Author : Ayshakhair Category : Love
samun wannan rahmar ta Ubangiji Kuma Malaccin da idan ya aikama da masifa Babu Wanda ya Isa ya cirema shi face yayi izinin hakan Alrahim Mai qaunar bayinsa Wanda yake fushi har in bawan sa yaqi roqonsa Wanda mutane dayawa Allah Yana Jarabtar sune Dan su dawo garesa su naima buqata agunsa bawai Dan baya qaunarsu bace aa saidai Yana fushi idan baka roqansa Allah ka karamana qaunarka acikin rayukanmu ya Allah ka Kuma sa mu mutu masu Imani da shahada)
Da kansa zai bama kansa amsa Dan bamai iya basa amsa inda zaice : "lillahi wahidul qahhar" (Allah shi kad'ai keda ita)
Ameen ya Allah !
Qarasowa 'yar uwa love tareda Dr Saad sukai suna Tayani murna Dan ayaukam an rantsar Dani nazama lawyer cikakka Mai zaman kanta! Kai Allah abin godia hmmmm !
Wanda nagani tsaye ya hard'e hannayensa Yana wurgomun murmushi ne Mai Cike da so da qauna yasani saurin zaro idanu bakina na rawa ina furta "yaa.. yaaah Hydar!
Da sauri su Dr Saad suka juyo Dan San ganin Wanda nakira d'in Amman wayam basu gansaba hakan yasasu tambayata lfy Aina kikaga Hydar din cikin yanayi mmakin 6acewar sa a daqiqu Soma nunamasu da hannu inda nagansa Amman wayam Babu shi¡
Dariya Yar uwa love tayi tana Mai Kama hannuna tana fad'in:
"Kayya swantyn Hydar masoyiyata zomu tafi hai babu wani Hydar anan shida yake Nigeria!
Kama hannuna tayi mukasoma barin wajen Niko nabita kman raqumi da akala Dan wlh nikam dagaske idanuna sun ganemun yaah Hydar d'in wlh nagansa to yaakayi Kuma ya 6ace kodai kawai Dan nayi mafarkinsa jia Akan yazomun taron murna ne yau nagansa mafarkin ya haskomun shi? Banda Mai ban amsa haka naruqa bin wajen da kallo har muka fita muka shiga mota Dr Saad ke tuqi habeebty na gaba Ina baya kmn ance na waiwayo kurum nagansa a bayan motar mu Yana dagamun hannu alaman bye bye da sauri nakuma kallonsa Dan banso kwakwalwata takuma cewa ba shi d'in bane da gaske kallan saman la66ansa nayi bisa alama sunana yafurta hakan yasani 6ullo da Kaina ta window ina furta "yaah Hydar........... ✍🏼
Real pure moment of life writers
😭 AURAN WAHALA KOH SAKI?!😭📝🙆🏻
by Ayshkhair☺
page 47&48
Ban jira wani tambayan su Dr Saad kurum ba 6alla murfin motar na yi hany'ar inda naga Yaah Hydar yabi! Da mamaki suma suka fito suna kirana Amman Sam bana majinsu burina kurum nagan na Isa kun Yaah Hydar d'ina! Wani kalan fad'uwan gaba naji a lokacinda nariqe bayan rigar Yaah Hydar d'in lokaci guda Kuma hannuna yasoma 6ari Dan bansan irin tarbar da Yaah Hydar d'in zaimun ba ga mamakina Yana waigowa sainaga waninsa sa6anin shi Yaah Hydar d'in hakan yasani saurin jany'e hannuna akan rigar mutumin Wanda inma mafarki nakeba ta66as da ita Naga Yaah Hydar da shi tohm kodai kodai idona gizau takoma yi Akan Yaah Hydar d'in ko Kuma aljanine ke zuwan mun a siffarsa Dan ganin tsananin son shi da nakeyi? Tohm inba hakaba ai wlh da idona nagansa Yana dagamun hannu sannan Kuma yana mun murmushin da ba Koda yaushe yake yinsa ba Ohni Aymanah 'yar Mubin jikar Aliyu! Wata kaliyar rayuwa Kuma nakeson jefa Kaina?!
