Ameera Da Adam Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Romance

Chapter   12 / 18

33K to 36K   out of 51.1K words

ban yarda da itaba ƙara ma da ta mutu. Ta na cikin haka taji ana ƙoƙarin buɗe dakin nata, hakan yasa ta dawo da kallonta izuwa gurin. Adam ne ya shigo yana tafiya a gwale kamar ɗan kaciya hakan yasa Ameera kafe shi da ido ta na son yin dariya, ganin yanda ya haɗe fuska ne yasa ta ƙara jin dariya ya zo mata, ai kuwa ta ke ta saki kayar ta harda tafa hannu ta na nuna shi. Adam kuwa ganin irin dariya da take yine yasa ya ƙara jin wani mugun haushin ta, haka ya shige toilet ba tare da ya tanka mata ba. Ya na shiga ta bishi ciki ta na dariya. Bai ce mata komai ba ya shiga cire kayan jikinsa ya juya mata baya amma da dawo ta gaban sa ta na kallon yanda suka koma kamar ta yara. Lokaci ɗaya ta ƙara sakin dariya harda faɗuwa. Sosai Adam ya kai chan sama mutuƙar ƙuluwa, amma a zabar da ya ke ji ba zai biye mata ba, shi dai hukuncin da ya yanke kawai shi zai aiwatar. Haka Amera ta ke ta faman dariya har ya yi wankansa bata damu da jiƙata da yayi ba, ganin ya kusa gama wankan ne yasa itama ta fara nata wankan ba tare da ta cire doguwar rigar jikinta ba.

Adam na fitowa ya saka doguwar jallabiya ba tare da ya saka wando ba, ya kwanta yana kallon sama yana addu'ar Allah yasa dai abun na sa su tashi kar su samu matsala. Ya na cikin haka yaji fitowar ta. Rintse ido ya yi yana jin wani faduwar gaba lokaci ɗaya, hakan yasa ya riƙe gefen zuciyarsa ya na salati. Ameera kuwa tun a cikin toilet ta gama shirya irin muguntar da zata masa badan komai ba sai domin taga yanda zai yi. Ta na fitowa daga ita sai tawul wanda girman cikinta bai sa ya ɗauru sosai ba. Ta na fitowa tazo gaban sa ta ce "Malam ina bukatar haƙkina a gurin ka yanzu.

Ita kanta da ta yi maganar taso ta yi dariya domin ganin irin kallon da yayi mata, amma ta dake ta na ƙoƙarin ɗaga rigarsa. Adam da ko magana baya jin zai iya yi ya ce "Idan kika taɓa ni Allah ya isa ban yafe ba. Adam ya faɗa kamar zai yi kuka tsabar takaice. Ameera ta ce "Ban gane Allah ya isa ni da hakkina ba, yo ta ina Allah ya isarka zata bini bayan Allah bai hana ba, kawai ka tashi ko na kwata da ƙarfi na. Ta ƙara sa ta na ɗaga rigar tasa. Idan da tasan irin azabar da yake ciki da tai masa uzuri amma ganin da gaske ta ke yasa Adam faɗin. "Dan Allah kiyi haƙuri. Ameera kuwa cike da mugunta ta ɗage rigar tana ƙara kallonsu tasa hannu ta taɓa, sai kuma ta kama da niyar jansu ko zasu tashi. Ai kuwa Adam ya kurma ihuu wanda yasa Ameera saurin sakin su tana kallon sa. Ganin haka yasa Ameera ƙara dawo da shi ta ce "Malam Allah fa sai na karbi hakkina. Ta ƙara kwantar da shi zata ƙara kamawa jin tana son kashe shi ne yasa Adam faɗin. Idan kika ƙara taɓawa wallahi a bakin auranki!. Kina karawa na sakeki. Ya na faɗa hawaye na zubowa daga idanun sa.

