ASHE ZAMUGA JUNA

Author :  MRS ISHAM Category :  Love

Chapter   29 / 33

84K to 87K   out of 97.2K words

wadace ba, hatta golding eye balls din seda suka ɗan canza kala.

Idanunsu ne ya sarke cikin na juna.bakaramin tsorata ta yi ba da ganin idonsa ga kuma irin kallon da yake mata,babu abinda take tunawa irin rabuwar da sukayi daren jiya ga shi yanzu ta kawo kanta da kanta.

Shi kuma kallon da yake mata,kallon me yakawo ki dakina har kan gado na.

Hannunsa yasa ka ya rike ta gam yanda bazata samu damar guduwa ba,tana kwance akan kirjinsa, fuskarsu na fuskantar na juna.

Bude baki ya yi ze yi magana,tsoron jin abinda ze furta mata ne yasa da sauri,tasa yatsan ta,guda daya ta daura akan libs din sa.tana kallon cikin idanunsa,saukar da idonsa ya yi ya kalli hannunta da ta daura masa akan libs,watsa mata harara ya yi,duk da hakan bata cire ba.

"Ya Taj,an ce ne in zo in tasheka zamu je asibi.....".

Wani mugun kallo ya watsa mata da ya sa ta gagara karasa maganar da take masa.

Hannu yasa ya janye yatsan nata ya maida shi baya ya matse, ƙara ta sa sakamakon zafin da taji ya ziyarci hannunta.

"Kirana kika zo yi shine se kin hau har kan gado na!?"ya tambaye ta murya a narke ba kamar yanda ya saba yin magana ba.

"To ai na baka hakuri"ta faɗa tana murguɗa masa baƙi,tsurawa dan karamin baƙin nata da take murguɗawa ido ya yi,yana jin kamar yasa almakashi ya gimtse sa.

"Tashi a jikina,wato kinga farar fata, mekyau yana shining, shine za ki kwanta akai,yafi na wa'yannan nan kazaman yan iskan samarin naki".tura baƙi ta yi jin abinda ya faɗa.

"Bazaki tashi min a jiki bane,ko se na yi wurgi dake tukun nan!?"ya faɗa yana jefa mata harara.

Kamar zata fashe da kuka dan takaici,ta ce"to ka sa'ke ni mana".

Kura mata ido ya yi,yaga yanda ta ke mutsu_mutsun kwatar kanta.da hannunsa guda daya ya rike ta amma ta gagara kwacewa.

"Meye kike shiryawa!?"kamar saukar aradu haka taji tambayar ya sauka a kunnenta,dago idonta ta yi,cikin tashin hankali,murya na rawa ta ce"bangane abinda kake nufi ba".

Murmushin gefen baki ya yi irin na bakida hankali, ya ce"ina saurayin naki yake!?,ina guje miki yin aikin danasani saboda rashin sanar da ni inda yake dede yake da jefa rayuwar ki, cikin hatsari,ni rayuwata,na ƙasa ta ce,in na mutu nayi shahada,amma ke in mutum daya ya mutu ta dalilin ki,to se Allah yabiwa wannan bawan nasa hakkinsa,je kiyi tunani akai".gaba daya ya kashe mata jiki da maganganunsa,kenan hakan yana nufin ya san tayi waya da Fu'ad kenan?,taya akayi ya san abinda suke shiryawa.

Meye hakan yake nufi to, Fu'ad ya sanar da ita cewa LTG shine yake kokarin zaluntar al'umma,shi kuma LTG ya ce mata,in mutum daya ya mutu ta dalilinta se Allah yabiwa wannan bawan nasa hakkinsa.

Har ya sa'ke ta bata ma sani ba,ta faɗa duniyar tunani.

Ɗagata ya yi a jikinsa ya tashi zaune ya barta akan gadon,miƙewa tsaye ta yi,jiki a mace.

"Kai ma ai zaluntar al'umma ka ke kokarin yi,ka kuma cutar da ni,da yar uwata".

Be kalli inda take tsaye ba ya bata amsa da.

"Ke ba ki kai matsayin da zan tsaya ina miki bayani ba,je ki yi duk yanda kika gadama".

Da gudu ta fice a dakin,tana gudu numfashinta na sauka da sauri sauri,kirjinta ya rike,sun sa ta a tsaka me wuya,yanzu da maganar waye a cikin su tasan zata yi amfani?.

