da tayi. Rigar tai mata kyau amma rashin iya sakawa yasa basu zauna mata da kyau ba. Cikin sanyin murya ta fara cewa "Keda wa kuka dafa wannan abincin? Haura ta ce "Ni ɗaya ce"
"A ina kaka samo ƙwai har kika yi amfani da shi?
"A kicin na samu, ai a kwai da yawa"
Ameera ta saki ajiyar zuciya ta ce "Yaya ma sunan garin ku?
Haura ta amsa da "Garuk"
"Kince ku ba musulmai bane ko? Haura ta ɗaga kai.
Ta ce "To kuna yin tsafi ne! Ko dai aljannune ku? Haura ta ce "A'a ba aljannu bane. Kuma bama... Kafin ta ƙara sa an turo ƙofar palon an shigo haɗi da sallama. Umma ce sai Nana a bayanta fuskokinsu babu sauƙin kallo ga mai laifi. Da sauri Ameera ta nufi Uama tata cikin fara'a da ɗoki tana ƙoƙarin rungume ta amma Umma ta daka mata tsawa tana faɗin "Sannu shaffiya da mai, wato dan tsabar rashin hankali da gidadanci irin naki sai da kika san ta yadda kika yi har kika raba wannan auran ko? Auran da ya rage wata ɗaya amma yazo kin haifar da tashin hankali a gidaje guda biyu, yanzu ga shi yazo wai dole sai an bashi kayan sa, shi kuma Abbanku yace sai ta samu wani kafin a ba shi kayan sa hakan ya haifar da faɗa harda manya a ciki kuma duk kece kika haɗa a wannan ban zar halayyar taki ta shirme wacce bamu san daga ina kika aro kika yafa ba.
Cike da mamaki Ameera ta ce "Ma sha Allah tunda an fasa auran yanzu kowa sai ya huta! Ta faɗa ki a jikin ta. Umma ta kai mata mari amma amma ta kauce ta ce "To Umma dan Allah kuma ku manta da lamarin wannan yaron wallhi ɗan iska ne, hannu fa ya ƙe riƙe mata a cikin mutane fisabililahi! Kuma ma ai indai faɗan Nana da Nasiru ne kowa yasan zasu shirya kawai ku barshi da kansa zai dawo idan har da gaske son nata yake ba iskanci ya kawo shi ba. Cike da takaici Umma ta ce "Allah dai ya wadai wallahi idan ma hannu ya riƙe mata sai ki fara zaginsa ba nasiha ba, haka ake gyara! To yanzu haka Abbanku yana police station duk a dalilin ki. Ameera ta ce "Police station dai? To a kan me?
"A kan ya ce ba zai bada kaya ba sai ƴarsa ta samu tsayayye ba.
"Cicin faɗa Ameera ta fara "Wallahi wannan mutanan basu da mutunci yanzu a kan kayan lefen da kwata-kwata guda nawa suke da sadakin da ya kawo shine zasu kai Abba police station, to wallhi basu isaba ni dama nasan wannan yaron ba ɗan arziki bane, wallhi ɗan iska ne. Cike da zafin zuciya da Nana ta gama ƙunsa a gurin yayar tata ta ce...
"Wai kina ta cewa ɗan isa, me yayi na is kanci ne? Saboda ya riƙe hannuna ne ko? Ta ci gaba da faɗin idan sabo da haka ne to ke lokacin da Adam ya ke nemanki meye bakuyi ba? Ina ce har kowa sai da yasa muku ido tsabar zallar iskanci da kuke yi, wacce irin runguma ce baya miki a gaban mu, ko kina ce mun manta ne, to a gurin ki na koya. Take Ameera ta fara masifa "Yanzu Umma a gaban ki yarinyar nan take faɗa min irin wannan maganar ko? Wato har raini ya shiga tsakanina da ke har haka ko, ni zaki wa sharri, to idan ma haka ne ai ni ya aureni dan uwarki. Umma ta ce "Gani nan uwar tata zage ni yadda kikeso. Haura dai abincinta ta ci sannan ta miƙe ta bar palon.
