faru. Take ta sanar masa da komai akan wai hanata zuwa gidan Ameera ya yi shine ita kuma taƙi. Sosai ran Abba ya ɓaci har ya na zubar da ƙwalla. Sosai yake tunanin halin da Ameera ta ke ci, komai a ce Ameera, Ameera dai yarinyar da kaf anguwar nan ake kwatance da ita wajan hakuri da natsuwa amma yanzu ta koma hk. Haka Abba ya tanadi lauya suka fara gabatar da Shari'a da dangin Nasiru.
Ihu ta ke yi tana riƙe cikin ta da yake murɗawa kamar zai fashe, sai faman kiran sunan Nana ta ke yi, ita kuma Nana da ke tsaye a kanta sai sannu take mata. Sosai Ameera ta fita a haiyacin ta, hakan yasa Nana ɗaukar waya ta kira Umma ta sanar mata da kamar fa aihuwa ce. Hakan yasa Umma faɗin ta kira mai gidan ta ta sanar da shi sai a kaita asibiti. Wani irin ihu da Ameera ta sake yasa Nana saurin ka shi wayar tana mata sannu.
Haura da Ɓultuwa kuwa suna gurin gyaran jiki da Adam ya kai su domin kuwa yau za'a ɗaura auran, hakan yasa Ɓultuwa tanai mi da ya basu kuɗi zasuyi gyara irin kitso da lalle da dai sauransu, shi kuma Adam ya ce zai kai su har gurin da a ke yin kitson, haka kuwa ya ɗauke su ya kai su sannan ya basu kuɗi yace su rika a hannunsa, sannan ya biya mai wankin kan.
Adam da yake gaban malam wanda za'a ɗaura auran dake gaban nasu kafin a zo kan nasa yaga wayarsa na ƙara, bai so ya ɗauka ba amma ganin Nana ƙanwar Ameera ya sa ya ɗaga ya na tambayar ta dalilin kiran. Nana ta sanar masa da cewar Ameera ce zata aihu. Ai tun kafin ta ƙara sa yaji irin ihun da ta ke yi. A hankali ya ce "Ina zuwa yanzu amma kafin nazo ki ɗauke ta ki kaita asibiti kafin na iso. Nana ta ce "Wallahi ba zan iya ba, kawai kazo yanzu. Adam ya dawo gurin Malam ya sanar da shi cewar har yaje ya dawo ko? Malam ya ce "Eh har ka dawo domin kaga ba'a ma fara wannan ba, sai dai karka daɗe ka dawo da wuri.
Ko da ya iso gidan Ameera ta gama fita a haiyacin ta, ta haɗa zufa kamar mai wanka. Lokacin da ya ganta sai da gabansa ya fadi, domin bai taɓa ganin yadda ake naƙuda ba. Sosai tsoron Allah ya ƙara kama shi yana jin ƙaunar mahaifiyarsa a ransa, nan take ya mata addu'a cikin ransa. Bai ankara ba yaji hawaye na zubowa daga idanunsa. Sosai ya ke kallon Ameera wancce take ta shure-shure kamar zata mutu, idanun ta sun tsaya, sai kiran sunan mutane ta ke yi harda sunan sa. Nana ce itama da sai yau ta taɓa ganin naƙuda ta fara kuka dan itama tsoro abun ya bata. Sun tsaya sai kallonta suke yi suna kuka sun kasa bata wani taimako duk jikin su ya mutu!. Adam ne yayi ta Maza ya zo kanta ya kamota da niyyar ɗagota amma ta sake kurma wani ihu ta na kiran sunan Allah. Lokaci ɗaya Adam ya ajiye ta kukan sa na kufcewa ya faɗin "Sannu honey Sannu, in sha Allah ba za ki ƙara aihuwa ba daga wannan I'm so sorry my Honey I love you so much please don't let! Sosai yake kuka ya rungumota jikinsa yana mata sannu. Lokaci ɗaya ya kamota ya ɗaga ta ya nufi Mota da ita, izuwa lokacin Ameera neman sumewa ta ke yi. Nana ta biyo shi da gudu ta na kuka, haka suka bar gidan cikin namijin gudu har suka isa asbinti. Lebo rom (ɗakin aihuwa) aka shiga da ita cikin sauri, da gaske Adam yazo zai shiga amma a ka tsayar da shi a kan ba'a shiga. Haka suka tsaya shida Nana a gurin suna safa da marwa. Nana ce ta tuna da kayan aihuwa hakan yasa ta tambaye shi. Shi ma sai yanzu ya tuna ya ce taje ɗakin Ameera ɗin ta kwaso komai. Ya ce "Kin iya tuƙa mota? Nana ta ce "A'a ban iya ba. Adam ya zaro kuɗi ya bata ya faɗa mata inda kayan su ke.
