Ameera Da Adam Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  S Reza Category :  Romance

Chapter   3 / 18

6K to 9K   out of 51.1K words

ganta bane yasa shi nufar cikin ɗakinta yana kiran sunanta "Honey..."Honey. Daga cikin kicin yaji ta amsa da "Na'am Honey welcome back. Har ya juya zai nufi kicin ɗin ya hango wayarsa a gefen gado, hakan yasa ya je ya ɗauka ya nufi waje cike da mamakin sauyin matar tasa, yana tafiya yana godiya ga Kadija domin yasan itace ta lallasheta. Yana shiga palon ya ganta sai girki take yi ita kaɗai ta haɗa zufa. Yana shiga ya rungumota ta baya yana faɗin "Waye ya saki girki keda baki da lafiya Honey?

Murmushi tayi haɗi da cewa "Ni lafiya ta ƙalau kawai girki nake marmari kuma na gargajiya.

Adam ya ce "To me kike dafawa ne haka? Cikin ƙosawa ta ce

"Kaje waje idan ya ƙarasa zaka gani ai.

"A'a ai tunda Allah yasa na dawo baki gama ba to sai dai na tayaki mu ƙarasa. Adam ya faɗa yana ƙoƙarin zagayowa ta gabanta. Ita kuwa Ameera gaba ɗaya ma bata son ganinsa hakan yasa cikin masifar dake cinta da take ta dannewa ta ce

"To sai kazo ka dafa kai ɗaya haba mana dan Allah na ce Kaje waje yanzu zai ƙarasa kazo ka dameni to gama kicin ɗin nan ka dafa harda kanka. Tana faɗa ta bar masa palon cikin ɓacin rai. Shi kuwa Adam da sauri yabi bayanta yana bata haƙur a kan wallahi zai fita, ita kuwa jin haka yasa ta ce yayi wanka zai kaita sufa makert zata sayo abun sha domin duk irin wanda take so ɗin sun ƙare. Jin haka yasa shi amsawa da sauri ya shiga ɗaki domin yin wanka ita kuma ta koma kicin domin ƙarasa aikin nata.

Tun lokacin da Ameera taji fitar Najib da Kadija tasan asibiti zasu nufa, hakan yasa ta fita da sauri ta samu mai gadi taja masa kunne akan kar ya sake ya sanar da Adam komai, kuwa da wasa ya sake ya ji to sai ya bar aiki a gidan. Shi kuwa Baba mai gadi jin haka yasa ya riƙa bakinsa da hannu a lamar ya kulle bakinsa. Gurin da Kadijan ta ɓata da jini tasa mai gadin ya wanke sannan ta shiga ɗaki ta ɗauki wayar sa tasa a jirgi (plane mode) sannan ta shiga kicin domin yin girki.

Ko kafin ya fito daga wanka itama har ta gama girkin ta zuba a plas ta rufe ta jera su a dainin tebul sannan itama ta shiga ta ƙara shiryawa. Yana fitowa itama ta fito cikin shigar abaya baƙa ta yane kanta da mayafin a bayar sai kuma baƙar jaka mai shigen kayan sai taƙalmi ja mai irin adon duwatsun gaban abayar. Batayi kwalliyaba amma ta ɗan shafa hoda, sosai tayi kyau ga ƴar ramar da tayi ya ƙara fito da haskenta.

