Zaki Gane Kurenki Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   3 / 14

6K to 9K   out of 40.3K words

yace zamuyi dama yanzun can zan kaishi, to kayan da zaisa fah kun tanaza ne ? nurane yasake magana, nasa wani zaikawo anjema.
yace kushirya da wuri ,alhj yaji dadin yadda nura yakeyi yawuce yana fadi Allah yayi muku albarka. tuni kayan amarya suka iso da yan uwanta guda uku bayan sugama gyara dakin suka koma katsina.

Tofah rana bata karya yaune za,a daura auren faruk tunsafe suka fara shirye sheyen tafiya daura aure gidan duk ya hargitsi faruk ne ya fito ko wanka beyi ba yatarar da yaya sulaiman a falo yasha manyan kaya yace yaya harka zo ? kai mekakeyi baka shirya ba, har yanzo kana kan bakan ka kenan, kaidaiyi ahankali kar wata rana muga kana yar murya. yace habadai Allah ya kauta yar tatsitsiyar yariyar zanwa haka.yaya yasake cewa kataba kiranta kowa? a,a nakirata nace mata me, niban kirata ba. yace lallai faruk nan gaba akwai aiki wlh kare cika baki, yanzu jeka shirya .
bayan faruk yayi wanka yadauko wani yadi daga cikin kayan shi zaisa kenan saiga nura da Ismail abokin faruk suna shigowa suka fara tsokanan faruk nura ne yace cire wannan kayan gawanda zaka sa nan yamika mai leda hunnushi yakarba ya futo da kayan yadine me kyaun gaske fari tas da hula da takalmi da agogo aciki. faruk ya kalli nura yace kaidai wlh dan wahala ne, kanata kashe kudin ka abanza. yace nidai ko me zakace kace,amman kai sauri kasa kayan. bayan yasa kayan ne suka fito, da fitowan shi yan,uwa suka hau fadi kaika kaga angon har wani haske ya kara lallai angoci yayi. yace bawani angoci dama da haskena. lokacin duk su alhj suntafi su faruk ne kawai da abokan sa. ya leka dakin momy nanma cike yake da mutane bayan ya gaida su ne ya tsaya abakin kofan yayi shiro can ya dago yace momy zamu tafi. itama tadanyi shiru na wani lokaci sannan tace haka zaka tafi daura auran a murtuke fuska ba fara,a to dan Allah inaneman alfarma kasake ranka bece kome yasake cewa na tafi. momy ma kasa cewa komi tayi amma tamai andua azuciyar ta sai yan dakin ne sukace Allah ya tsare yakuma sa adaura asa,a bece komi ba ya fita. bayan sun futo harabar gidan ya tarar da friends dinshi da yawa awaje harda yan office dinsu, mutoci kuwa ba,a magana wannan na wane waccen yana futowan suka hau yimai shakiyan ci irin nasu na abokai. shedai faruk ba baka saikunne sun isa katsina lfy inda nanma sun tarar da mutane makil, nan da nan muroka sukayo kansu sunata kirari wani abokin faruk ne ya nuna musu ango suko isa gareshi, faruk dabesan hayaniya yabude aljihu yanata basu kudi duk dandai su barshi ya huta nandai dubban mutane suka shaida auran faruk yusuf faruk matawalle, da amaryarsa aisha humaira nasir. faruk yatuna maganar momy dan haka yafara ya'ke. mutane sunmai ca kowa kokari yake sugaisa anata mai Allah yasanya alheri yana ameen ameen nura ne yalli faruk yaga yasake yanata fara,a ya