Chakwakiyar Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Romance

Chapter   3 / 9

6K to 9K   out of 24.3K words

ji ba zan iya ba don Allah abar shi kawai. Cikin san ya ga ya taimake ta ya ce:
"Kar ki saka tsoro a zuciyarki, ba abin da zai iya."
Suna cikin haka ne, suka hango motarsa tana zuwa gurin. Amar ya ce:
" Ki dage ina kusa da ke, kar ki ji tsoro."
Yana gama fad'in haka ya bar gurin, cikin sauri, domin kar ya gan shi. Basma tana ganin ya tafi, tsoro ya k'ara kama ta, ga shi kuma mugun yana zuwa.
Kamal tun daga nesa ya hango ta, yana tafiya idon sa yana kanta. Wani irin shu'umin kallo yake bin ta da shi, har sai da ta tsargu. Ta ji gabad'aya ta k'ara tsanar shi.
Kamal yana zuwa, ko sallama babu ya ce
" Ga ni na zo me za ki mini?"
Cikin muryar 'yaniska yake magana, me za ki ban? Fad'a min mana. Basma ta kasa magana sai ja baya take yi, shi kuma yana bin ta.Tana kallon gurin da Amar ya nuna mata cewa ba za su bari ya yi mata, komai ba. Kamal ya cigaba da cewa.
"Me kike kallo ne a can ki yi magana mana."
Basma suna had'a ido da Amar ya yi mata nuni, da hannu a kan, ta yi magana. Cikin juriya kuwa ta fara magana.
"To me za ka yi? Na ce me za ka yi? Ko kana tunaninn ina tsoran ka ne,? To bari ka ji in gaya maka, Na kira ka nan ne domin in shaida maka, daga yau. In har ka k'ara shiga harkata, Wallahi sai ka raina kanka, ban za wawa. In ka isa ka taɓa hannuna, tana miƙa masa hannun, tanabin shi. Yana ja baya, kamar yanda ya yi mata d'azu. Ka ta'ba na ce in ka isa. Tana ƙara tura masa hannunta.
Kamal cikin mamaki yake kallon ta. Ya ce
" Ke ko kin sha wani abu ne?"
Yana maganar alamar storo a fuskarsa. Ya ce
"Na ga alama ba kya cikin hankalinki."
Za mu haɗu wani lokaci, ya ja yaransa suka bar gurin da sauri.
Basma lokacin da ta fara ganinn alamar tsoro a fuskarsa, hakanne ya ƙara mata, ƙwarin guiwar cigaba da abin da take yi. Ta yi mamakin ganin bai iya yi mata komai ba.
" Ashe ma mugun matsoraci ne."
Ta fad'a a fili daidai lokacin da Amar ya ƙaraso gurin.
Amar ya ce
"Da ma na gaya miki yanzu ga shi kin gane, ko shi ɗin waye."
Cikin jin dad'i, ta ce
"Amar na gode sosai."
Ta zo da gudu ta rungume shi tana dariya. Amar wani abu ya ji, lokacin da jikinsu ya had'u guri d'aya. Kasa yin magana ya yi, har ta sake shi ta bar gurin. Tana farin ciki ta nufi cikin School.
Amar, tsayawa ya yi a gurin kamar wanda aka kafe, shi yana bin ta da kallo. Har ya daina hango ta, kafin ya ja numfashi, ya bar gurin yana murmushi.
Tun daga ranar ala'karsu me 'karfi ta shiga tsakanin, Amar da Basma. Rawar ma yanzu ba sosai yake koya mata ba.
Ɓangaran Kamal kuwa tuni, yake shirin yadda zai 'bullo mata.
Gobe za ba da hutu school kuma gobe za a rufe, school d'in. Kuma shi Amar wannan shi ne, final year d'insa.
Suna zaune su biyu suna zancen makomarsu, in aka ba da hutu, ya za su yi. Basma Tun lokacin da ya raba ta, da Kamal take jin sa a a zuciyarta. Hakan ne ya sa, take ganin ya dace su samu mafita.
