Author : Ayshakhair Category : Love
rufe Kuma ko ya nanan ma ba kasafai yake Bari ana shugo Masa ba sabida wani dalili nashi.Girgiza Kai kurum Marwa tayi tana Mai tunanin irin rayuwar da zatayi da wannan murd'ad'an yayan nasu insunyi aure! Itadai har ga Allah Aymanah Tama yaah Hydar kwad'ayin aure sabida tsaban da cewan da sukayi dalili kuwa shine Aymanah tanada matuqar sanyin Rai kuma tana da sauqin Kai irintane kurum zasu iya Zama a inuwa d'aya da masu kalan Hali irin na yaah Hydar hot tempers marasa fara'a Sam! Amman ya satayi qaddara ta riga fata sai dai adu'a kurum Dan itakam batajin zata iya jure zaman aure da yaah Hydar duk da tasani shid'in ba qaramin namiji bane every girls dream husband Amman wani zubin zuciyan mutum ya kamata ka ruqa lura ba Wai halittaba na fuska Kona jiki!
Shugowa falan da tayine yasata tsagaita tunaninta Kallan falan kurum takeyi tana furta "wow" a k'asan maqoshinta lallai falan Nan ya had'u sai take ganima tamkar duk gidan sashen yaah Hydar yafi kyau hoton sa dake manne a saqo da lungunan falan ta ruqa kallo har ta idasa shiga d'akinsa nanma ya had'u sosai gyara tasoma dukda d'akin bawani qura tayi ba bayan ta Gama tashiga bayi ta wanke ta feshe ko Ina da turaruka masu d'adi tana gamawa tafito da niyyan fita Amman hango wani d'aki a wajen corridor da zai sadaka da dining area ne ya sata d'an tsayawa kaman ta wuce sai Kuma tayi tunanin shiga ta gyara Shima straight taje da niyyan bud'a d'akin Sai dai taji shi a datse har tasoma tafiya sai ta hango key a saqale a wajen kofan hakan yasata d'auka had'i da bud'e qofan qamshin turaren da ya bigi hancinta a lokaci guda ne yasata saurin juyowa Dan tabbatar da abinda hancinta suka jiyo Mata!
Ganin bakowa ne a bayan nata yasata d'an mamaki tana Kuma furta qamshin turaren Aymanah" qarasa shugowa d'akin tayi sai dai d'akin da duhu yake hakan nema ya d'an tsoratata gashi kuma qamshin turaren Aymanah sai dad'a yawaita yakeyi a cikin d'akin Kai kace tamkar tana kusa dakaine tana fesa turaren Dan tabbas wannan qamshin turaren datake shaqa tabbas tasan bamai irin qamshin sai Aymanah to Mai qamshin ta keyi a d'akin Nan! A hankali tasoma Kiran sunana waiko Ina d'akin neπ!
Jin shuru yasata soma laluban inda zata kunna wuta da kyar ta samu saidai tana kunnawa wani blue haske ne yasoma bayyana a hankali Kuma kunna wani tayi nanma orange light ne ke fitowa a hankali Nan ta cigaba da kunna wutan har kala biyar a hankali d'akin ya baibaye da haske saidai hasken na bayyana wani hotuna ke moving a saitin bangon d'akin d'ago kai Marwa tayi tasoma qarema hotunan dake haskowa A d'akin da kallo a hankali take kallo bayan taga hotunan sun qarene yasata Kuma waiwayowa tana qarema maka makan frames d'in dake d'akin kallo hotunane kurum take gani wasu daka gani kasan mutum ne ya zauna ya qera hotunan da dukkanin basiran da Allah ya Bashi Saida ta Gama Kallan hotunan tsaf sannan tayi wani kalan kayataccen murmushi tana furta " wow ma Sha Allah yaah Hydar Kennan in ka gansa tamkar bazai aikata hakaba tamkar baisan Mai ake nufi da kalman LOVE ba! "πΌπΉ
Wani d'an littafi ta hango saman wani table dake cike da hotuna irin pices d'inan duk birjik a saman table in kujeran table in ta jany'o ta zauna ta na Kallan hotunan tana yalwataccen murmushi sannan takai hannunta ta kunna wani lanta da shi ne zaka iya karanta littafin dake kan table in kasan tuwan yanayin wutan d'akin yake in mix colours bayan ta kunna ta bud'e littafin ta Karan ta heading din "my PA diary life" shine rubuce akan littafin kaman karta karanta Amman abinda tagani a next page in yasata Zama ta karanta littafin Nan tsaf daga farko har sai da in da taga ya ajiye pen d'insa alaman Yana cigaba da rubutawa ne mamaki ne fal ran Marwa ita mamakin da takeyi shine dama Wai yaaah Hydar ya iya. Soyayya haka tohm itakam tunda AllH ya halicceta ko a film da Novel Bata tab'a cin Karo da zazzafayen kalamomin soyayya masu sanya natsuwa da shauqi ga Wanda aka furtasu mawa ba kaman Wanda taga yaah hydar ta zauna ya tsaraba murmushi kurum takeyi tana fad'in ayyah Yaaah Hydar Kai d'in u are slow poinsion green snake under green grass!