Shi kuma sanye yake da riga da wando flawa yad masu ruwan ganye, sai hula mai shigen kayan sosai shima yayi kyau dukda bai wani tsaya ya gyara kansa sosai ba. Kallo ɗaya tai masa ta kawar da kai ta nufi hanyar fita. Amma jin tambayar da yayi mata ne yasa hantar cikinta kaɗawa. " Wai ni Kadija har ta tafi ne daga zuwanta? Duk da razanar da tayi bai hanata dakewa ta ce "Eh ai bata dade ba ta juya wai tana sauri. Ta faɗi maganar hankalinta a kwance kamar batayi komai ba. Adam ya ce "Ok ai ina shigowa gidanan daga irin tarɓar da na samu nasan sister tazo gidanan. Ya faɗa daidai lokacin da ya ɓude mata motar ta shiga shi kuma ya zagayo ɓangaren direba ya shaga yana cigaba da yabon sister ɗin tasa. Ita kuwa Ameera ƙara ɓaci ranta keyi jin da gaske dai gulma ya kai mata shine yasa tazo. Sai yanzu ma take jin daɗin abun da ya faru da Kadijan Allah ma ya ƙara maganin masu gulma, sai yanzu ma take jin bata tsoron ya sani domin ko ya sani ai maganin magulmaciya tayi. Ganin ya ɗauko wayarsa zai sa a caji ne yasa ta kalli wayar taga har yazu a jirgi take hakan yasa taji daɗin cewar babu yanda za'ayi ya sani har sai gobe dan uban magulmaciya. Sosai ta cika tayi fam a cikin motar jin yadda yake ci gaba da yabon kirkin sister ɗin tasa jin yaƙi dainawa ne yasa ta ce "Wai dan Allah ko dai mu koma ne kaje ka ɗauko wannan kadijar sai kaci gaba da mata godiyar ne, haba dan Allah ni kazo ka dameni kamar wani kai ne kaɗai mai ƙanwa. Jin haka yasa Adam yin shiru yana kallonta ganin tana ƙara ɓata rai.

Bayan sun shiga sun maga sayan komai da take buƙata ne sun zo hanyar fita daga cikin supar makert ɗin sai ledar hannun wata ƙaramar yarinya ya suɓuce daga hannun yarinyar bai tsaya a ko ina ba sai a ƙafar Ameera, take ledar ta wargaje kayan ciki suka watse wanda Ameera ta je taka gurin da ake sauƙa, sai kawai bata ankaraba ta taka gwanganin matar ai kuwa sai ji kayi tayi sama ta dawo tim a kan gurin. Da ƙarfi ta saki iho wanda kowa na gurin saida ya tsaya yana kallonta. Da sauri Adam ya iso gareta yana mata sannu ya ɗagota tana kuka wurjanjan domin kuwa ta bugu. Kuka take yi tana kallon gurin da yarinyar ke tsaye da uwarta ko irin su zo domin ɗagata ma babu wacce tayi. Ai kuwa cikin ɓacin rai da zafin ciwo yasa tana tashi ta nufi gurin da yarinyar take babu wata-wata ta ɗauke ta da mari hanu bibbiyu. Tana kuka tana marin yarinyar a gaban uwarta, wacce hakan yasa itama yarinyar rushewa da kuka, Amera na kuka yarinyar ma tana kuka. Uwar yarinyar ce tayi kan Ameera domin ramawa ƴarta amma Adam yayi saurin shiga tsakiya yana baiwa mata hakuri. Ita kuma Ameera baki yaƙi mutuwa sai zagin uwar yarinyar take yi, itama uwar yarinyar na ramawa kamar zasu buɗa. Ganin haka yasa Adam juyawa ga Ameera ya ce "Wai wannan wani masifane ina miki magana amma bazaki saurareni ba. Amma Ameera sai ƙundumawa uwar yarinyar asher take yi. Uwar yarinyar ta ciro wayarta da ke ruri ta ɗaga ta na ɗagawa ta ce "Abban Hanifah ka shigo ciki wata mara kunya ce ta bari Hanifah. Ta na faɗa ta sauke wayar tana jin yadda Ameera ke cigaba da kutuntumu zagi kala-kala tana surfa mata. Babu yadda Adam baiyi da itaba amma taƙi yin shiru ƙarshe shima ta shiga surfa masa nasa masifar tana faɗin "Kana kallo zata kasheni baza kace komai ba sai ni da nazo ƙwatarwa kaina ƴanci shine zakace na yi shiru to wallahi baka isa ba idan ma bakinku a haɗe yake to nafi ƙarfi ku, Banza mara kishin matarsa kawai. Yau kam iya kunya Adam ya gama jin kunya jin irin zagin da take masa a cikin mutane.

