Author : Maman Teddy Category : Romance
ki debi kayan da zasu isa banyan ta gama , tace nagama hadawa. yauwa to zomuje dakina ki tayani hada nawa da sauri tace muje ta shige gaba yana binta abaya tana shiga yasa ma dakin key
[6:35PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞
43 to 46
✍MMN YAZEED
Humaira bata lura ya rufe kofar ba, dan haka ta isa ta fara ciro kayanshi tana sawa a kwati, yace kala nawa zaki diba? tace kai kwana nawa zakayi? nima inaganin satin zanyi , ya matsa kusa da ita, ya kalli akwatin yace ashe kinsan kayan da nafi son. batace kome ba, dayaga ta gama tana kokarin rufewa, saiya mike yace zoki ga wani abu afuskar ki, da saurinta ta taho ta dago mai fuska yafara shafa fuskar yakai bakin shi ya sunbace ta, humaira nason ta hana faru amman tanajin tsoro karyace ya fasa kaita gida gobe, faruk kuwa jikinshi har yawa ya keyi, humaira tafara jin yana wuce gona da iri dan haka ta fara ture shi , faruk murya adaku she yace karkimin haka fa, humaira ko baki son zuwa gida ne? inaso yaya karfe nawa zamu tafi? Ko yaushe kike so, ya fada yana kokarin cigaba da abida yakeyi har yayi nasaran kaita gado tun humaira na iya jure har aka kawo gurin da bazata iya jurewa ba, tafara mai kuka faruk be saurari humaira ba , dan inaganin ko jintama bayayi ta fara ihu bawanda bata kira sunansa ba agidan har samira da suke yar tsama saida ta kira tana fadin suzo su ceceta faruk zai kasheta , faruk yau be bar humaira ba saida ya karbi hakkinsa kamar yadda yake fada, bayan hankalin shi yadawo jikinshi yafara samata albarka, tare da ganin wautan shi da beyi aure tuntuni ba, ashe haka rayuwan aure yake, ya juya ya kalli humaira yaga ko motsi bata iyawa, bayan ya tsarkake jikinshi , ya hada wani ruwan , yakoma kanta ya tsaya, ji yake kamar ya kara amman ina humaira ta gala baita , gata dai akwance amman ba bacci take ba, dan haka ya kinkime ta yasa ta aruwan dumi ta saki kara danma muryar ta ta dashe ba ajinta sosai,ta fara tureshi dan haka ya juya ya fita, bayan ya gyara gadon ,ta fito tana dafa bango, ta nemi guri ta kwata, shima kwaciya yayi , saida aka kira sallah sannan yatashi yayi alwala ya tafi masallaci , humaira ko bata masan me akeyi ba , saida ya dawo ya tashi humaira danyin sallah amman taki ta shi , haba humaira ta tashi kiyi sallah mana , tace bazan tashiba kazo ka karasa ni, mugu kawai mara imani, inbaka kasheni ba Baka cika sunanka faruk ba . toh naji Allah ya huci zuciyar ki humaira kiyi hakuri ki yafemin, kinji tashi kiyi sallah. ni dakina zantafi . to tashi muje naraka ki. tamike amman ina jikin ya riga ya yayi tsami ta kasa koda daga kafa ya taho ya sure ta saida yakaita toilet sanna ya direta, ya koma dakin shi, faruk bashi yatashi ba sai gurin 10:18.
Ya leka dakin humaira yaga tana bacci haryan zun dan haka ya wuce dakin momy, momy tace yauko takwarata lfy kuwa bata fito makaranta ba ,kodan taga meena bata nanne .
Faruk yace naga kamar bata da lfy ne, faruk beson momy ta fahimci abinda yake faruwa.
au kama ma kagani bazaka iya tambayan ta kaji me yake damunta ba. yace momy kindai san halin yariyar nan, ina ganin mura ce dan naji muryarta ta dashe bara naje nasamo mata magani.
bayan ya kawo mata magani ta sha ya shirya ya tafi office humaira ko sai sharar baccin ta take tama manta da maganan katsina humaira dai ba ita ta wastsake ba sai washe gari bayan tayi wanka ta shirya ta bude akwatin ta kara kaya sanan ta nufi dakin faruk, tayi sallama ya amsa mata ta same shi babu kaya ajikinshi dagashi sai gajeran wando danha ta kara tsorata da shi , yace shigo mana . kazo mutafi na shirya. zoki zauna mana takarasa ta zauna bakin gado . yace ke da mukayi dake tun jiya zamu tafi meyasa jiya bakiyi magana ba. to bakai bane kasa jikina yake min cewo. to kiyi hakuri , karfa kece zaki gayawa momy dan ba agayawa kowa ko bikisani ba? Nidai kazo mutafi. humaira kiyi hakuri sai nadawa gobe zan tafi da zarar nadawo zankaiki, humaira ta fahimci dama wayu yayi mata dahaka taitamai rashin kunya iri iri, shedai baya kulata amman bayaso tamai agaban mutane .