Jin kaman idar da sallan azahar d'in da akayine yasata saurin miqewa ta rufo d'akin tafito da sauri ta rufe sashin takoma part din yapendo ranta fal farin ciki da Kuma mamaki!
****************
Rayuwan qunci da uquba Babu irin wa'inda bana Sha wajen mubash kullum Yana kan bakansa akan Kota halin mainene sai ya zubar mun da ciki sannan Kuma sai yasa an juyamun mahaifata nadai qala ban cemai saidai binsa da Ido kurum Dan abin NASA ya girmama tunanina kawai abinda nasama Raina yanzun shine nasan Allah nasane Dani Kuma shi ya tsaramun hakan a rayuwata Kuma nasan shi zai magancemun Dan haka kullum cikin aduaa kurum nake Allah daurani Akan mubash!
Ana haka watarana mubash ya dawo yaban wani juice yace na kwankwad'e ba musu na amsa na shanye dan Sam bana Masa musu ko tijara yanzun komai yace nayi kafun ya Gama magana ma zan Fara aikatawa Dan mu rabu lfy Dan jikina Kar ya gayamun ga laulayin ciki ga duka Dan ba qaramin aikinsa bane yamun d'an Karan duka ko agefen kwalansa!
Bayan Shan wannan juice d'in dakimanin mintuna uku naji cikina na murdawa tamkar ana yaqin biyafra aciki tun Ina jurewa Ina botsarewa har hakan ta faskara ihu da salati da jerama Allah kirari kurum nasoma yi Jin ihu na yasashi fitowa daga toilet da sauri ya kamoni yana mun sannu Yana fad'in:
Daure ko? Daure yanzun Nan cikin zai fita ki rage Jin azaba !.
Ina nikam banma San yanayiba tsabaragen azaban danake Sha kalmatul shahada nasoma karantowa Dan jin yadda nayi a lokaci d'aya cikin nawa ya birkicemun jinake tamkar Raina ake cirewa jini ne yasoma liliyowa ta qasana ahankali chan Kuma sai ya b'arke tamkar panpo Kallan mubash kurum nayi ya daka tsallan murna yana furta "yes! Yes! Wlh shegen ya zube yes!
Sannu ko sorry "innalillahi wa'inna ilahirajiun kurum naketa furtawa a hankali idanuna sai kakkafewa sukeyi yanzun mubash zubdamun da cikin Nan yayi? Koda bana qaunar ubansa Ina qaunar d'ana Dan bansan iya Kwan da Allah ya rubutamun zan kyank'e she ba adoran qasa shisa ma tunsanda mubash yace zai zubda cikin na shiga xullumi d'ana Dana samu a sanadin aure yau shine ake cema shege yafita! Kai Allah gani gareka!
A hankali nake ta furta kalmn shahada idanuna na rufewa a hankali har suka rufe gaba d'aya bakina ma a hankali yasoma daina furta komai a hankali bakin nawa Shima ya daina motsawa nakoma na sulale a qasa shiko mubash Bina kurum da idanu yakeyi Yana furta:
"No ai an tabbatarmun bazaki mutu ba cikin ne kurum zai fita oya kitashi"
Shuru ban amsa Mai ba hakan yasashi jijjigani Amman Aymanah batada alaman motsi hakan yasashi saurin wawurarta yasata a mota yayi hanyar asibity da ita suna shiga likitoci suka amsheta akayi emergency room da be!*Real pure momment of life writers*
π *AURAN WAHALA KOH SAKI*πππ
By " *AYSHKHAIR*"
Page 39&40
Likitocin sukai kimanin awa 1 akan Aymanah!
Likitane ya fito dan yay magana da Mubash dan Aymanah na buqatan jini saboda jinin datayi loosing dayawa! Koda likitan ya fito sai bai iske Mubash ba gashi any momment frm now inhar baasamu ansamata qarin jinin ba zata iya rasa ranta!