Wasa-wasa aihuwa har ƙarfe biyar babu alamar fitowar jariri. Sosai hankalin kowa ya tashi musamman Adam, ita kanta Nana duk ta fita a haiyacin ta, Umma sai kira ta ke tana tambayar an aihu? Misalin shida na yamma Allah yayi ikon sa, Ameera ta haifo jariranta guda biyu mace da namiji, sai dai ita uwar jini ya ɓalle mata. Sosai lokacin da Adam da Nana suka ji batun aihuwar suka yi murna, amma jin halin da uwar take yasa murna ta koma ciki.
Ɓangaren su Haura kuwa an daɗe da gama musu komai amma har yanzu Adam bai zoba, gashi basu da waya. Haka dai su kai ta jiran sa amma shiru, har ran Ɓultuwa ya fara ɓaci da irin wannan abun. Wasa-wasa har shida na yamma suna gurin, ga shi basu san sunan unguwar da su ke ɗin ba. Suna gurin har bakwai babu alamun Adam. Kawai sai suka tare mai keke napen ya kai su gurin da suke bara. Koda suka zo gurin sai suka fara tunanin abin yi, shiru Haura ta yi tana tuno sunan anguwar su Adam ɗin ranar da zata kai musu abinci asibiti. Da ƙyar ta iya tunawa hakan yasa suka tare mai keke napen again suka faɗa masa inda zai kai su. Suna isa suka sallamshi suka tako har zuwa ƙofar gidan. Sai dai ƙofar a rufe take. Haka suka samu gefe suka zauna suna jiran dawowarsa, basu kawo komai ba domin dama Adam ɗin yana rufe gidan yanzu tunda babu mai gadi.
Cikin yardar Allah aka tsayar da jinin sai dai ana buƙatar jinin da za'a saka mata domin ta zubar da jini sosai. Haka Adam ya kamata a ka kwashi jini leda biyu bayan gwajin da a kayi masa babu wata matsala a jinin nasa. Bayan an gama kwasar jinin nasa ne Adam ya ce da Nana taje gida gobe sai ta dawo. Taso tayi musu amma ganin yadda ya haɗe rai yasa ta kama hanya. Har zata ta fi ya ce "Dama kin tabbatar kin rufe min gidan ko? Nana ta amsa da "Eh na rufe.
Har asuba jinin bai gama shiga ba, a wannan lokacin Adam ne ya kifa kansa a bakin gadon bacci ya ɗauke shi kasancewar jiya bai samu rsintsawa ba. A cikin barccin yake mafarkin wani yazo zai raba shi da Ameera, hakan yasa yayi saurin buɗe ido ya sauke a kanta wancce take kwance tayi fari sosai, lokaci ɗaya yaji wani irin sonta na fusgarsa, ga wani irin natsuwa da yake jin ya samu yanzu.