Washe gari ya fito cikin shirin shi na tafiya yace momy nizan wuce tace to Allah ya tsare, humaira na gefe sai hararar shi take , shiko sai kallonta yake, yace humaira ba sallama. eh bazanyi ba mugu kawai . da sauri momy tace ke kina da lfy kuwa faruk kuwa juyawa yayi ya tafi , momy tarufe humaira da fada , humaira sai kuka take,
Satin faruk biyu da tafiya amma ji yake kamar ya shekara biyu duk ya kosa yadawo yaji domin matar shi , gashi ya kirata awaya hàr ya gaji, taki dauka.
yau faruk satin shi hudu da tafiya humaira da momy suna zaune adaki harda meena, saiga kira ya shigo wayar momy ta daga bayan su gama , faruk yace momy su dai meena basa zuwa ko inako? tace kadai ce humaira bata zuwa ko ina . humaira tace momy kece mai zamu gidan baba usman , tana maganar da miyau cike da bakin ta tamiki da sauri ta shiga toilet can ta fito , tace kin gaya mai, ban gaya ba, ke kamar ma baki da lfy ko ? a,a lfy ta lau. naga sai ki ta tara yawo abaki ko bacin ciki ne, gashi baki son shan magani' hamaira dai batace komiba wuce tayi ta kwanta taita bacci saida ta share awa uku tana bacci .
momy tace wa meena je ki tashe ta tayi sallah ko abinci rana bata ciba. meena tace momy na tasheta taki tashi momy ce tashiga da kanta ta tashi humaira ta fara layi zata fadi momy ta rigeta saida aka taimaka mata tayi alwala bayan tayi sallah aka bata abinci taci sosai bayan ta gama taji zuciyarta na tashi tafara ya tsina fuska, momy da ke kallonta ta ce lfy. ai kafin taba momy amsa ta tashi da gudu tayi toilet taita kwara amai momy tace azuciyar ta kardai yariyar nan ciki gareta hankalin ta ya tashi tana fadi afili yau na shiga uku a Ina yariyar nan ta samo wannan abu, tabita ta same ta galabaita ta rikota suka fito, meena ce ta gyra wajen .
momy ta shiga tunani yanzu duk alamumi ciki sunbaiyana ga humaira, yanzun me zata cewa alhj idan faruk ya gane humaira tana da ciki bayan , taki yadda da shi, tasan faruk saiya daga hankalin kowa agidan nan, inama cikin faruk ne da humaira taga gata, taje ta sami alhj da maganar , alhj yariyar nan humaira kamar ciki gareta. alhj yayi murmushi yace Alhamdulillah Allah ya rabata da shi lfy , alhj bafa abinda ya shiga tsakanin su, dan ana gobe zaitafi ya kawo min karanta taki yadda da shi, kuma harya tafi basa magana. Alhj yace a, a karki yanke hukunci kibari ya dawo , alhj ya dan tsorata dan haka yace kiyi shiru karki kara gayawa kowa.
bayan momy ta koma dakinta takira faruk tace da shi yaushe zai dawo yace insha Allahu gobe yana tafe dan haka momy tace wa humaira ta shirya suje asibiti , momy ta yanke shawara indai har ciki ne ,to ko zata sa azubar da shi dan baza ahaifar musu shege agida ba , dan a yanzun ji take ta tsani humaira
[6:36PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞
47 to 49
✍MMN YAZEED
Bayan humaira ta fito suka dauki hanya gidan hadiza kanwar momy suka shiga, momy tacawa humaira zauna anan ina zuwa , ta shige ciki, mama hadiza tace lfy kuwa , na ganki wani iri momy tace ba lfy ba wlh hadiza hankali na atashe yake, humaira duk abida taci sai amayar da shi, ke duk wani alamumi na me ciki ya baiyana ma humaira, hadiza tace maye abin tada hankali, ai murna ya kamata kiyi.
ai hadiza baki san wani abuba humaira fa, ba abin da ya shiga tsakanin ta da mijinta, ana gobe zai tafi ,ya kawo min karan ta, kan cewa taki yarda dashi, kuma har washe gari da yatafi ba shiri suke ba, dan ko sallaman arziki ba su yiba. hadiza tace innalillahi wa,inna ilaihir raji,un, amman kin tabayi humaira? Me zan tambaye ta hadiza inna tambaye ta me zan yi, aini abinda nake gani kawai azubar da cikin, ko ya kika gani. hadiza tace anya kuwa ayi haka, baza abari shi faruk din yadawo ba, atambaye shi, kisan fa tsakanin mata da miji sai Allah. Hmm hadiza kenan, yaran da kulum cikin fada suke yanzu ne ma narula hankalin shi ya fara juyawa kanta, ni bana son yadawo yaji wannan lbrn dan inhar yaji bazai rufa mata asiri ba, bashi da hakuri, nikaina ina matukar son yariyar nan amman yanzon naji natsane ta, abu daya nake dubawa, hadiza mahaifin yariyar nan yamana halarci , momy tafara share hawaye.
