Ameera Da Adam Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Romance

Chapter   2 / 18

3K to 6K   out of 51.1K words

ce "Kinci abincin ne ke? Cikin tsiwa da matsuwa da ganin yabar gidan ta ce "Ina ruwanka da naci ko banci ba. Tana faɗa ta tura shi waje ta rufe gidan tana Jan tsaki.

Tsaye Adam yayi a waje daga shi sai doguwar riga sai yanzu ya kula da ko takalmi ma babu a ƙafarsa wayarsa ma a ciki ya baro ta, afili ya ce "Inna'ilaihi wa inna'ilaihi raju'un! Wai me ke damun honey ne, anya kuwa ba sauyamin ita a kayi a asibiti ba, to idan ba haka ba menene matsalar daga jiya zuwa yau na kasa sakewa a gidana babu damar nayi gwaninta. Ya na laluba aljihunsa yaji babu makullin mota, sannan babu ko sisi da zai hau mashi izuwa gidan ƙkanwar sa, kasancewar babban abokinsa take aure. Ko da yazo mai gadi barci yake yi abunshi haka ya buɗe get ɗin ya fita yana kallon titin tsit sai ɗai-ɗaikun mutane masu tafiya a ƙasa. Sai da ya daɗe kafin ya samu mai mashi ya hau izuwa gidan su Najib. Koda suka isa ya tsaya a bakin get d'in gidan yana bugawa, amma sun kai minti biyar babu wanda ya amsa harma mai mashin ɗin ya fara magana, suna cikin haka mai gadi ya buɗe get ɗin da masifar katse masa barci da a kayi, domin yasan dai masu gidan suna ciki. Amma ganin Adam yasa ya saki fara'a yana masa barka da safiya.

Cikin jin kunyar ganinsa a haka da mai gadin yayi ya ce "Kamin mgn da Najib yanzu please. Ko da Najib yaji cewar Adam ne da sauri ya fito yana mamakin zuwansa da sassafennan dama jiya kadija ke sanar masa da cewar Ameera tanada ciki kodai ba lafiya bane. Kafin Najib yace komai Adam ya ce "Please sallami mai mashin ɗin nan yana faɗa ya shige gidan ya bar Najib da mamaki ganinsa a birkice.

Ameera kuwa bayan fitan Adam palo ta koma ta zauna ta ɗauki shayinta ta fara sha, jin yayi sanyi yasa ta koma kicin ɗin, ta ƙara haɗa wani, zata ɗauki keck amma taga ya ƙare, ita kaɗai sai kumbure-kumbure takeyi, tana jin haushin komai ma shi kanshi gurin da a ke ajiye Keck ɗin ganin babu saida ta rufe gurin da ƙarfi har yana tsagewa. Firiza ta buɗe ko zata samu super commando domin shine drink dinta shima ganin babu yasa ta ture firiza ɗin da ƙarfi har yana faɗuwa ko ta kansa bata biba ta duba bredi shi Kuma taga saura kaɗan Kuma ya d'an bushe hakan yasa tayi wurgi dashi ta shiga ɗaki ta ɗauko kuɗi ta nufo gurin mai gadi.

Tsabar masifa na cinta ma ko sallama bata yi ba ta fara buga ƙofar ɗakin kamar ɗakin ne yayi mata laifi. "Baba mai gad...Baba mai gadi!... Da sauri baba mai gadi ya fito yana amsawa domin ya gane muryarta.

"Na'am hajiya lafiya dai ko?

"Saboda nazo kiranka shine kake tambayar lafiya? Ok idan da lafiya ban isa kiranka ba kenan ko? Na ce ban isa kiranka ba kenan ko?

Jin yayi shiru yasa ta harareshi sannan ta ce "Aikenka zanyi kuma saura kamin shirme kuma wallahi ka dawo yanzu! Tabna faɗa ta jefa masa dubu ɗaya ta ce "Abu mai laushi zaka sayomin yanzunan karka ɓata mini lokaci. Ta na faɗa ta juya ta fara tafiya ta bar baba mai gadi da buɗe bakin ganin sabon lamari daga matar gidan nasu. Matar da ko ɗaga ido ta kalleshi bata yi, bare har tai masa ihu barema aike, shi dai tun da yake a gidannan bata taɓa zuwa ta aikeshi ba, wani lokacin dai Adam ke turota ta ce inji Adam ka sayo abu kaza. Ganin zata shige be kuma gane aiken ba ne ya ce

"Hajiya wani abune mai laushi bansan wanda zan sayoba?