Ana cikin haka sai ga wani gurjejen mutum sanye da rigar sojoji yana zuwa ya nufin gurin yarinyar da suka kira da Hanifah ya na zuwa ya rungumota ya fara lallasheta haɗi da tambayar waye ya taɓata kuma mai ya faru. Ai kafin yarinyar ta fara magana uwar yarinyar ta kwashe ƙarya da gaskiya ta sanar masa harda cewa wai ita da mijinta ne suka daki Hanifah itama harda zabga mata mari sannan ta rushe da kuka tana riƙe ƙunci. Ai kuwa wannan sojan jin haka yasa ya na juyawa ya ɗauke Adam da wani lafiyayyen mari ya riƙe kwalar rigarsa ya dinga zabga masa naushi, dukansa yake yi yana ihu yana ƙara masa, ita kuwa Ameera ganin haka yasa da gudu ta nufi gurin motarsu ta shiga, amma ganin kamar za'a biyota ne yasa ta fita daga motar ta tare mai a daidaita ta shiga ta bar gurin gaba ɗaya. Sai da wannan sojan yayi wa Adam ɗan banzan duka wanda har sai da bakinsa da hancinsa suka fitar da jini kafin ya barshi yana tambayar matartasa ina ita matar mutumin take. Nan suka naimi Ameera sama da ƙasa basu ganta ba, sannan sojan ya kalli Adam ya ce "Daga yau ka ƙara dukan matar wani dan ubanka idan baka da hankali, yana faɗa ya ƙara takurinsa a ruwan cikinsa sannan ya kama hannun matarsa da ƴarsa suka bar gurin.

Sai da ya bar gurin kafin mutane suka zo da sauri suka ɗaga Adam ɗin dake ta zubar da jini ta baki da hanci. Sosai ya daku ko tsayuwa ma baya iya yi, hakan yasa suka saka shi a mota suka nufi asibiti...✍️

Kubi S-Reza a hankali labarin na daban ne.


*Whatppad*
Salis m Reza


*One love💘*
*One house🥰*
*Comment's🤝*
*Shering please👏*
*Love my all fan's😍*
*S-REZA typing...✍️*

_*AMEERA DA ADAM*_



*(By S-REZA✍️)*



*First class writer's asoo..*



3️⃣
...Ɓangaren su Kadija suna isa asibitin suka samu taimakon gaggawa kasancewar har zuwa lokacin da suka isa bata farka ba. Shi dai Najib ya na ta mamakin abun da ya samu matar tasa, tsabar tashin hankali ma bai ko tsaya ya tambayi mai gadin abun da ya faru ba. Ya kai kaman awa ɗaya a tsaye yara jira kafin wata daga cikin likitocin ta fito ta kira shi. Ko da ya iso sun gama shiryata an saka mata bandeji agurin sannan an saka mata ruwa ta na barcin wahala. Kallo ɗaya yayi mata yaga yanda ta rame ga kuma a lamar rashin jini a jikinta domin kallo ɗaya za kai mata kaga tayi fari. Nan likitan ta sanar masa akan za'a ƙara mata jini bayan ta farka, kasancewar jininsa group O ne yasa ya je a ka ɗiba a nasa. Bayan an gama ne ya fito yana son kiran Adam domin sanar da shi halin da ake keci ganin har lokacin bai ga Ameera ko Adam ɗin ba. Haka ya kira numbar Adam ɗin amma ba'a ɗagawa ya masa kira har sau huɗu amma babu amsa, hakan yasa ya bari zuwa an jima. Ko da ya koma ɗakin da Kadijan take kwance ya ga har yanzu barci take yi sai kawai ya fita izuwa masallaci. Ko da ya dawo ya sake kiran Adam amma yazu yaji number a kashe, sosai yanzu abun ya fara bashi tsoro. Sai yanzu kuma ya tuna cewar Adam fa a gida ya bar wayarsa, har ya yanke shawarar zuwa gurin aikin Adam ɗin amma yayi tunanin kar kuma ya tafi ita kuma Kadijan ta farka baya nan, hakan ne ma yasa ya zauna har sai ta tashi ta sanar tashi abun da ya faru.

