Author : Maman Teddy Category : Romance
taje ta aje abincin ta fara zubawa yayi maza yarike hannuta yace to gani na dawo , koda yake kince zan gane kure na ko? tayi shiru batace komi ba. me nayi miki kika daina gaishe ni? nan ma bata kulashi ba, nan yafara tunani wannan yariyar innayi wasa ko muyar da nake dan samo saiya zama aiki , shi ko rashin kuyar ne ma tayi mi shi yana so dan haka ya mike ya zagayo kusa da ita ya zauna yana rike da hannun ta. saida taga yayi kusa da ita sosai sannan tace ni wlh ka sake ni. yakara rike hannun yace kwantar da hankalin ki, niba wani abu zan miki ba, magana kawai zamuyi kinji, kisan me Nene ? ko kalloshi batayi ba , humara kiyi hakuri nasan nayi miki laifi ba nayi bane dan na bata miki rai bane, ni bana son kitafi ke daya ,ki bari da zarar na samo lokaci zan kaiki da kaina amma kema kidaina min abida kike yi min ki dinga bin umarni na nifa mijin kine, ko bikisa hukunci matar da take yiwa mijinta haka ba" yana maganar yana kara shigewa jikinta. tace nidai kasake ni. kuma wlh idai sai nabi umarnin ka zaka kaini gidan to na hakura da zuwa. haba humaira me yayi zafi haka. tafara ciki cikin kwace hannun ta, da taga bazata iyaba tasa bakinta ta gantsara masa cizo da karfi amma ko gezau beyiba saida wurin ya fashe harya fara jini sannan ya saketa . ta ,kwasa da gudu ta nufi hanyar waje , shima tashi yayi aguje ya tare ta, ta fashe da kuka tana ganin kashin ta ya bushe.
zo ki zauna ba abinda zan miki kinji, yanzo fa saikice dakin momy zaki ko, dan Allah humaira ki daina haka yanzun ba dama muyi abu adaki sai kinje kin gayawa momy, zoki zauna bazan miki komi ba. biyoshi tayi suka zauna sannan ya saketa , yace bari na wanke hanuna na dawo, ta kalli hannuta taga jinin faruk sosai ya fita har a kasa , dan haka tamike tace so yake ya dawo ya zaneni babu me cetona.
futowa yayi be ganta ba , beji dadiba dan beso momy tasani ba dan haka ya kasa zuwa dakin, yaneme guri ya zauna. zuwa can anjuma saiga anty amarya ta shigo da sallama, tasamu faruk yana shafa man zafi ahannu shi ga digon jini akasa, tace faruk wai me yafaru ne, ga humaira can taki magana sai kuka take. ya daure fuska kukan munafurci take anty , cizo nafa tayi . cizo kuma, kai humaira itama bata jin magana, ta juya ta fita, saiga momy rike da humaira tashigo tace karka sake kace zaka tabata yanzun haka mugunta kaje yi mata . momy magana fa kawai nake mata ta kamo hannuna ta ciza. to naji abar maganar ke humaira zoki bashi hakuri. tace Allah ya baka hakuri bece komiba ta shige dakin.
washe gari da safe nura yayima faruk waya bilkisu matar shi bata da lfy. dan haka yaje dakin momy yagaya mata sannan yace tama humara magana su tafi tare. bayan momy tama humaira waya bata bata lokaci ba, ta fito suka dau hanya, suna cikin tafiya ya waigo yace, baki cemin ya jiki ba kuma jiya da zazzabi na kwana. banza tayi da shi, yayita magana ya gaji yayi shiru ,yana kallon hanya, can taga ya tsaya ya dawo da baya , ya tsaya agaban wata kyakyawan yariya , budurwa ce amma zatai kanwa da humaira tana ta karai raya, yace sajjida ina zuwa haka dasafe ? wlh yaya makaranta zani gashi na dade tsaye anan. yace shigo na kaiki mana. ya juya ya kalli humaira yace humaira sauka ki koma baya
[6:35PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞
36 to 38
✍MMN YAZEED
Bata kula shiba saida ya sake maimaitawa ta bude murfi tafita ta koma baya itako sajjida shiga tayi ta zauna ta tam baye shi wannan wacece , yace yar uwa tace, sukaci gaba da hirar su humaira na jinsu, tace azuciyar ta Ashe gaskiyar samira ne , dace faruk nada yan mata, zuciya tazo mata har woya da haka suka isa inda sajjida zata sauka ya tsaya ta fita, tayimai godiya ta wuce faruk yace humaira dawo nan . a,a ni bazan dawo ba" saboda me? mudaije kawai ahaka" nace miki ki dawo nan" wlh banzan dawo ba, kabari inkakuma ganin wata saika Dakota" yayi murmushi yace ai wannan ma da kikaga