Nana da Umma ne suka shigo ɗakin ɗauke da kayan abinci da ruwan zafi na yiwa baby's wanka, domin Nana ta sanar musu da cewar ta haifi tagwaye mace da namiji. Bayan sun shigo ɗakin ne Adam ya gaida Umma sannan ya ta shi daga gurin da yake. Ummu ta ce "Kaje gida ka watsa ruwa sai ka ɗan huta kafin ka dawo ko? Adam ya amsa da "Ok Umma. Ya fita ba domin zai iya mata musu ba, yana fita ya tuno a she fa bai sanarwa da kowa bafa. Nan take ya kira Najib bai ɗaga ba, ya kira Kadija kira ɗaya ta ɗaga haɗi da yin sallama. Adam ya amsa lokacin da yake shiga cikin motarsa. Kadija ta gaida shi tana jiran taji ya mata batun auran sa da zai yi jiya domin jinsa cikin farin ciki. Adam ya ce "Sister albishirin ki? Najib dake kusa da ita ya ja tsaki ya kawar da kai! Cikin ƙarfin hali ta ce "Goro Yaya na" ya ce "I'm a daddy now! Ya faɗa yana dariya. NAJIB da Kadija cike da rashin fahimta suka haɗa baki gurin ce wa "Me kake nufi? Sai a lokacin Najib ya kula da ya yayi magana. Shima Adam ɗin da makin jin muryar Najib ya ce "Ameera ta aihu ta haifi ƴan biyu yanzu haka muna asibiti. Yana faɗa ya kashe wayar yana dariya. Daidai lokacin ya karyo kwanan anguwar su. Tsayawa yayi a daidai get ɗin gidan sa، kana ganin sa kasan yana cikin farin ciki. Fitowa ya yi ya buɗe get ɗin sannan ya zo zai shiga motar domin shigar da ita ciki sai yaji an kira sunan sa cikin fu shi da ɓacin rai. Ɓultuwa ce ta ce "Adam yanzu dan Allah ka kyauta mamu da ka barmu muka kwana a waje? Tun jiya daga kaimu gurin wankin kai sai ka manta da mu, Allah dai yasa an ɗaura auran?....✍️
Comments dinku shine ƙwarin guiwa na.
One House
One love
Love all
Typing
S-Reza
*AMEERA DA ADAM*
_19_
*By S-REZA*
*Chapter1️⃣9️⃣*
...Ɓultuwa ta yi tambayar cike da nunu ɓacin ran da suke ci ki. Da sauri Adam ya juyo ya na bin su da kallon mamaki domin shi harga Allah ya manta da su. Haura ya kalla ya ga ta na wani cin magani sai kawai ya ce "Ku yi hakuri na manta ne, amma yanzu kuzo mu shiga ci ki. Haka Adam ya buɗe get ɗin suka shiga shima ya mara musu baya da motar ta sa. Su na shiga Ɓultuwa ta ce da Haura "Kinga yanzu ke matarsa ce, sabo da haka ki je ɗakin sa ki yi wanka idan yaso sai ku fara maganar kafin na zo, kar ki ji tsoron waccer matar ta sa domin yanzu duk ɗaya kuka kin ji dai ko? Haura ta amsa da kai. Hakan kuwa a kayi, ɗakin Adam ɗin ta shiga cikin sanɗa dukda tasan baya ciki amma sai ta tsinci kanta da fargaban aiwatar da hakan. Ta na shiga ta ga babu kowa a ciki, ga kuma ɗakin ba'a gyare yake ba kamar ma dai yau ba'a kwana a cikin sa ba. Haka ta shige toilet duk jikinta na rawa, ta na shiga ta fara cire kayan ta, sai da ta yi tsirara kafin ta sakar wa kanta ruwan sanyi ta na lumshe ido gami da sauke ajiyar zuciya ta na godiya ga Allah da yasa yau ta zama matar Adam.
Ya na shiga palon gidan nasa ya nufi ɗakin Ameera domin a ce ya ke so ya yi wanka, sai dai ya na shiga ya fito dalilin ganin ɗakin ba'a gyare ba, nasa ɗakin ya nufa cikin farin cikin yau ya zama baba. Ya na shiga ɗakin ya shiga cire kayan sa sai da ya gama yin zindir kafin ya tura ƙofar toilet ɗin ya shiga ɗauke da addu'ar shiga bayan gida ("A'uzu bika minal kubusu wal-kaba'isu)
Ɓangaren Malam kuwa ganin har zuwa lokacin Adam bai dawo ba ne ya sa ya ce "To ko wani zai karɓa masa wakilcin yarinyar a ɗaura suran ne?, sai kuma Malam ya tuna bai san sunan yarinyar ba. Haka dai akai ta jiran Adam amma shiru, ga kayan ɗaurin aure amma babu ango kuma babu wakilin sa, haka dole Malam ya bada haƙurin cewa ina ga dai ba lafiya ba ne. Haka kowa ya watse ba tare da ɗaurin auran ba.