"Are u okey?"!
Maganan sane yadawo Dani duniyar tunanin Dana fad'a da sauri nad'aga Ina kallon mutumin da ya kafeni da qananun idanunsa yasason Jin ba'asin riqe Masa bayan rigar danayi batareda nayi wani tunaniba ta kalla hannun nawa dake riqe da hannun rigarsa nayi saurin cire hannuna ina mamakin tohm ayaushe Kuma nariqe rigar hannunsa bacin Kuma bayan rigarsa na riqe? Ta6e baki nayi sannan nace:
"Am...am...am Dan Allah sorry it was a mistake perdone me!"
Girgiza Kai kurum yayi ya juyamun baya yasoma tafiya abinsa nikuma nabi siririn bayansa da kallo🤔 tohm ko uwar Mai nake kallo abayan NASA? Ohon mun wata zuciyar tace qilan fuskan Yaah Hydar kikeson yafito a bayan bankaiga wani tunanin ba naji an dafani sosai na juyo Ina qare Mata kallo nad'an saki wani lallausan ajiyan zuciya Ina kallan habeebty murmusawa tayi takama hannuna tajani har cikin mota inda *besty Saad* ke jiranmu dukamun bayan motar muka shiga nida habeebty sannan *besty* ya tada motar yabata wuta muka bar haraban *bar* d'in Saida mukai tafiya Mai d'an Nisa sannan 'yar uwa ta dafani takira sunana a hankali:
"Masoyiya"
A hankali nad'ago idanuna da tunda muka shiga motar band'ago na kalla kowaba! Kallanta nad'anyi duk fuskarta cikin damuwa hakan yad'an sani tunanin ban kyauta masu abinda nayi yanzun ba!
"Naam "
Kama hannuna tayi sannan tace:
"Kinason kikoma gida gun Yan uwanki ko? Masoyiya? "
D'an murmushi nayi sannan na kalleta nace:
" Aa 'yar uwa ai nasan zan koma"
Wani ajiyan zuciya tayi sannan ta kalla Dr Saad Wanda yake tuqi Amman dukkanin hankalinsa na akanmune ta mudubin mota yamata maagana da ido Ina gani itama ta mayarmai amsa ta wutsiyar ido sannan ta lumshe idanun nata ta bud'esu Akan nawa sannan tace:
"Hakane Masoyiya in Sha allah Zaki koma cikin watan da zamu shiga Dan in Sha allah zamu shiga shari'arki da mubash Nanda 2wks Dan nayi nasarar damqosa yanzun haka yadawo qasar birki nafaso akaro na biyu Wanda awannan karon rabuwarki dake dashine takawosa! "
Sany'any'an ajiyan zuciya nayi Danni yanzun ba mubash bane agabana Yaah Hydar ne dan komai nawa tunanina zantuqana komai na Yaah hydarne ban tunanin zan iya musany'a kalamai Dani da mubash Dan duk kalamaina sunaga Yaah Hydar ne Wanda zuciyata tayi naam aduk lokainda nagansa saina fallasamai sirrin zuciyata saidai inzai bigeni yayi gunduwa gunduwa Dani Amman Kam Yasin saina gayamai kozan sama zuciyata tarage wani abar a dangane dashi!
Amman Kuma inna tuna aurena dake Kan mubash sai Kuma naji inamai son sake ganin mubash in Dan kwantan takardata kota hany'ar qaqaniqaqa nasan ko kud'i nace zanbaiwa mubash Dan yaban takaddata zaiban tunda lashe money ne zaiyi komai Akan kud'i!
Niko Ayshkhair nace:
"Anya kuwa Aymanarmu in mubash yaganki ayanzun a yadda kiken Nan zai so rabuwa dake kodako dollars Zaki basa? 🤔😯?"
Mudaije zuwa zamu sama amsar mu ai in Aymanar tacigaba daban labarin nata!