Sosai Nana ta furta abubuwan da ke ranta ita kuwa Umma bata hanata ba domin itama abun da Ameera ta yi ya ɓata mata rai sosai. A haka Umma ta bar gidan ita da Nana tana sanar mata kar ta ƙara shiga sabgar Nana da Nasiru ko da Allah yasa abun ya shiryu. Amma Ameera ta ce "In sha Allah ma ba zai shiryu ba. Hakan yasa itama ta yi fushi ko irin Allah ya tsare hanya ɗin nan ma ba tai musu ba bare ma aje ga batun rakiya. Suna tafiya ta dawo kan Haura ta sauke mata gaba ɗaya baƙin cikin da ta ƙusa, domin kuwa duka tai mata babu laifin fari bare na baƙi, dukda abubuwan kirkir da tai mata.
Haka suka cigaba da zama da Haura kullum cikin sabon abun mamaki take yi, har yanzu bata ƙara leƙewa asibiti gurin Adam ba haka bata kira su Umma taji a wani hali suke ba, ko da kuwa jin an saki Abba ne ko har yanzu yana ƙullen ne. Kullum kwanan duniya sai ta daki Haura duk da irin ƙoƙarin da take yi, komai na gidan itace amma kuskure ɗaya zata yi ta sha duka. Izuwa yanzu ta daina mamaki da lamarin Haura domin ta gene cewar su din matsafa ne.
Tana kwace a palo kan kujera tana karatun littafin da ta siya na Batul Mamun mai suna uwa uwa ce wanda labarin ya ɗauki hankalin ta sosai, sai murmushi take saki ta na sake juyawa dags kwancen da ta ke. Sosai take mamakin halin yaran innayo, ace yara mata kusan guda shida amma duk babu wacce take taimaka mata gashi kuma mazajensu masu hali.
Kwana huɗu kawai ta ɗan ƙara kumbura cikin ya ƙara fitowa ga ƴar ƙiba da ta yi. Sosai ya tsaya ya na ƙare mata kallo daga ƙofar ɗakin duk yayi kewaarta barinma cikin dake jikinta, hakan yasa lokacin da Najib ya ce su wuce gidansa ya ce a'a shi dai yana son zuwa yaga halin da matarsa ke ciki. A hankali ya isa saitin kanta yasunkuyo kusa da kunnenta ya ce "Honey I'm back" Zumbur ta meƙe har tana sakin wayar, ganin sa yasa ta saki tsaki ta na kawar da kanta. Cikin murmushi ya ce "Please Honey I miss you and my baby. Ya faɗa ya na son shafo cikin nata. Da sauri ta ture hannunsa ta na faɗin "Ba kai kace baka son ganinmu ba, kawai kaje ka zauna da su Kadija da abokinka tun da mu bamu da wani amfani a rayuwarka. Ta ƙara sa tana jin furicin da yayi tun a lokacin yana dawo mata sabo. Adam ya ce "I'm sorry honey ba haka nake nufi ba baki fahimce ni bane please I'm sorry.
