Zaki Gane Kurenki Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Romance

Chapter   10 / 14

27K to 30K   out of 40.3K words

ki daga mai hankali.
tace to bashi bane yaki dawowa.
ba asan ranshi bane humaira shima fa ya kosa ya dawo.
humaira tace yauwa dama inason na tambaye ka .
nura yace ina jinki.
tace dama budurwar yaya faruk a gidan malam take?
nura yasa dariya , meena tace duk ma wadda ya gaya miki karya yake gidan Inna ba wata budurwa.
tace ke yayane fa ya gayamin da kansa.
nura yace ke meena waye ya gaya miki babu budurwa, akwai budurwa agidan mana zarka dediya, ita faruk yake nema .
meena tace to shikenan ki tsaya su yita shigar da ke.
humaira tace wlh yaya nura sai naje har gidan nasame ta.
nura yayi dariya yace gaskiya da kin birge ni , ni inzaki ma zan rakaki , dama haushi take bani.
meena ko haushi yasata ta mike tashige dakin momy.
nura yaji dadin tashin meena, yace humaira dama ina son muyi wata magana dake .
tace ni kuma ?
yace eh, humaira nifa son meena nake, dan haka nayi kamun kafa dake, nataba yima faruk magana da dadewa yace wai zanja ta raina shi, nakasa hakura ne , ki taimake ni kishgar dani agun meena tunda naga kawar kice.
humaira ta gama kallo nura da mamaki a idonta tace anty bilkisu zakawa kishiya da meena.
to me nene Humaira?
mikewa tayi , yaya gsky meena bazata aure kaba, yaya za,ayi kama anty kishiya ai wlh bazai yuwo ba .
shigewa gefanta tayi tabar nura zaune afalo.


nura na zaune jikin shi asan yaye, yamike ya shiga dakin momy, ya gaisar da momy, meena tace yaya nura ka gama zura anty humairan ne?
nura yayi dariya yace faruk ne ya zurata bani ba.
meena tace momy wai yaya faruk ne yace mata yana da buduwa agidan malam.
momy tayi dariya tace me sunan malam bashi da kunya wlh inna fa yake nufi .

humaira ko tunda ta shiga daki tunanin take dole tadau mataki shiryawa zatayi taje gidan inna tame yariyar da faruk ya nema tayi maganin ta.

washe gare da safe faruk na taye ya gama shiryawa damin yau zai dawo gida kuma be gayawa kowa ba dan yana son yama humaira dirar bazata.
Itako humaira ta shirya tsaf dan tafiya gidan Inna bata tambayi faruk ba dan tasan kota tambaye shi ba bari zai yiba , sai dai tai tunanin bari ta Kira shi ta tambaye shi sunan yariyar, lokaci da ta takira shi yana mota yaci rabin tafiya yaji kiran humaira da sauri ya yadaga, bayan ta gaida shi tace yaya yasunan budurwar ka, ta gidan inna?
sai da yayi dariya sannan ya ce sunanta zee baby .
da sauri ta kashe wayar tafito.
dakin momy ta shiga tace momy zanje gidan inna .
wani irin gidan inna kuma kibari mijin ki ya dawo mana.
momy nafa tambaye shi yace naje.
ayho to saikin dawo tajuya ta tafi.

✍07014197556
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞


72 to 74

✍FADEELA LAMIDO
MMN YAZEED


Humaira ta isa gidan Inna tana ta haki saboda yanzun koya ta danyi tafiya sai taji haki na taso mata.