Ya na shiga toilet ɗin Haura ta juyo a tsorace da lilin jin karatun da yayi, hakan yasa shima saurin tsorata dalilin da yasa suka haɗa goshi bata tare da kowa ya an kara ba. Ganin sa tsirara yasa Haura saurin juyawa ba tare da itama ta rufe komai daga jikinta ba. Shima Adam ɗin cikin tsoro da mamakin ganinta a cikin toilet ɗin sa ya sa ya yi kamar zai rusa ihu! Sai kawai bakinsa ya shiga furta "Inna'ilaihi wa inna'ilaihi raju'un! Ya na faɗa ya na kallon yadda ta juya masa baya, shima
sai neman shagala da kallon bayan ta da yaso yi, amma jin ya na ƙoƙarin kasa saita kansa ne ya sa ya juya ya fita daga toilet ɗin ba tare da ya biyewa ɗaya gada cikin zuciyar tasa dake angiza shi taɓa wani sashe na jikin ta ba. Ta na jin ya fita ta sauke a jiyar zuciya ta na ɗaura tawul da niyyar fitowa. Sai da ta fara leƙowa ta ga baya cikin ɗakin kafin ta fito da saur ta buɗe ƙofar zata fita shi kuma ya kama zai buɗe ya shigo. Ta na buɗewa suka ƙara cin karo har sai da tawul ɗin jikinta ya kunci, amma ta yi saurin taro kayan ta tsaya ta na kallon sa ganin sa shima ɗaure da tawul ya na kallonta da duk ta rikice. "Mai ya kawo ki cikin toilet dina yin wanka? Adam ya watsa mata tambayar ya na bin jikinta da ke rawa da kallo. Sai yanzu yake ƙara tunano lokacin da ya fara ganinta tsirara, sai yau da ya ƙara ganin ta. Jin ta yi shiru ne ya ƙara ce wa "Tambayar ki na ke" Haura ta ce "Wanka nazo yi saboda naga nima matarka ce yanzu shi ne kawai. Cikin ɗan mamaki ya ce "Mata kuma matar wa?! To ya kika zama matar ta wa? Lokaci ɗaya gaban Haura ya fadi domin ba yadda ya saba mata magana ya ke yi yanzu ba, wannan karan Adam ne a gaban ta. Ganin haka yasa kawai Ɓultuwa ta ke son gani domin ita tasan san abun yi. Hakan yasa ta raɓa ta jikin sa har suna gogar juna ta nufi ɗakin su. Ta na zuwa ta sanar da Ɓultuwa cewa ba'a fa ɗaura auran ba. "Cikin tashin hankali ta ce "Kamar ya ƙarya ne wallahi an ɗaura. Haura ta ƙara cewa "Babu alamar ma fa yasan da wani batun aure ma fa. Ɓultuwa ta kalli Haura ta ce "Ina ce dai ita shigiyar matar ta sa ta na cikin gidan? Haura ta amsa da "Babu alamar ta na cikin gidan, anya ma kuwa ba aihuwar ta yi ba. Da ƙarfi Ɓultuwa ta ce "Aihuwar uwarki! Wallahi ba zamu ga wannan baƙar ranar ba, ta ma isa ta aihu ban sa ni ba. Haura dai ta shiga sauya kaya cikin rawar jiki. Ita dai Ɓultuwa sai sake-sake da kwance-kwance ta ke. Idan har aihuwar Ameera ta yi kenan shikenan asirin ya tonu kenan, ita Haura zata san gaskiya, kuma mutanen garin Ƙaruk ma zasu gano ta. Sanin dukkanin sirrukanta ya dangana ne da aihuwar Ameera, lokaci ɗaya ta fara tunanin kashe Adam ɗin shi da Haura sai ta gudu, amma sai ta tabbatar da cewar Ameera ta aihu.