matsa kusa dashi yamika mai hannu yace inatayaka murna, faruk yace zaka fara ko. bayan muta ne sufara wucewa ne saiga aminu yana tahowa wurinsu yace baba yace kuzo ku gaisar da baki nan suka kama haya da wasu daga cikin abokansa bayan sun gaisar da sune suka fito . su alhj ma sunfuto da tawargar su sun tafi, wasu da cikin abokan faruk ma suntafi sauran kowa sunajira afuto musu da amarya nura ne yaga shirun yayi yawa yace bari dai nashiga naga mesuke jira ne har yanzo. faruk yace nifa nagaji zan wuce . nura yace ina zuwa yasakai ciki , ya cidda su mama hadiza zaune afalon yace wai ina amaryan ne yamma fa nayi saiga wata dadtijuwa ta fito da wata kyakyawan yarinya tasha ado da zanan fulawa ahanu da kafafuwan ta mama hadizya tamike ta mikawa yarinyar hannu takama tana kuka me tsuma zuciya nura yace amarya tamuce kai masha allahu yadafa azuciyar shi bayan sudauki amarya da yan uwata suka kama hanya, a mota nura yace ma faruk ba kaga yarinyar ba wlh ta hadu tanada kyau sosai . yace to ni meya dameni da kyanta, kaima inaruwan ka da ita zakazu kana cemin wani tana da kyau kaje ka kare ma yariyar mutane kallo nura ya kwashe da dariya yace kace dai nakare ma matarka kallo. yace niba haka nace ba
motar amarya ita tafara isowa baayan anshiga da amarya dakin momy. momy taga yariya nata kuka fuskarta arufe tace taso kizo nan humaira. humauira tamike taje gaban momy ta tsuguna , momy ce ta jawo ta jikita tace kidaina kuka nan ma gidan kune ki kwatar da hakalinki, bude fuskarki kisha iska, tasa hannu da kanta taja mata gyalen.
bayan sauran mutocin sun karaso ne suka. dauki amarya akakaita dakinta gaskiya anshirya daki ,nera tayi kuku .
washe gari yan rakiyan amarya nata shirye shiyen komawa amma yan uwan hjy fatima sunason ganin faruk
kafin suwoce, dan haka suka je dakin. momy suka suna son ganin furuk, momy ta daga waya takira shi, yace gashi nan zuwa sunan zaune sunata dan hirarsu, saiga furuk ya shigo, momy tace zoka zauna .tamike ta fita , bayan sungaisa daya daga cikin matan tace dama humaira ce dan Allah gatanan amana kaiyi hakuri da ita yarinya ce karama bata da wayo sai anyi hakuri da ita. yace bakomai dayar tace muma mugama shiryawa. yace to dama yanzun motocin zasu karaso .
haka suka dinga dauko jakarsu da daya baya daya suta fita batare da sani humaira ba , can humaira taji tashin motoci ta leko ta window taga wasu mutocin har sun wuce, tasaka kara tafito da gudu dankwali ahannu da gudu ta sakko faruk da abokan sa suna tsaye bakin motar data rage su momy ma suna gefe sunrako baki saiganita kawai sukayi ta fito aguje tarike motar . samira ce tafara kokari riketa amma ta kasa nura ne yace ma faruk kaje ka kamata mana. yace caf ninema zan kamata. dakyar suka samu suka maidata ciki tana kuka maiban tausayi momy ma kuka take tausayin yarinyar ya kamata dan haka ta turamata meena ta tayata hira
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞

11 to 13

✍MMN YAZEED

Bayan faruk ya baro gidan kakanin shi yana kan haryar sa tazuwa gida, yaji kira daga alhj ahmad. yayi kamar karya dauka saida, takusa katsewa ya dauka.
tare da sallama. alhj ne yace kana inane? yace ina hanya zanje gida. gashi kuma, inason ganinka? faruk yayi shiru na dan wani lokaci, yace ganinan zuwa. bayan sunkare wayan faruk yayi zurfi atunani, waisu wadan,nan ina suke son nasa kaina ne, kullum magana daya ko gajiya basayi, ni wlh nagaji da maganar nan, nifa inhar suka takura min, kararsu zankai gun malam.
dawan nan tunani ya isa gidan, kofar dakin nura ya buga . nura ne yace waye ?
gafara malam zoka bude min. ai nura najin muryar faruk da sauri ya taso dan ya dauka maganar yazo yamai, yana budewa yafara fadin ango kasha kamshi.
bafa nason irin wannan wasan. bayan yashiga ya zauna ,yace ina madam ?tana cikin gida, lfy? yace ruwa zata kawo min . bari na kawo ma mana bayan suyi hira sama sama nura ya fahimci faruk besan dawan garin ba, dan haka yaja bakin shi ya tsuke. faruk ne yace zomu je ka rakani gun baba . a,a nikam bazani ba ai wan,nan ganawar takuce, bani cikinta. faruk yasake cewa zomuje kana kara batamin lokaci fa. nifah wlh baxanje ba, zanjira ka awaje, ko murfen mota ne na bude maka,inkuma abin ya gagara nakaika gida.
faruk be gane me nura yake nufiba, yace saikace wani mara lfy, banaso je ka kwata kawai wawa da kai .
nura yace kadai bini ahankali, in bahaka kuwa zaka gane kuranka.faruk yayi tsaki ya shiga cikin gidan .ya tarer da alhj yana tattara takardu, bayan sungaisa alhj yafara jan faruk da hira, tun faruk na dari dari harya sake jikinshi sonata hira can alhj ya dauko ledan dake gefenshi ya mikawa faruk ,yasa hannu buyu ya karba. yace gashinan ko kana da wanda zakaba alewan sa ranar kace.
gaban faruk ya fadi nandanan gumi ya fara fesu mishi, yace ansa ranar ne? eh rana itayau ne.
yace baba gaskiya yayi kusa da yawa,aiban shirya ba, kuma bani da wajen da zan zauna.
alhj yace baka gama gininka na abuja ba? a ,a ban karasa ba.
yace to karka damu dama koka karasa ma ba acen zaka zauna ba, za abaka wanjen zama .faruk dai ya sunkuyar dakai idon,nan jawur bashi da sauran dama, duk ta inda ya bulowa alhj sai ya kauce , ya zauna yakasa tashi .hjy ce taga shirun yayi yawa. tace kaci abinci kuwa ? banajin yunwa ya fada kansa akasa. tace waikai lfyr ka kuwa, kaifa namiji ne ,ba macce ba, to kai kanayin haka mace kuma tayi yaya. alhj yace rabuda shi, tashi kabani waje. yamike ba magana yayi dakin momy tana ganin shi gabanta ya fadi fuskar nan ba rahama ,ya zauna ,meena na zaune agefi tana danna waya yace momy dama nazo na miki magana dan Allah ki roki su baba adan kara lokaci, lokaci nan yayi kadan kuma duk agidan nan wa,akayima irin wannan auren, saini za acemawa wai wani sati daya . dakata ,suda suka gaya maka meyasa baka gaya musu haka ba, koko nice marainiyar wayonka, to wlh bari nafada maka karka kaskura ka kara tarana da irin wannan maganan kuma auren nan kama daina tunanin za a daga shi, mumungama shiryawa gobe anty ku zata hadu akwati. . yace aiko wlh duk yarinyar da aka hadani da ita zata gane kuranta. momy takalle faruk, nikake gawa haka. faruk ya dukar dakai ga dukkan alamu subutar baki yayi momy ce tace ai dama alhj ya karanci bakin halinka, shiyasa yace agyara sama ka zauna.
au asama ma zan zauna, gaskiya ana cutar dani saiga hawaye yana zuba a idon faruk. momy ta lura, tace ma meena dake gefe zokifita, meena ta wuce falo. tace dashi wai kuka kake ne ? yayi shiru kawai yana share hawaye. momy tace amma wlh kaji kunya kayi asara namiji nefa kai ba mace ba , ni wlh har yariyan ma tabam tausayi, me shekara talatin da wani abu, yana kuka ita kuma me goma sha, tayi yaya. yace ba kuka nakeyi ba fah. kadaiji kunya wlh. yamike zaifita sukaci karo da meena zata shigo tadan bigeshi kadan yakai mata duka tayi bayan momy tana kuka, tazaci zaibiyu ta saitaga ya wuce. lokacin da faruk ya shiga dakinshi karfe goma shadaya saura ya hau gado ya kwata yana tunani kalakala azuciyar shi.