Inna tace ke kuma daga ina .
humaira tace Inna bakiyi murna ganina bane ?
ko kadan ni tausaya miki nakeyi, ga ciki gashi ke abu ba au ki ba. ,
inna kenan ina dan tsohon mijinki .
Inna tace ahaka kuma kuka manne mai.
Allah ya kiyaye me zamuci da shi.
Inna ta sake cewa ina kawarki yau baku taho tare ba? ai bata ma san zan taho ba .
to me zakici na dafa miki dan ni inada duma me.
a ,a nima zubu min dumame zanci.
Inna ta tashi tazubu mata tuwo , ta bata yaji da man shanu.
humaira tana cin tuwo tana raba ido ko za taga zee baby ta wuce , harta gama cin tuwon bata ga kowa ba .
dan haka tace inna ina zee baby ko batanan ne.
inna tace wacece kuma haka, nifa wannan iyayin naku ba gane shi nakeyi ba.
tace kai inna sai kace yar kauye, to zainab
auke kema iya shegen da mijinki yake yimin kika zo kiyi min.
wlh inna ba haka bane daga tambaya, yaya faruk ne yace in nazo nace miki ki nuna min zee baby.
tace to gani nice zainabu.
a,a wannan fa yace min budurwar shice. tace to aini ce budurwar tashi, yanzu nan da gaske ke kinzo gani budurwa faruk dinne, ta kwashe da dariya, ta mike taje kusa da malam tana gaya mai, shima dariya yayi sosai.

Sai yanzun maganar meena tazo mata Ashe gaskiyar meena ne, bayan sun gama hira Inna tace kinga bari naje na miki dan wake kitafi da shi, ko yanzun baki son dan waken.
Inaso mana amman fa kiyi sauri.

shikuwa faruk humaira ta fita bada da dewaba ya dawo, ya shiga gidan da karfin shi burin shi kawai ya rungumi humaira danki momy yadosa dan yasan da wuya in bata cen.
momy ganishi kawai tayi ya shi tare da sallama.
tace menene haka kuma ai ya kamata in zaka dawo ka rinka bugo waya sai dai kawai mu ganka ka shigo.
yace momy saika ce wani bako inzan dawo saina sanar.
ya mike Ina zuwa a kawo min abinci yunwa nake ji .
tace to zo ka dauka yanzun indai bani zan kawo maka ba , meena ma bata nan.
Yace humaira fah?
ai bata dawo ba .
faruk dawowa yayi ya tsaya ya zaro ido, daga inna momy?

ba tace kace taje gidan Inna ba .
ni ? Ko dazun fa muyi waya da ita, bata cemin ta fita ba, momy ni gaskiya bazan dauke irin wannan ba, wannan ai raini ne, bari naje gidan na same ta wlh sai ranta ya baci.

momy tace karka fita kabari ta kusa dawowa, zakaje ka tara musu mutane ne agidan.
momy dan Allah wannan wani irin abu ne kilama ba yau ta fara ba.
Injiwa yace maka bayau ta fara ba , bana son irin magan ganunn nanfan, waya ta daga tace da aminu yaje gidan inna ya dauko humaira yanzun nan ya kawo ta gida.
momy ta tashi da sauri taje da kanta ta kawo mishi abinci.
yace momy dama kinbar shi kawai banajin yunwa.
tace ai kai kaga matsalan ka kenan kabi ahankili mana.

humaira na zaune aminu ya shigo yace fito mutafi sauri nake wlh.
humaira tace yauwa da yanzun sai naji titi zan samu mota.

suna shigowa harabarar gidan taga motar faruk, tace na shiga uku yaya yadawo ne?
Yace yadawo kenan nima banda lbr.

dakin
momy ta shiga momy nagani ta shigo ta rufe ta da fada, ashe baki da hankali har ni na tam baye ki kice min shine yace kije, dan tsabar rashin mutunci.
gani yadda momy taketa fada yasa hankalin humaira yatashi zubewa tayi akasa tana fadin momy dan Allah kiyafe min bazan kuma ba, wlh nasan inna tambaye shi bazai bariba shiyasa nayi haka, kuma wlh nayi niyar innadawo na fada mai.

momy tace je ki bashi hakuri, kaikuma kayi hakuri nasan tayi maka laifi amman kayi hakuri, banda zafin zuciya, ta mike tabar musu dakin.