Bayan balcony ta je in da babu wanda ze ganta,ta zube akan guiwowinta tana maida numfarfashi.

Se da ta kusa 20minute a haka kafin ta samu nutsuwa.

"Ko ma me ze faru sede ya faru amma bazan taɓa juyawa Fu'ad baya ba, wannan alfarma ne da ya nema a wajena taya zan watsa mishi kasa a ido in ƙi cika masa burinsa na son ganin al'umma tasamu zaman lafiya".

Ita kadai take magana kamar wata zautacciya.

Se da ta gama samun nutsuwa kafin ta mike ta koma main part Sudais, yana ganinta ya ce"Sabriyah ai na kika tsaya ne!?,ina LTG?"jiki ba kuzari ta ce "ya ce wai baze je ba".

Gyada mata kai ya yi.

Shiga motar sukayi suka wuce asibitin.

shigowar su dakin da aka kwantar da Asmita sun samu ta na jingine da filo.Saghar na gefenta ga kuma fruit agabanta,tasha kadan ta bari,jin sallamar su ne yasa suka maida idonsu baƙin kofar.

Mamaki da al'ajabi lokaci daya ya kama Sabriyah ganin Asmita kwance akan gado ga kanta dake nade da bandage,da gudu ta shigo dakin,ta zauna akan gado, bata gajiya da kallon Asmita da itama din ita take kallo.wato wayo sukayi mata,su ka dinga ce mata Asmita na hutawa,ashe basa son tasan an yi aikin ne.

"My Jerry yaushe akayi miki aikin?,yanzu ya kike jin ki!?,me yake miki ciwo yanzu!?, sannu kinji".ta watso mata tambayoyi ba tare da ta bata damar amsa mata ko daya ba ta sa'ke cewa.

"My Jerry,kanki ba ya Miki ciwo ko!?"murmushi kaɗan Asmita ta yi.

Murya na fita a hankali ta bata amsa da.

"My Tom ina lafiya".

Zata sake yin wata maganar Saghar ya dakatar da ita ta hanyar faɗin.

"Ba'a son ta dinga magana sosai".

Gyada masa kai ta yi tana riƙe hannun Asmita.

Sannu su kayi mata da jiki kafin suka zauna suna.

Har karfe hudu na yamma suna tare a asibiti mazan kuma sun tafi wajen aikinsu.

Kullum se sunje asibiti duba jikin Asmita, Alhamdulillah jikinta yana sauki sosai, Sabriyah ta fara zuwa school an sa ta a jss 2,an samo malamin da yake koya mata karatun addini a gida,kuma ba laifi tana ganewa sosai da sosai.in ta dawo gida kuma su Parsa haka suke haɗuwa su sa'ke koya mata duk wani abinda bata gane ba,sune malaman lessions din ta.

Bayan wata daya, abubuwa da dama sun faru,mom Rumanatu ita da yaranta sun koma katsina.an sallamo Asmita daga asibiti jikinta ya yi sauki,har ta fara maida kibanta,sunci gaba da zuwa makaranta tare da Sabriyah sun yi kyau sosai sunyi fresh sun zama yan gida su ma,duk abinda za'a yiwa su Rameesa tare ake yi musu.kullum se ta yi waya da Fu'ad idan ta tabbatar da kowa ya yi bacci,duk da ta rage alwashin da ta dauka akan LTG domin taga duk tunaninta, LTG ya take ta ya shanye,ita yanzu tsoro ma yake bata,wani abun kamar akan idonshi takeyi hakan yasa ta watsar da mukaman ta,duk da haka Fu'ad be dena in gizata ba.duk da yaga yanzu ita ta karaya.wannan dalilin yasa ya sake sabon mugun shiri.

Daga LTG, Sudais, ACP Jawan duk busy ya musu yawa kullum karfe shida na safiya suke fita,su dawo tara ko goma LTG kam yana kaiwa har karfe daya wata rana ma baya kwana a gidan.aiki ya sha musu kai suna nan suna dakon shugaban kungiyar Italian Mafia,domin any moment ze iya yin abinda yace ze aikata.

Wannan dalilin ne yasa rabon da Sabriyah tasa LTG a idonta hatta manta domin yakai kusan sati biyu rabon da taga ko da gilmawarsa,sede tana yawan ganin major Marry.