Tun daga gurin da take ta nufoshi cikin masifa kai ka rantse zaginta yayi, har tana haɗawa da gudu ta iso gurinsa ta ce "Kai baka da ilimi ne baka san abu mai laushi ba har sai ka tambaya to kaje ka sayo goriba ko rake tunda baka da lissafi, yanzu abu mai laushi har sai an faɗa maka in banda samun guri, to wallhi kaje ka sayo min yanzu ina jiranka. Ta na faɗa ta juya fuuu ta nufi ciki ta bar baba mai gadi tsaye yana juya kuɗin yana nazari to meye abu mai laushi! Kuma da sassafe haka, anya kuwa hajiya lafiya taka. Haka dai ya fita badan yasan me zai sayo ɗin ba.

Ita kuwa Ameera bayan ta koma ta nufi gurin da firizan da tafaɗar tana son ta ɗaga amma ta kasa, tati-tayi amma ko motsashi ta kasa, haka ta dawo ta zauna tana jiran baba mai gadi domin taga mai zai kawo mata, domin ita kanta bata san me takeson ci ba, ita dai tasan Abu mai laushi take marmari, idan da za'a yankata bata san me take son ci ba, kuma bata son cin bredi hakan yasa bata ce masa bredi ba.

Najib da kadija cikin mamaki suke tambayar Adam lafiya dai yazo a haka. Cikin rashin sanin abun yi ya ce "Wallahi babu lafiya gidana tun jiya ba lafiya. Da sauri kadija ta ce "Mai ya samu Ameera ɗin Yaya? Wani abun ne ya samu cikin nata?

Shi Adam har ga Allah harma ya manta da cewar cikene gareta. Cikin su'butar baki ya ce "Au wai dama ciki gare ta?

Da mamaki Najib da kadija suka Kalli juna jin abun da ya ce.

"Yaya ina ce kai da kanka jiya ka kirani kace Ameera nada ciki ko dama tsokana ta ka keyi? Kallonsu yayi ganin sun kafeshi da ido sai ya sunkuyarda kai ya ce

"Eh gaskene kawai sha'afa na yi.

"Ban gane ka sha'afa ne ba, wai wani abu ne yake faruwa ka fito ko takalmi babu ga shi ko kayan arziƙi babu a jikin ka, yanzu kuma wai kace ka sha'afa ne lafiya kuwa? Najib ya faɗa yana ƙara nazarin abokin nasa.

Cikin murya tausayi Adam ya fara cewa "Wallhi tun jiya da muka dawo daga asibiti Amerra ta sauya, dana tun kafin jiyan ta zama abu kaɗan fushi da masifa, to daga jiya kuma abun ya ƙaru komai nayi masifa, idan nace taci abinci masifa,idan na tasheta a barci faɗa, yanzu haka itace tace wai na tashi na tafi gurin aiki, nace mata lokaci baiyi ba wai wallhi sai na fita, ta barni na sake kaya ko naci abinci ma wallhi taƙi, harfa waje ta rakoni tana dukana da filo. Ya ƙarasa kamar zaiyi kuka.

Dariya kadija ta yi tana cewa "IKon Allah ita Ameeran ce harda dukanka? To ko dai nata cikin ne yazo mata da ƙunci da ɓacin rai?

"To Kuma sai tayi ɓacin ran harda ni mijinta? Adam ya tambaya cikin rashin yarda.

Kadija ta ce "Ta to wallhi yaya in dai irin wannan cikin ne to mutum koma waye sai ta masa, wani lokaci ma idan bata samu abokin yi ba to kuka zata fara ita kaɗai ko kuma ta samu wani abu a gidan ta huce a kansa, irin wannan yanayin mata da yawa na shiga irin sa, Kuma suna shan wahala sosai dole sai kayi haƙuri, dama ai Yaya ka sha faɗin cewar idan Ameera ta samu ciki zaka tarairayeta kamar ƙwai, to kaga haka zaka daure.

