Ameera Da Adam Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Romance

Chapter   9 / 18

24K to 27K   out of 51.1K words

daga nesa ya zuba mata ido ko rsintsawa baya yi, sosai ya yi suman tsaye yana kallon matar tasa kamar an sauya ta, har ta ƙara so gurin yana tunanin lokacin baya da ta taɓa irin wannan wanka kafin su yi Aure wanda ranar tsabar kyau har faɗa suka nai mi suyi domin shi Adam bai san lokacin da ya rungumota ba ita kuma bata tsammaci haka daga gare shi ba domin basa haka a rayuwar soyayyar ta su.

Ita haushi ma ya bata da irin wannan kallon hakan yasa ta ce "Wai dan Allah me ye wannan ɗin, kaman wacce bata saba yin wanka ba, yanzu fisabililahi idan wani ya gani ai sai ya zata bana maka kwalliya ne sai wata-wata. Adam da ya dawo daga tunanin sa ya ce "Honey kenan ai ke kullum wankanki idan kin yi Allah ƙara rikitani kike yi, kalleki fa kamar wata amarya. Ya faɗa yana ƙara sawa kusa da ita ya shiga shafo cikin nata kamar ya fito da yaron dake ciki. Ganin abun nasa ba na ƙare bane yasa ta ce "Wai zamu tafi ne ko dai sai ka gama wannan abun na ka? Adam ya ce "No mubari wannan yarinyar ta fito domin tare zamu tafi, idan na ajiyeki sai mu ƙarasa da ita mu sayo kayan. Take gaban Ameera ya bada wani darararammm! Jin kamar zata faɗi ne yasa ta naimi guri ta zauna tana kallon sa. "Kenan da gaske Adam yake yi a kan wannan yarinyar! To me yake nufi da haka! Haka dai bata ce masa komai ba har Haura ta fito cikin shigar ta na doguwar riga babu mayafi sai kanta da ta yane, sosai rigar ta amshi jikinta sai sunne kai take yi kamar tai wa sarki laifi. Da kyau Ameera ta kafe yarinyar da kallo ta na so taga ko a kwai wani abu na daban a jikin yarinyar da bata san da shi a gurin mata ba ne. Haka suka shiga motar gaba ɗayan su ba tare da Ameera ta ce komai ba. Har suka isa gidan shi kaɗai yake zan censa domin Ameera kamar ma bata cikin motar. Fitowa ta yi ta na miƙawa Haura jakar hannunta alamar ta ƙarɓa su tafi.

Adam ya ce "Tare da ita fa zamu tafi ko kin manta ne? Ai kuwa dama abun da take jira kenan, dama tana so ta ji ko yana da kunya ko baida ita, jin ya nuna mata tsan-tsar rashin kunya ne yasa cikin harziƙowa ta ce "Tunda ita ɗin ƙanwar uwarka ce ai dole ku tafi tare, yarinyar da ba maharramarkaba itace zaka ce min wai tare zaku tafi, dama naso naga ƙarshen rashin ta idon ka ne, kuma ka nuna min, dama na lura gaba ɗaya ka manne ma wannan yarinyar to wallhi ka sani sai ta bar gidan nan ko kaso ko baka so ba. Adam da ransa ya gama ɓaci jin har tana zaginsa ya ce "Ni kike zagi akan nace zan je da ita na sayo mata kaya? Ya tambaya cikin ɓacin rai! "Ameera ta ce "Ni dai ban zageka ba sai dai ko kaine kaji zagin amma babu inda wannan yarinyar zata bika har ga Allah! Ta na faɗa ta dakawa Haura tsawa dake zaune a cikin motar tana sauraron su. Haka kuwa ta fito daga cikin motar riƙe da jakar tana komawa gefe ta tsaya. Tana fita Adam ya tada motarsa ya fuzgeta a guje ya bar unguwar ba tare da ya ƙara ce mata komai ba. Afili Ameera ta ce "Idan ka ga dama karka tsaya har wata uku kana gudu.