Yau Friday tun 12:00 aka tashe su daga makaranta driver yazo ya maida su gida.suna shiga suka ga samarin gidan gaba daya cikin fararen shadda ɗinkin half jumfa bakaramin kyau sukayi ba,sun shirya zuwa masallaci tare da su Abbie da Abbu, uncle Hameed,suna zaune da alama akwai wanda suke jira ya fito.

Tunda suka shigo cikin falon Saghar da Asmita suke satan kallon junansu.uniform din jikinta da ta saka ne yau yasa ya ji kishi yakamasa ransa ya ɓaci ya rasa dalilin da yasa ranshi yabaci dan yaga Asmita da uniform din bayan kuma Sabriyah ma shine a jikinta amma be ji hakan ba,kuma su Rameesa ma makarantar sukayi amma be taɓa jin akwai wani abu dangane da uniform din ba se yau da ya gani a jikin Asmita.

Riga da wandon spot Wear ne wandon yana da fa ɗi,haka rigar ma yana da girma kadan da kauri,irin kayan yan kwallo,sun saka baby hijab.ga school back din su dake rataye a kafadarsu.

Kauda idonsa ya yi daga kanta ya fuske kamar be ganta ba.

Shigowa sukayi wajen su, suka gaishe su cikin girmamawa.

Murmushi Abbie ya yi "sannunku da dawuwa yan boko,kun sha gajiya kam"su ma murmushin suka yi, Asmita ta ce "Abbie ai ba wahala,kawai de zama"dariya sukayi.

ACP Jawan ya ce "to ai babu maraban dambe da faɗa" "tom wannan waya gaya maka Hausa ya ishe ta ɓalle ta san me kake nufi"cikin zolaya Sudais ya faɗi haka.

Shagwabe fuska ta yi "Abbie ka ga ya Sudais ko!?" "Kyaleshi kishi yake yi dan kina zuwa makaranta shi baya zuwa".dariya Sabriyah ta yi jin shirmen Asmita.ga Abbie ma da ya biye mata.

Duk yanda tasan zata yi Saghar ya kalleta ko za ta samu nutsuwa amma abun ya ƙi,tunda ya sunkuyar da kansa kasa yafara danna wayarsa be sa'ke dagowa ba.

Fitowa ya yi falon yana sanye cikin farar danyen shadda half jumfa ,me tsadar gaske,an yi mishi aiki na alfarma,yana sanye da bak'ar takalmi,ga Rolex wrist watch daure a hannunsa.kan sa babu hula se gyararren bakin sumar kanshi da yasha gyara yana sheki da daukar ido.ga baƙin tsadadden sun glass manne a fuskarsa,ya ƙara ƙawatar da fuskar.

Ya yi kyau sosai me matukar nutsuwa da daukan hankali,duk yanda ka kai ga kamewa,idan ka masa kallo ɗaya se ka ji sha'awar sa'ke daura ido a kan sa,ga daddadar Kamshin turaren dake tashi a jikinsa.

Tunda ya shigo falon Sabriyah ta kasa dauke ido akansa,bata taɓa ganin sa da manyan kaya ba se yau,se ta ga manyan kayan ma sunfi mishi kyau da karban sa.

"Tajuddeen manyan kaya suna maka kyau sede bakason sawa"Abbie ya faɗa yana dafa shi.

Kallon Abbie ya yi be ce komai.

Haɗa ido ya yi da Sabriyah dake satan kallon sa, harara ya watsa mata.

Tabe baki ta yi,magana kawai ta yi.ba tare da kowa ya ji ba iya labban bakinta ne yake motsawa yanda iya LTG ne ze ganta ta ce.

"Ko kyau bakayi ba,ka dena wani yanga,kanajin kanka na wani girma".

Hannunsa yasaka a wuyansa ya mata alamar se na yanka ki.

Dariya ma yabata.yanda ya mata alama da ze yankata ne abin yasata dariya.

Tana dariya ta ce"to se kun dawo Allah ya kiyaye hanya, Abbie, Abbu, daddy,amana addu'a " "in sha Allah "suna bata amsa ta haura part din su Asmita ma tabi bayan ta.

Abbie da Sudais su kadai ne suka lura da abinda LTG da Sabriyah sukayi,su kansu abin nasu ma dariya ya basu, wato tsakanin LTG da Sabriyah babu shiri.