Cikin mamaki Adam ya ce "Wai dama cikinne yasa wannan abun? Nifa duk inace barcin yamma da tayi ne yasa ta haka, yanzu dan mace nada ciki sai ta fara masifa Fisabililahi! Najib ya ce

"Ai kawai abokina haka zaka daure, yanzu dai ka shiga kayi wanka ka fito muci abinci anjima kadija sai taje gurinta kar a barta ita ɗaya a gida kaga babu daɗi. Adam ya tashi ya tafi ɗakin da suka nuna masa yana tafiya yana mamakin wannan lamari, yanzu kawai sai mace ta fara masifa saboda ciki, shi bai ta'ba jin wannan labarin ba.

Tana zaune idonta ƙurr a ƙofar falon Mai gadi ya turo ƙofar falon hannusa riƙe da leda, idonta a kan ledar domin ganin mai ya kwaso mata. Shi kuwa baba mai gadi jikinsa har rawa yake domin yasan dole sai ya she masifa barin ma yanzu da ya ƙara haɗa ido da ita ganin yadda ta kafe ledar da ido. A zuciyarsa ya ce "Yanzu fisabililahi ki aiki mutum ba tare da kin sanar da shi abun da zai sayoba, fatan kawai ki wahalar dani, yanzu nasan dole sai na koma. Jin tsawar da ta daka masa ne yasa shi saurin ƙarasawa gabanta ya miƙa mata ledar kamar zai faɗi. Karɓar ledar ta yi ta na ƙoƙarin buɗewa, ganin ledar na mata gardama ne yasa ta yaga ledar tana jin ƙamshin abun da ke cikin ledar, cikin mamaki take kallon abun da ke ciki. Ɗagowa tayi ta kalleshi kafin ta Kara kallon abin da ke ciki ta ce...



Kubi S-REZA a hankali kusan bai saba baku kunya ba.

*Whatpad*
Salis m Reza

*One love💘*
*One house🥰*
*Comment's 🤝*
*Shering please👏*
*Love my all fan's😍*
*S-REZA typing...✍️*

*AMEERA DA ADAM*






_*(By S-REZA✍️)*_


*(Writer of Uwata ce sila. Meera & Nusee)*



*PAGE 2️⃣*

...."Baka da hankali ne me ye wannan ɗin haka? Ta yi tambayar ta na turo masa ledar gaban sa. Cikin tsananin tashin hankali Baba mai gadi ya ce "Hajiya ƙosai ne na gani ana soyawa a ƙarshen layi to shine na sayo miki domin wallahi ban san wani abu mai laushi bayan wannan ɗin ba a irin wannan lokacin. Lokaci ɗaya taji kwaɗayin ƙosan a rainta amma tsabar masifar dake cinta sai cewa ta yi "To dan tsabar gidadanci sai kawai ka sayo mini ƙosai saboda kaga ana soyawa a ƙarshen layi ni nace ka sayo mini ƙosan ne? Baba mai gadi yayi shiru yana sauraronta. Jin ta yi shiru ta faɗan ne yasa shi ɗako kai da nufin kallonta sai kawai yaga tana cin ƙosan. A zuciyarsa ya ce "Ikon Allah a she ana so! Ganin haka yasa Baba mai gadi meƙewa ya bar palon ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Ameera kuwa sosai taji ƙosan ya shiga ranta hakan yasa ta ɗauki guda ɗaya ta ci, jin yayi mata daɗi sai kawai ta cigaba da ci har bata san lokacin da Baba mai gadi ya bar palon ba. Tashi ta yi ta koma kicin ta ƙara haɗa shayi ta fito palo ta zauna ta sha kayanta sosai sannan ta ƙulle sauran ƙosan ta koma ɗaki ta sake kwantawa ba tare da ta gyara gidan ba, tana kwanciya barci ya ƙara ɗauketa.

Tana cikin barci taji ana kiran sunanta hakan yasa ta miƙe fuska a haɗe ta nufi hanyar waje. Koda ta buɗe sai taga Kadija ce hakan yasa ta ɗan saki fuska. Cikin yanayin barci tai mata maraba sannan ta juya izuwa cikin gidan.