Da sauri Ameera ta miƙe tsaye ta saki dariya ta na faɗin, ai ko baka faɗa haka ba ma ba yi zan yi ba, to ina abun ya ke, dama ina so ne kawai na gani ko zasu iya tashi. Ta na faɗa ta nufi gurin kayanta ta ɗauko wata doguwar rigar irin ta jikinsa ta saka bata ko shafa komai ba sai turare, ta zo kusa da shi ta ce "Honey dan Allah ka ƙara ɗauko mana wata mai aikin please ni ba zan iya komai na gidan nan ba, idan yaso wannan karan ka samo mana tsohuwa kaji? Adam ya lumshe ido ya buɗe ya ce "Tom" Amera ta rungumo shi ta na kantar da kan ta a kan ƙirjinsa ta ce "Na gode Honey sannu Allah ya baka lafiya kaji. Ta faɗa cikin seriously.

Jin ta yi barci a jikinsa ne yasa ya tashi ya zauna ya na kallonta. Lokaci ɗaya hawaye suka wanke masa idanu idan ya tuno da cewar wai Amera ta Adam ɗin sa ce ta dawo haka, Ameera da bata ko iya ɗaga sautinta a kan nasa, Ameera da take son abin da yake so fiye da shi, Ameera da bata son ko damuwarsa amma wai ita ce yau take son kashe shi. Shi dai har yanzu bai yarda laulayin ciki ba ne wannan, wallahi wannan yafi ƙarfin laulayin ciki domin idan ya tuno abubuwan da ta yi sai ya ƙara tabbatar da cewar ba laulayin ciki be. Azuciyarsa ya ce "To me kenan? Sai kuma ya yi shiru ya na tunani. Shi dai yasan babu komai kuma babu alamar komai a tare da ita. Tashi ya yi ya koma waccen ɗakin ya ɗauki wayarsa ya kira Najib a kan yazo gidan yanzu, amma Najib ya sheda masa cewar baya gida yanzu kuma ba zai dawo ba sai dare ya bari kawai su haɗu gobe. Ya na sauke wayar tunanin Haura ya faɗo masa. Ya ce "Yarinyar kirki mai haƙuri Allah yasa ki dawo muna kewarki. Ya na faɗa ya tashi ya cire wannan doguwar rigar ya saka ƙananan kaya da wando gajere so yake ya kai karar Ameera gurin iyayenta domin susan halin da ake ciki. Ya na gama shiryawa ya fita daga gidan, amma ganin irin tafiyar da ya ke yi ne yasa dole ya dawo domin yasa tabbas kallo ɗaya za'a ai masa a gano a kwai wata damuwar. Kadija ya kira amma bata amsa ba sai kawai ya tura mata da saƙo akan ta saka shi a cikin addu'a.

Da yamma da kansa ya shiga cikin domin yasan ita kam ba shiga zata yi ba, shi kuma yunwa ya ke ji, hakan yasa ya shiga ya haɗa musu abinci mai sauƙi. Bai gama abincin ba har kusan an fara kiran magariba hakan yasa ya na jere abincin ya yayi wanka ya fita Masallaci. Kafin ya dawo itama ta ta shi ta kara yin wanka ta fito palo ta na hamma. Ganin abinci a jere yasa ta ja tsaki ta nufo gurin abincin ranta duk a jagule. Ta buɗe ta ga abin da ke ciki sai taji ita kawai ɗan wake ta ke son ci ba taliya ba, komawa ta yi ta daura alaula ta fara Sallah. Bai dawo ba sai da ya tsaya a ka idar da sallar isha. Ya na shigowa ya sameta zaune ta ta na jiransa. Ba tare da ya ce mata komai ba ya zauna ya buɗe abincin ya fara zubawa, ganin bai ce mata komai ba ne ta ce "Honey ya jikin baka?

Adam kaman yayi kuka dan takaici, yau she ya ce mata bai da lafiya, idan ma abun da take nufi ne ai ita ce sila. Bai ce komai ba ya ci gaba da zuba abincin sa. Sai ta ƙara ce wa "Honey ni me zan ci ne? Ta yi tambayar domin shima yasan bata son taliya.