Kunnen Haura ta kamo ta murɗe tana faɗin "Shigiya dan gin arna wata ƙikama karuwa ce ke, ko kuma wani abun ki kai wa mijina har yake neman damuwa da ke. Haka suka nufi gidan kunnen na hannunta Haura kuwa ta kasa ko yin ihu sai rintsaye ido da ta yi.

Sai da suka zo shiga gidan kafin ta sakar mata kunne tana shiga gidan nasu da sallama. Sosai ta yi murna jin an saki Abban nasu, sai dai abun da ya ɓata mata rai shine jin cewar wai auran Nana da Nasiru yana nan wai sun shirya. Afili ta ce "Kai wannan yaro ina ga wallahi maye ne ko dai yana da dangi mayu! Haba duk irin abubuwan da suka faru amma ya dawo, anya Umma wannan yaron alkairi ne a gurin Nana kuwa? Umma ta yi saurin faɗin. "In sha Allah Nasiru alkairi ne kuma shi ba maye bane, sannan ki dinga iya bakinki a kan abun da zai fito daga ciki, sharrin maita bata da sauƙi. Ameera ta saki guntun tsaki ta na faɗin "Wannan auran dai kawai ganganci za'ayi, ya za'ayi yaro kullum dukan ta tun kafin ayi aure amma hakan ace wai shi zata aura, anya Umma kun duba wannan lamarin da idon basira kuwa? Umma ta kafe Ameera da ido ta ce "Wai ke manene matsalar ki da wannan yaron ne? Ameera ta yi caraf ta ce Dukan ta da ya ke yi, kinga duka ko a addinin Musulunci haramunne namiji ya daki matarsa. Kinga Umma in sha Allah zan kawo miki wani littafi mai suna Addininmu mu wanda S-REZA ya rubuta nasan in sha Allah zaki ƙaru sosai littafin yana faɗin abubuwa da dama a kan addininmu, nima ban daɗe da fara karatun sa ba. Umma ta ce "Allah ya tsareni da karatun shirme da ƙarya, tun da banyi ba sai yanzu, idan sanin addini ni to ga Alkur'ani mai girma ko sauran littatafai irin su Mahuwul Islam da ƙawa'idi Ahadari. Ameera ta ce "To ai daga cikin su ake ɗaukowa a rubuta. Umma zata ƙara magana sai ga Nana ta shigo tana sallama.

Tana haɗa ido da Ameera ta zo da gudu tana faɗin anty Meera albishirin ki? Dama ke naso na fara sanarwa da wannan albishir ɗin. Ameera ta ce "Kinga ni ɗagani karki ƙarasa baiwar Allah. Nana ta kalli Umma ta ce Umma ɗan bamu guri, Umma ta ce "Ko baki faɗa ba ta shi zanyi ai! Bayan Umma ta fita Nana ta kalli Haura kafin ta yi magana har ta miƙe zata fita. Ameera ta ce "Munafuka ai da kin tsaya kinji gulma. Nana ta ce "Wai wacce wannan ɗin ne? Ameera ta ce "Wannan bai shafe ki ba.

"To ai naga bata kama da mijin naki ne bare nace ƙanwarsa ce ko ƴar uwarsa. Amma ta ce "Wai Nana a ina kika koyo munafunci da gulma da
Gutsiri tsoma ne? Ganin zata fara masifarne yasa Nana faɗin. "Anty Meera kin san me?

Ta ce "Sai kin faɗa "

Nana ta gyara zama ta na faɗin "wallahi wai harda makulli mota zai haɗo min a sabon lefen da zai kawo, wai yana so ya bawa mara ɗa kunya. Ameera ta ce "To ai idan yana so ya burge ko kuma yayi abin da wasu basu yi a wannan layin ba to jirgi zai baki, domin mota tsohon yayi ce, ko baki faɗa masa cewar Adam ya haɗe lefena da sabuwar mata ba ne, kuma shi bai taɓa shiga har cikin gidan iyayena ya ci musu mutunci ba, ko kuma yasa a kulle ubana a police station ba, to shi wannan in bada rashin kunya har ya iya ƙara haɗa ido da mu dan gyatumarsa. Nana da izuwa yanzu ta gana ƙuluwa ta ce "Ta ce to anty ko dai ɓakin ciki keke min ne da wannan abun arziƙin?...✍️


