Chakwakiyar Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Romance

Chapter   7 / 9

18K to 21K   out of 24.3K words

ya ka mata kasan irin maganar da zaka din ga furtawa Wan'nan abin da kake gaya an yishi ne tin a baya sabo da haka duk sun wuce.

Amar yace.. Haka ne ko? Wato sabo da ni yaro ne ku kuma man yane ko? Cikin kuka ya ke yin Wan'nan maganar. Yanzun ina son in muku wata tambaya? "Muna jin ka kayi tambayar ka, in ji Abdul wan da tin da Amar ya fara maga kallon sa ya keyi dik jikin sa ya mutu kuma har ga Allah dik abin da Amar d'in yake fad'a gaskiya ne.

Amar yace.."Wata yarinya anyi tunanin bata cikin farin ciki ita da mijin ta, Se ya tafi domin tabbatar da haka in kai ne ya za kace? Shin zaka fad'i kuna da wata ha la'kane tsa kanin ku kokuma baza ka fad'a ba?

Yaci gaba da cewa.. Idan yarinya tana soyayya da wani kuma taje ta auri wani daban shin shi wan cen meza a cemasa? Kaga kenan zan iya cewa kana da mummu nan hala'ka da wacce nake so rabin rayu wata, "ya ishe ka Amar baka da hankali ne angaya maka hakuri tsuro ne? Cikin ihu ta yi masa maga san'nan ta shigq d'akin ta tana kuka. Shima Abdul d'in hawa yen ya keyi ya tashi ya bita d'akin.

Amar kuka ya keyi kamar wanda a ka dake shi, afili yake furta, walhi ina sonki kuma Allah se nasa shi da kan sa ya sake ki, kuma na aureki, dan ke akayi ni nima kuma dan ke aka yini, a haka shima ya tashi ya nufi nasa d'akin.

*_________ALHAJI SANI*
Zaune suke shida uwar gidan sa wato Zainab hankalin sa a mu tu'kar tashi, kallon Ali yayi wan da shima hankalin nasa a tashe yake yace.. "An ya kuwa Ali bamuyi rashin tunani ba? "Ali yace abin da za'a yi kawai shine mushir ya zuwan baza ta dumin mu tabbatar" Alhaji sani ya ce.. "Gaskiya ina son yarin yata san'nan kuma bazan yarda ni da kai na in selaka ta a tsaka me wuya ba, walhi abin da ya faru da 'yar gidan mlm bala bana son ya faru a kan yarinya ta, gaskiya kashir ya mana tafi ya *ABUJA* gobe kuma bana so ta sani domin muje mu tabbatar da abin da muke tunanin, a haka suka tayar da maganar.

*TOFA MENE NE ZE KAWO ALHAJI SANI GIDAN BASMA? SHIN MASU KARATU DAMA DE BAKU MAN TADA 'YAR GIDAN MLM BALA BA WAN CE RANAR DA SUKA 'DAUKO AMAR A MOTAR SU HAR SUKA GA, WANI SAU RAYI WAI SHI DOLI SEYA AURETA, SHIN ME YA FARU DA ITA? ,HAR ALLAJI SANI YAKE TSORAN KAR YA FARU DA 'YAR SA, SHIN KUN SANE DA CEWA BESAN AMAR YANA GIDAN SU BASMA A ZAU NEBA?* KUKA SAN CE DA S REZA




*WASHE GARI* Da wuri basma ta tashi ta fara tar yar ba'kin su da abinci kala-kala, Seda ta kusa kammala girkin ne Lubna ta 'kirata ta sanar da ita cewa baza su samu da mar zuwa ba pls dan Allah tayi ha'kuri, amma zasu zo wata rana, bata ji d'iba haka taci gaba da 'kara girkin.

Mesalin 9 nasa fe kasan cewar yau lahad'i ranar hutu ce yasa Amar da Abdul babu wan da ya farka ita kuma se had'a musu abin ci take yi, tana cikin haka ne taji ana matsa 'kararrawar alamar mutum tayi mamakin jin haka domin kuwa tasan basu da wani b'ako, tin da lubna ta sanar mata sun fasa zuwa.