Koda mai keken ya sauketa bata tsaya bashi guɗi ba tayi hanyar shiga gida da gudu, tana zuwa ta tura ƙaramin get ɗin ta shege ciki da gudunta. Mai keke kuwa ganin haka yasa ya biyo bayan ta yana masifar bata isa ba wallahi. Mai gadi dake zaune yaga ta wuje da gudu ya bita da mamaki baki a sake yana ganin ikon Allah na sauya rayuwar wannan baiwar Allahn cikin lokaci kaɗan. Yana cikin mamakin yaga mai keken ya shigo har cikin gidan yana zage-zage. Mai gadi ya tare shi yana tambayar sa. Nan mai ɗan sahu ya sanar da shi cewar kuɗi zata bashi. Dama a kwai sauran canjin kuɗinta a gurin mai gadin na ƙosan ɗazu hakan yasa ya tambaye shi nawa ne kuɗin sai ya cira ya ba shi. Ita kuwa Ameera ta na shiga palon ta fara sauke ajiyar zuciya ta cire ɗan kwalin a bayar da ke kanta sannan ta samu guri ta zauna tana riƙe bayanta gurin da ta bugu. Firiza ta nufa domin ɗau kan ruwa mai sanyi sai taga frizan a dungware a ƙasa socket ɗin ma baya jikin wuta, ga kuma babu komai a ciki, sai yanzu ta tuna da cewar a shefa kayan freza ɗin suka tafi sayowa. Komawa ta yi ta zauna ta ciro wayarta ta latsa kiran numbar Honey, amma taji wayar a kashe, sai ta tuna da cewar a she fa ita ce ta ka she masa wayar. Sai kuma tunanin Kadija ya faɗo mata kasancewar saboda su Kadijan ta kashe wayar. Afili ta furta "Oo ni Allah na Ameera me yake faruwa da ni ne! Yanzu fa sai ace wannan duk laifinane bayan kuma ni duk ba laifina bane. Sai kuma ta miƙe tsaye ta fara ƙoƙarin kuka tana kiran sunan Adam.

"Allah dai yasa Honey ya ƙwace ya gudu daga hannun wannan mugun, Allah yasa bai ji masa ciwo ba, waiyo ni Allah Honey na mai ya kaika faɗa da sojoji! Sosai kuka ya kufuce mata tana yi tana kiran sunan Honey ganin kukan ba zai kaita bane yasa ta fita waje da sauri sai kuma ta dawo ta ƙara surar jakarta da ɗan kwalin ta har ta kusa isa ƙofar waje sai kuma ta dawo da baya ta zauna ta dafe bayanta da yake mata wani ciwo. A fili ta ce "Allah ya isa tsakanina da wannan Hanifah ɗin shegiyar yarinyar, kimin laifi amma saboda ubanki soja ne sai kawai baza'a hukunta ki ba, ai kuwa wallahi ƙaryane sai dai idan ba Ameera kika taɓo ba. Ta shi tayi ta leƙa wajen cikin gidan ta ƙwaɗawa mai gadi kira, bayan yazo ta sa ya kwashe abincin da tayi tace yaje ya cinye. Da murna mai gadi ya kwashe abincin ya fita da shi ya na godiya. Ɗaki ta koma da niyyar sake wanka tayi alaula kafin Honey ya dawo ganin magrib na dosowa.

Ɓangaren Adam kuwa ana zuwa da shi asibiti bai ko yarda an kwantar da shi ba ana gama wanke masa ciwon bakinsa ya sallamesu ya fito daga asibitin bayan sun rubuta masa magungunan da zai siya, sai da ya biya ya sayi maganin kafin ya koma ya ɗauki motarsa ya nufi hanyar gida. Yana cikin tafiya ya ɗauki wayarsa domin kiran Najib yana danna kiran sai yaga kiran ya dawo. Sai da ya duba yaga wayar a jirgi. Sosai yayi mamakin hakan domin dai shi da kansa bai sa wayarsa a jirgi ba, Nan take Ameera ta faɗo masa, girgiza kai kawai yayi yana kiran numbar Najib ɗin bayan ya cire wayar daga jirgin.