Comments dinku shine ƙwarin guiwa na. (Bana yin posting ranar juma'a da Lahadi)

*One love*
*One house*
*Comment's*
*Shering please*
*Love all my fan's*
*S-REZA is typing...* ✍️


*AMEERA DA ADAM*
*10*



*By S-REZA*

*WHATTPAD*
_Salis M Reza_






*PAGE1️⃣0️⃣*

... Ɗauke da mamaki Ameera ke kallon Nana jin abun da ta ke faɗa a kan ta wai baƙin ciki. Cikin sanyin murya ta ce "Yanzu Nana nice ke miki baƙin ciki!? Nana ta gyara zama da kyau domin kuwa ranta ya ɓaci da irin cin mutuncin da yayar tata kewa Nasiru. "To idan ba baƙin ciki ba meme ne wannan? Mutum ya yi abun burgewa amma baza'a ya ba masa ba sai kuma cin mutunci ya biyo baya, haba Anty Meera ni ban san yaushe kika zama haka ba dan Allah ki dawo yadda kike please ki bar wannan halin hassadar da kika ɗauko wallahi bata ɓullewa. Nana ta ƙarasa ta na ƙoƙarin barin tashi ta bar ɗakin. Ameera da har wani kumfar masifa ne ke fita a bakinta ta miƙe ta janyota ta rufe ta da duka tana faɗin. "Wallahi Nana kin yi kaɗan ki rainani har haka, daga faɗa miki gaskiya sai ki fara zagina harda kirana da munafuka magulmaciya, ke ɗin banza yaushe har kika girma kika san daɗin saurayin da zakimin rashin Kunya a kansa. Sosai take jibgarta babu ƙaƙƙautawa. Nana kuwa jin Ameera na ƙoƙarin sumar da itane ya sa itama ta fara mayar mata da martani bata duba ƙaton cikin dake jikinta ba. Cikin ƙan-ƙanin lokaci Ameera ta fara ihun waiyoo cikinta. Sosai ta ke kuka ta na riƙe da ciki. Hakan yasa Umma saurin shigowa ɗakin tana tambayar ba'asi. Amma idonta ya sauƙa a kan Nana ta danne Ameera sai duka ta ke Kamar Allah ya aikota. Da sauri Umma ta rafka doguwar salati ta na isa gurin ta kama Nana ta wanka mata mari sannan ta jefar da ita kefe ɗaya ta yi kan Ameera wacce izuwa yanzu ta ma daina ihun sai numfashi da take saukewa a hankali.

Ganin haka yasa kafin Umma ta dawo gurin Nana har ta fita daga ɗakin. Nana na fita Haura ta shigo ɗakin tana tambayar lafiya. Umma da zuwa yanzu duk ta rikice ta ce "Kin iya tuƙa Mota? Haura ta amsa da "A'a ban iya ba. Umma ta ajiye Ameera da take kan cinyarta tun ɗazu ta nufi ɗakinta domin ɗaukar waya ta kira Abban su. Tana dawowa taga Ameera na sauke ajiyar zuciya Haura na mata sannu tana cigaba da rike cikinta. "Waiyoo Allah Umma cikina zan mutu! Ameera ta faɗa tana kallon Umma da take mamakin ganin lokaci ɗaya ameera ɗin ta magantu.