nadauka na santa ne , dawo nan mutafi , haka faruk yayita magana ya gaji ya wuce , bayan sun isa gidan alhaji ahmad ,motar bata gama tsayawa ba humaira ta fita , faruk ya sake baki yana kallon ta , tashige ciki ko juwuwa batayi ba, lokacin da faruk yake kokarin shiga gidan ,ita kuma ta fito zata shiga dakin bilkisu, bayan ta gaidata da jiki ne , bilkisu tace saida ya tasoku saida na cemai naji sauki, nura ne shida faruk suka shigo dan haka humaira tayi shiru. Bayan ya gaida ta da jiki suka ci gaba tattaunawa shida nura, itako humaira sun shige cikin dakin billkisu , balkisu ta kula da halin da su humaira suke ciki dan haka tafara ba humaira shawara yadda zata kula da mijin ta" humaira me yasa ke kullum indai faruk yana waje saiki ta daure fuska, ki daure ki dan dinga sakarmai jiki mana abinfa yayi yawa " anty ai shima baya sakarmin jiki, kuma wane jiki zan sakarmai shida ba sona yakeyi ba, yana can yana harka da yan matansa" humaira ke kuwa meyasa kike irin wannan tunani, zargi fa bashi da kyau" anty bilkisu wlh bawai zargi nakeba , nima nagani da ido na, kuma anty samira ma ta fada" gsky duk ma wanda ya gaya miki ni inagani dan handasa fitina ne amman faruk ni zan iya bada sheda akanshi" yanzun nan fa muna tafiya hanya ya tsaya yadauki wata budurwa haryana cewa wai nafita na koma baya, kuma wlh bazan kara zama agaban motan ba tunda karuwar sa ta zauna agurin" ke humaira ana baki kina roko, yazun haka ma gwada ki yayi yagani ko zakiji haushi" wlh yasan ta sai kallon tafa yake " suna cikin haka faruk ya kira humaira tazo su tafi, ta tashi ,tadan sake fuskarta kadan ta fito ,da alama faruk yaba nura lbr dan taga suna mata wani irin kallo, nura ya rakosu har gaban motar bayan faruk ya shiga ya zauna , humaira ta fito, nura ne ya zagayo ya bude gaban motar , ranki ya dade . tsayawa tayi cak taki shiga, zoki shiga mana" yaya ni bana so abaya zan zauna" haba humaira ya zaki bar mijinki agaba ke kuma ki koma baya" yaya katam bayeshi dazun ina zaune ya tasheni yasa buduwar shi, faruk ya juwo da sauri yace ninace miki budurwa tace? karka sake yimin magana ni ba ruwana dakai " nura ya matsa kusa da ita yace humaira tsokanan ki yakeyi fa bawani alaka a tsakanin su , karki bari yagane lagwanki , kar ki kara nunamai kinji haushi tsokan ki kwai yakeyi" faruk yace nura rabu da ita tazo ta shiga bayan.
har suka isa gida ba mai cewa kowa komai suna tsayawa ta fito da sauri tayi cikin gida samira tagani tsaye ashe tana ganinsu tunda suka tsaya , da isarta kusa da ita ta kwashe da dariya harda shewa shishigi babu kwarjini ,tir dai ba aji dadin hali ba" humaira ta juya tana neman abin duka idon ta bai nuna mata ba saita cire takalminta ta jefawa samira daidai lokacin faruk ya shigo ya hango abinda yake faruwa, samira kuwa dafe kirjinta tayi tana fadi humaira lfyn ki kuwa me nayi miki? humaira tasake cire dayan takalmin zata kara jefa mata faruk ya taho da sauri yarike ta , ya karbi da kalmin, ranshi ya baci sosai Dan haka ya rufeta da fada haryayi ya gama bata ce da shi komai ba ila hawaye da yake fita a fuskar ta, samira ko ta natsu kamar mutuniyar kirka, faruk yabata hakuri humaira naganin yana bata hakuri tayi ciki tana kuka bagare ta tashiga taci gaba da kukanta , samira taji dadi ta tsokane ni amman ta dake kamar ba itaba yanzun kona fada ba yadda za,ayiba burinta ya cika yanzun momy laifina zatagani,
shiko faruk daki momy ya shiga yagaya mata abinda ke faruwa, momy kidaina shagwaba yariyar nan duk abinda tayi bakiyi mata fada gashinan abin yana dada gaba yanzun daga shigowan ta kawai tafara kaimata duka , yariyar nan ko anya ba mahaukaciya bace kuwa, yanzun jiya fa daga muna magana ta cije ni, gaskiya aje a dubata" momy dake sauraran shi tace lfyr ta lau babu abinda yake damun ta, aini na zauna da ita nasan wasu daga cikin halayeta, tanada zafin zuciya ne, kuma ita da samira kwai abinda yake hada su, ba haka kawai bane , kaima inzaka fadi gaskiya haka nandai bazata kama ma hannuka ta ciza ba samira ko sundade basa magana sai sama sama kaga akwai abinda ya hada su, yanzu abinda nakeso dakai kaje ka lallabeta tagaya maka me yake faruwa tsakanin su kuma hargagi zaka mata ba kabita a hankali" momy to ki kira samira ki bata hakuri, a,a bazan kira taba , ai dukkansu susan ina cikin gidan amman da matsala ya shiga tsakanin su basu neme ni ba, kila basa san na sani ne, in mijita ya dawo ka gaya mai ya tambaye matar sa