Ya na wanka ya na tunanin maganar Haura wai ta zama Matarsa, ko mai ta ke nufi ohoo! Bayan yayi wanka ya shirya ya fito daining tebul ya zauna ya na jiran fitowar Haura ta kawo masa abinci. Ya na zaune sai gata sun fito ita da Ɓultuwa sun nufo gurin sa. Sai da suka gaida shi kafin Haura ta shiga kicin ta kwaso abun da suka dafa ɗin. Haka suka shiga cikin abincin su uku ba tare da kowa ya ce komai ba, sai Adam da ke dana waya ya na murmushi! Ɓultuwa ce ta yi gyaran murya ta ce "Uhumm ahamm! Ya batun auran jinyan an ɗaura ko dai an ɗaga ne?. Adam ya kalleta domin maganar da ƙarfi ta yi. Adam da yake so sai ya gama cin abinci ya nai mi ƙarin haske sai kuma ga shi an hutar da shi. Ya ce "Wai wani aure kuke maga na a kai ne? Ban ga ne ba, munyi maganar aure da ku ne? Nan take Ɓultuwa ta rikice domin tabbas lissafi ya kwafce mata. Ta ce "Jiya kai ne ka kaimu gurin gyaran jiki ka ce zaka gurin ɗaurin aure idan ka dawo zaka zo ka ɗaukomu shi ne ba ka dawo ba. Da ƙarfi Adam ya bigi teburin abincin wanda sai da duk sauran abincin da ke gurin ya zube. Ya ce "Karna ƙara jin wannan banzar maganar domin ban san anyi haka ba, kuma ni na ɗauki Haura domin na taimaka mata ne, muddin na sake jin wannan zancen sai kunbar min gida, wannan wani irin shirme ne haka. Haka Adam ya bar gidan cikin tsananin ɓacin rai. Koda ya koma asbintin Ameera bata farka ba, sai kawai ya nufi gurin yaran ya na kallon su cikin so da ƙauna. A haka har Najib da kadija suka shigo ɗakin. Sosai Kadija ke murna ta na kallon yaran nata. Adam ya kalli Najib ya ce "Wai Kaji wani shirme da yarinyar nan dake aiki a gida na wai ni ne nai mata alƙawarin aure? Najib cike da mamaki ya ce "Eh ai gaskiya ne, nima nan kazo wai a lallai sai na mata wakilci, sabo da na ƙi ne yasa ka fara faɗa min baƙar magana. Adam ya ƙurawa Najib ido ya ce "Najib wallahi Allah ɗaya kenan ko? To na rantse da shi ban san aiyi duk wadannan abubuwan ba. Cike da mamaki Najib ya ce "Adam to wallahi ka kori mutanann daga gidan ka, idan ma taimakon zaka kai musu to karka barsu a kusa da kai. Haka dai Najib da Adam sai mamaki su ke yi.
Sosai dangi da abokan arziki ke ta tururuwar zuwa asibiti, sai dai har zuwa yanzu mai jego bata farka ba. Najib ya sanar da Kadija komai da Adam ya sanar masa, itama dai mamakin ta yi ta na faɗin wallhi sai an kore su ko baya so.
Ɓangaren kotu kuwa sosai shari'a ta yi zafi inda a ka yanke hukuncin dole sai Nana ta samu miji kafin a baiwa Nasiru duk dukiyar da ya ka she mata, sannan kuma Abba ya shigar da ƙarar babu ɗan su ba ƴarsa, ya ce ya na so a shiga tsakaninsu. Nan ta ke alƙali ya shiga tsakanin Nasiru da Nana kar wanda ya ƙara shiga samgar wani kwata-kwata. Da wannan ƙara ta ƙare. Sai dai kuma Nasiru da Nana da bazasu iya rayuwa babu ɗaya ba. Kwana uku da yi musu iyaka da