Ya ƙara sa yana kamota ya haɗe jikinsu guri ɗaya. Take ta saki kukan kewarsa da tayi. Soyayyar Adam ta daban ce a cikin zuciyarta ita kadai tasan irin wahalar da tasha na rashin sa. Adam ya shiga shafa cikin nata yana faɗin I hop baby yana lafiya dai ko? Shiru ta yi tana ƙara lafewa a jikin sa. A hankali ta ce "Ya jikin naka ? Ta faɗa tana ɗagowa tana kallon gurin da ya warke sai tabo kawai. "I'm fine jiki yayi sauƙi sai godiyar Allah, ina fatan dai lafiya kike zaune da wannan ƴar aikin ko? Ameera ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Hakan yasa ya jata suka shiga cikin ɗakin yana riƙe da ita. Suna shiga toilet ya jata suka yi wanka tare sannan ya shafa mata mai itama ta shafa masa cike da farin ciki. Kayan ƴan boooll na Chelsea mai ruwan blue mai ɗauke da sunan Yokohama a gaban rigar suka saka, sai kuma bayan rigar mai ɗauke da sunan Hazard mai labba goma a baya kasancewar Adam na son mutumin. Sosai cikin nata ya ɗaga rigar har ma rigar na neman yi mata ka ɗan. Nan ya shiga ɗaukar su hotuna wanda sun kwana uku basu yi ba. Sosai Adam ya rungumota a jikin sa yana faɗin Ameera ta Adam ikon Allah! Ameera ta saki murmushi ta ce Adam na Ameera sai ikon Allah! Duk dariya sukayi domin tunawa da lokacin baya da sukayi. Nan take wasan ya sauya kowa ya shiga faranta wa ɗan uwansa, wanda kowa ya nunawa ɗan uwansa yanda yayi kewar ɗan uwansa. Adam sai saka mata albarka yake yi kamar ba gobe. Haka suka sake yin wani wanka suka ƙara saka irin kayan amma wannan karan masu ruwan kunun ɗorawa (yalo). Haka ya kamata suka fito Palo tana manne a jikin sa.
Koda suka iso sun samu Haura tana gyara palon hakan yasa ta gaisar da Adam haɗi da tambayarsa ya jiki. Adam ya amsa da sauƙi yana kallon yanda itama ta sauya sosai. Afil ya ce "Hony ke ce kika siya mata kaya ne? Ameera ta taɓe baki ta ce "Yaushe zan iya zama da tsama-tsama, ai ya zame mini dole na saya kafin ka dawo kar a kashe ni da tsami. Ya ce "God bless you my beautiful wife, kinyi ƙoƙari gaba ɗaya ma ni na manta ne da batun tafiyar, yanzu kalla yanda ta yi kyau ba kamar lokacin da tazo ba. Ameera ta kawar da kai tana faɗin "Kin gama abincin ne? Tayi tambayar duk da kuwa tasan abinci kamar ma ba girkawa a keyi a cikin gidan ba.
"Eh na gama tun ɗazu kafin Yallaɓai ya shigo" Bata ƙara cewa komai ba suka nufi gurin abincin. Nan Ameera ta zuba musu a flet ɗaya suka fara ci. Suna cikin ci ne Haura zata wuce wa ta kusa da su zata shiga kicin Adam ya bita da kallo. Sosai hankalin sa yayi gurinta wanda ya manta da cewar Ameera na kallonsa. Kallon gurin da yake kallo tayi sai taga Haura na tafiya, tsabar mamaki sai taga kamar tana karkaɗa masa ƴan ƙananan mazaunan ta ta ke yi! Take taji gabanta ya faɗi, lokaci ɗaya wasu banzayen tunani suka fara zuwar mata. Ɗan buka cokalinta tayi a cikin flet ɗin wanda hakan ya dawo da Adam daga kallon tv dan ya tafi. Bai san lokacin da ya furta "Kisa saka kaya "
Cike da mamaki Ameera ta ce "Wani kaya kuma zan saka?
