki ke ganin haka yarinya, kar ki biyewa saurayi Kibar maganar iya yanki domin in hakan ya kasan ce babu wata riba da zaki samu.

Saurayin yace wa Alhaji Sani "bama bu'katar wani 'boye-'boye kafito fili kafad'a mana abin da kake nufi? Cikin jin haushin yaran Alhaji Sani ya ce...

Kari fe min bakin ka na shirme haka, waye kai a ina kake dik wan'nan ba shine abin da muke soba. Idan uba ze ba da auran 'yar sa gayaro to ya tabbatar yana da wata madafa domin komai ya tafi cikin nutsuwa. Yaci gaba da cewa Soyaya ai kowani matashi ma ai yana yin ta, amma in baze iya d'au ke d'awai niyar yarin ya ba ai ya zama a banza. Gaba d'aya dik saboda irin kune ya sa zama nin na ya lalace. Ya cigaba da cewa... Mu idan zamu aurar da yaran mu muna so musamu wa 'yen da zasu iya d'au ke damuwar sune bawa 'yenda daga 'kwana biyu zasu nad'e hannun su suce ya zan yiba, kai ma kuma ina ganin kana cikin su saboda haka kabar nan gurin. Yana nuna wa saurayin hanya.

"Cikin rashin Kunya sau rayin yace "ba damuwa nina san abin da zanyi ai."
Alhaji Sani "yace koma meza kayi kayi yaran ya ta fi yana surutan sa. San'nan ya dawo gurin baban yarinyar yace... "Kar kada mufa haka yaran zamanin na suke, mlm sani wato baban yarinyar ya ce.."badamuwa nagode sosai. Sannan suka koma motan dik su ukun suka tafi.

Dik abin nan da yafaru a'idon ammar, Haqik'a Alhaji Sani dik magan ga nun sa gaski yane to yan zu me kenan hakan yake nufi? Maganar da Alhaji sani ya yine ya sa ya dawo daga tinanin nin sa.

Kun ga irin samarin zamanin ko , se ka gama shan wahalar ka da yarin yar ka wani cen yazo ko aikin yi babu, wani ma zaman banza ya keyi wanima dan shaye-shaye ne, se yazo yasa yarinya ta fara sonsa , kuma kana aura masa kwana 2 zece ya gaji. Har suka 'kara so gida abin daya ke ta fad'a kenan. In da shima Ali dama sarkin surutu ne suka cigaba.

Bayan sun 'kara so gidane tin kafin Kowa ya fito Ammar ya fito ya nufi sa shin sa da yake cikin gidan kana ganin sa kasan wani abu na damun shi. Ze shige d'aki kenan yaji maganar ta. Juyo wa yayi ta ce.."kagama shiryawa ko? Domin gobe da Asuba zamu tafi" Kallonta yayi da'kyar ya 'ka 'karo murmushi ya yi mata , Sannan ya d'aga mata kai alamar eh ya gama shirin be jira ta 'kara cewa komai ba ya shige d'akin nasa.

Basma ganin kamar dawa ni abu da yake damun sa yasa taji babu dad'i, amma kuma tinda de ya amin ce zasu yi aure to ai shi kenan, bayan auran zata mantar dashi dik wata damuwar sa, da wan'nan tina nin ta koma d'aki tana jiran dare yayi ta fara shirya kayan ta.

Ammar yana shiga d'aki kan kujera ya zauna yari' ke kansa yana jin yana juya masa. Tashi yayi Domin jin 'kiraye² sallar magariba. Bayan yayi sallar ne ya zauna shiru yana

4 / 9