Umma cikin faɗa ta fara faɗin "Wallahi kin bani mamaki Ameera, tsabar rashin sanin ciwon kai ki tsaya kina faɗa da ƙanwarki kina ɗauke da wannan tsohon cikin! Koma me zata miki bazaki haƙura ki barta albarkacin wannan cikin da ke jikinki ba, yanzu idan yazo da tsau-tsayi cikin ya samu wani matsalar fa? Ana cikin haka Adam ya ƙara so gidan dalilin kiran da Umma tai masa. Yana zuwa cikin tashin hankali ya sunkuceta izuwa Mota Haura tabi bayansu suka nufi asibiti. Suna fita Umma ta shiga kiran sunan Nana cikin wata iriyar murya wacce kana ji kasan ranta a mugun ɓace ya ke. Sosai ta ke kiran Nana ta ko ta ina amma babu Nana babu dalilin ta, lungu da saƙo na gidan babu inda bata duba ba amma babu Nana hakan yasa ran Umma ƙara ɓaci tana jin yau sai ta kusa sumar da yarinyar nan idan ta ganta.

Sosai likitan ya hau Adam da faɗa bayan ceto cikin da suka samu suka yi da ƙyar. Faɗa sosai ya yi masa akan wai a daina wasa da cikin domin wannan da ƙarfi aka mawa cikin wanda hakan yasa sai da ɗan cikin ya juya daga yanda ya ke. Sosai Adam ya shiga amsawa da za'a kiyaye wannan ma baya gida ne shine yasa. Likitan ya ƙara ɗorasa a kan sharuɗa irin na masu tsohon ciki. Ya ce "Kar a barta ta yi wani aiki mai wahala koda shara ko wanki da sauransu. Sannan banda yawo ta zauna guri ɗaya domin ɗan cikinta ya jigata sosai yin wani babban abun zai haifar da damuwa. Sai da yamma aka sallamo su wanda kafin wannan lokacin sai da Haura ta je gida ta dafo musu abinci. A hanya ne Adam yake tambayar ta me ya sameta. Ameera ta yi shiru ta na kallon gefe ɗaya zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Adam ya dawo da tambayar kan Haura ita kuma ta ce bata sani ba. Har suka isa gida bata ce komai ba sai hawaye da ke zubowa a idonta. Sosai ranta ke mata suya zuciyarta na mata zafi tana jin kamar a kwai wani abun da ya kamata ta yi domin taji daɗi. Sai ta ke jin duk duniyar ma ta tsani kowa, kaman babu wanda yake sonta a duniyar. A hankali take tuno komai da ya faru tsakanin ta da Nana. Shi kansa Adam tausayi ta ne ya rufe shi ganin yanda ta riƙe cikin ta ga kuma hawaye da yake zubowa ba tare da tayi kuka ba. Sai yanzu ya ƙara jin tausayin ta ganin ita kuma irin nata laulayin kenan. Itama Haura kaman tai mata kuka tsabar tausayi domin har ta rame sosai. Haka suka iso gidan mai gadi ya buɗe musu get. Kafin ma Adam ya ƙara sa tsayawa Ameera ta buɗe ƙofa ta fito ta nufi cikin gida da sauri. Bata son ganin kowa a kusa da ita, ta gaji da wannan duniyar bata san mai taiwa kowa ya tsaneta har haka ba.

Ganin haka yasa shima bai gama saita motar ba ya kashe ta ya fita yabi bayanta yana sanar da Haura da ta rufe motar. Ya na shiga ya sameta ta ƙifa kanta a bakin gado tana shesheƙar kuka. A hankali ya ƙara so kusa da ita ya fara mata magana a hankali "Honey dan Allah ki yi haƙuri wannan kukan ma zai iya kara haifar miki da damuwa keda ɗan cikin ki, please I'm so sorry kinji. Jin bata daina kukan bane kuma bata ɗago ta kalleshi ba ne yasa ya matso kusa da ita ya sa hannu zai ɗagota. Yana ɗora hannunsa a jikinta ta yi zumbur ta meƙe kamar mai jiran hakan. Wallahi babu wata-wata ta ɗauke fuskarsa da mari, ta cakumi rigarsa ta fara zaiyano komai da take jin ya tsaya mata wanda tun ɗazu take jin idan bata amayar ba zata iya mutuwa "Na tsane ku bana son ganin kowa ku fita a sabga ta wallahi bana son ganin kowa mutuwa ma kawai zanyi mai nai muku ina kuke so naje. Ta na faɗa tana cigaba da dukan Adam a ƙirjin sa. Ganin haka yasa Adam ƙoƙarin kwantar da ita a ƙirjin nasa amma ta ƙwace jikinta ta nufi gurin kayan kwalliya ta kwaso su ta watsar a ƙasa, ta ɗauki kwalbar turare ta wurgowa adam wanda yayi saurin kaucewa, ta ɗauko kwalbar mai shima ta wurgo masa tana kuka tana fasa duk abinda ta gani a cikin ɗakin harda madubin da ke gurin kwalliyar saida ta tarwatsa shi, sosai ta koma kamar mahaukaciya , Adam dai da abun nata yayi mugu-mugun bashi tausayi da mamaki ya tsaya yana kallonta har ta yi ta gaji ta zube a gurin tun tana jan numfashi har barci yayi gaba da ita.