Adam ya ɗaga kai ya mata kallo ɗaya sai yaga kamar ba fuskar Amearan sa ba tsabar haushin ta da ya ke ji. Ganin dai ba tamka mata zai yi ba ne ya sa ta ce "Wai ina ta magana ka min shiru, kai kasan ni ba wani damuwa na yi da wannan taliyar ba, kuma ka dafa duda kasan bana so, na zo ina maka magana kuma ka yi shiru?

Adam ya ce "Abun da na ke so na dafa kema zaki iya zuwa ki dafa abun da kike so. Ameera ta kalleshi ta ce..

"Ok tanan ka ɓullo kuma? To ni ɗan wake nake so ka dafa mini, please shi nake son ci. Ta faɗa cike da bada umarni. Adam ya ci ga ba da zuba abincin sa ba tare da ya ce komai ba. Ta ce "Ba ka ce komai ba fa?

Ya ce "Bazan iya ba"

"To me ka ke nufi da bazaka iya ba? Kenan haka zan kwanta banci komai ba?

Cikin tsananin bacin rai da wannan taƙura shi da ta yi Adam ya ce "Na ce ba zan iya dafa miki ɗan wake ba, idan kina so ki tashi ki yi kayan ki na gama magana. Ya faɗa cike da ƙunci da takaicin ta. Jin haka yasa Ameera faɗin...

"To wallahi ba ka isa ni na kwana banci abinci ba kai kuma ka ci, sai dai duk mu kwana a haka. Ta na faɗa ta ture kulan abincin ƙasa ta ɗauki wanda ya zuba a fleet ta ɓarar da wannan ɗin shima, sannan ta ce "Sai dai kowa ya kwana bai ci abinci ba a cikin gidan nan wallahi. Adam da rabon sa da abinci tun safe, tsabar yunwa har wani jiri-jiri yake ji. Kallonn kulan abincin ya yi ganin duk ya zube babu komai sai yaji kamar an cire masa duk wata laka ta jikinsa, lokaci ɗaya ya ji wani irin abu na ɓacin rai da bai taɓa jin irin ba ...✍️


_Comments ɗinku shine ƙwarin guwa na_


*One love*
*One House*
*Comment's*
*Shering please*
*Love all my fan's*
*S-Reza typing...*

AMEERA DA ADAM
14



By S-REZA

WHATTPAD
Salis M Reza




Chapter1️⃣4️⃣
... Tsabar ɓacin rai muryasa har rawa ta ke yi ya ce "Yanzu abincin da zan ci ɗin shine ki ka zubar Amera? "Ai muddin ka ce bazan ci abinci a gidan nan ba to sai dai kowa ya huta wallahi " Amera ta ƙarasa ta na miƙewa zata bar gurin. Adam ya ce "Haka kika ce ko? Ta juyo ta ce "Eh haka na ce babu wanda zai ci komai yau. Ta na faɗa ta ci gaba da tafiyar ta cike da jin haushin rashin dafa mata Ɗanwaken da take son ci. Sai da ta shige ɗakinta sannan Adam ya iya miƙewa daga gurin ya nufi ɗakinsa da niyar ɗaukar kin mota ya fita waje ya naimi abinci domin ba zai iya kwanciya bai ci abinci ba saboda wata iriyar mahaukaciyar yunwa da ya ke ji. Ɗan makulli kawai ya ɗauka sai ATM dinsa ya na tafiya ya na jin haryanzu jiri na ɗiban sa.