washe gari ya kama Sunday dan haka faruk bai fito da wuriba sai karfe tara da rabi lokaci yashiga bankare mahaifin shi domin gaida shi yacidda dakin rufe ya tabbatar ya fita, yace azuciyar shi ina abba yaje dasafe bayan yau babu aiki, ya nufi dakin momy yana dosan dakin ya fara jiwo hayaniyar muta ne adakin ya shiga tare da sallama ,nura yagani zaune da kati agaban shi daga gefe kuwa mama hadiza ce kanwar momy sai anty amarya da samira matar aminu. nura ne yace yanzun nake shirin karasowa. faruk yace mezaka min ? bakomai nazo miyi shawara ne . nikuma na rasa wadda Zanyi shawara dashi saida munafuki . mama hadiza tace faruk wai baka ganni bane ? faruk yace naganki mana, bakiji inata kawo gaisuwa bane.
tace karya kake ko nima fushin ya shafeni ne.
yace waye yace miki inafushi niba fushi nakeyi ba. tace to ai shikenan .yace mama akwai lbr fah. tace to faruk aini inanan har ayi baki. yace lallai abinnaku nayine. nan mama hadiza da anty amarya suka mike suka fita momy nace musu kodin zai isa kuwa . sukace inba bai isaba zanyi waya saiki turo meena. faruk yamike nifa wucewa yanyi . nura yace inazaka bayan yau Sunday? yace gidan malam zani .
nura yayi murmushi yace dama kabar wani kame kamen kafafuwa agidan fah aka raba alewar sunsan komai furuk yace kana nufin malam yasan za ayimin auren dole ? yace susani mana kaini nakaisu fah kai sadakin, amma basu gaya min ma idazamu ba, haka sukai ta bari na a mota kamar maigadi, saida muka shiga gidan malam naji inna anrangala buda sai wani murna take . faruk yace har inacewa zanje gunta ashe ita ta kitsa musu, yasake cewa har ina kukaje neman aure ne.
nura ya kwashe lbrn ya fada masa. faruk jikinshi yayi sayi dayaji cewa yarinyar alhj nasuru ce, yasan ma kamar anyi angama ne momy tanajin hirarsu batace komai ba.
faruk ne yace amman wlh inna zata gane kurenta bazan kara zuwa gidan ba. momy tasako baki karka kara zuwa mana saime .suka futo nura yace zo muduba masu aikin sama mana, bayan sun hau sama nura yace ka musu bayani yadda kake son ayi. yace koma yaya ne suyi kawai. .sai nura ne ya nuna musu yadda zasuyi.
bayan sun koma dakin faruk nura yamika mai katin, yaki karba, yace kaje karaba kawai nime zanyi da shi. yace to naji zanraba, amman dan Allah ka rage nuna kiyayyan ka akann auren nan ya kamata kamusu biyayya kagafa sunyi iya bakin kokarin su ka kawo mata kaki, to inbahaka ba ya kakeson sumaka, yadauko wata yartakarda a aljihusa ya mika mai wannan number tane kakirata sunanta HUMAIRA

Wacece humaira
humaira yariya ce kyakya sonkowa farace tas matsakaiciya ce itaba ba duguwa ba itanaba hajeriya ba , batada kauri sosai saii uban gashi hargado baya, bagaren halaye kuwa tana da ladabi da biyayya ga nagaba da ita, saidai inkatabo ta bata da kuya ga shagwaban tsiya da surutu , lokacin da tasami labari za, amata aure tayi kuka kamar ranta zaifita acikin kwana biyu duk tafita haiyacinta, hjy rabi kowa ansame abinda akeso dama babban farin cikinta taga fatima da iyalanta cikin bakin ciki inbanda shewa ba ,abinda take, itako hajiya fatima tana ta shirye shiryen auren yarta take ,amma fukarta babu walwala dan tausayin yarta da take ji
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKK💞💞