Sai da ya bari barcin ya fara mata nisa kafin ya ɗauke ta ya kaita ɗakinsa ya kwantar da ita ya nufi ɗakin Haura da nufin kiranta ta gyara waccen ɗakin. Tun kafin ya tura dakin yauma yaji kamar ba Muryar mutun ɗaya yake ji a ɗakin ba hakan yasa shi saurin tura ƙofar ɗakin yana mai kai kallonsa izuwa cikin ɗakin. Cikin tsananin mamaki Adam yake kallon wannan tsohuwar matar mai yin bara nan wato mamar Haura. Zaune ya same su a gefen gadon ga soyayen naman kaza a gaban tsohuwar tana ci tana surutu. Gefe ɗaya kuma Haura ce zaune itama tana cin naman suna ta fara'a da yaransu. Kafin Adam ya ce komai Haura ta ce "Ammi ta ce tazo yanzu ina so idan ka fito na faɗa maka ne.

Adam dai bai ce komai ba sai bin tsohuwar da ido yake yi, itama tsohuwar sai kallonsa cikin ido take yi. Ganin haka yasa ya ce "Ok kizo yanzu. Yana faɗa ya saki ƙofar ya fita da mamaki. Shi dai bai yarda cewar yanzu wannan matar tazo ba, to idan ma zuwa zata yi sai kawai ta shigo kan ta tsaye, to shi yasan ma mai gadi ba zai barta ta shigo kai tsaye ba, hakan yasa Adam cewar sai ya tamba yi mai gadi ko shine ya barta ta shiga. Yana tsaye a Palo ta ƙaraso kanta a ƙasa. Kallonta ya ƙara yi sai yaga kamar ta ƙara zama yarinya. Sai da ya sauƙe ajiyar zuciya aɓoye kafin ya ce "Kije ɗakin Ameera ki gyara komai, a kwai kwalabe ki yi a hankali. Haura ta amsa da "Tom za'a gyara yanzu " Adam na faɗa ya nufi gurin mai gadi. Yana zuwa bai bi ta kansa da ya fara wasu zantukan daban ba ko gaisuwar ma bai amsa ba ya ce "Amm bayan mu wani ya shigo gidan nan yanzu ne? Baba mai gadi cike da mamaki ya ce "Ranka shi daɗe gaskiya babu wanda ya shiga gidan nan bayan ku ukun da kuka shiga yanzu, kuma yau kasancewar ba kwa gida yasa ban je ko ina ba, abinci ma Haura ce da ta dawo ɗazu ta kawo min har nan, ai Allah ya sakawa wannan yarinyar bata gajiya kamar a gogo. Adam bai ce komai ba ya bar gurin yana girgiza kai alamun nazari.

Koda ya koma ciki yana shiga sai yaga kamar ƙiftawar mutum, amma bai ga kowa ba hakan yasa ya nufi ɗakin da yasa Haura aiki ɗin domin yaga ko ta fara. Yana shiga yaga ɗakin tsaf-tsaf a gyare komai an mayar da shi mazaunin sa kamar ma ba'a komai a ciki ba. Cikin wani sabon mamakin

9 / 18