Sai da yazo bakin ƙofar palon ya ganta tsaye da makulli ta na masa wani irin kallo. Lokaci ɗaya gabansa ya faɗi domin bai tsammaci ganin ta a gurin ba. Bai ko iya mata magana ba shima ya tsaya ya na kallonta kamar yaga wata halittar. Kallon-kallo kawai suke wa juna kamar wasu abokan karawa. Shi Adam ya na kallonta ne cike da mamakin yadda a ka yi Ameerar sa ta dawo haka, domin ya lura wannan halittar da ke gabansa mai amsa sunan Amera wallahi kashe shi ta ke son yi, domin shi dai zai iya dafa Alqur'ani mai girma a kan cewar wannan ba Ameerar sa ba ce, kallonta yake yi sosai ya na son ya gano wata sheda da zata nuna masa cewar ba ita ɗin ba ce, amma babu alama sai wannan ƙaton cikin dake jikinta wanda izuwa yanzu babu abin da ya tsana kamar wannan munafikin cikin.

Ita kuma Ameera ta na mamakin ƙarfin halin sa ne ganin shi yaƙi ya dafa mata nata abincin amma shi ya zo zai fita ya je ya ci ita kuma ko ohoo ko! Dama ta yi wannan tunanin hakan ya sa ta na shiga ɗaki ta yi saurin ɗaukar kii ta fito domin tare shi. Sun kai kusan minti biyar a haka kafin Adam ya ce "Bani hanya zan wuce? "Babu inda zaka je na faɗa maka, idan kuma kana son fita to ka tsaya ka dafa min abin da na ce maka sai ka je duk inda kake so ka sayo abincin ka.

Adam yayi shiru ya na tunani. Baida ƙarfi a jikinsa badan haka ba da sai yai mata dukan raba raini kafin ya fita abinsa, ga kuma yunwa da ke ta kiɗan amaja a cikin sa, ga har yanzu gabansa zafi yake masa. Sa ke kallonta ya yi ya ce "Dan Allah wace ce ke? Cike da mamaki Ameera ta ce "Ban gane ba wai ni ka ke tambaya? Adam ya ce "Dan Allah ke wace ce? Mai nai miki kike son kashe ni? "Cike da takaici da mamaki ta ce "Wai ko ka fara shan ƙwayoyin gusar da tunani ne? Au wai kai dama kallon da ka ke min kenan? To ni ce dai Ameera wacce ka sani. Cikin rashin sanin abin yi Adam ya juya ya koma ɗaki harda hawaye. Sai da ya shiga ɗaki amma ya fito ya sameta har lokacin ta na Palo a zauna da alamar dai shi take fako, bai ce mata komai ba ya shige kicin ya tsaya ya na tunanin dame-dame ma a ke buƙata idan za'ayi Ɗanwake!

Ruwa ya fara ɗorawa sannan ya buɗe buhun fulawar da ko taɓawa ba'ayi ba, Nan take ya ɗaibi daidai da yanda ya ke tunanin zai masa, sai da ya juye a wata roba sannan ya zuba ruwa sai kuma ya fara tunanin anya ba'a zuba wani abu bayan fulawa? Shiru ya yi yana tunani, gashi kuma ya bar wayarsa a ɗaki kuma baya so Ameera ta taya shi Gashi yana bukatar sanin wani abun, shi tun da kaye bai taɓa ko gwada yin ɗanwake ba, bai ma san dame-dame ake buƙata ba. Kaman zai yi kuka ya shiga tunani, lokaci ɗaya Haura ta faɗo masa arai ya ce "Ina ma ta na nan! Ya daɗe a haka har ma ruwan ya fara zafi sai ya shiga dube-dube a cikin kicin ɗin, ganin babu sarki sai Allah ne yasa shi dole fita domin ɗauko wayarsa ya kira Kadija. Daidai zai fita ita kuma Ameera ganin ya daɗe a cikin ɗin sai ta biyo bayan sa ta gani ko ya fara yin ɗanwaken ne. A bakin ƙofar kicin ɗin suka haɗu ya wuce ba tare da ko yayi mata magana ba. Ita kuma ta ce "Ko ɗanwaken kake dafawa ne? Ta yi tambayar ta na shigewa ciki. Ɗakinsa ya shiga ya ɗauki wayarsa ya kira Kadija amma ba'a ɗaga ba, yana ƙara kira ta ɗaga ta na faɗin "Yayana na kaina barka da dare? "Lafiya alhamdu lillah ya jikin na ki? "Jiki da sauƙi "

"Ok please ina so na tambayeki ne cikin gaggawa "

"Ok Yaya ina sauraronka Allah yasa na sani"

"Adam ya ɗan sai ta muryasa ya ce "Please dan Allah ya ya ke haɗa ɗan wake?