Da sauri wata nurse tafito daga d'akin tana kwala sunan likita kallanta yayi da sauri yace: "what!"
Cikin haki nurse in kecewa:
"Dr she needs oxgyn"
Da sauri likitan ya shiga d'akin yadda ya tarar numfashin Aymanah nasama taqasa tamkar ana cire mata rai yayi mugun firgita likitocin d'akin kallan machine din dake nuna heart beaten nata sukayi sukaga yana 0.3 tabbas yana kai 0.0 zata rasa ranta da sauri likitocin suka d'au oxgyn na mannawa a qirji dan saurin ceto ranta shikuma dr saad yayi saurin zuwa lab yaduba blood group din Aymanah da sauri yaje ya d'au leda biyu na jini ya zo ya maqala mata a duka hanna yenta biyu da kyar numfashinta yasoma tafiya in 0.7 alaman jinin yasoma shiga jikinta wani sanyayyan ajiyan zuciya likitocin suka sauke suna fur Thank God! Saida suka tabbatar komai na tafiya normal sannan suka fito Dr saad ya wuce office nashi ya zauna sai faman tunanin wani kalan maganine Aymanah tasha na abortion haka da har yake shirin salwantar da rayuwanta!
Ganin bamai bashi amsa ya sa shi cigaba da aikinsa ransa fal tunanin mubash inda yaje yabar Aymana acikin wannan halin!
Kwanan Aymanah d'aya a asibityn amman ko Alamar giftawar mubash babu a asibityn hakan ne yasa Dr saad tunanin qilan kawota kurum yayi dan ya taimaka mata or somtn lyk that!
Shugowan Dr Saad d'akin da shi da wata nurse yayi daidai da qarar machine din dake nuna gudun zuciyan aymanah yasoma bugawa a hankali a hankali da sauri likitan ya qaraso yana tab'a wasu wajen yana kuma mai kallan Aymanah dake sauke ajiyan zuciya da sauri da sauri qarasowa yayi daf da ita ya cire mata Oxygn d'in dake saqale a dogon hancinta dan tasamu tayi fast breath hannuntane yasoma motsi alaman tana farfad'owa sosai kallan jinin da aka qaramata yayi yaga ya qare wurwus kuma wannan jinin shine leda 5 kenan daaka qaramata!
A hankali Aymanah tasoma bud'e idanunta har ta waresu tsaf akan likita saad kallansa takeyi quri da idanu batako kyaftawa dan so take ta tuna mai ke faruwa a hankali komai ya soma dawomata sabo runtse idanunta tayi a hankali tana fad'in:
"Dan allah ku rabani da shi ....zai kashe ni da yarona......
Saida likita saad yakai kunnansa daidai la66anta sannan yajiyo abinda take fad'i hakan ya sashi mamakin kalamanta a hankali ya qarba alluran baccin dake hannun nurse sannan ya ma Aymanan dan tasamu ta yi bacci aiko yana mata bada jimawa ba ta soma bacci!
Kallanta likita saad yayi duk tausayin yarinyan yabi ya isheshi kallanta yakeyi kamar qanwarsa data rasu wajajen haihuwa runtsa idanunsa yayi sannan yace ma nurse din amaidani d'akin hutu nurse tace masa okey sir! Daga nan ya wuce office nashi dan duba wasu patience d'in!
Sai wajajen qarfe 4pm sannan na farfad'o ina qarema d'akin kallo bisa alama a asibity nake hakan ya tabbatar mun da maganin da Mubash yabani na zubda cikine shafa cikina nayi a hankali na furta:
"Kayi haquri d'ana Allah jiqanka kuma Allah zai saka maka in sha Allah gwara da Allah ya qaddara rashin zuwanka doron duniya hakan ba qaramin gata mahaliccinka ya maka ba sabida karka taso ka tarar da baqin azalumin mahaifinka! Allah zai saka mana!"
Diga haka kuka yasoma cin qarfina a hankali na shiga rairo kukan ina kiran sunan mamanmu da marmy da yayyena a haka likita saad ya shugo ya taddani da saurin sa ya qaraso yana fad'in;
"Subhanallahi baiwar Allah kukan fa namainene?keda zaki godema Allah ya barki da rayuwarki shine kuma kike kuka!
Kallan likitan nayi da kana ganinsa zakaga zallan kamanninsa da 'yan burki nafaso!
A hankali nace;
"Likita da mutuwan nayi dana fijin dad'i samada idan inada rai kuma igiyan aurena yanaga mugun miji!
