Auran Wahala Ko Saki Complete

Author :  Ayshakhair Category :  Love

Chapter   11 / 13

30K to 33K   out of 37.6K words

yayi danasani danadama harba adadi yasan haqqin matarsa Aymanah ce ke d'awainiya dashi kaico Aymanh kiyafemun natuba Allah jiqanki Nima nakusa zuwa gareki Dan Nima nasan mutawar zanyi! 😭a haka sai ya fashe da kuka aranar daaka kamasa zuwa qasar birki nafaso aranarne yasaki Zeenat bisa umarnin data bashi Dan wani qaton Arne aqasan waje nasan holewa da ita Dan zuwa ma zatai tasameshi Nan tace mubash yasaketa Aiko secns be qaraba ya maka Mata saki 3 Kuma tace ya takarkata yabar Mata gida nanfa hankalinsa ya tashi danbaisan inda zai nufaba bai da ko sisi fitowansa Keenan cikin gidan en sanda sukai gaba dashi mubash Babu irin kukan dabaiyiba but abanza tohm Mai yayi dazaa kamasa? Yana ji Yana gani akasashi a jirgi sai birki nafaso anan aka kullesa har tsawon watanni biyu Keenan tareda horo maiban tsoro da al'ajabi da habeebty tasa anamai danduk aikintane inkaga mubash bakaso kakuma ganinsa akaro na biyu ba! Niduk diraman Nan Banda masaniya nadai San Yana qasar but bansan halin da yake ciki ba Dan Masoyiya tace a6oyemun Dan tasanni da shegen sany'in zuciyan bala'i nandanan zance Kar a hora mubash akyalesa itako yadda ta kwallafa Rai Akan cin duduniyar mubash ai wlh ko waye yace kartayi bazata sauraresaba Dan taqudurci aniyan masu hali irin na mubash duk dainawa zasuyi Dan saitayi exposing d'inshi duk duniya Susan halinsa sukuma kyamacesa shida kansa aduaan mutuwa zai ruqama kansa Akan rayuwannan hmm baridai sakin Aymanah ya shigo hannu takun!



Yau ta kasance 20 ga watar June 2019 Wanda yayi daidai da ranarda muka shiga kotu Dani da mubash!


Zaune nake cikin lauyoyi jikina sany'eda kayansu idanuna Sany'e da siririn spectacles (glashin Ido) kaina adurqushe Ina nazarin wasu takardu shigowan alqali cikin kotun ne yasa kowa dake cikin kotun miqewa Dan girmama alqali Saida ya zauna sannan ya buga wani 'yar guduma alaman ya amsa gaisuwar mu muzauna Nan kowa yashiga misimisin zama Dan kotun Cike yake maqil da jamaa Ni har mamakin hakan ma nayi Nan alqali bayan zazzaunawan mu yabuqaci a fiddo da Mai laifi buguwa zuciyata tasomayi naji nasoma loosing control a hankali nasoma furta aduaan samun sauqin lamura gun Ubangijina aduar itace *Salamun qaulan min rabbir rahim* sau babu adadi naketa maimaitawa har wata ni'imtaccen nutsuwa ta ratsa sassan jikina ajiyan zuciya nayi Wanda adaidai lokacin wasu 'yan sanda biyu suka shugo cikin kotun riqeda mubash dake Sany'e da ankwa kallo d'aya yaymun ya d'auke idanunsa gareni Dan alamu Sam bai ganeniba Dan dama maiganeni sai yasha fama Dan sanjawar danai! Niko quri namai da ido Ina qaremai kallo sabida tsoro da tausayin halittar mubash Dana gani yayi wata muguwar Rama Dan ciwon sa dalilin qin samun maganin da batayi yasa duk tafara cinsa Inka gansa yanzun kaman wani kwashoko!

Yayi baqi sosai duk kwalisan Nan ta mubash babushi Babu alamarsu kman ba wannan d'an kwalisan Mai shegen d'aukan wanka ba na sace zuciyan Yan Mata *mubash*! Ay wata kalar Imani ce tasoma ratsani sosai Kai lallai duniya juyi juyi duniya Mai yadda tasoma mutum yau Wai mubash shine awannan halin Allah Mai komai da komai Mai iyawa da hanaawa waiyioo duniya budurwar Wawa duk Wanda yad'au duniya da zafi wlh qarshe zata nunamasa inda yadace Wai yau mubash maicin duduniyata Mai dukana Mai azabtar Dani shine yau ahaka Kai Allah kasa mucika da kyau da Imani!