Faruk yaji zuciyar shi ta mai sanyi saboda fadan da yaga momy tayi mata, bata goyi bayanta ba kamar yadda ta saba.


Humaira zuwa tayi gaban shi ta tsuguna tace yaya dan Allah kayi hakuri bazan karaba, kaji?
ban za yayi da ita tai ta magana taji yayi shiru, takara matsawa ta daura hannayen ta akan cinyar shi tace dan Allah kayi min magana mana wlh bazan kara ba, magana take amman kamar tanayi da gunki, dan haka takai hannuta ta fara cire buturan rigarsa, be hanata ba harta gama, takai hannun ta kirjin shi tana shafa shi amman ko mutsi beyi ba , gajiya tayi ta mike dan ya fara bata tsoro , mutun ba abinda yake mutsi ajikin shi sai tashin numfashi, gefa ta matsa tafara kuka , faruk ko da ta tashi be mutsaba
Sai da ya gaji dan kansa ya mike ya fara maida butir din rigar sa, ya fita.
dan haka humaira takara bashewa da kuka, momy taji kukan humaira tashigo tace to yaya meye kuma na kuka.
momy bemin magana ba fah.
tace to aishi kinji matsalar shi, tashi ki bishi ki kara bashi hakuri.

lukacin da humaira tashiga yana zaune afalo yana shan ruwa, yana ganin ta ,yace koma, ta bude baki zatayi magana ya daka mata tsawa da gudu ta koma.

tana fitowa falo ta fadan kan kujera, kifawa tayi ta danne cikin tasake kara me firgitar wa

✍07014197556


[11/10, 7:04 AM] ‪+234 703 443 5155‬: *💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞*

_*75 To 77*_

_*FADEELA LAMIDO*_
_*MMN YAZEED.....✍*_


_Godiya Ta Musamman Ga *Faty Afreen* Marubuciyar_ *'YAN BIYU NE, SANADIN CAMERA etc* _Thank you very much for the extra help you gave me, I know how busy you are, so I really appreciated the time you spent with me._
.
_*Godiya Ga Masoya Na Masu Karanta Novel Dina Da Masu Kirana A Waya, Ina Godiya Kwarai Dagaske.*_


Faruk ya riga kowa fitowa da gudu ya iso ya dagata su hajiya na kokarin riketa, momy tace meya faru, babu me bata amsa dan ba wanda yasan me ya faru.
humaira kuwa sai rike ciki take tana kuka, bayan an zaunar da ita , momy tace akaita asibiti aduba agani ko lafiya.

momy ta shiga ban garen aminu ta kira shi tace yazo su kai humaira asibiti.
yace me yafaru da ita?
momy tace naga kamar faduwa tayi, da sauri ya mike yana fadin muje .

kafin su futo faruk ya bude murfin motar shi, aminu ne yace to ku kushiga motar yaya mana.
momy ta harareshi tace inbazaka kaimuba ka koma gida.
dan haka da sauri aminu ya matso da motarsa kusa.
faruk na kallon su suka wuce tasa motar suka shiga mutar aminu, haka ne ya tabbatar mai da momy fushi tayi da shi.
bazai iya zama ba dan haka yabisu abaya.

lokacin da ya isa har anshigar da humaira gun Dr mansur, ya samu momy zaune bakin office din, hajiya kowa sun shiga da humaira, momy ta daga ido ta kalle shi tace me kazoyi ai ka koma gida kawai inba hakaba zanma zanma wulakanci anan wurin, ya bude baki zaiyi magana yaga momy ta mike, ranta abace , dan haka ya juya ya nufi gida da tunani kala kala azuciyar shi.

bayan Dr mansur ya gama binciken sa ya
tabbatar musu da cewa cikinta nanan lafiya sai dai sanadiyan buguwa da tayi cikin ya takure waje daya, dan haka yace su rika kula da ita sosai, ya kuma basu magunguna.