Tana bud'ewa ido ta zaro waje cikin mamaki had'e da far gaba da kuma tsoro duk a lokaci d'aya, Daddy ne shida Ali , da gudu tazo ta fad'a jin sa tana dariya, tace "daddy welcome san'nan ta gai sar sa Ali tana basu han yar shiga cikin parlour, tace.." Daddy me yasa zaku zo amma baka sanar da niba" "muna son muyi muku zuwan ba zata ne kuma gashi munyi muku ya me gidan naki?"

Dede lokacin da Amar ya tashi da wata shegiyar yunwa, ya man tama daga shi se rigar barci iya guiwa da wani gajeran wandan rigar, yabfito se wata mi'ka ya keyi yana hamma. Dede Daddy ya na tambayar ta cewa ya naji baki tambaye ni little b... Ai be 'karasa ba sukayi ido biyu da Amar wan da ya ke saukowa, shima sud'in yake kallo cikim mamaki da firgici, Daddy ne yayi 'karfin halin tambayar ta cewa shin Wan'nan meya keyi a gidan nan? Cikin kame kame Basma ta ce.. amm amm dama dama whi dad dad.......✍️📝




End of part 1️⃣1️⃣
To be continued..

Please comment and Shere🙏

This is my new number 08100785178. S REZA

By S REZA
[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CAKWAKIYAR SOYAYYA*

*Story and writing..✍️ *S REZA*


©🎆
*Al'umma Writers Asso...✍🏻*

_{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._
https://www.facebook.com/102282991949826

بسم الله الرحمن الرحيم...


*Cakwakiyar* *Soyayya*🥰💔♥️

*PAGE* 1️⃣0️⃣


........ ABDUL yace" badamuwa bari inje sai mu kwana da shi ai ba damuwa, Kafin tayi magana ya sau'ko daga saman ya nufi d'akin da suka sau'kar da Amar d'in. Basma cikin mamaki tabisu da kallo har suka shige, bata iya cewa ko mai ba itama ta shige nasu d'akin.

A cikin d'akin madai kafin suyi barci abubuwan ban haushi ya ke tayi masa, irun su 'kurnanin barci da kuma d'aura masa 'kafa, kuma duk abin da ya keyi Abdul d'in yana jinsa amma ya nuna masa barci ya keyi. Shi kuwa Amar duk abinda ya keyi da saninsa ya keyi wai shi hakan kishi ya keyi.

*WASHE GARI* bayan sun kammala breakfast ne, wanda shi ma gurin breakfast d'in saida akayi abinda a kasaba. Abdul ne ya fara tashi ya ce" Basma ni zan tafi office. "Ok nima dama na gama shiryawa zan huce school bari se mutafi tare, kasan cewar dama tana cigaba da karatun ta` Har sun fara tafiya suka ji Amar ya ce"

Nikuma me Zanyi to?Sai ka kula mana da gida ko kuma kuyi wasa da teger, Tana nuna masa gurin da d'an 'karamin karan da suke kiransa da tegar. Shima kallon karan yayi yace "Dama kina nufin kun kirani gidan ku domin in yi wasa da tegar ne ko kuma in yi gadin gidan ku? Kafin suyi magana ya ci gaba da cewa to a cikin ku ina so in bi wani, Kallon junan su sukayi San nan Abdul yace " tom ba damuwa tashi mu tafi.

Suna cikin tafiya a motar ba wanda yake yiwa d'an uwansa magana, sai cann wani lokaci Abdul ya kalliAmar yace" Ka saka belet d'in ka, Amar ya ce "ok sannan ya ce yanzu a ina zamu ci abincin rana tunda ita matar gidan ta tafi school? Abdul be kalli in da yake ba yace"sai lokacin cin abincin yayi, Amar ya ce" Duk yanda kace ai haka za a'yi.