hadiza tace kiyi hakuri yaya ki kwatar da hankalin ki kibarmi ita anan takwana biyu. momy tace
gobe fa zai dawo , kuma kiga inyadawo bata gida bazaiji dadi , yanzon kawai abinda za ayi kizo muje ki rakani gurin kawarki Dr zainab.
hadiza tace to bari nakintsa , badan ran ta nasoba ta fito suka tafi.
bayan sunje wajen Dr zainab sun mata bayani amman ba suce mata matar aure bace, ta basu wasu kwayoyi , saida suka biya suka maida mama hadiza gida , sannan suka kama hanyar gida , itako humaira batama san meke damunta ba itada kawai taji jikinta ya canza, bayan sun koma gida momy tabata magani , ta karba ta sha.
humaira ko abinci bata nemaba takwata ta fara bacci, can cikin bacci taji marar ta naciwo, tabude ido , ta mike ta zauna . tun humaira na iya jurewa har ta kasa ta fara rike cikin tana kuka, can taji wani lema nabinta, momy ce ta shigo ganin jini tayi yana bin humaira, ta iso da sauri , toilet ta nufa da ita, zuwa ni lokaci jinin ya tsaya, bayan ta bata ruwa tagasa jikinta , tafito tayi wujuga wujuga duk ta rame , akan gado momy ta kwatar da ita, momy ta nemi guri ta zauna anya cikin nan ya fita kuwa , itadai bataga wani guda guda ba , jini ne dai yadan fita dan haka ta shiga zullumi
Washe gari da safe humara na tashi tace , momy kinsan yau me nake son ci?
a ,a saikin fada. wlh dan,wake nake so.
momy jitayi kamar ta mangare ta , tace to ai ina zaki same dan,wake? tace momy yau basai a yiba.
muba shi zamuyi ba inbaza kici abinda muka dafa ba saidai ki bari. humaira ta juyo ta kalli momy, taga momy ta juyar da kanta can gefe, meena ce ta shigo zata tafi makaranta, humaira tace meena dan Allah in an tashi ki biya gidan inna kece mata tabani dumamen tuwo.
momy ta dago cikin fada tace wa meena kar kisake ki biya ko ina ,da an tashi kiyo gida, wlh naji ance kin biya wani waje sai ranki ya baci.
humaira tace momy wai yau menayi miki ne,. ba abida kika min naga dai kincika kwadayi ne.
momy ba fa dagangan nakeyi ba. mikewa momy tayi tafita.
4:25 faruk ya shigo gida . yasame mutan gidan duk a falo humaira ce kawai bata gurin bayan sun gaisa suka dan taba hira, yayita jira yaga humaira ta fito amman shiru dan haka ya mike ya nufe bangaren su, aminu ya bishi da akwatin sa , yana shiga dakin humaira ya nufa, yaji shiru, da haka yafito da sauri dan yana zatan ko taji wani wajene , yana futowa ya tsaya afalo yace banga humaira ba. hjy tace munsiyar da ita. faruk yayi dariya yace da kuwa kunje kun karbota. itama dariya tayi , tace lallai baka da kunya tana daki ba lfy.
da sauri ya shiga dakin yasame ta kwance miyau ya cika bakin ta, ya isa gabanta ya tsuguna yabude ta daga rufan da tayi , yataba jikinta yaji zafi rau yace humaira me yake damun ki . bata bashi amsa ba dan bazata iya magana ba bakinta cike yake da miyau ya tai maka mata ta zubarda ta dawo, yace meyake damunki , tace nima basan abinda yake min ciyo ba nidai kawai bani da lfy. Faruk yayi shiru can yace kina cin abinci kuwa? humaira tace ai dana ci abinci amai nakeyi . yace baki jin kina son wani abu. eh tace da shi amman azuciyar ta sotake ta kwanta ajikin shi dan ayanzun babu abinda take so ila kamshin jikinsa batassni ba turare ne ,ita koma dai meye shi take so, amman bazata iya gayamai ba. shikuwa faruk laifin momy yake gani yaya zayi yarinya bata da lfy abarta agida ta rame haka, suna haka saiga momy ta shigo , yace momy shine humaira bata da lfy haka, ba a kaita asibiti ba. momy tace waye ya gaya maka ba akaita ba, sonawa muna zuwa, sauki ne sai ahankali, shawara ce taimata mugun kamu. yace a sibitin ne sukace muku haka? nidai nace naka sun bamu magani amman basuce ga abinda yake damunta ba faruk yayi shiru ya dokar da kanshi kasa ,can yadago yace to momy anyi mata test ne, da a keta bata magani. cikin fada momy tafara magana test din me za ayi mata, tashi kafita kabani waje.