"Ameera ta Adam yau dai Allah ya amshi addu'o'in mu ya bamu baby da muke ta nema. Kadija ta faɗa lokacin da ta zauna. Murmushin yaƙe ta yi tana jin babu daɗi a ranta. Ganin haka yasa Kadija sake cewa "Kawai sai mukaga Yaya da sassafe wai kin kora shi aiki ko taƙalmi babu a ƙafarsa kamar ɗan gudun hijira hala wani laifin yayi miki? Kadija ta faɗa duk domin ganin ta jata da hira ganin kamar ranta a ɓace yake. Daidai lokacin Ameera ta ce "Kice gulma ce ta kawoki gidan ba komai ba, ina ruwanki idan ma laifin yayi mini, shima zai dawo ya sameni daga cewa ya tashi ya tafi aiki shine zai ɗauki ƙafa yaje gidanki yana kai miki ƙara ke ga uwarsa ko uwata ko? Shine harda zuwa ki kuma zaki ɗauki mataki ko? To gani dan Allah ki ɗauki mataki nice na koreahi. Tana faɗa tana ƙarasowa gaban Kadijan cikin tsananin ɓacin rai domin har ga Allah abun da Adam ɗin yayi ya sosa mata rai, daga cewa ya tafi aiki shine harda zuwa ya kai ƙaranta kamar wacce tayi wani abun laifi. Cike da tsananin mamaki Kadija ke kallon Ameera wacce ada ko iya magana ma batayi da ita tsabar kunya, hasalima wani lokacin har faɗa take mata cewar ki saki jikinki dani ni ƙanwar mijinki ce ba yayar mijinki ba, amma haka Amera zatayi dariya ta kawar da kai. Ganin Amearan a gabanta kamar zata saka mata hannu ne yasa tayi ƙarfin halin cewa "Ameera ni kike faɗawa haka dan na tambaye ki? Cikin harzuƙowa ta ce "An faɗa miki ɗin uwata, ke ɗin banza kika iya shigowa gidana da niyar gulma bakiji kunya ba sai ni ce zanji kunyar faɗa miki gaskiya to na faɗa ko ƙarya nayi ba gulmar kika zo yi ba, ina ruwanki da tsakanina da mijina, mijina ko mijinki?

Duk yadda Kadija ta kai da tayiwa Ameera azuri amma sai take jin wannan ba laulayin ciki bane, wallahi kawai iya shige ne da alama asalin halintane take baiyana wa yanzu,to da ma a ce laulayin ciki ne ai nata cin mutuncin yayiwa, dama itama Kadijan ba haƙuri gareta ba. Hakan yasa Kadija faɗin "Ya isa haka ƙaramar mara kunya, ke har kin isa nazo gidan Yayana kina zagina, to ƙaryane baki koreahi ɗin bane? Kuma idan bai zo gidana ba duk duniya wayakeda shi da ya wuce ni, wato zakiyi ƙarya da ciki kina cin mutuncin munatane ko, to wallahi ƙarya kike yi yarinya. Kadijan ta faɗa itama ta na cire mayafin kafaɗan ta tana ɗaurawa a ƙuƙunta alamar shirin faɗa. Kasancewar su ɗin kusan sa'anye ne domin ko Kadija zata girmewa Ameera to sai dai ko irin da shekara ko watanni, domin ko auransuma tare a kayi, kuma dukkanninsu babu wacce Allah ya baiwa ciki sai yanzu da Ameera ta samu.

Jin abun da Kadijan ta faɗa ne yasa Ameera jin kamar an watsa mata garwashin wuta cike da fushi da jin cewar a zo har gidanta a naimi buɗe mata ido, ga kuma duk ƙuncin da take ji yazo ya tsaya mata a wuya bata son magana sam, hasali ma ita bata son ganin kowa a kusa da ita, hakan yasa ta ɗauke fuskar Kadija da mari wanda Kadijan batai tsammani hakan ba, shi yasa marin ya shige ta da kyau. Ji kake tass tass tass har sau uku. Sannan ta chakumeta ta watso ta waje ta rufo ƙofar gidan ta tana cigaba da zagin ta.