Basma ta ce. Amar, cikin wata irin murya. Bai kar'ba mata ba ya juyo yana kallon ta ta ce.
"Wannan k'warin guiwar da ka ba inda da soyayya a cikin ta, ya za ta kasance? Please ina so ka kasance a rayuwata har abada. Amar na yarda da kai please."
Tana gama fad'in haka ta tashi ta bar gurin, shi kuma ya bi ta da kallo ya kasa magana.
Har ga Allah yarinyar tana burge shi, amma kuma shi halaiyarta ne suke ba shi mamaki. Domin ita ba ta kunyar ta rungume, shi a gaban kowa. Ko kuma ta gaya masa kowacce irin, magana ta zo bakinta. Amma in ba haka ba yarinyar ta yi. Haka dai yake ta tunanin. Abin yi .
Amar ne a gaban mahaifinsa, wato Farfesa Salisu. Shi ma a makarantar yake koyarwa, ya dubi yaron nasa ya ce.
"Gobe za a ba da hutun school, kuma kai gobe za ka gama gabad'aya. Ina son in sanar da kai cewa, har na sama maka, aiki a Abuja. Domin can na ga za su fi biyan albashi mai kauri."
Yana gamawa Amar ya ce.
" Baba ni ba zan iya barin garin nan ba!"
Wace ce yarinyar nan da nake, ganin ku tare a school?"
Ya tambaye shi.
Ya ce. Basma ce.
"Saboda ita ne ba za ka bar garinnan bako? To ni dai na gama magana. Ba ni da darajar da zan sama, maka aiki a cikin garin nan."
Amar ya ce.
" No baba zan samu wata makarantar na dinga koyarwa kafin wani lokaci."
Abbansa ya ce.
"Oho dai in ka ga dama kar ka koyar da kowa, ka tsaya kai ta yawo a gari. Kana koyar da rawa da ba komai kake samu ba."
Ya ce
"Baba kar ka damu na kusa zama wani abu."
Ya fad'a cikin dariya.
______Basma
Cikin tunanin abin da zai ce mata ta dawo gida, tana zuwa gida wanka ta yi. Sannan ta fito Parlon gindan ta zauna, tana tunani. Can ta mi'ke tsaye ta nufi d'akin daddy tana shiga ko sallama babu, ta tura k'ofar d'akin. Ta same shi, shi da Little suna shan kankana. Tana zuwa da gudu ta nufo shi, shi kuma ya ware mata hannu ta fad'a jikinsa. Cikin shagw6a ta ce
"Daddy ni gaskiya wani abu nake so kai mini."
Ya ce
" Gaba 'yar daddy me kike so? Ko mene ne, ki fad'a mini a shirye nake da yi miki."
Bayan ya d'auki kankana, ya saka mata a baki.
Ta ce
"Daddy ka san gobe ne za a ba da hutun school ko?" Daddy ya ce
" E na sani me ya faru? Ta ce.
"Daddy wanda yake koya mini rawa ne, nake so a kawo shi gidan nan. A rik'a biyan shi yana koya min rawa, tun da bai samu aiki ba ka ga sai ait's dinga biyan shi kud'i mai yawa ko daddy?"
Ta k'arasa maganar, ita ma tana saka masa kankana a baki.
Sai da ya shanye kankanan Ya ce.
"Wannan ai ba wata damuwa ba ce, 'yar daddy, kar ki damu ki fad'a masa ya zo ya same ni za mu yi magana da shi kin ji."
Cikin farin ciki ta manna masa kiss 💋 a goshi ta ce "I love you my daddy"
Tana fad'a, ta tashi ta ri'ke hannunn little, suka fita Izuwa d'akinta.
Waya ta d'auka ta kira shi bai d'aga ba. Hakan ya sa ta yi masa text message sannan. Ta kira Lubna ta ce ta zo gida ta same ta za su yi magana.
Amar ne tare da Alhaji Sani wato baban Basma , Bayan ya gaishe shi, Alhaji Sani ya bi shi da kallo daga sama har 'kasa, Sannan ya ce.