"Shikenan Yar uwa love Allah kaimu nagode sosai"
Koda muka dawo gida 'yan uwan su Dr Saad sai zuwa suke suna Tayani murnar kammala karatuna lfy kowa sai tsokanata yake da mighty barrister!
Ni sunanma Daria take ban Amma ce da Dr Saad da Kuma Masoyiya da Abbansu suka had'amun wata taron liyafa Wanda d'unbin gwamnonin birki nafaso da Kuma senatoci da many'a many'a Yan kasuwa da abokann Dr Saad da dangi duk sun hallara wlh sosai taron ya qayatar na amsa kyaututtuka Wanda harbansan iyakarsu ba aduk cikin kyaututtukan daakaban ba Wanda yafi d'aukan idona kaman Wanda Dr Saad yaban sosai nakeson kyautar harma Yana bani na miqama Yar uwa nace ta ajiyen shi daban amsa tayi tana mun murmushi Wai nafion na Dr Saad Akan nata itakam key in wani had'ad'iyar mota taban Wanda Shima sosai naji dad'in kyautar Amman Kuma bansan maisa naji duk cikin kyaututtukan nafison Wanda Dr Saad yaban gashidai acikin wani matsakacin box yake! Amman Kam akwai d'aukan ido!
Taro yatashi lfy inda nayi godia sosai ga wa'innan bayin Allan! Alhmd komai ya tafi yadda akeso Dan a yau d'in Kuma aka kawo kayan gaisuwar autar Amma watau autarsu Dr Saad *iftital* inda akasa bikin Nanda 3wks a yadda naji zamuje umra Dani da Dr Saad da habeebty da iftital da Kuma habeeb dan kishian Amman! Waiyooo dad'i kasheni masu karatu nayi murnar nayi murnar harda kukana waiyooo Ni ayamana Ashe da rabon zuwana gidan Allah darabon zuwana Inga kabarin habeebullah nabiyullah ! Hmm lokacinda akai zamu nida Marwa a gidanmu abin bai yuba sabida wasu dalilai ase ase zuwana Saudi sai a birki nafaso akuma dalilin mubash Kai ko banza AURAN WAHALAN danai da mubash yad'an amfanamun wasu abubuwan ba 100% cutata yayi ba Dan Kam adalilin AURAN sa ai na kammala karatuna nasama motocin Kaina sannan kuma da yardar Mai duka jirginmu zai d'aga saman samaniya ta luluqa qasar nabiyullah Muhammad sallallahu alaihi wasallam👏🏻 wani jarabawar ta Allah baiwace Kam!
Ina kwance Akan gadona Ina sauke ajiyar zuciya Dan Kam na wahala yau d'innan firgit namiqe tunowa danai da gift d'inda nabaiwa Habeebty ta ajiyen har Ina sa hulana Dan miqewa zuwa amsa sainaji anturo qofan d'akina bakinda liqeda sallama amsa Mata nayi asaman la66ana Ina kallonta tana qarasowa da kyautan nawa murmushi nayi nace:.
"Aiko Yar uwa yanzun nake cewa Bari Nazo na amsa spacial gift d'ina Wanda duk ciki nafiso"
Daria tayi tana maizama akusadani tana fad'in:
" Hummmm su better half in *Zawj* anji gari Maine kikama bestyn naki haka har yabaki kyautar danasan kikafiso huun? "Ta ida maganar tana kallan fuskata rufe fuskan nawa nayi sannan nace:
" Ohohoh yazan sani aikinsan nid'in better half d'in tasace ta musamman shiyasa yaban spacial gift din ai😝"naqarasa maganar Ina Mata gwalo miqamun box din tayi sannan tace:
"Ay shikenan ungo abinki nikam Bari naje nasoma Mana shirye shiryen tafiya! "
Kallanta nai Ina Mai amsan box din sannan Kuma alokaci d'aya inamata magana:
"Kai Yar uwa love shirye shiryen tun ayau"
Daria tayi tace inbanda abin Masoyiya ai tafiyan namu jibine
"Jibi fa?"! Na Tambayeta da Dan mamaki a fuskana "iyyi jibi in Sha allah kinsan zamu gari har uku Kan muje umrar"..