Da mamaki likitan ya kalleni yace:
"Baiwar Allah keko maisaki furta wanga kalamai?"
Murmushin da yafi kuka ciwo nayi sannan nace:
" Wlh da mutuwa nayi nakoma ga mahaliccina dana fi kowa farin ciki a doran duniyan nan!
Kallona kurum likita yasoma yi yana mamakin wannan kalaman nawa chan ya nisa yace mun:
"Baiwar Allah niko kazaki iya gayamun maike damunki haka? Dakika zab'a kimutu sama da ki rayu?!"
Murmushi nayi dan ni kam bana shakkar gayama ko waye labarin quncin Auran danayi ! Murmusawa nakuma yi sannan nace:
"Lbarina yana da tsawo amman labarin yasoma kaman hakane...............
nan na bashi dukkanin labarin Auran wahalan danayi da Mubash daga farko har iska kaina danayi a wannan asibityn!
Tabbas koban gayaba idanun dr Saad sun kad'a sunyi jajir tsananin tausayina suka baibayeshi a hankali ya furta:
"Kaico duniya Allah ya kyauta Allah kuma zai saka maki Aymanah mubash saiya qasqantu a duniyan nan dakuma lahira karki damu kicigabada haquri sabida Allah nacewa acikin littafinsa mai tsarki *Innallaha ma'assabirin* lallai Allah yana tareda masu haquri saboda haka kiyi haquri nikuma in sha allah zan taimaka maki har sai na maidaki gun iyayenki in sha Allah!
Murmushi nayi sannan nace:
"Likita ngde dason taimakamun da kakeson yi saidai muddin mubash na nan bazai barka ka taimakamun ba"
Murmushi yayi sannan yace:
"Hakane saidai mubash tunda yakawoki asibity har zuwa yanzun bai dawoba kinga ko zan iya taimaka maki ta hanyar.............
Nan likita saad ya zayyanomun tiryen tiryen yadda zai taimakamun ba tareda Mubash yayi zargin an taimaka mun na kub'uta a hannunsa ba!
Har cikin raina nayi na'am da wannan kalaman kuma nama likita saad godia sosai!
Chanzamun d'akin kwana likita Saad yasa akayi akamaidani private ward Chan sama d'akin yake sosai nasoma Jin dad'i a Raina na kusa komawa ga dangina kai Allah nagodema da ka aikomun da wannan bawa naka ya Allah kaid'in ubangijin taliqai ne maijin Kiran bayinsa garesa Allah nagodema !
Sai washegari mubash kaman Wanda ka wanchakala yazo asibityn office din Dr Saad yanufa kallo d'aya likita Saad yamai ya shedashi Dan haka cikin zuciyansa yaja wani siririn tsaki maganan da mubash yayine ya maido kallansa garesa:
"Amm likita Ina matata? Dan na duba d'akin da aka kaita Bata gurin"
Zaro glashin dake idanunsa Dr Saad yayi sannan ya kalla mubash din yace:
"Dama matarka ce?!
" Eh"
Mubash ya basa amsa ataqaice, d'an murmusawa likitan yayi sannan yace:
"Asha kana inane tun ranar daka kawota baka sake zuwaba sai yau haka?"
Kallansa mubash yayi sannan yace:
" Mushkila aka samu! "
D'an fuskan tausayi Dr Saad yayi sannan yace:
" Well inaso kasanyama ranka haquri kakuma San kowani bawa da tashi lokacin! "
Kallan likita kurum mubash keyi Yana qoqarin sakala maganganun nasa Dan yasamu ya fahimta inda zantukan likitan ya nufa Amman ganin bai fahimta komai ba yasashi cewa:
"Likita ban gane Mai kake cewa ba fa Sam!"
Ta6e baki Dr Saad yayi sannan ya Kuma sauya fuskansa zuwa na ban tausayi yace:
" Well we couldn't save her!"
Kallan uku saura kwata mubash yamasa Yana fad'in:.
" As in wat are u trying to say like this?"
Miqewa Dr Saad yayi ya zagayo inda mubash ke zaune sannan yadafa hannayensa saman kafad'un mubash d'in sannan yace:
"I mean kayi haquri dukkanin Mai Rai mamacine Allah ya amsa ran matarka tun aranar daka kawota munyi iya qoqarinmu Dan ganin munceto ranta Amman abin yaci tura cux ta zubda jini sosai mun nemeka sama da qasa Dan kabata jininka bakanan kafin aje anaimo jinin da zai yimata Allah ya amsa abarsa! Am sorry Allah jiqanta!