"Ya sunanka?"
"Sunana Amar"
ya ba shi amsa.
Daddy ya ce ya yi kyau.
"aikin me kake yi?"
"Na kammala P h d yanzu haka ina jiran aikin yi ne."
( SLHAJI SANI FA BEYI KARATUN BOKOBA KAR KU MAN TA)
Daddy ya ce.
"Wato karanta tsare-tasre ko?"
"Amar ya ce.
A'a ana nufin 'kididdiga Kenan."
Daddy ya ce.
"Kana nufin ka ce mini kana da takardun kammala Karatu ko? To ni ba wannan nake son sani ba. Ina son sanin taya kake samun kud'i wani aiki kake yi yanzu?"
"Ya ce
" ina d'an koyar da rawa Ana biyana."
Daddy ya ce.
" To daga yau ka daina koyar da kowa. Sai yarinyata sannan za ka dawo gidan nan da zama har zuwa lokacin da za ka samu aikin yi."
Cikin mamaki yake bin daddy da kallo. Saboda ya ji ya ce zai dawo nan.
Daddy ya ce.
" Kar ka damu wannan tsarina ne zan dinga biyan ka dubu 50, a kowanne wata. In dai har Basma ta ji dad'in zama da kai."
Jin kud'in da aka ce za a biya shi ne ya sa ya fasa fad'in abun da zai ce sai godiya yake yi cikin jin dad'i, ya tashi ya bar Parlon.
Yana fitowa ya kira ta a waya domin tun da ya shigo bai gan ta ba, tana d'agawa ta ce zan kira ka leter "ok" ya ce.
Haka ya je ya sami Abbansa ya gaya masa, duk abin da ya faru. Amma bai ce masa a gidan zai zauna ba. Don kar ya yi sa a abbansa ya amince.
Washegari haka ya sanar wa da Sadam` shi ma ya yi masa fatan Alkairi.
Bayan ya iso gidan ne Alhaji Sani, ya had'a shida Ali` wanda yake cikin gidan A kan ya nuna masa 'barin da zai zauna.
Suna cikin tafiya ne.
Ali ya ce
" Wannan gidan da ka shigo yana da hatsari sosai` za ka iya yi wa kowa laifi har da Alhaji ya bar ka amma kar ka ta'ba 'yarsa."
Amar ya ce " Ai kuwa ni ma kar ta mini shirme, domin ni ina zane mutane mutuk'ar suka yi ba daidai. A gurin koyar da rawa."
Ali ya ce
"Nan shi ne gurin da za ka zauna ba kowa sai kai ka kad'ai. Can da kake gani sashina ne ni da matana, ba na shekararmu 25 da yin aure amma har yanzu Allah bai ba mu haihuwa ba.
( *ALI IRIN MUTANEN NAN NE MASU SHEGEN SURUTU* )
Amar ya ce
" To Allah Ya ba ku yana zama a kan kujerar da ya gani a cikin d'akin."
Mash Allah! Abubuwa suna tafiya daidai, inda soyayya tsakanin Amar da Basma ta girma kuma Babu wanda ya sani a cikin gidan .
Kafin me afkuwa ta afku yanzu ne za a fara, Cakwakiyar yanzu ne komai zai fara faruwa. Yanzu za a shiga labarin asalin abin da zai faru.. 📝✍️
*TO FA! YANZU ZA A FARA RIKICIN ABUBUWA ZA SU FARA FARUWA , KUDE KU KASANCE DA NI* ~S REZA~
~HAQIQA ALK'ALAMI YA FI TAKOBI ✍️📝~
The end fart 3️⃣
To be continue...✍️
*ALK'ALAMI S REZA..✍️*
PLEASE COMMENT AND SHERE DON ALLAH 🙏🤣
*BY S REZA ON LOVE*
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CHAKWAKIYAR SOYAYA*
NA

S REZA



©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...