bayan sundawo gida faruk na ganin su ta window, da sauri ya taho dan dama ya kosa yaji lafiyan humaira, yana zuwa ya tura kofar momy yajita rufe , yafara buga kofar ahankali, daga ciki yaji muryar momy tace Waye?
yace nine.
tace me ya kawo ka, ka wuce ka barmin kofa karka kara nufumin daki.
momy dan Allah kiyi hakuri ki bude min, momy bata kara kulashi ba har ya gaji ya tafi.


faruk ko da ya koma daki kasa bacci yayi amma baya son yaga ran momy ya baci, musamman idan ya tuna shi yasata acikin bacin rai, shi yanzun gani yakeyi ma kamar momy tafi son humaira akanshi, ba dama taga yayi ma humaira wani abu saitai ta fada.

washe gari faruk ya tashi dawuri dan kosawa yayi gari ya waye yana tashi yashiga wanka bayan ya gama duk yan shirye shiye shi ya fito dan yana tunanin kila yanzun momy ta huce.

itako humaira tunjiya azuciyar ta taso ta koma dakinta dan badan tama faruk laifiba da gobe zasu tafi katsina, dan haka taso momy takira faruk ta bashi hakuri amman tasan baza tayi haka ba, dan jiya tana jin su.

faruk na zuwa ya taba kofar momy yaji ta kulle , Dan haka yasan ko ya buga ba budewa zatayi ba, dan haka ya yanke shawara bari yaje gidan Alhaji Ahamad ya fada masa dan yasan ko abban sa ya gayawa shima fadan zaiyi.

momy na zaune taji muryar yaya ahamad afalo, tara kokari tashi dan ta gaida shi, saijin shi tayi bakin kofa, yana fadin aisha zo ki bude min kofa.

da sauri ta isa bakin kofar ta bude,alhaji yana sa kafarshi a dakin, yana cewa basa matarsa me yayi miki zaki rike mai Mata.

momy tana dariya tace yaya laifi ta mai koma ta bashi hakuri yake ya hakura, ni da kaina na bashi hakuri be hakura ba, to ya yake son ayi, ayi shi yasa nace tabar mishi dakin, tun da ya koro ta kila akwai abinda yake nufi ne.

Alhaji yace babu wani abinda yake nufi kawai dai ki bashi matar sa, ya juya yace da faruk kai kuma in angaya maka magana ka rinka sauraran ta uwa fa ba abin wasa bace, duk inda kakai da son abu tace bari to kabar shi,
komi sonda kake ma abin kuwa, dan haka kar na kara jin, tace ka bari ba bari ba.

Faruk yayita yima alhaji ahamad godiya, sannan ya dauke shi ya maida shi gida.

yana dawowa kuwa dakin momy ya shiga , humaira ce kadai adakin yanemi guri ya zauna bece mata komi ba, har momy tashigo itama batace masa komi ba , faruk yasan fushi take da shi dan haka yace momy har yanzon baki hakura bane.

momy tace ai kai ne kana da matsala wlh, mutun sai kafiyar tsiya.
yace momy kiyi hakuri ba ason raina nakeyi ba wlh , ki dinga yimin ardu,a in Allah ya yarda zan daina.
momy tace to Allah ya shirye mu gaba daya.
faruk ya amsa da ameen.

momy ta sake cewa humaira fa tagama shirin hutafiya gobe.
yace momy to ai naga ba cikaken lafyya gare taba.
aiko dai alkawari bece haka ba, ya kamata ka cika alkawari.
faruk yace to shikenan goben sai mutafi.


humaira ba karamin dadi taji ba dan bata zata zai yarda cikin sauki ba.
furuk kuwa mikewa yayi ya tafi bece ma humaira komi ba, itama bata ce mishi ba.
yana fita momy tace ma humaira tashi ki koma dakin ki.
humaira tace momy tsoro nake ji , bece min komi ba fah.
tace to ke kin mai magana ne be amsa ba.
a,a nima bance masa komi ba.
to ke kimai magana mana ko kema girman kanne dake.