Maganar alkaline tamaidoni duniyar tunanin danake ciki sannan namaida idanuna Dana kafe mubash dasu Kan alkali dake magana:

"Ina lawyern Wanda ake qara?"

Shuru ba lauyan daya miqe hakan ya tabbatar mun cewa Yar uwa love Bata daukanma mubash lauyaba hmm ai he don't deserve that wata zuciyata ta rayamun hakan!

"Babu Keenan?" Alqali ya Kuma jeho tambayar Nan sectary lawyer yace eh Babu Yan rubuce rubuce alqali yayi sannan yace Ina lauyan Wanda yake qarar Mai laifi? "

Nan kotun tayi shuru ana jiran miqewar lauyan Wanda ake karewa Shima mubash zuba idanu yay yanason ganin lauyan dakuma Wanda ya maka Masa case shida bai ko ta6a fad'a da wani a birki nafaso ba habeebty dasu Amma da Dr Saad duk sun zuba idanu suna sauraron miqewata Saida alqali ya Kuma nanatasa sannan namiqe a hankali inda duk idanun jama'an cikin kotun yakoma Akaina tsuru da idanu mubash yamun Dan kurum ji yayi zuciyansa na buguwa sai kallona yakeyi yanason tuno inda yasan fuskannan Dan sai yanzun yake ganin muguwar kamar da fuskar tamai da kaman yasan fuskan maganartace tamaidoshi duniyan tunanin da yakeyi;

"Ur majesty sunana barrister Aymanah Mubin Aliyu lere Kuma nice lauyan Mai Kare ............


Bankaiga qarasa maganata ba kaman saukan Aradu naji muryar mubash daban ta6a sanin Yana da itaba tana furta!



"Wa.... Waaa.... Wat?!

Yanayi Yana fito wa daga box in dayake tsaye Yana nunani da d'an yatsa ilahiri jikinsa da ga66o6insa sai kerma suke Niko wani daure fuska nayi ina kallansa Rai 6ace Nan fa idanun jamaa suka koma kanmu!

Zuwa yayi daf Dani bakinsa na karkarwa yake fad'in:

"Ay.... Ay .... Ayma.... Aymanah?! Yanayi Yana nunoni da d'an yatsa Niko na tamqe fuska kaman wacce aka aikoma mutuwa had'a girar sama da qasa nayi Ina ballamai harara shiko mamakine fal ransa haaa'a yaza'ayi ace wannan Aymanah ce ba ancemai Aymanah ta rasuba toh Wanda ya mutu Yana dawowane?!

Jawoshi da wasu Yan sanda keyine yasashi dawowa duniyar tunanin dayake yi Yana Mai tsananin mamakin wannan al'amarin! En sanda Saida suka maidasa box section in sannan suka barsa alqali yabuga 🔨alaman kowa yayi shuru sakamakon hayaniyar data kaure a kotun tsit kowa yayi kaman wa'inda ruwa yaci kowa yamaida hankalinsa gun alqali danjin maizaice gyara tabarun idanunsa alkalin yayi sannan yayi gyaran murya yace:

"Barrister kotu tana sauraronki"!

Na nagyara muryata nawaigo Ina kallon habeebty da Dr Saad da Amma wa'inda suma sukamun tsuru da idanu gyad'amun Kai habeebty tayi alaman *go on* Shima Dr Saad jinjinamun hannu yayi sannan na maida idanuna Kan mubash Wanda Babu abinda yakeyi sai kallona shifa wlh har yanzun baiyarda cewa Aymanah bace Dan Aymanarsa ta rasu likitoci sun tabbatar Masa da hakan sannan Kuma Aymanarsa batakai wannan kyau da girmaba Niko nace(😒sadda Ayamah ke qanqanuwa kasanta ai lokacin kyawunta da surarta Basu idasa fitowaba sannan shekaru 6 aiba kwana 6 bace ko sati 6 malam mubasshir🤗)!