*SADAW KARWA GA*

```MAMAN ADNAN🥰 BADAN HALIN KIBA. WANNA NAKINE KEDA ADDNANM`DAKUMA ABBAN ADNAN🙏```

CA'KWAKIYAR SOYAYA
PAGE ⚓️ 4⃣

....... Amar. Zaune Yake akan Mashin d'insa Yana jiranta, Amma shiru yakai 30mt, Agurin yana jiran ta har yafara tinaninn komawa gida, Se jinyayi tace "Sorry Amar Walhi daddy ne yakeson jin ina zanje, Kuma mezan jeyi Shinefa na shirgamasa 'karya Shine yasa kaga nadad'e, Tana magar nar tana 'ko'karin hawa kan mashin din. Amar yace "to yanzu wani 'karya kikamasa Har yabarki. Basma tace "kai nifa ban iya garyaba, Rasa irin 'karyar dazan Masa ne, shine kawai nacemasa, Zamufita Yawon sha'katawa ne nidakai. Cikin wani mahaukacin Tsoro Amar yataka birkin mashin d'in, Yajuyo yana kallonta, Yace.. "Please Dagaske Haha kika cemasa?

Basma cikin dariyar da take 'boyewa Tafito fili tace.. "eh mana Ai nacemaka ban iya 'karyaba Shine kawai nafad'a masa gaskiya, kuma bagashi ya barmuba, Tagarasa tana dariya🥰, Gani tayi yajuya kan mashin d'in Izuwa gida yana cewa "nide Walhi bazan je ba, Meyasa Zaki fad'a masa haka, kin San cewa in har yasan da wani abu a tsakanimu, to Walhi da matsala, Cikin dariya Basma tace "kai Walhi dawasa nake makafa nacemasa, zani gidan su Lubna nefa. Abin dayasa kaga nadad'e, Yace wai semuje Nida Little nefa, nikuma na'kiyarda , Se a lokacin Amar ya jidad'i, yace "kokefa amma Walhi har kin sa gabana yafara Dukan tara²

Sun yi nisa Sosai Kafin Suka tsaya, wani gurine irin gurin da masoya sukezuwa, domin Jin dad'in Rayuwar su, Wata iska akeyi mekamada irin iskar damuna, Hadirine Yake haduwa, shine ake kad'a wata iska me shiga cikin Zuciya,

Bayan Sun Samu Guri Sunzaunane, Amar yace.. "Basma cikin sanyin murya, tace "na'am. Yazuba mata ido Sannann yace.. "Basma Ha'kiga na yarda kina sona kuma Kina min Zonda ban yitinaninn shi daga garekiba, kin San meyasa nace muzo nagurin? Girgiza masa kaitayi alamar aa, yacigaba dacewa "Basma Ganinakeyi Soyaya nidake bazata yuba, Dubada ke y'ar waye a garinninnn, ina tsoran kar nagama yarda da sotayar ki daga baya a zo a samu Matsalar, Basma Walhi ina son ki, ina Kuma ina miki so banawasaba, Wani lokaci Senaji zuviyata! tana Cemin Basma bamatar aurena bace, Idan naduba irin Soyayyar da, Daddy Yake nunamiki, Walhi senaji kamar Baze yarda da Soyayyar muba, To shine yasa nakiraki nann domin in ji daga bakin ki.

Shuruu Basma tayi Sannann Tace.. "Daddy na yana sona kuma kaima kasani, Dik abin da nakeso shine za'binsa, Sabodahaka kar kasa komai a ranka mutugar, Naje masa da zan ce koda wani irine to daddy, Yana yarda, Nide fatana Kari'kemin Amana.

Amar yace.. "Inde nine karki damu kece kad'ai a Raina, Sonda nake miji bazan iya had'ashi da nawata ko nawaniba, Karma kisa Wannan azuciyar ki, Amar nakine ke kad'ai, Tagarasa maganar Yana ma'kemurya kamar wani ustaz. Dariya Sosai Basma tayi Sannann itama tayi irin muryar sa ta ce.. "Dama ban sa a rainaba bare kace in cire. Dariya dikkaninn susukayi, Sukaci gabada Hirarr Soyayyar su cikin Farin Ciki.