Adam ya waske da faɗin kisa ke kaya mu je mu sayo abubuwan da babu a gidan, in yaso itama wacce yarinyar sai a ƙaro mata kayan ko? Ameera ta yi shiru tana kallonsa har sai da ya tsargu. "Lafiya dai wannan kallo Honey karfa ki hango muni na? Afili ta ce "Ka bari sai gobe yau bana jin daɗi sosai"
"To Allah ya kaimu lafiya matar Adam ita kaɗai babu ƙari" Kafin Ameera ta ce wani abu sai ga Haura ta sake fitowa daga kicin riƙe da flet ta nufo gurin da suka. Tun daga nesa ya kafeta da ido har bai san yana sakin murmushi ba. Shi tun lokacin da ya ganta tsirara to koda yaushe idan ya ganta to a haka yake ƙara kallonta, ga kuma dama ita bata saka hijabi gashi doguwar riga ce mara nauyi siririya a jikin. Ameera ta saci kallon Adam ai kuwa ta ga harda murmushi yake saki, sannan ta kalli Haura sai taga kamar itama murmushin take masa harda ma huro masa isa da su kanne ido ɗaya. Take Ameera ta ƙware tana ta famam tari! Hakan yasa Adam jawota jikinsa yana mata sannu. Haura kuma ganin haka tayi saurin ajiye abincin da ta kawo ta tsiyayo mata ruwa ta zo ta kusa da Adam tana miƙa masa ruwan ya bata. Lokacin da Adam zai karɓi ruwan sai taga kamar murmushi suke yi, sai taga ya riƙe hannunta ɗaya ya jawota jikinsa yana ƙoƙarin hade bakin nasu...✍️
*Comments dinku shine ƙwarin guiwa na. Kunga ana samun posting babu ɓats lokaci, so kuma ku daure kuna yin comments da shiring dan Allah ina yin ku .*
*One love*
*One house*
*Comment's*
*Shering please*
*Love my all fan's*
S *-REZA typing...✍️*
*AMEERA DA ADAM*
*9*
*By S-REZA*
*WHATTPAD*
*Salis M Reza*
*PAGE9️⃣*
.... Sunanta da Adam ya kira ne ya sa ta dawo hankalinta, sai wani zazzaro waje take yi kamar wata munafuka. "Sorry Karɓi ruwa ki sha Honey Please ki dinga cin abinci a hankali kinji? Adam ya faɗa ya na kai mata ruwan saitin bakinta. Babu musu ta karɓa ta kafa kai sai da ta shanye ruwan kafin ta fara sauke ajiyar zuciya ta na kallon Haura wacce tun ɗazu take fama da sannu-sannu. Ta shi ta yi daga gurin ta nufi ɗaki domin so take ta samu damar yin tunani. Sai da ta kusa shiga ɗakin sai ta juyo da nufin ganin yanayin da suke ciki. Ai kuwa ta na juyowa sai taga kamar Haura ta yi saurin sauƙa daga kan cinyer Adam ɗin ne, shi kuma taga kamar shima Adam ɗin gyara jikinsa ya ke yi. Haka ta shige ɗakin har zata zauna sai kuma ta fara leƙe daga cikin ɗakin kasancewar daga cikin ɗakinta ana iya hango wanda yake daining tebul.
Ta na leƙowa sai taga Adam ne kaɗai a zaune a gurin, afili ta furta "Muna fiki Allah yasa na kamaka da laifin cin amana ka gani, wai ma to me yake nufi ne!.
Adam kuwa sai da ya tsaya ya cika cikinsa sosai har yana tambayar Haura a ina ta iya girki har haka mai shegen daɗi. Ita kuwa sai ta yi murmushi ta ce "Babu wanda ya koya mata da kanta ta koya. Adam ya kalleta ya ce "Da kanki kuma? "Haura ta amsa da kai. Haka har ya gama lokacin itama ta gama cin nata ta koma ɗaki. Shima yana gamawa ɗakin nasa ya nufa amma sai yaji kamar Muryar mutane biyu a dakin Haura ɗin, hakan yasa ya nufi ɗakin cikin sanɗa. Ya na zuwa ya kara kunnen sa domin saurara, ya kai minti biyu bai ji komai ba hakan yasa ya fara shawarar buɗe ɗakin. A hankali ya tura ƙofar ɗakin yana leƙawa. Zaune ya hangota ta dafe kanta hawaye na zubowa daga cikin fararan idanunta, da a'lamar wanka zata shiga domin ɗaure take da wani ɗan ƙaramin tawul wanda tun ranar da Ameera ta ce ba'a fitowa wanka tsirara yasa ta fara ɗaurawa.