humaira ta shiga da sallama ya amsa ta , taji har gaban shi tace yaya kayi hakuri bazan kara ba.
fuskar shi adaure yace ya wuce.
humaira ta dade azaune bece mata komai ba, abinda humaira bata sani ba satar kallon ta yake ta gefen ido shi tunda yake adoniya be taba ganin matar da ciki ya mata kyau ba kamar humaira.
itako humaira mikewa tayi dan taje ta hada kayan tafiya.

Washe gari 8:00 humaira ta gama shiryawa, falon alhaji ta nufa , bayan ta gaida shi .
Yace humaira yau sai tafiya ko.
Eh abba ai sallama nazo maka.
Yace to yayi kyau bari na baki nashan ruwa , yaciro kudi aljihun sa masu yawa ya mika mata.
ta karba tayi godiya .
Alhaji yace to sai yaushe zaki dawo.
nima bansani ba abba amman ya taba cewa sati daya zanyi.
Alhaji yace sati daya ai yayi kadan , ya daga waya ya kira faruk.
faruk yayi sallama ya shigo da alamun faruk bacci yake yi aka taso shi.
bayan ya gaisar da abba , humaira ta gaida shi ya amsa.
abba kallon su yake da mamaki ya dai kauda Kai, yace yakai baka shirya ba gashi ita ta shirya tuntuni.
faruk yace wlh abba nina manta ma da tafiyar, yanzun dai zan shirya.
yace to ai gara kutafi da wuri tunda kai ai yau zaka dawo, ita kwana nawa zatayi.
faruk yace kwana biyu.
abba ya tashi daga kishin gidan da yayi yace wani irin kwana biyu kuma, babana, wai shin kai kulle zakayi ne haka, shekara daya fa kenan kusan da rabi bata taba zuwa gida ba , ina lefin tayi sati biyu .
yace abba sati biyu yayi yawa.a




[11/10, 7:04 AM] ‪+234 703 443 5155‬: *_💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞_*


*_78 to 80_*

_*FADEELA LAMIDO*_
*MMN _YAZEED.......✍*_

_*Jinjina Agareki Faty Afreen Everything would be better if more people were like you!*_

_*Bazan Manta Kuba Smart Triplet & Narjis Da Duk Sauran Members Gaisuwa A Gareku Baki Daya.*_


Alhaji yace yanzo nan kai dan baka da kunya sai ka je kace ka kawo ta tayi kwana biyu?
faruk shiru yayi ya dukar da kai.
alhaji ya sake cewa kabar ta tayi sati biyu , duk tabi yan uwan ta ta gaida su, ai sun mana kara tunda aka kawota babu wadda yazo, kuma nasan alhaji ne zai hana .

faruk yace sati buyu fa yayi yawa fah ,abba sai dai ta bari indan an kwana biyu sai na kaita tayi sati daya.

alhaji ya kalli faruk ya girgiza kai ,yace to yanzun me zai hana ka kaita yau din tayi sati dayan.

faruk ya dade zaune ya dukar da kai yayi shiro .
sai cen yace bari naje na shirya.
alhaji yace to ka sai mata tsara ba ne.
yace eh muyi waya da nura zai suyo ya kawo, bari ma na kira shi naji.
mikewa yayi yana cewa abba bari naje na shirya.
alhaji yace ai sai dai nace muku Allah ya kiyaye hanya danni fita zanyi.

faruk dakin su ya nufa ya zauna a folo.
itako humaira daki momy taje.
momy tace a,ah har kun shirya .
humaira tace yaya ne har yanzun yaki shir yawa.
tace rabo da shi yau duk tsiyar shi dai yau sai kinje gida.
suna cikin magana da momy kiran faruk ya shigo wayar ta.
da sauri ta daga

10 / 14