Basma waya ta d'au ka takira 'kawarta domin gaskiya lamarin Amar ya fara bata tsoro. Lubna Daidai lokacin tana duba wani mara lafa wanda ciwon ha'kori yake damun sa, dama ita 'ban garan data karanta kenan. 'Daga wayar tayi had'e da sallama, Bayan ta gama jin duk abinda Basma tace mata, san nan taja wani gajeran num fashi!! tace"

"Gaskiya wannan abinda ki kayi baki daidai ba ya za a yi ka kawo shi gidan ki tare da mijin ki wai ke hakan kina son ki temaka wa rayuwarsa? wai ma ina tinanin ki da hankalinki sukaje ne? lokacin da kika yanke wan nan d'anyan hukuncin? Gashi kince jiya yazo kuma daga kwana daya kacel kince yafara baki tsoro, to ina ga yakai sati daya ko biyu?

Basma ta ce"Ni zan iya fuskantar duk wata matsala a rayuwa in dai Amar zai koma cikin Rayuwarsa ta da, kuma nasan in sha Allah zai koma d'in. Lubna ta ce "kina ganin Amar zai iya dawowa cikin Hankalinsa nan kusa ?kinsan fa Amar yana son ki bazai yarda Bata bari ta'karasa ba Ta ce "sai anjima ta kashe wayar ta, Taja wani tsakii san nan ta ce" Dama nasan halinki shi yasa ma lokacin da zan kira shi ban nemi shawararki ba saboda nasan zaki iya 'bata min lamari.

Idan mun shiga office duk wanda ya tambaye ka kace masa kai aboki na ne, Abdul ne ya ke gayawa Amar haka lokacin da suke shigowa cikin camfanin. Amar ya yace"Idan kuma na gi fad'a fa Nace musu ni ne tsohon Saurayin matar ka Lubna fa? Yaba shi amma ata'kaice, ganin yanda ransa ya 6aci ne yasa shi saurin waskewa, ya ce" Ina nufin in na fad'a hakan baza kaji dad'i ba, Abdul bai masa magana ba ya huce suka ci gaba da tafiya ganin sun shigo ciki, kuma gashi ma'aikata sai gai she shi sukeyi.

office ya shiga, ya tarar ta ai'ki a gabansa sosai hakan ne yasa ya d'au lokaci yana ai ki. Amar kuwa ma'aikatan kamfanin gaba d'aya ya tara yana basu labarin cin amanar da Budurwarsa ta yi masa, Daidai lokacin da Abdul ya fito daga office d'insa ne yaga abin mamaki! wato Amar ya tara duk ma'aikatan yana basu labari ,su kuma sai dariya sukeyi suna washe baki. abin bai gama baki mamaki ba saida yaji abinda Amar d'in ya ke cewa,

Bama ai so d'aya ko sau biyu ba ai sau da yawa, wani daga cikin ma'aikatan yace" Kenan ta kasan ce har class d'in ku ta ke zuwa a school d'in ku? Kai amma gaskiya yarinyar kirkice, Wata mace daga ciki ita ma ta ce " kuma yanzu tana cikin farin ciki kuwa? Amar yace Ban sani ba amma nasan bata cikin farin ciki, wani ya 'kara cewa"

To me yasa bata kira ka ta sanar da kai ba se kawai ta auri wani? gaskiya bata kyu ta maka ba, Wan nan mace ta 'kara cewa "Gaskiya kam bata kyuta ba ai yakatama ace lokacin da a ka saka ranar ta kira ka ta sanar da kai in yaso se kusan abin yi,amma kuma taje ta auri wani gaskiya batayi ba, ta 'karasa maganar tana wani ya tsine fuska.

Amar yace" Ba damuwa fa yanzu haka ma yarinyar tana nan a *ABUJA* ita da mijin ta, amma fa wan nan ba komai bane bafa kawai dai ina baku labarin yaudarar da tamin ne. Duk abin da yafaru a kunnensa domin yaji komai Amma ya nuna masa baiji me yace ba.