Baki hancin kunne fuska duk a sake nace:
" Kai Yar uwa wannan ai zamu kashe kudad'e diyawa"..
" 🤣hummmm Aymanah kenan! "
Daga haka ta sumbaci goshina sannan tasakeni tana mun dariya sannan tayi ficewarta tabarni riqe da box Ina binta da kallon al'ajabi!
Ta6di suko saikace basusan ciwon kud'iba kyautana nasoma bud'ewa danson ganema idona abinda keciki!
Wow na furta a hankali", box in d'auke take dawani diamond ring blue maishegen yalqi da d'aukan Ido kaidakaga wannan zoben kasan yakai kimanin miliyoyi bankaiga Gama yaba zoben na hango wata dalelliyar silver wrist watch Mai shegen kyau da d'aukan Ido wow" nakuma furtawa ayayinda nake d'aga wani frame daaaka lullu6e dawani farin kyalle Mai yalqi da watsin stones a hankali nad'au frame in nasoma bud'ewa!
Turus na tsaya Ina kallan pic in dake cikin frame in da kallo cikin in ina nake furta "a... A... Aa Ina besty yasamo pic innan?"
Hotonane aciki lokacinda nake baby tym in Ina nusry 2 Sany'e nake cikin rigar sany'i white colour yanada ratsin jaa sannan suwaitan Mai gargasane hulan Kaina Kuma Shima farine da rantsi jaaa yanada dogon igiya hannuna rungume da wani qaton heart jaaa Wanda yake d'auke da sunana akai *AYMANAH* hoton and'aukenine cikin snow lokacinda mukaje US dani da Yaah Hydar da Marwa da yapendo Azma tym in muna wajenta dazama nida Marwa Kai Ina bala'in son hoton wlh Dan Koda na girma Saida na tambaya yaaapendo taban hoton Amman tacemun tamanta inda yake Amman zata naimo daganan ma batasakemun maganan hoton ba Nima ganin hakan sai na share kurum ganin inada Wanda mukai tareda Marwa!
To shi besty Aina yasamo hoton? Gaza Mai bani amsan tambayar nayi harna miqe Dan zuwa tambayan sa sainaga wani d'an qaramin takadda hakan yasani miqa hannuna nad'au takardar! Na warwareta wani rubutune Mai shegen kyau aciki Soma karantawa nayi kaman haka:
_baby lawyer! 🙌🏻Jinjina agareki qaramarsu babbarsu natayaki murnar kammala karatunki lfy I pray u got a successful life ahead Allah kawo miji nagari kamanni gareki stayi bless and tyt love u_"!🙌🏻❤ _baby lawyer na_
Ni sunan Daria ma taban sosai sai yanzun nakuma maimata sunan Dan yamun dad'i wlh _baby lawyer_ Kai Amman besty akwai zolaya Wai Allah bani miji nagari kmanshi🤣🙌🏻hakane Kuma fa Daman kullum Ina cemasa yamun roqon Allah yaban miji nagari kmn shi shine yau yamun aduaan kenen🤣🙌🏻woooo besty na Keenan!
Miqewa nayi nad'au box in nasakashi a closet Ina sannan na d'au zoben nasama hannuna huwuuwooo waiyoooo zanso kuga yadda zoben Nan ya kar6a hannuna ma Sha Allah murmushi sa6e a fuskata na numfa falo Dan tambayan Best inda yasamo pic in!
Kodana fito na iskesa shi kad'ai kaqarasowa nai nace:"Kai Amman besty wlh kyautanan taka tamun tafi nakowa wlh i really like it"
D'agowa yay yana kallona bisa alama waya yakeyi murmusamun yayi kawai yamaida hankalinsa Kan wayar Niko bandamuba nasama gu nazauna Dan tambayarsa inda yasamo hoton nidai banji abinda ake cemasa cikin wayanba kawai naji yace "ok alryt" had'i da cire wayaar akunnensa ya mayar daidai Kan hannun kujerar danake zaune yakife wayar murmusawa nayi nace:
"Waikai besty Aina kasamo best pic Ina?"