Shiru Kadija ta yi ta na jin tausayin yayan nata domin tasan wannan aikin Ameera ne a wannan daran da kowa ke so ya huta amma ita ta wani haɗa shi da yin ɗanwake. Afili ta ce "Yaya bari yanzu na dafa sai Najib ya kawo maka kaji? Adam yayi ssurin cewa "No har fa na ƙwaɓa fulawar kawai ki sanar dani ɗin yanzu pls. Kadija ta ce "Ok zan turo maka yanzu ta message. Ta faɗa ta na kashe wayar Adam kuma ya nufo kicin ɗin yana yi yana duba wayar tasa.

Yanzu ma daidai zai shiga itama zata fito riƙe da kofi ɗauke da tii mai zafi. A hankali ta ce sannu da aiki domin ta yi mamakin ganin yanda ya daɗa ƙwaɓar ɗan waken bai yi ruwa ba kuma bayi tauri ba. Ba tare da ya tamka mata ba ya shige yana jin ƙarar saƙo a wayar tasa. Kafin ya buɗe ya kalli gurin da fulawar ta ke sai yaga an ƙwaɓa daidai yanda kawai sai dai a fara zubawa aruwa. Kallon hanyar waje yayi yana jin taikaicin taimaka masa da ta yi. Haka ya shiga jefa ɗanwaken har ya gama sannan ya soya man gyaɗa, dama sunada yaji mai daɗi a ajiye, lokaci ɗaya shina abin ya shiga ransa ga wani ƙamshi dake tashi daga cikin man da ya sha albasa, a gefe guda kuma ga ɗan ƴen tumatur da albasar da ya yanka, sai kuma soyayen naman da ke cikin firiza shima ya ƙara soyawa. Tun tana Palo ƙamshin man da na naman ya cika mata hanci, har wani leƙe take yi tana Allah-Allah ya fito ta fara kaiwa bakinta. Haka ya fito da gaba ɗaya abincin Palo sannan ya koma ya ɗauko mai da naman, sannan ya ƙara komawa ya ɗauko fleet da cokula masu yatsu. Sosai ya ke yin komai cikin sauri saboda yunwa da ke ta hautsuna halittun cikin sa. Sai da ya gama zubawa yana nufin miƙa mata amma tayi wani saurin fusge wa saura kaɗan ya zube ta na ce ko nasa ne. Ita kanta sai da taji kunyar abun da ta yi. Girgiza kai kawai Adam ya yi shima ya shiga haɗa nasa. Sai da ya gama zuba komai ya na ƙoƙarin ƙara yaji yaji tana faɗin ƙara min wannan yamin kaɗan.

Kafin ya ce komai ta ƙara ɗauke na gaban nasa domin kuwa ɗanwaken yayi mata daɗi sosai. Ta ce "Ai dama kai taliya zaka ci ko? To kawai ka bar min sauran gobe da safe zan ci, in yaso Kai yanzu sai ka shiga ka dafa taliyar ta ka yanzu ka ji? Ameera ta ƙara sa ta na rufe sauran ɗan wake dake ruwa a robar. Cike da mamaki Adam ya ce "Ban fahimta ba, yanzu kina nufin sai na ƙara shiga kicin nayi girki bayan ga wannan da yawa? Ameera ta ɗago kai baki ceke da ɗan wake ta ce "A'a dan Allah kar mu yi haka da kai! Kaifa ka ce taliya kake so ni kuma na ce ɗan wake kuma ni yanzu gashi ka min nawa ba sai kama ka yi

12 / 18