Ko wannensu motarsa ya shiga driver yaja su , sojoji da kuma da polisawa da securities ne suka musu taki har masallacin.

Suna shiga dakinsu suka tarar da su parsa a ciki,suna taɗi, hiran wani saurayin da Zoya ta yi jiya sukeyi,suna dariya.

Ɗago kai sukayi dukkansu, dama zaman jiran dawuwar su, sukeyi su basu labari.

Cikin dariyar mugunta Rameesa ta soma cewa "gwara da Allah yasa kuka dawo yanzu" cire hijab din kanta Sabriyah ta yi,dama bata saka hula ta ciki ba gashin kanta baki wuluk na daure da ribbom babba ja.

Ta ce"ai ke Rameesa in an ga kina irin wannan yar iskar dariyar taki tofa abun mugunta ne ya samu"sa'ke tuntsirewa ta yi da dariya.

"Dadina da ke Sabriyah akwai ki da gane abu.kinsan jiya Zoya da iklas sun je gidan ya Abbas,to wai su iyayen kinibibi suka fita siyan abu waje,a hanyar dawuwar su ne suka haɗu da wani wai yana son Zoya.nan ya fara cika su da surutu kamar wani aku.Sau uku suna ce mishi zasu tafi amma yana dakatar dasu,har ya kure hakurin Zoya,kin san mutumiyar taki,nan fa ta mishi tas bata raga masa ba!"dariya Asmita da Sabriyah suka kwashe harda tafawa.

Asmita dake cire safar ƙafarta ta ce"haba ke kuwa Zoya,kin yi saurayi amma shine zaki kora shi da masifarki".galla mata harara ta yi,"ku fa baku da hankali. dan de baku gansa bane Wallahi kamar wani ɗan shaye_shaye".

Haka suka ta hirarsu,suna shan dariya, Zoya har kwatanta musu yanda saurayin yake magana yana wani buɗe ƙafadata kamar wani boss take yi,su kuma suna kallonta kamar sun samu Tv suna dariya.

Daga masallaci ACP Jawan station ya wuce saboda kiran da DPO yake masa ya wuce misali.jikinsa ne ya bashi akwai abinda yake faruwa,shisa ana idar da sallah ya wuce direct station.

Yana shiga yaga yan sanda se shige da fice suke yi.

Yana shigowa suka sara mishi.

Office dinsa ya wuce ya samu waje ya zauna.shigowa DPO ya yi da tarin files a hannunsa da a ƙalla zasu kai guda goma zuwa sha wani abu.

Sara mishi DPO ya yi kafin ya fara magana "ACP!yau tunda garin Allah ya waye muke ta karban cases din kidnapping,i zuwa yanzu an yi kidnapping mutane sama da goma.shisa nake ta kiran ka,this is getting out of hand ACP".Shuru Jawan ya yi yana wani tunani,inde tunanin sa ya bashi dede to wannan aikin Italian Mafia ne.

Kallon DPO,ACP Jawan ya yi kafin ya ce"have a sit"zama ya yi yana"thank you sir ".

Danna kira ACP Jawan ya yi ya kira, commissioner a waya suka yi magana ya sanar dashi halin da ake ciki.

Suna cikin yin magana,wata mata ta shigo station din tana kuka haɗe da kururuwa.ta cika station din da kuka.

Tambayarta kurtun yan sandan sukayi nan take sanar musu da yaranta mata guda biyu da ta mallaka a duniya an yi garkuwa dasu.

Da sauri wani dan sanda ya shigo office din ya sanar dasu.

Fitowa suka yi ACP Jawan ya taimakawa yar dattijuwar ta mike ya zaunar da ita akan kujera yana lallashinta,da bata karfin guiwar cewa da yardar Ubangiji za'a ga yaranta.

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*

Page 28,29,&30

*_Story & written_*



By

*MRS🌹ISHAM🌹*

( Yar lelen Jarumai)

📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️

Three in one

Page 28,29&30

Rubuta report matar ta yi sannan ACP Jawan ya bada umarni aka mayar da ita har gidan ta.

Da haka shima ya koma gida bayan yasa yan sanda sun fara binciken yaran da aka sace.