Dariya yayi sannan yace "better half Keenan nibanda amsar tambayarki yanzun"
Shagwa6e fuskata nayi sannan nace Mai:
" Kai besty y now? Har sai yaushe abeg gayamun Mana"
Noqe kafad'a yayi yace:
" Aa Better half not now zan Gaya maki Amman ba yanzun ba sai Nan da wani tym karkikuma tambayata ok? "
Ya ida maganar Yana kallona ta6e baki nayi nace shikenn Allah kaimu yace ameen miqewa nai nace Mai zanshiga bacci nagde Sarai yasan banji dad'in yadda ya amsamun tambayata ba Amman sai ya dake
Shigewata d'aki nayi na kwanta ragwaf nasoma tunanin mutumin naku Yaah Hydar! Haka har bacci 6arawo yasaceni!
Haka muka ruqa shirye shiryen tafiyan mu ba qaqqautawa munyi dukkanin shirye shiryen da ya kamata gobe kawai muke jira jirginmu ya d'aga!
********************
Washegari da misalin 9:30am jirginmu yad'aga zuwa qasar Holland........ 🙌🏻✍🏼
*Real pure moment of life writers*
😭 *AURAN WAHALA KOH SAKI*?📝🙆🏻😭
_by Ayshkhair_☺️
_page_ 49.
Satin mu d'aya a qasar Holland sannan muka takarkata muka koma italy inda anan ne muka shafe kwanaki har goma kasantuwan kayan d'akin iftital da muka tsaya siya sannan muka gungura zuwa garin habibullah mustapha sallallahu alaihi wasallam🙏🏻Nan muka sauke farali muka gudanar da umran mu cikin kwanciyan hankali Babu irin roqar Ubangiji na davanyi ba Akan ya karkatomun hankalin Yah Hydar izuwa gareni yasoni tamkar yadda nake sonsa yakuma sa mu kasance ma aurata har qarshen rayuwar mu! Ban Bari nayi sayi sake da aduaa taba sabida muhimmancinta Kuma dayardar Allah bazata dawo batareda an amsamun ba!
Satinmu 1 a makka muka karkato muka koma Dubai munyi siyayya Kam Dan har haqorin makka nasa yamun kyau Kam mun Sha hotuna munyi siyayya kala kala fatan dai mudawo gida lfy kurum daga Nan Kuma Nima nakoma gun iyayena duk sadda na tuno na kusa koma garesu sainaji wani Dadi na ziyartata waiyooo Ni Aymanah bayan shekaru d'ad'ai har 6 bana tareda su sabida AURAN WAHALA da ya jamun Kai Allah shi kyauta kurum banama kowani klan bawa na Allah Koda maqiyi nane fatan shiga gararin rayuwar aure irin tawa! Wlh mu nutsu wajen za6ama 'ya'yayen mu uba nagari shi fa aure sannan manzone Wanda baison aure tom tabbas bai qaunar sunnan annabi! Mu nutsu sosai wlh kafin mu tsunduma kanmu gayinta Kar rud'un soyayyan namiji yasaki saurin son aurensa ko Kuma kud'insa ko mulki ko kyawunsa kifara bincike sosai akansa kisan kyawawan halayyansa kinsan inda yafito kisan tarbiyarsa kisan aikinsa sannan kisan da mutanen dayake huld'a dasu ki guji ke6ewa keda namiji batareda wani muharraminki akusaba kafin AURAN naku nasan baku manta yadda muka kwashe da mubash lokacin sauran sati d'aya bikinmu a *Daveen hotel* Mata kudaina saurin son aure Dan kunga Wai qawayenku nayi ko shekarunki sunyi Nisa kokuma iyaye da mutanen unguwa sun dameki da yaushe zakiyi aure! Hummmm wlh yawancinmu wannan ne kesasu jefa kawunansu cikin masifa da bala'i na aure shifa aure kaman mutuwa take idan lokacinki yazo ko mijin yayarki ko qawa saikiji kin aura aure kaman layin markad'e