Faruk yamike cikin zafin zuciya bari naje nasami Dr mansir din saina ci uban shi yaya zayi akawo mara lfy, ba ayi test ba yakama darka mata magani, yajuya yafita da sauri ,
[6:36PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞
50 to 53
✍MMN YAZEED
07014197556
Momy ta ce da abdallah ya bi faruk da gudu ya kirashi, momy har yanzo bata fahimci komai ba ,ta fara tunanin ko dai faruk ya ganu humaira nada ciki ne yanzo ta ina zata bullo wa, al amarin ne, be jima da fita ba saiga shi ya dawo shi da nura , dakin momy suka shiga baya sun gaisa da nura , ya tambaye ta me jiki, tace da sauki, yasa ke cewa wani asibiti aka kai humaira ? tace au yaje ya dauko ka ne ku tsareni ? nura yace haba dai ai munyi kadan ,dama faruk ne yace, Dr mansir yace mai, ba gunshi aka kaita ba . tace eh banan mukaje ba kuzo kumin abinda za kumin. ta mike ta fita. faruk ya juya ya kalli humaira tana ta bacci . su kuwa kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyar shi, suna haka abdallah yashigo da gudu yace , abba faruk alhj na kiran ku, faruk yace yanzun haka kila momy ce tace mun mata rashin kunya, na rasa abinda ya ruda momy wlh duk ta rikece ko inna da take tsohowa batai rike ce haka ba. lokacin da suka shiga falon cike yake da ahalin gidan, samira ce kawai babu. suna ko shiga alhj yafara fadin me yasa baku da kunya ne, mamar ku tana iya kokarin ta akan humaira amman ku kuna rainawa . faruk yace ba rainawa nayi ba, abba amma ai gara asan abinda yake damun ta.alhj yace kuma fa da gaskiyar shi, aisha akaita asibiti yan zun nan, momy tamike da sauri dan bata saba ma umarnin shi, nura ne yaja su , shikuwa faruk alhj yace ya dauki shi suje su gaida alhj usman da beda lfy ,faruk beso hakaba yaso atafi da shi asibitin.
bayan suje gidan alhaji usman sun fito , sai alhaji yace da faruk yawuce dasu asibitin suga me jiki. alhj da kansa ya kira momy yace kun gama ne? tace , ai gado ma aka bata. wane asibiti kukaji ta gaya mai sunnan asibitin alhj yaso akaita wadda suka saba zuwa amman , besan dalilin da yasa momy tayi haka ba .
lokacin da suka shiga dakin da aka kwantar da humaira suntarar da Dr zainab na kanta tana kara dubata, dan haka furuk ya matsa kusa da ita , yace yariyar nan kun gwada ta ne kunga meyake da munta ? Dr zainab tace yanzun dai za ayi mata test. maganin da kika bata da na meye ?Dr zainab ta rasa me zatace , ta juya ta kalli momy tace wannan wanene? momy tace rabo da shi kiyi harkar gaban ki. faruk najin haka hankali shi ya kara tashi idon shi jawur matsawa yayi yasha mata kwula yana fadin ke wacce irin mahaukaciya ce? baki da hankali ne wlh wlh inhar wane abu ya faru zaki gane kuranki,
Alhj dake gefe yafara dakawa faruk tsawa , momy ce ta lura faruk baji yakeba dan haka ta fara kaimai duka, sakinta yayi yana fadin wlh inhar ciki take da shi ya zube bazan yarda ba , sai nayi maganin ki , yafara kokarin komawa wajen Dr zainab, nura ya tareshi, momy ko tsayawa tayi tana kallon faruk tana son ta dada tabbatar da abinda taji faruk ya fada .
bayan Dr zainab ta gama gyara rigarta tace dama yariyar nan tanada miji, yanzun hjy aisha kin kwauta min kenan. momy tarike hunnun Dr zainab suka fita. Shikuwa alhj cigaba yayi da fadan da yake yi . basu dade da fitaba momy ta dawo jikinta asanyaye ta nemi guri ta zauna ta dukarda kai dan bataso ta hada ido da faruk dan ya bata kunya , ta fara ardua Allah yasa cikin be fita ba, bayan Dr zainab ta dauki humaira domin doba lfyr cikita dansu dama tuni sunsan tana dauke da cikin , bayan wani dan takai tattan lokaci tadawo da humaira tare da tabbatar musu tanada cikin dan sati hudu , ta matsa gaban furuk ta