Daya ke Abdul yana da sau'kin kai yasa ko lokacin da ya 'karaso gurin su babu wanda ya ji tsoran kar ya same su a haka, 'Daya daga cikin ma'aikatan ne yace" Gaskiya yalla'bai wan nan abokin naka ya had'u kaji labarin soyayya da ya ke bamu yanda kasan a cikin film wallahi gaski labarin abin tau sayi,

Abdul ya ce"Labarin soyayya kuma soyayar wa? Ya tambaye su, Wani ne ya ce "Yalla'bai labarin soyayar abokin sane ya ke bamu, Abdul ya ce" Tom tashi mutafi yana kallon Amar d'in Kafin Amar d'in yayi magana wan nan macen tace"Yalla'bai gashi kuma labarin ya fara dad'i kuma zaku tafi yaushe zaku dawo da shi domin ya 'karasa mana? "Cikin jin haushi yace kowa ya tashi ya koma bakin aikin sa ban san shirme!!... Haka kowa ya tashi yana ganin yanda Ran ogan nasu ya 6aci lokaci d'aya.

Bayan sun fito Ne suka biya ta wani kamfani wanda shima na Abdul ne, sai wajen biyar suka iso gida' suna shiga gida Abdul ya ce" Duk ranar litinin bama cin abincin dare a gida muna zuwa restaurant ne muci a can kashirya mutafi zamu same ta a can din.

Bayan sun iso ne kamar yanda yace kuwa a cen suka sameta tana jiran su, bayan sun zaun ne an kawo musu komai da suka bugata, se kawai Amar ya kama dariya yana kallon 'kanon abincin da yake gaban su, sai a lokacin itama Basma ta kula da abinda yake yiwa dariyar, nan take itama tafara dariya, dariya sukeyi babu 'ƙaƙƙautawa. ganin dariyar tayi yawa ne yasa Abdul ya ce"

Shin zaku iya gaya min abin da kuke yiwa dariya? Sai a lokacin suka d'an tsaya da dariyar, Amar ya kalli Basma ya ce" Kigaya masa,itama tace" aa kai kaga ya masa, haka suka dinga wasa da Hankalinsa hardai Amar ya ce"To bari in sanar da kai abinda mu ke yiwa dariya, yace"

Wata rana ne ni da Basma muka tafi wani gidan abinci ,dani yar cin abinci Saida muka ci muka 'koshi, wai a she bata zo da kud'i ba nikuma a wannan lokacin ko nera biyar babu a gurina, haka mukayi tsuru-tsuru muna neman mafi ta, Sai ga kiran Abokina Sadam tofa shine ya zo yabiya mana kudin abincin, Shine yanzu muka tuna muke dariya.

Basma ta ce" Ba gaskiya yafa d'amaka ba, tana kallon Amar d'in yanda ya iya shirya wan nan 'karyar kamar gaske! Ya kasance shi maicin abinci da yawa ne in zaici abinci flet ukku yake cinyewa shi kad'ai, To abinda yasa kake muna dariya shine wan nan abincin ba isar sa zaiyi ba koda kuwa duk har da na mu zaihad'a ya cinye Saboda tsabar cinsa. Tana fad'a tana dariya, duk da kuwa uban kallon da ya ke binta da shi alamar kar ta fa'da amma saida tafa.

Shima Abdul saida yayi dariya dajin magar tasu, San nan ya ce" To ai wan nan ba komi bane, bari in sa a 'karo maka ko? Haka dai suka cigaba da cin abincin su cikin nishad'i,shi kuma Amar cikin jin kunyar tonon sililin da tayi masa` Bayan sun gama ne suka fito domin zuwa gida.

Amar ne ya fara fitowa Sai kuma Abdul wanda suka jero tare da Basma tana rataye da wata jaka a hannun ta na hagu, Dama itama tazo da motar ta, hakan ne yasa tanufi motar ta daniyar shiga,su kuma har sun shige tasu motar sun tashi zasu bar gurin.

Basma daidai ta bud'e gidan driver domin ta tashi ta tafi. Jitayi an sha ganta tabaya, kafin tayi ihu kuma an jefar da ita a'kasa daniyar d'au re mata baki da hannu. Abdul dayaga sun kusa fita daga wajan zuciyarsa ta raya masa bari yagani ko itama ta taso?? le'kawar da zaiyi ai kuwa yayi ido biyu da wani 'kato yana danbe da matarsa!!.......✍️📝


*TOFA, ANYA WAN NAN BA KAMAL BANE ?KUN SAN FA KAMAL MA BE HAKURA BA. SHIN ABDUL ZAI IYA TEMAKONTA ?KODE AMAR NE,? KUKASAN CE dDA S REZA.*



*End of fart* 1️⃣0️⃣
*To be *continue*..