yake if niqan yazo kanki wlh ko kina wata uwa duniyace sai kinji andaura maki aure walan da Wanda kikeso ko akasin haka so en uwana muguji AURAN sauri ba bincike wlh Kar son namiji ya kaiki yabaroki keda danginki zaibarma ta6o shikam ko akwalar rigarsa labarina ya isheku darasi Kam! Dan alokacin aurena na gwammaci Saki Akan aurena yoto ba gwara *sakin ba* akan *AURAN WAHALA* aiduk Wanda ya karanta labarin Nan nawa kokuma yaji lbrn wannan rayuwar tawa koshi aka tambayesa *AURAN wahala ko saki*? Nasan sakin zai za6a dukda Allah na fushi ga macen data buqaci saki fiyeda auranta Amman a irin nawa ko a sharian musulunci raba AURAN shine mafita tunda aure da asiri ai ba aure bane! Waiyoooo yaah Hydar d'ina karkadamu nimai qaunarkace inanan dawowa gareka in Sha Allah ! 🙌
Kwananmu 4 a Dubai muka dawo huuuu masu karatu zanso kuga yadda nasanja wlh nadawo wata kala kaman ba Aymanarku ba nayi haske da d'anqiban hutu naqara tsawo da girma halittun jikina sunfito d'as dashi mansha Allah yoo yanzun fa shekaruna 23 a duniya nazama cikakkiyar mace ajin farko maiji da kyau da kud'i da Kuma ilimi duk inda NASA qafa sainabar magana tsaban d'aukan idon danakeyi samari kalakala Kai kace Mara aure tunda inkaganni zaka rantse Banda aure Kuma ban ta6a sanin wani Abu Wai shi aure ba!
😕tohm inda ace d'ana na raye fa? Bazaa yarda d'ana bane Keenan!
Hmm bayan dawowar mu rayuwa Mai dad'i muka cigaba da gudanar wa a rayuwar mu ciki ko har bikin iftital daakai hmm munci bidiri Autan amma anyi aure bayan bikinta suka koma qasar Germany ita da mijinta Daman Nan yake aiki fatanmu Allah Basu zaman lfy!
Kwanaki mintuna awowi sakanni sai tafiya take rayuwa saiqara habbuwa yake nikam yanzun Banda wata matsala inba takomawa Nigeria ba shid'inma next month zankoma Dan yau sora sati d'aya tal mushiga kotu da mubash Wanda aka kaime sammaci batareda yasan dawaye zaiyi Sharianba shikam abin duniya ta taru tamai yaawama Dan yayi aurensa da Yar Cameron d'innan Ashe Yar cutar qanjamau ya aurarma kansa wannan dalilinne yasa iyayenta amincema AURAN su Ashe Dan kawai sunsan Yar su nada ciwon HIV tarasa mijin aure sabida kowa yasanta da halin karuwanci anan tasamo cutar gashi tayi auran shiko mubash jiyayi ai yabude sabuwar rayuwa Dan Babu irin dukiyarda Zeenat Bata 6arar Mai gashi Kuma Yana mugun tsoranta lokaci da dama yakan tuno Aymanah yata cewa Allah jiqanta yau abinda yake Mata shi akemai ciki ko har kawo maxa cikin d'akin kwanansu da Zeenat keyi suyi holewarsu son ransu sannan tafita club sai safe take dawo wa at times ita ke gayyatarsa shimfid'arta taitayi yadda takeso dashi son ranta kaikace itace mijin mubash matar inta Gama Kuma tabiyasa kud'i kaikace ba aure sukaiba!
Awata ranar litininne yatashi da ciwon ciki Wanda harsaida Zeenat takaisa asibity ananne aka tabbatar Mata Yana HIV kaman yadda take dashi tab ko ajikinta mubash in nedai daaka gayama harda suma sau uku Allah ya Isa Kam kwando kwando baninkin baninkin Babu Wanda baima Zeenat ba itako tarama mubash