Ballamai harara nayi sannan namaida idanuna Kan alkali nasoma magana tiryen tiryen tun abinda yafara had'ani da mubash har auransa har gudowarmu birki nafaso harkuma zamana gidansu Dr saad!

"Ya Mai girma Mai shari'a da wannan dalilan nawa da Kuma hujjojin Dana gudanar agaban kotu nakeson wannan kotun Mai adalci data amsarma Aymanah 'yancinta wajen azzalumin Nan tahayyan raba aurena Dani dashi ! Nagde ya Mai girma Mai sharia! "

Da wannan maganar nawaiga Ina kallan mubash Wanda yabud'e idanu baki hanci duk yasaukesu Akaina yanamai kallona Cike da mamaki Kai shifa kansa a d'aure yake yaza'ayi hakan tafaru yaakayima ya yarda Dr Saad lokacin maiyasa baiyi tunanin tym inma cewa Aymanar zata iya had'a baki da likitocin asibitin Dan taku6uta a hannunsa Kai! A lokacin maike damunsa ne baiyi wannan tunaninba iyye?! Niko nace(ikon lillahine ya haneka hakn ai malam mubasshir)

Waigawa nayi nakalla habeebty tajinjinamun Kai alaman Jinjina hakanma Dr Saad d Amma suka jinjinamun Nan nakoma nazauna kotu tahau surutai masu tsinema mubash nayi masu tausayamun nayi en rubuce rubuce alkali yayi sannan ya d'ago tareda buga 🔨kowa saiyayi shuru ana sauraren abinda alkali zai ce!

Kallon mubash alkali yayi sannan yamaida idanunsa gareni sannan ya Kuma ciresu Akaina yamayar Kan mubash in! Gyara murya yayi sannan yace:

"Mubbashir shin kaji abinda Aymanah tace gareka tareda hujjojinta da proves inta agareka? "

Gyad'amai Kai kurum mubash yayi kman wani agama lizard shi duk mamakima ya ishesa!

"Ko da abinda zaka iya cewa akai? Kafin kotu ta Yankee hukunci?"

Kuka tururus tururus Malaminku mubbashir ya fashe dashi yanayi zai6ud'e baki zaiyi magana ay sai wani sabon kuka ta tasomai Niko wani haushima yake ban walle😒!


Chandai yace:

"Haakane duk abinda tafad'a ya Mai shariaa saidai wlh nayi nadama Dan Allah Aymanah kiyafemun nasan na cuceki a rayuwa Dan girman Allah kimun afwa wlh nayi nadama kitausayamun Aymanah wlh Ina matuqar sonki wlh Aymanah bazan iya rabuwa dake ba!"

Aikuwa kaman ya doke zuciyan Aymanah tawani miqe jijiyar wuyanta sai tafarfasa yake ta Mike ta nuna Mubash da d'an yatsa tana furta "objection my loard ya kamata mubashhir yaruqa sanin irin maganganun dazai ruqa furtawa ga Aymanah ya Mai girma Mai shariaa ko a addini baa auran tursasawa inaakayi la'akari da sammun da mubash yamun Dan na afka tarkon sonsa wannan ya aurenine bisa asiri bawai yarjejeniyar soyayyata ba ya Mai shariaa inason kotu ta amsan mun takardar sakina agun mubash Dan banida shaawar qare kasancewa matarsa ba!"

" Aymanah karkimun haka Dan Zeenat ma tayaudareni ta barni da ciwon qanjamau nasan duk hakkinkine ke Bina ki yafeni Aymanah kizo muzauna kiyi jinya ta har tsawon kwanakin da ya ragemun a duniya Dan nida gawa duk d'aya make ayanzun Aymanah kitaimaka nasama wacce zatamun takaba at least Nima nasamu matata tamun takaba burin kowani mataccen miji Dan Allah Aymanah!"