Karfe 5:00 dede ya iso gida polisawa suka bude masa kofa,yana fitowa suka sara mishi fara tafiya ya yi suka yi kokarin mara masa baya hannu kawai ya daga musu, dakatawa sukayi suna "Yes sir".

Ko part din sa be shiga ba ya wuce na LTG nan ya samu baya nan,ga shi tun yana office ya ke kiransa be yi picking ba,dama LTG haka yake in ba wai shi ya kiraka ba tofa in ka kirasa ma,abanza domin baya daga kira se in ya zama urgent and important.

Koma wa nashi part din ya yi,wanka ya fara yi sannan ya sauya zuwa ƙananan kaya. ACP Jawan da LTG suna tsananin kama da juna sede abinda ya bambanta su shine, kwayar idonsu ya sha bambam dana juna LTG nasa golding eye balls wato Hazel eye balls,which is the combination of green, brown,gold.yake dashi wanda ya gado a wajen kakar su Ammi da anty amarya,hatta farinsa ma irin na turawa ne da kuma sumar kanshi,while ACP Jawan nashi kwarya idon sa brown ne shida Umaisha.

"Me yasa ke dakikiya ce kam Naziya!?,ke kullum a ce bazaki nutsu ki san ciwon kan ki ba!?,to ko mutuwa zakiyi se kinzo Maiduguri kuma bazan taɓa canza abinda na yi niya ba,gwara ma ki rufawa kan ki asiri ki zo ki dangwali arziki ki barsa a inda yake,in kika auri Tajuddeen ai ba ma mu kadai ba,gaba daya danginmu sun warke,amma tsabar doloncin da ke damun ki,kin ƙi nutsuwa ki bani haɗin kai.to na riga da na gama magana ta gobe_goben nan za ki ta ho.saura kuma ki zo ki dinga nunawa mutane wannan shegen sanyin halin naki"ita de tunda antyn nata ta fara magana kawai jinta take yi amma ita ko kadan bata son zuwa musamman ma da tasan manufar da ake son amfani da zuwan nata.ita ta riga da tasani ko mutuwa zatayi tasan bata ishi LTG kallo ba ɓalle har ya ce ze aure ta shisa ta ke ajiye kan ta inda Allah ya ajiye ta,ko zuwa Maiduguri ma sau biyu kawai ta taba zuwa.

Cikin sanyi murya irin na ta,ta soma magana.

"Anty khareema da kinyi hakuri da wannan burin na ki,ni takura min kikeyi,tun ba yau ba,kinsha min wannan maganar amma na nuna miki banida wannan ra'ayin.mijin da zan aura har gida ze zo ya sameni in sha Allah,amma kin dauki buri da son abin duniya kin daurawa kan ki.ki ji tsoron Allah anty khareema.ni de bazan zo abanza ki dinga ja min wulakanci ba".

Cike da Masifa da ya rufe mata ido ta ce"kam uban can dan uwarki Naziya Ni ki ke cewa in ji tsoron Allah?,in ban ji tsoron Allah ba tsoron ki zanji,yar iska bagidajiya,kar ki ga dan kina kanwata kice zaki faɗa min maganar banza in kyale ki,yar karamar ƴata ita ce sa'ar ki!,amma saboda reni ya shiga tsakanina dake har ina magana kina bani amsa ko Naziya???".ya mutsa fuska ta yi kamar tana gaban Ammuh din.

A hankali ta ce"ai dama ita gaskiya ɗaci gareta,to nide banaso babu yanda za'a yi in yarda kiyi mini dole akan wanda baya sona baya ra'ayina, shine kawai anty khareema".

Ummah dake gefen Ammuh suna saurarar abinda ta ke faɗa, domin wayar na a handsfree.

Ta mata alama da ta danne fushinta, ta lallaba Naziya din wuyarta tazo ne ai.

"Shikenan yar kanwata yanzu de mu bar maganar Tajuddeen ki shirya gobe ki zo ki kawo min ziyara".

"Ni fa anty khareema na san halinki kawai de wayo kike son ki min, Wallahi in na zo bazan wuce sati daya ba zan dawo,taraba!".

Haɗiye bakin cikin da ya tokare mata wuya ta yi, saboda inde ta ce zata tsaya suna sa'insa da Naziya tasan ba zuwa zatayi ba.

"Shikenan na amince yanzu zan tura miki 100k a account din ki,ki biya kudin motar".

Tabe baki ta

29 / 33