Please comment and Shere


By *S* *REZA*[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: ─────────────────────
*HIGHER STANDARD WRITERS ASSOCIATION®* 📖📚✍️✍️
─────────────────────
https://facebook.com/Higher-Standard-Writers-Association-100702755812959/

```Alƙalami Ya Fi Takobi```
___________(✪)___________







*CAKWAKIYAR SOYAYYA* 💋

Story and writern..✍️
S REZA




Na sadaukar ga wannan Page ɗin ga mahaifiyata jigon rayuwata 😢 komai nazama kece silar komai. Ina Alfahari dake.
(I LOVE`YOU MY MOM)









PAGE1️⃣2️⃣

............Cikin tsawa daddy yake tam bayarta, nace meyakawo wannan cikin gidan nan? yana nuna gurin da Amar yake "Daddy wallhi fa ban san ni fa amm dady "tsawar da daddy yasake mata ne yasa ta sake rikicewa. tarasa me zatace masa kan ta ya ƙulle "Daddy ai abokinane...

Cewar Abdul yana sauƙowa daga ɗakin nasu, cikin fara'a yace.. "daddy zuwa babu sanar wa haka? sannun ku dazuwa. daddy Amar Basma Ali, Duk tsyawa sukayi suna kallon sa shi kuwa ko a jikin sa. Abdul yaci gaba dacewa.. daddy Amar ai abokina ne, yazo garin nann yin wani aikine shine muka
haɗu dashi, kuma damuka zogida shine itama Basma tace min wai tasan shi, to shine fa mukace kawai ya zau na a gidannan har ya kammala ai kin sa base ya kama hotel ba.

Basma da Amar kallon juna sukayi cikin mamakin abin da Abdul ɗin yace "Daddy yan zu shikenan kadena yar dadani kadena sonako? cewar Basma tana ɓata rai. Haƙiƙa Daddy ya yarda da bayanin da Abdul yamasa domin kuwa yasan halin sa.

daddy yace.. "haba ƴar daddy ai ban san haka abin yake ba. Yana kama hannun ta suna shiga cikin falorn. Amar kuwa mutuwar tsaye yayi domin har ga allah yagama tsorata sosai, kuma abin da Abdul din yayi yabashi mmk, afili ya ce... Gaskiya gayan nann yahaɗu kuma yan zune ma za'afara wasan.

Bayan sun karya kowa yayi hani an. Abdul yace... Ni zan fita zamuyi wani aiki a office amma yanzu zan dawo. nann take Basma ta haɗe rai alamar bataso yatafi Shi kuwa saraii ya ganta amma ya ɗauke kansa kamar be gan taba.

Duk abin da sukeyi a kan idon daddy da Ali harma da gogan naku wato Amar. Bayan Abdul yabar gurin itama tashi tayi tabi bayan sa... Tana zuwa tace.. haba Abdul daddy nane fa yazo amma bazaka iya haƙura yau ɗaya ba? yau ɗin ma kuma baranar aikiba haba mn Abdul kokana son Daddy yayi zargin wani abune?

"Haba mana a'maryata walhi nima ban so hakan ba kuma ai nace miki ba zan daɗeba yan zu zan dawo, yana gama faɗa ya man na mata kiss a'goshi sannan yatafi yana sauri. Abin yabata hau shi haka takoma gurin ran ta a ɓace.

Alhaji Sani ne zaune shida Ali da kuma Amar. Ali ne yace... Amar naji an ce ka kai sati ɗaya a gidan nann ko? "eh gaskiya ne satina guda harda wasu ƙanaki in ji Amar, Ali yace.. "Tom masha Allah hakan yayi. Dama wani abu ne yake tafe damu akan Basma, a gaskiya muna tsoran kar wani abu yafaru muzo muna da mun sani.

Ali yace... Ka tina ranar da

7 / 9