15 to 17

✍MMN YAZEED


Meena nata jan humaira da hira harta dan sake jikinta da ita, har dare meena na dakin har sukayi sallah sukaci abinci tare , bayan sunkare saiga anty amarya ta shigo, tace sunnuku kuta hira, tawoce toilet din dake cikin dakin , bayan wani lokaci tafito tace, humaira tashi kije kiyi wanka, tamike tacere kayan jikinta ta daura towel tashige toilet, anty amarya tabude akwatin humaira taciro wani yadi maikyau ta aje agefen gadon, tace da meena inta fito tasa wadan kayan, tajuya ta fita.
meena tana dan latsa wayarta saiga humaira tafito, bayan tagama shafan ne meena tadauki kayan ta bata tasaka, meena tace kai Anty kinga yadda kikai kyau kuwa. humaira tayi murmushi tace nagode. meena ce tasake cewa bari na tashi natafi karsu yaya su sameni. ta waigo ta kalli meena tace ina zaki kuma ba anan zamu kwana ba. a,a ba anan zan kwana ba amman gobe da sassafe zan shigo. tace wlh indai zaki tafi nima binki Zanyi. meena ce tamike tace to bari naje nadawo. to kiyi sauri karki dade.
meena nafita tayi dakin momy tagaya mata abinda humaira tace. momy tayi shiru tace gashi mijinta ba hankali gareshi ba bare yalallashe ta.suna cikin haka saiga faruk da abokan shi sun shigo nura ne agaba duk suka tsuguna furuk na gefe ya dukar da kai kasa nura ne yace momy munkawo miki ango ne kiyi mashi fada. tace nime zance mai aida gun hajiya kuka kaishi Allah dai yasa su zauna lfy kuma yaji tsoran Allah. daganan kuma sun kaishi hargun alhj shimdai fadan da yayi mishi kenan yaji tsoran Allah.

lokacin da suka shigo bacci yafara daukan humaira haniyar sune ya farkar da ita tadau gyalanta tarufa. sun shigo harciki suka zauna suta shakiyancin su , ita dai humaira ba fahimatan su takeyi ba ita bata masan waye mijin ba kuma badamu tasan shi ba. haka suka gama surutun su suka fita gaba dayan su. tana ganin sun fita tamike tayi daki momy, tatura kofar ta shiga bataga momy ba, sai meena dake bacci akan gado, danha tadau filo takwata akasa momy kuwa tana dakin alhj dan
yau itake da girki shikuwa faruk da yadawa daga raka abokan shi yarufe kofar falon su bekoma dakin humaira ba ya nufi dayan dakin yayi kwanci yarshi.

da subahi bayan alhj yatafi massala ci , momy ta nufi dakinta tatura kofar sai kawai taga yarinya kwace akasa tai salati ta sanar da uban gije ta matsa kusa da ita ta tashe ta, tashi kiyi sallah ta matsa ta tashi meena itama taji mamakin ganin humaira adakin. bayan alhaji yadawo daga sallah momy ta koma tagayawa alhj abinda ta gani.alhj yaji mamaki, yace turo min ita bayan tazo tagaida alhj yace matso nan ,yata taje kusa da shi ta zauna, yace faruk koroki yayine ? tace a,a nidaice nafito. yasan kinfito ? a,a ai lokacin sunfita . alhj ya girgiza kai yace ikon Allah kuruci dangin hauka
momy ce tace bari nakira shi . yace karki kirashi barni da shi kawai.
faruk ko tudda yadawo sallah yashige dakin shi yana sharar baccin shi saida gari ya waye yatashi yayi wanka yafito ko kallon dakin beyi ba yafice be nufi dakin momy ba falon alhj yanufa , yatar da alhj ya kishingida ya zauna yace abba ina kwana. fly lau yace dashi ya iyali .
faruk ya durkusar da kai yace lfy lau . ya baku fito tare ba jeka kirata . faruk yamike yafita, yayi sallama adakin yaji shiru yasa kai dakin bega Kowa ba, ya bude toilet bakowa , be tsora taba saida yaduba dakin momy beganta ba.
momy ce tace lfy kashigo bako sallama kana mana dube dube . yace yariryar nanne abba yana kiran ta. wace yarinya mu bamuga wata yariya ba

3 / 14