Dagaske ainun mutawar Aymanah ta sosa zuciyar mubash sabida ji yayi tamkar a dalilinsane aymanan ta rasa ranta wani sabon soyayyarta ne lokaci d'aya ya dawomai ji yake inama Akan maida hannun agogo baya da tabbas zai maida yasoma rayuwar aure Mai dadi da Aymanah Amman is too late now abubuwan dayake mata kurum yaruqa tunowa mubash harda d'an kwallansa!
(Niko nace maida hawayen naka munafukiπ€¨πai hawaye da kuka tartilan yanzun kasoma yinsu malam mubash save ur tears Dan nangaba karka naimesu karasa Dan sune zasu zaman Maka farin cikiπ)
"
" Aymanah ki yafemun ki yafeni Allah jiqanki"π°
Yana maganar Yana share kwallan sa Dr Saad ko ta6e baki yakeyi aransa Yana fad'in:
"Mugu azalumi kurum ai Dana biyema da tun bayauba Aymanah ta rasun na gaske Wawa!"
Amman a fili sai ya tausasa harshensa Yace:
"Ayi haquri aduaa kurum take buqata ba kukaba"
" Hakane likita Amman Ina gawar nata yake? "
D'an ta6e baki Saad yayi sannan yace:
" Dake bamuganka tym din ba yasamu tunanin ko ba matarka bace taimakonta kayi yasamu maida gawanta mutuware Dan Nan ne kurum gawan nata will be save kafin anaimo danginta Amman tunda kazo zamu iya baka gawan nata sai muje kayi signing ka Kuma biya naira dubu tamanin na kulawa daakayi da ita na wannan lokacin"
Zaro idanu mubash yayi yace:
" 80k fa? "
Girar sama da qasa Dr Saad ya had'e Yana fad'in:
"Yadai haka price din yake waima Dan wannan 3days ne kurum!"
"Banida wannan kud'in yanzun Kuma bamuda kowa a Nan birki nafaso likita! "
" Ok ai zaka iya barin gawar har sai ranar daka samu adadin kud'in da tayi sai ka biya abaka gawar nata"
Wani dabara ne yafad'oma mubash Dan haka yace: axuciyansa:
" Ko na amsa gawan ma uban wa zan naimo sumata salla gwara tayi zamanta anan inyaso insun gaji da ajiyeta sa San yadda zasuyi da ita Dan nikam anjiman Nan ba gobe ba zan tattara na koma Nigeria!
Murmusawa yayi yace:
"Likita abarta anan d'in in yaso nasama kud'in saina zo na biya aban gawan"
Wani qayattacen murmushi Dr Saad yayi ganin cewa plan d'inshi yayi working yadda yakeso Kuma zai iya taimaka ma Aymanah kenan lumshe kyawawan idanunsa yayi sannan yace:
"Ok as u wish Allah kaimu ranar!"
"Ameen "..
Miqewa mubash yayi Yana ma likita Saad musabaha Yana cewa:
"Toh Dr sai ka gannin"
Murmusawa kurum Dr Saad yayi sannan yace:
" Alryt see you then! But bazaka ga gawan nata ba kan ka tafi?"
Waigowa mubash yayi yace:
" Will see her some other tym Allah jiqanta banson warin gawane Kuma kasan yadda mutuware yake da seant Mara dad'i"
Murmusawa ta gefen baki kurum Dr Saad yayi sannan yace: cikin ransa" better for u"
Amman a fili sai yace;
"Ok ok I get u! Bye then!"
Fita mubash d'in yayi ba tareda ya waiwayo likitan ba shiko likita Yana fita yaja dogon tsaki ya furta a fili:
"Very stupid human being da sannu zaka biya abinda kayi"
Daganan ya juya ga wani camera Yana fad'in:
" We are done pretty"
Niko wani kalan ajiyan zuciya nayi sannan na jinjinamai hannu alamun good job duk abinda suka tattauna Ina zaune Ina kallo a system dake jone da CCTV din office d'in Dr Saad !
Kulle system din nayi Ina furta Allah Alhmd................
.*Real pure moment of life writers*
π *AURAN WAHALA KOH SAKI*?ππ»ππ
*by Ayshkhair*
βΊ *Jinjina Agareku Ayshkhair novels da Romantic writers fans tnx so much for the love huuun*π
_Bazan manta dakuba kud'in na musamman ne Ayshkhair naji daku_:
*Maleeka*
*Hauwee*
*Temmah marafa*
*Maman inteesar*