Dolene duk wani mahalukin dake zaune awannan kotun mubash yabasa tausayi wlh kO ita Ayamah sai da tausayinsa ya karad'e Ilahirin jikinta da ga66o6in jikinta Amman Sam baza sake yarda ta koma ma Mubash ba tayi nisa batajin Kira agun son kasancewa da Yaah Hydar d'inta Dan haka saita dake ta gimtse tace fafur sai yabata takar dar ta Nan alkali yabukata mubash ya sake ta ko inyaqi kotu taraba auran!

Mubash da gumi yarigada ya rufemasa ilahirin jikinsa har futsari yaruqa fesowa ajikinsa lokaci lokaci share gumin fuskansa kaman wani sabon akuya yasoma magana cikin kuka yace:

"Saidai kotu ta raba AURAN Amman nikam bazan iya sakan Aymanah ba!"

Shuru kowa da abinda yake saqawa a xuciyansa alkaline yayi en rubuce rubucen sa sannan ya d'ago Yana kallan jama'an dake Cike da kotun maqil gyara tabarun idanunsa yayi sannan yayi gyaran murya wanda kowa yamaida hankalinsa kan alkalin dansonjin abinda zai zartar;

"Abisa hujjoji da dalilai da barrister takawo ga wannan kotun,Dan haka kotu ta gamsu da hujjojinta tareda amsarmta hakkinta! Wannan kotu Mai adalci tayanke hukuncin raba AURAN mubbashir Musa da Aymanah Mubin kotu taraba auran nasu har sau uku sannan kotu ta Yankee ma Mubash hukuncin daurin shekara 5 a cell dalilin zubarda cikin matarsa dayayi wannan shine abinda kotu tayanke,!

Alkali nagama fad'in hakan yabuga🔨 Nan kowa yamiqe Dan girmama alkali ihun mubash ne yamaido hankulan jamaa duka akansa ihu yake Yana Aymanah tayafe Masa mutuwa zaiyi Tama Allah ta yafemai ganin yadda duk mubash in yasusuce yadawo ne a lokaci qanqani yasa jikin kowa yin la'asar!

jiki a sanyayye Aymanah ta Isa gareshi yadda ta iske mubash ya koma a sakanni dabasu wuce 3 ba abin yayi mugur firgitata gawani garaji da qirjinshi keyi Kai kace murane ta tarun Mai awajen yakasa fiddawa sunanta kawai yake mitan nanatawa akan tayafemai zai mutu ai batasan lokacinda tai zum ta iso gareshi Yana Nan kwance warwas aqasa kowa yaja da baya ganin yadda yake fidda numfashi a 360 riqe hannunsa tai shiko yariqe Gam har riqon yaso tsorata Aymanah Dan saitaji tamkar ba riqon mutum d'aya ba kuka tafashe dashi kurum Mubash yace cikin muryarsa da yake fita a hankali


"Aymanah ki yafemun ki yafe mun ko zan samu nasamu sassauci agun Ubangiji Dan Allah Aymanah kiyafemun mutuwa zanyi ki yafemun Aymanah ki yafe..........!


Baikai ga qarasawa ba jikinsa yasaki kwas!


Alamun d'aukewan lumfashinsa Keenan komai najinkin sa yasaki hannunsa dke cikin na Aymanah ma yaski lakwas cikin zazzare idanu Aymanah tasoma kallonsa daga Kan fuskarsa har kafarsa innalillahi wa'innan ilahiri rajiun shine abinda ke fita abakina hakn yasa habeebty da Dr Saad saurin isowa gareni Niko sai faman jijjiga mubash nake Ina Kiran sunansa "mubash! mubbashir😭 kamiqe Dan girman Allah Karka mutu wlh nayafema ka miqe Dan Allah Karka mutu Dan girman Allah.......!

Nan kuka yaci qarfina kurum nafashe da kuka Mai tsuma Rai na kwantar dakaina Akan qirjin mubash in Ina dukan qirjin NASA a hankali Ina Kar yatafi ya6ud'e idanunsa na yafemai!


Wallahi tallahi masu karatu harga Allah mutuwan mubash ya rikitani Kuma yashigeni sosai da sosai in maqiyinkama ya mutu ya kakeji bare mubash Wanda yakasance miji agareni adaa dukda zaluntata dayayi na gwammaci _Saki Akan _auran wahala_ !