Da sauri Adam ya ƙara so gurin da take ya na tambayar lafiya? Da sauri Haura ta ɗago kai sai ga hawayen jini na fitowa daga idanunta ta. A ɗan tsorace Adam ya ce "Inna'ilaihi! Jini ne fa yake fitowa daga idon ki, ya faɗa yana ƙoƙarin komawa baya domin ya tsorata ainin. Da sauri ta fara goge jinin tana ƙaƙalo murmushi ta miƙe tsaye. Ai kuwa ta na miƙewa tawul ɗin ya kwance kafin ta tare shi ya dangane da ƙasa. Adam ƙamewa yayi agurin ya kasa kawar da kansa yayin da ita kuma Haura ta yi saurin shigewa toilet ta na barin tawul ɗin a gurin.
Sai a lokacin ya dawo hankalin sa ya sauke a jiyar zuciya yana juyawa ya bar ɗakin cike da rashin ƙwarin jiki.
Washegari ma kafin su ta shi Haura ta gama haɗa musu komai na kari, hakan yasa suna tashi daga barci suka nufo daining tebul ɗin suka zauna suna cin abincin cike da jin daɗin sa. Ameera ta ce "Honey zaka kaini gida yau idan ka dawo daga aiki sai ka biyo mudawo. Adam ya kalleta kafin ya ce "Kin ce yau zamu ƙarowa wannan yarinyar kaya ko kin manta ne? Ta ke ta ce "An fasa ƙaro mata kayan wanda ta samu ma ta gode. Adam ya ce "No ba za'a yi haka ba, idan na saukeki ni zan je na sayo mata kayan. Da ƙarfi Ameera ta ce "Na ce an fasa sayo mata kayan ko bakaji bane? Wai Adam me kake nufi ne da wannan yarinyar ne naga kana shishige mata da yawa fa, wallahi zaka yi mata sanadin barin wannan gidan.
Da mamaki Adam ya ce "Ina shige mata kuma? Haba honey me kike nufi da zantukanki, ashe baki yarda da ni ba har yanzu. "Eh! Wallahi ban yarda da kaiba in dai akan mace ne ban yarda da kai ba, kuma na faɗa maka karka kuskura ka ƙaro mata kaya, ni nasan kalan kayan da suka dace da ita. Adam dai bai ƙara cewa komai ba har ya kammala cin abincin sa kafin ya koma domin shirin tafiya aiki.
Cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin ƙananan kaya sai zuba uban ƙamshi yake yi kaman anyi ɓarin turare a jikin sa. Ya yi nufin shiga ɗakinta ya kirata amma ya hango Haura ta na goge-goge a palon hakan yasa ya nufo ɗaya daga cikin kujerun palon ya zauna yana kallon ta. Haura kuwa da tun zamansa ta kula da shi sai gaba ɗaya ta kasa sakewa da irin kallon da taga yana mata, ita ta kasa gane masa, haka abun da ya faru tsakanin su jiya ya ƙarasa taji kunya sosai, hakan yasa ta miƙe zata koma ciki idan ya fita ta dawo ta ci gaba. Amma taku ɗaya ta yi ta tsinkayo muryarsa yana kiran ta da kee. A ɗan tsorace ta amsa da "Umhum" Sai kuma ta tsaya tana kallon sa.
"Nan zaki zo. Ya faɗa da ɗan ƙarfi wanda yasa ta ɗago ta saci kallon fuskarsa. A hankali ta ce gani.
Sai da ya gama kallonta sama da ƙasa kafin ya ce "Kije ki shirya zamu fita dake yanzu, kuma karki ɓata mana lokaci. Haura ta ce "Tom" Ta na faɗa ta miƙe daga zaman da tayi a ƙasa tana barin gurin. Bata daɗe da shiga ba sai ga Ameera ta fito cikin shigar wani Les uban su, domin kallo ɗaya ka ɗai less ɗin ke buƙata a gane nauyin kuɗin sa. Ta sha kwalliya kamar ka sace ta ka gudu, ga cikinnan yayi turtsitsi a gaba. A hankali take sauƙowa tana ƙoƙarin yafa ɗan ƙaramin mayafin da ke hannunta fuskar nan tata a murtuƙe babu ko a lamar fara'a.
Tun