Lokacin da faruk ya shiga dakin ya sami humaira kwance tayi shiru, ya zauna bakin gadon, humaira tashi muyi magana mana, tayi mamaki dan tazaci da fada zaizo mata, dan haka ta tashi ta zauna, yace ki gayamin gaskiya meye ya hadaki da samira , wane sabon kukane ya sake taso mata, ba ita bace take cemin wai Baka sona Ina manne maka, taita gaya min bakaken maganganu , yanzon kuma da shigowa na tafara min dariya" bata gama magana ba , yace ya isa haka daina kuka ita waye yace mata bana soki karya takeyi" da gaske ne ai ba sona kakeyi ba" ran faruk ya baci jiyake kamar yaje ya rufe samira da duka, ya matsa ya rungume ta yafara fadin , tunda kike kintaba jin na bude baki nace bana sonki ? Amman aika nuna alama kowa yasani" humaira basu fahimcini bane amman ni inasoki kuma zannuna ma samira irin sayayyar da nake miki
07014197559
[6:35PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞
39 to 42
✍MMN YAZEED
Ba wani ni kasakeni ba yanzun nan kamin wulakanci akan budurwa ka ba zakazo kace wani wai kana sona .
Ke ,yarinyar nan fa ba budurwa ta bace kanwar wani aboki na ce ,ki kwantar da hankalin ki, bani da wata budurwa , kuma kome samira zata ce miki karki kara kulata ki barni da ita. to naji amman nina gaji da zama agidan nan dan Allah ka kaini katsina in zaka tafi. aina riga nafada miki saikin sake jikin ki dani zan kaiki. aina saki ba gashi muna magana ba. a,a ba irin wannan ba, hakkina zaki irinka bani, ko bikisan hukunci matar da take gudun mijinta bane "nifa ban iyaba bane danni ba yar iska bace. humaira ji nan, kinason kice baki san hakin miji akan matar sa bane? humaira tagane nufinshi sarai amman saitace , to innasani ai ban iyaba. Ran faruk ya fara baci, ke komai akace miki kice baki iya ba, wannan wani irin aure ne, nina gaji wlh inbaki bariba zan kaiki kara gun abba. me zaka cemai ? faruk ya kara kulewa yace ina runki .
Haka abubuwa suka cigaba da faruwa faruk yayi iya kokarin shi ya shawo kan humaira amman duk ta inda ya bullo mata sai ta zille gashi har sun cika she kara daya da aure amman ba wani lbr dan haka ya fara tunanin kodai ya neme aure ne kon dan yasauke laluran shi dan gaskiya yagaji da zama haka zuwan faruk katsina biyu humaira bata saniba saidai inyadawo yace suna gaisheta hakan besa humaira ta bashi abinda yake soba faruk yakasa hakuri dan haka ya yanke shawaran yasame abba ya gaya mai ammafa yanajin kuyar abba gara gara momy dan haka ya tashi ya nufi dakin , yashiga bega kowaba a dakin ba yana kokarin juya momy ta shigo . dama ina neman ka. Lfy ? malam ne bejin dadi kaje ka gaida shi .
Yace toh ko zai gan gara ne.
ubanka ne zai gan gara.
faruk ya yayi dariya , yace kai momy. Ka daiyi kokari kaje dan naga yanzun baka son zumuci yaushe rabonka da zuwa gidan hadiza har tayi magana ta gaji . zanje ne momy bari komai ya daidaita , momy inason muyi magana ne. to inajinka me ya faru ? Momy humaira ce sai kun mata fada , yafara yan soshe soshe , momy ta lura yanajin kunya dan haka tamike tafara kokarin gyara gadonta, tana fadi me tayi ? taki yadda dani , faruk yaji momy tayi shiro kamar bazatayi magana ba , sai can tace , kai amman humaira ta birgeni , faruk ya dago kai da sauri ya kalli momy yace momy kinji abinda nace kuwa? najika sarai, ai tayi daidai maganin ka kenan wani irin wula kanci ne baka mata ba, sai yanzon ne zaka ce taki yadda da kai, ita daba sonta kake ba aisai ka rabu da ita.