Mutuwarsa ta ratsani Kuma taqaramun imani sabida mutuwar tasa ta tabbatarmun da duk fariyan bil'adama da wannan ran ne yake tinqaho da fariya kwantil kwanta inta fita daga sassan ruhin mutum shikenan fa! Shikenan fa wlh komai NASA yaqare iliminsa dukiyarsa mulkinsa qimarsa fa! Komai NASA taqare wlh saidai fa amai komai fa amai wanka a sallaceshi a haqa gabari abinnesa kowa ya Kama gabansa abarka dakakai sai halinka da sallolinka fa! Shikenanfa 'ya'yan ka matayenka iyayenka abokanka Yan uwanka dukiyarka motocinka komaifa bazasu zo su zauna dakaiba iyakarka suma rakiya gidan gaskiyarka iyaka asaka motarka akawoka aciki yanzunkamma da talakan da Mai kud'in duk cikin akora kura fa akesa gawan nasu akawofa!

Kaico duniya da haka Kuma zakaga muta dasa buruka kala kala a duniyan Nan dafa anciremana ran Nan shikenn fa tamu ta qare shikenan fa wlh lokaci qanqani zaa manta dakai! Kai jamaa wlh murage wasu abubuwan damuke aduniyan Nan Dan mutuwa Bata sanarwa Bata Kuma fashin d'aukan kowayene kuwa a duniyan Nan tunda Wanda Ubangiji ma yafisoduk duniya nabiyullah mutuwar tazo ta tafi dashi uban wayene bazai tafiba? Wayene nace bazai mutu ba? Wlh Babu kowa komai da kowa zai mutu wlh mukoma ga Allah!


D'agoni da habeebty tayine yasani kallanta itama kobaa fad'amunba tana cikin wani yanayi na tausayi fad'awa nai jikinta nasoma Rusa wani sabon kukan Wanda ta kyaleni inayi batareda ta lallasheniba Dan shine kurum zai kawomun sassauci a yanzun Babu abinda nafi buqata sama dashi in ayanzun! Kai Allah jiqan mubash dai kurum masu karatu inaji Ina gani aka dau mubash akamai wanka akamai sutura aka Tara mutane aka sallaceshi aka kaisa gidan gaskiyarsa!


Ohni Aymanah shikenan fa mubash ya mutu ya tafi bazaa sake yayinsa ba Kuma Kai jama'a yanzun duk abinda mubash keyi adaaa akacemai haka rayuwarsa zai qare ai bazai ma sakema Wanda Yama Mai wannan maganar Koda kallon kirkiba!

Hmm masu karatu haka rayuwannan take fa yau Kaine gobe ba kaiba waiyioo! Masu karatu wlh muji tsoron Allah!

Mubash Allah dai yajiqanka ya kyautata makauncinka ya Kuma yafema laifuffukanka!


Haka naruqa jinyar mutuwar mubash a zuciyata sainajima dama wlh bankai qararsaba na amsa sakina cikin ruwan sauqi kurum Kai wlh duk nice sanadin mutuwarsa! 😭

Yar uwa na yawan nusata Akan nadaina cewa nice silan mutuwar mubash kawai haka Allah yatsara mutuwarsa zata kasance!


Sosai suke kwantarmun da hankali itada mijinta harnasoma sakin jiki Amman akowacce sallata Ina saka mubash a aduaa Allah cigaba damai gafara!


Masu karatu kwanaki fa sai tafiya yake sakanni da mintuna sai shud'ewa take ana maraici dare zai tsala safiyama tayi haaka rayuwa taita cigaba da tafiya da dad'i ba dad'i yanzunkam namance mubash saidai inamasa aduaa ba fashi hankalina yanzun duk yayi gida gun dangina kurum nakeson tsintar kaina Danko duk dad'in gidan uban wani gidan ubanka yafi kodako ace Kashi kukeci agidanku Kam!