Ita kuwa Kadija tsabar shigan marinne yasa bata ma san lokacin da a ka watsota wajenba, sai ji tayi ta ƙara buga kanta a jin abun da bata san ko meye ba, ai kuwa take ta baje a gurin sumammiya. Cike da ɓacin rai Ameera ta ɗauki wayarta domin kiran Adam ta sauke masa kwandon masifar amma taji wayar na ƙara a cikin ɗaki. Sosai wannan karan ranta yayi mugu-mugun ɓaci, azo har gida a naimi cimata kashi. Ɗakin ta shiga ta ɗauki wayar tana ji kamar ta bugata da ƙasa, sosai take jin ɓacin rai fiye da kullum, ji take da Adam zai shigo gida yanzu da sai ta kusa ɓallashi tsabar ta kaici, yanzu kenan duk abinda sukayi sai yaje yana sanar da ƙanwarsa tsabar rainin hankali, to ko ita an faɗa masa bata da ƙannen ne, to Allah ya kawo shi gidan lafiya, ita kuma wannan ta nuna waje sai na yi maganinta bata san wacce ni ba. Haka ta zauna tana jiran shigowar sa.

Adam kuwa haka ya saka kayan Najib ya ɗauki motar Najib ɗin ya tafi gurin aiki, kasancewar Najib ɗin yau ba zai fita aiki ba saboda bashi da lafiya. Koda yaje gurin aikin yana ta tunanin halin da matar tasa ke ciki idan kuma ya tuna da cewar Kadija tana gidan sai hankalinsa ya kwanta. Yana aiki yana tunanin Allah yasa zuwan Kadija gidan yasa Ameera ta dawo asalin Ameeran sa, sosai halin da ta sauya yake damunsa daga jiya zuwa yau duk ya fita a haiyacinsa gashi yana son kiranta yaji halin da take ciki amma wayar tasa tana gida haka yaci gaba da aiki yana tunanin rikicin Ameera.

Ta kai minti ashirin a gurin kafin Baba mai gadi ya hango ta a kwance a gurin, hakan yasa ya nufo gurin da sauri domin yasan da shigar ta gidan. Cikin tashin hankali yake runtumawa Ameera kira bayan ganin jini ya wanke mata gaban fuska gaba ɗaya. Sosai yake kiran hajiyar tasa, jin bata amsawane yasa ya nufi ɗakinsa ya ɗebo ruwa a buta ya watsa mata,ai kuwa watsawa ɗaya ta ja wani dogon numfashi haɗi da buɗe ido. Daidai lokacin kuma wayarta ta fara neman ɗauki. Da sauri Baba mai gadi ya ɗaga haɗi da zaiyana halin da Kadijan ke ciki tun kafin ma yaji wanda ke kiran. Cikin tsananin tashin hankali Najib ya ke tambayar sa waye shi ɗin? kuma a wani guri suke? a rikice Baba mai gadi ya sanar da shi cewar shine mai gadin gidan Alhaji Adam kuma suna cikin gidan.

Ita kuwa Ameera ta na zaune ta haikince a Palo tana jiran shigowar sa sai taji Mai gadi na mata irin wannan kiran, far ko ta tsorata domin da ihuu ya kirata, har tayi nufin ta fita ta sauke masa buhun masifar dake cinta, amma tana buɗe ƙofar idon ta yayi gamo da aika-aikan da tayi , hakan yasa tayi saurin rufe ƙofar palon ta koma batare da mai gadin ya kula da itaba. Sosai ta tsotsa da ganin irin jinin da Kadijan ke fitarwa, zaunawa tayi tai shiru tana tunani, ko dai turata ɗin da tayi ne ta faɗi a kan ƙarfe, take jikinta yayi sanyi, amma har yanzu ƙasan zuciyarta zafi yake mata. Tana zaune a gurin har taji isowar ƙarar motar, ko bata leƙa ba tasan Najib ɗin ne yazo ya tafi da ita asibiti bata ko iya loƙowaba har suka bar gidan.

Misalin huɗu da rabi Adam ya turo ƙofar gidan haɗi da sallama yana wurga idanunsa cikin palon domin ganin ta ina zai hango ta. Ganin bai

2 / 18