Momy wai ni nace muku bana sonta na taba bude bakina nace bana sonta. saunawa kuma ba anan ka zauna kake cemin duk yariyar da aka aura maka zata gane kuranta ba, har kuka kake da hawayen ka za a haka da kaska, ko duk ka manta. yace kidaina tada wannan zancen yariga ya wuce kuma ai lokacin ban sata bane, amman ni tunda naganta naji ina sonta.
to ai irin abinda ake gaya muku Keenan, yanzun kaje ka lallabeta ba me sa muku baki agidan nan.
haba momy, ya zakice haka dan Allah ki mata fada mana nifa gaskiya nagaji. momy tace yau naga ikon Allah , to yanzo ya kakeson ayi ? kiyi mata fada ko kuma ki gayawa abba yayi mata fada. tace nikam bazan fada ba kai baka da baki ne.
faruk ya mike ran shi abace yabar dakin .
yana shiga ya same humaira tana waya , ya sami guri kusa da ita ya zauna da alama da maman ta take waya , bayan ta kare wayar tace yaya faruk dan Allah ka kaini gida ta fara kuka .
me yafaru agida? nidai inason zuwa ne kawai. humaira ai kece baki shirya zuwa gidaba in kin amece da abinda nagaya miki ko yau kike so zan kaiki. tayi shiru tana tunani bari na mai wayo. tace na amince amman sai ka kaini mundawo tukuna.
a, a ni ban amince ba , ni zakiyi ma wayo . wlh ba wayo nake maka ba, kai katon ka dakai saina ma wayo. Eh shiyasa nace ban yarda ba ai. Yajuya zai fita yace inkin shirya zuwa gida ki min magana.
daga nan waje nura ya nufa, bayan yadauki nura a mota suna tafiya zasu gaida malam . nura yace yadai mutumina ya naganka wani iri. faruk yace kasan me nene ? sai ka fada .
faruk yace na rasa yadda zanyi na shawo kan humaira, ta amince dani.
nura ya kwashe da dariya sosai har yana rike ciki , yace amma fa gaskiya naji dadi, kace ka kamo. hmm ai na dade da kamuwa kawai dai ina sharewa ne , hakurina ya fara karewa ji nake kamar na karbi hakkina kota karfin tsiya ne,amma saina kasa, yanzon ya kake ganin za, ayi ne. nura yayi shiru sai can yace ai lokaci be kureba ni tuntuni nagane kana sonta kawai dai kana fada ne , amman shawo kanta ai ba wahala zaiyi ba.
nidai yayi min wuya wlh , itakuma momy da nake ganin zata mata fada tace baruwan ta. nura yace gaya mata kayi. to yazanyi inban fada mataba, dahaka suka isa gidan malam Inna suka tarar atsakar gida tana shara,nura yace Inna bazaki zo ki tarye mu bane . aini banayin auren azo abani takarda ta . faruk yace Inna aibasaki mutu ka raba . inna tace tafi can wawa amma gata kaikana fushi, yariyan zukekiya da ita sankowa kin wada ya rasa. wani munafukin yace miki ina fushi . ni ina nan lbr yazomin aikayi ne.
to duk ma wadda ya gaya miki karya yakeyi , kuma kija bakinki ki tsuke karki bari humaira taji. Inna taiyi shewa tace ashema tsoronta kakeji.
Suje gurin malam sun same shi yaji sauki yana zaune yana cin abinci faruk na shiga yaji ya saka hanu ya fara cin abincin malam yace au dama da yuwarka kake tafe, faruk yace naji ance baka da lfy nace ko gangarawa zakayi ne. malam yayi dariya yace, ai mutuwa ta Allah ce faruk amman inason naga danka . faruk yaji dadin maganar malam dan haka yace karka damu malam zaka gansu insha Allahu.
bayan sunbaro gidan saida nura yakai faruk har gida ya juwa zaitafi faruk yace kace zaka gaya min wani abu, nura yace zokaji abin sirrine matso , faruk ya mata dafda shi yamai rada akunne , faruk yajuya yana dariya bayan dare yayi faruk yayi shirin kwanciya ya nufi daki humaira yasame ta tayi shirin bacci da kayan baccinta masu kyan gaske saida ya tsaya ya kare mata kallo humaira ko taji ajikinta ana kallonta dan haka tamike da sauri, tace to menene ka shigo min daki da daddaren nan . me kike tunanin ya kawoni. Oho
To ni bawani abu bane ya kawoni nazone ne nafada miki kishirya gobe da safe zamuje katsina .murna takama humaira ta dauko akwati tafara diban kaya tana fadin kala nawa zan dauka yaya.
Yace kwana nawa zakiyi tace sati daya yace to