Ayaude ansa ranar tafiyar mu nigeria Nan da 2wks kai masu karatu zanso kuga irin farin cikin danake ciki wlh Dan ko sadda habeebty tasanar Dani rumgumeta nayi Ina ihun murnarta harda raawata wlh yooo badoleba bayan shekaru aru aru har 6 zan sake ganin sany'in idanina su Marwa mamanmu mamy yapendo yaa Salim su anty ameena da Rabin Raina Yaah Hydar wacce kaliyar murnace bazanba ko makka aka biyamun iyakata murnarnan Kai masu karatu tsayawa labartamaku tsananin dad'in danake ciki Kam yanzun 6ata tym ne kawai kudai nabarku ku qiyasta! 🤗



Tun ranarda sakin mubash yahau kaima Amma fa tashiga gyarani gyara kuwa irin ta amare acewarta Dana koma Nigeria sai aure niko sai wani dad'i nakeji jikina harya Kuma murjewa sai yalqi da sheqi yakeyi ko giftawa nai sai nabar tsarabar kamshin jikina Dan qamshin danakeyi na dabanne acikin qamshi Kam! Kai Babu abinda zan iya sakama Amma dashi sai fatan gamawa da duniya lfy kurum Dan ko uwatace abinda zatamun Keenan wlh!



Zuwanmu Nigeria sai kankama takeyi fa 💃🏻Niko dad'i kaman ya kasheni tsaraba Kam saidai inban fitaba jidosu kurum nakeyi musamman Yaah Hydar kaikace nama rigada nazama matarsa ma 🙄ko ince Yama yarda ya amsa soyayyata ma ! Oho ni ina ruwana nidai jido tsaraba kurum nake kaman bansan ciwon kud'iba!


Su Yar uwa har mamakin iriyan San danake ma Yan uwana suke Dan Babu Wanda banma tsaraba ba kaf dinsu!


Ayau take jajibarin sallata fa masu karatu😂💃🏻ko ince jajibarin zuwana Nigeria aradu😂ai daka ganni zaka ga ainihin Aymanah Mubin tafarkon lbr Dan tsokana da barkwancina duk dawo dasu nai su habeebty mamaki suke waidama Ina magana har haka😂Niko nace tab ai inaji nafi aku marigayi mubash ne ya ladaftar da bakin😂!

Zaune nake ana mun gyaran Kai had'i da kunshi Mai kyau nida habeebty kaikace amarya 😉Niko yinakeyi da biyu Dan nabirge Yaah Hydar eheee🏃🏽‍♀Dan yanzun bazai ganni bai kyasaba Dan Aymanar yanzun tafi Aymanar daaa kyau da diri masu kyau kam😂!


Mungama gyararmu yayi kyau daganan muka nufa kasuwa mukasoma wasu siyayyan!



Nigeria Kam Yaah Hydar ya rigada yasan zuwan Aymanah Dan har yasoma tanadi da shirye shirye na musamman ! Yapendo har tambayarsa take kwana2 taga yasanja ne yadawo so cool da yawan faraa abinda baasansa dashi daba Daria yake Mata yace zatasan abinda kesasa faraa Nan bada jimawa ba!



Kowa fa adanginsu Aymanah nagani maqil agidan yapendo su yaa Fahad da Salim su anty ameena zubaida Kai duk 'ya'yan gidan namu da jikoki duk suna gidan su marmy da mamanmu da kakarmu kowa yayi jugum jugum a falo!

Yapendo ce ta Soma gajia tacire tagumin datayi sannan tace
"Salim Kuma kiransa Mana kozai shiga"

Kuma Kiran Yaah Hydar Salim yayi Amman amsar d'ace itace lanbansa a kashe!

Alama yayma Yapendo alaman haryanzun akashe!


"Toh shi yaron Nan Wai Mai yake nufine yatasa hankalin kowa yace Azo Abuja kowa yabar aikinsa gashi zuby dake lgs ma tazo mutane dake nesa duk yasa sun hallara Amman ya watsar damu tun jia ya kashe wayoyinsa Wai Mai Aliyu ya maidamune Wai!


Yapendo ta qarake maganar cikeda Jin haushi daddy ne yace Tai haquri tundadai akaga Hydar yayi hakan yanada babban daliline shiyasa Amman inba haka ba bazai kirasu abanzaba ai sudai qara bashi zuwa gbe!


Nandai aka cigaba da tattaunawa da mamakin

11 / 13