Tana shiga Najib ya ce "Hello Adam"

shima ta ɗaya bangaren ya amsa da cewar "Kana gida ne? Cikin ɗacin rai da ɓacin ran da Najib ɗin ke ciki dalilin jin duk abinda ya faru daga gurin Kadija ya ce "Wallahi Adam ka bani mamaki, wato saboda kar ma na kiraka na sanar da kai abinda matarka taiwa Matana shine ka kashe waya, kuma tsabary rainin hankali kana iya kirana ka tambaye ni wai muna gidane ko? To kaje gida ka ajiye mini motana kuma wallahi ka sani ba zan bar wannan cin mutuncin ba, ko mai ina za'a je sai dai aje. Yana faɗa ya kashe wayarsa yana jin wani ɓacin rai ganin irin halin da matar tasa ke t. Tsabar masifar dake cinsa ma har ya manta da cewar matar tasa ƙanwar Adam ɗin ce.

Cikin tsananin mamaki Adam yake sauraron abokin nasa jin abun da yake cewa, jin ya kashe wayar ne yasa ya fara salamulai a fili ya na cewa "Innalillahi wa Innalillahi raji'un! Meye Najib ya ke faɗa ne, wai Amera ce ta daki Kadija ko meye. Nan dai ya shiga kiran sa amma a kashe, haka ya nemo numbar Kadija itama a kashe, take hankalinsa ya ƙara tashi gabansa yana faɗuwa, domin tun da yaji muryar Najib a haka to yasan ransa ya ɓaci sosai. Gidan su Najib ɗin ya fara zuwa amma mai gida ya sanar da shi ai tun safe da hajiya Kadija ta fita shima Najib yabi bayanta basu dawo ba. Motar ya bari a gidan sannan ya nufi gidan sa cikin ɓacin rai yana jin yau sai ya ɓata wa Ameera rai, dan tsabar bala'i ma a ƙafa ya taka har zuwa cikin gidan

Ko da ya tura get ɗin ya shiga sai yaci karo da mai gadi ya saka kulolin abinci a gaba yayi tagumi yana kallon cikin babbar kular kamar zaiyi kuka. Yaso ya wuce ciki amma ya ƙarasa gurin mai gadin yana tambayar sa Amera ta dawo ne? A tsorace mai gadin ya dawo hankalinsa yana miƙewa yana masa barka da zuwa cikin yanayin tsoron yanayin da ya tarar da shi.

"Eh Hajiya ta dawo tun ɗazu tana ciki ma yanzu haka"

Har Adam ɗin zai huce sai kuma ya dawo da baya yana kallon cikin kular abincin da kyau ganin abun da ke ciki. Ɗan wake ne a kayi amma ya dame ya zama kamar ƙullun tuwo, ko kyawun gani babu. Lokaci ɗaya Adam ya gane cewar abincin da tayi ne ɗazu kafin su fita. Zai magana mai gadi ya ce "Mai gida hatsari kayi ne? To Allah ya kiyaye gaba ya tsare tsau-tsayi da a'sara. Adam ya amsa da Amin yana nufar cikin gidan.

Ransa a ɓace ya tura ƙofar palon gidan nasa yana ƙoƙarin danne zuciyarsa akan abun da take saƙa masa game da matar tasa. Yana shiga ya fara kiranan sunanta cikin kakkausar murya. "Ameera "Ameera. Kafin ya rufe baki sai ji yayi an rungume shi ta baya tana faɗin. "Sannu da dawowa Honey ya jikin ina dai fatan lafiya kake ko Honey mai sukai maka? Ta dinga jero masa tambayoyi kamar zata yi kuka domin kuwa tun lokacin da ta dawo ta kasa sakuni sai kaiwa da komowa take yi tana jiran ya dawo duk ta damu. Cikin ɓacin rai ya ce "Bana son zancen banza Ameera me ya haɗaki da kadija ɗazu da tazo? Yayi tambayar cikin ihu da ta kaicin abun .

Ai kuwa Ameera jin haka sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinsa da kyau ta fara faɗin. Ni ina gida ina tunanin halin da kake ciki duk na kasa sakuni amma ka shigo kana mini ihu harda kiran sunana da

3 / 18