Suna cikin hakane Aka tsinke da ruwan Sama, Ruwa ake yi sosai Hakan ne yasa Suka fito domin tafi gida acikin ruwan. Cek Suka Tsaya Suna kallon gurin da suka ijiye mashin d'in Naso, babu mashin din,

Tashin Hankali, Basma tace.. "Ina mashin di'n? Yace.. "Anan gurin fa muka ijiye yana nunagurin da hannu. Hakade aka duba mashin Sama da 'kasa amma babu shi babu a lamarsa. Haka suka hagura Suna jira domin a gama ruwan Su samu abin hawa Sutafi, Acikin ruwan sukayi sa a Suka samu me keke napen Wanda Shima ruwan ne ya tarashi yana kan hanya.

______Daddy
Tin dayaga an fara ruwa Amma bata dawoba Han kalin sa yatashi, Ya Kira number ta. Amma bata shiga, Yakasa sakewa, Damuwar sa Allah yasa Wannann ruwan be ta6ataba, Hakan neyasa yadawo harabar gidan yana kallon get d'in gida domin ganinn ko Zata shigo yan zu.

Lokacin da Suka garaso Ruwan saman yaragu Se kad'an² Bayan sun salami me keke napeng, Amar ya ce.. Yanzu baza mushiga tare ba saboda Yanxuhaka Nasan Daddy yana nann yana jiran dawowar ki, Saboda haka kifara shiga zan biyoki daga baya. Basma tace.. "Amma dan Allah kar kaima ka dad'e awaje Saboda sanyi, please ina shiga kaima kashigo kaji, Tana maganar tana Rawar Sanyi, Cikin son yaga tashiga Domin tabar Rawar sanyin da takeyi yace.. "Ok no problem yanzu zanshigo, yana fad'a yana mata a lamar tatafi Tana tafiya tana kallon Sa.

Tana shiga Daddy yataso da Sauri yana cewa.. Basma Daga ina kike haka? Me yasa baki Kira anzo an d'awkokiba? Cikin son Taga ambar maganar tace... Daddy Sanyi nakeji, haka yakamo hannunta, Har Cikin d'akinta ya kaita Sannan yace.. "Daga yau baza ki gara zuwa koinaba seda dreba, Kuma ita ita Lubna In bazatazo gidannan ba to Bazaki gara zuwa gidan Suba, Yacigaba da cewa kiyi wanka ki sake kayan jikin ki, Sannan kizo kisha mgn, Yakamo hannunn ta ya mannamata kiss 💋 Yace ina jiranki a parlor, yajuya yafita yana jin kamar Kar yagara barin ta tafita.

Amar, Bayan ya shiga yayi wanka da ruwan zafi Sannann, ya 'kawnta yana tinann waye yasace masa mashin? Agarin ya Bayan Kuma makullun mashin d'in yana gurina, To koma waye Wannann bibiyata yakeyi, kuma sena gano waye, Dawan nann tinanin yayi barci

Basma, Bayan tayi dik abin da Daddy yace, Tafito Parlon Tasameshi yana Zaune, da a lamar ita Yake jira, Tana zuwa ya ce my daughter Ina Kikaja? Hankalina be 'kawnta da Wannann fitar da kikayiba.

Ta ce.. Daddy Gidan Su Lubna Naje fa, Haba daddy na ai kasan bana qarya , Toma ni inama zan je, please nide daddy Allah babu inda Naje, Tagara tana kukan Sha'ko6a. Daddy da Izuwa yanzu yagama yarda da ita, Domin kuwa yasan bata masa 'karya yace.. "Sorry my daughter ya isa kin ji , Segashi ya koma rarrashin ta, Hakade har sukaci abin ci sannann yabata mgn tasha, Yace taje ta 'kawnta tahuta Segobe.

______WASHE GARI
Tin jiya da daddare Takira Lubna A waya Tashir ya mata garya akan tazo gidan su Tace Zasuje school Domin kar'bar wasu takardu, hakan kuwa a kayi Bayan Daddy

3 / 9